Amsoshi

 

Daga


 


Ibrahim Abdullahi Sarkin Sudan (Ph. D)


Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya,


Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.


e-mail: kontago2003@yahoo.co.uk


GSM: 08096266581/08036153050


 

GABATARWA


Kowace al’umma ta duniya tana da hanyoyi na musamman da take bi wajen gudanar da wasu al’adu nata da suka shafi zamantakewa na rayuwa. Irin wad’annan al’adu sukan bambanta da na wasu saboda wad’ansu tanade-tanade da al’umar ta samar wa kanta. Daga cikin irin wad’annan al’adu akwai matsayin mace da hanyoyin da za a bi wajen mallakar ta ga namiji a matsayin matar aure. A yawancin al’umomi na duniya, akan ba lamarin auren budurwa muhimmanci fiye da wadda ta ta’ba yin aure. Yawancin nazarce- nazarcen al’adu dangane da aure, sun fi mayar da hankali a kan wannan.

 

Mak’asudin wannan nazari shi ne a k’ok’arta duban irin tanade-tanaden da al’adar Maguzawa ta yi wa auren wadda ba budurwa. Wannan ba zai rasa nasaba da cike gi’bin da aka bari da yake, magabata sun fi mayar da hankalinsu ga duban irin kwaramniyar da ake yi a auren saurayi da budurwa. Sun sha’afa da cewa, kasancewar mace bazawara ba abin k’yama ba ce a al’uma tun da har akwai wani tanadi da aka yi mata. Haka kuma an yi tunanin karkata ga Maguzawa[i] ne saboda tunanin cewa, mutane ne da suke rik’e da al’adunsu sau da k’afa, kuma daga garesu ne ake ganin al’adun Hausawa na gargajiya suka tuzgo.

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/falsafar-daurin-auren-maguzawa/

2.0       FASHIN BAK’I


Bazawara ita ce matar da ta ta’ba zama a k’ark’ashin namiji a matsayin matar aure. Daga baya wani dalili ya sa ta wayi gari ba a cikin wannan yanayi na aure ba. Tun daga wannan lokacin da ta rabu da mijin har zuwa lokacin da ta yi wani auren ko ta koma wa mijinta, ana kiran ta Bazawara ko Zawara. Jam’i kuma a ce Zawarawa.  Yanayin da Bazawara ke shiga na fafutikar jan hankalin namiji ko jiran namiji ya fito neman aurenta shi Hausawa ke kira Zawarci. Akan kira namiji mai neman Bazawara musamman wanda ya ta’ba yin aure da Bazawari, (Bazawarin wance). Haka ma akan ce, “Wane shi ke zawarcin Wance,” idan aka ga yana hidimar neman Bazawara da aure. Akan bayyana dad’ewar mutuwar auren mace ba tare da yin wani auren ba ta kiranta tsohuwar Bazawara.

 

  • SHARU’D’DAN ZAMA BAZAWARA A MAGUZANCE


Mutuwar aure ita ke sa a kira matar da abin ya shafa bazawara. To sai dai hanyar da akan bi auren ya mutu ba d’aya ba ce. Akwai fuskoki biyar a maguzance da ke iya sa mace ta tsinci kanta cikin halin zawarci. Wad’annan hanyoyi har wa yau su ke sa Bazawara ta siffantu da halaye ko d’abi’u na musamman da suka bambanta da na budurwa.

 

3.1       Miji ya saki mace


A lokacin da ake zamantakewa na aure, akan sami sa’bani iri-iri tsakanin ma’aurata. Idan rayuwar aure ta kai k’arshe, miji ya fahimci ba zai iya ci gaba da zama da mace a matsayin mata ba, to yakan sallame ta, ta hanyar nuna mata ya gaji da auren, ta kama gabanta. Galibi akan kai ga wannan mataki ne bayan an bi hanyoyi da dama na sulhunta ma’auratan abin ya faskara. Tun daga ranar da miji ya ambaci ba ya bukatar zaman shi da mace a matsayin mata to ta zama bazawara.

 

3.2       Mace ta kashe aure


A al’adar Maguzawa, mace tana da ’yancin da za ta rabu da miji, ta bar gidansa idan ta fahimci ba ta son ci gaba da auren. Ita ma a wasu lokuta, kafin ta kai ga wannan matakin za ta nemi magabata su ja hankalin miji a kan wasu d’abi’u nasa da take ganin sun sa’ba wa zamantakewa ta aure. Haka kuma yanke wannan shawara zai iya zama sakamako ne na auren tilas da aka yi mata.  Idan ga misali ta fahimci wad’anda suka tilasta mata yin auren sun kau, kuma har zuwa wannan lokacin ba ta sha’awar ci gaba da zaman auren, to sai ta bar gidan mijin. Takan koma gidan iyayenta ko kuma gidan wasu ’yan’uwa nata ko  ta tare gidan wanda take so, daga baya a tabbatar masa da ita a matsayin mata bayan an bi wasu k’a’idoji da al’ada ta shimfid’a.

 

3.3       Mutuwar miji


Ba ga Maguzawa kad’ai ba, a yawancin al’ummomi idan mace ta rasa miji ta hanyar mutuwa, ta zama bazawara kai tsaye. Sai dai a al’adar Maguzawa, irin wannan mata ba za ta fara zawarci ba sai bayan wani lokaci na musamman da al’ada ta shata. Haka kuma sai ta gudanar da wasu al’adu da za su nuna wa jama’a cewa, tana zawarci.

 

3.4       Iyaye su raba aure


A al’adance, iyaye ko magabata daga ‘bangaren miji ko matar aure su ke sasanta rikici tsakanin ma’aurata. Su ake kai wa koke su bi bahasi don sasantawa. A lokacin da iyaye suka kasa yin haka saboda sark’ak’iyar lamarin, sai a d’auki matakin raba auren. Haka kuma idan bayan an yi aure, sai miji ko mata suka tsiri wasu halaye da suka sa’ba wa hankali, to iyaye ko magabata suna iya raba auren. Irin wad’annan halaye sun had’a da duk wani abin kunya da za su sa mutum yin da-na sani kamar sata ko kwartanci ko a kama matar aure tana lalata da wani da dai sauran su. Idan auren mace ya mutu ta hanyar yanke shawara daga iyaye na raba aure to ta zama bazawara kuma ta shiga yanayin zawarci tun daga wannan lokacin.

 

3.5       ‘Bacewar miji


A lokaci da miji ya bar gida na lokaci mai tsawo (shekaru), matarsa ko matansa za su ci gaba da zama da tunanin yana raye kuma zai bayyana wata rana. Tsawaitar wannan rashi yakan sa magabata su warware aure musamman ga matar da ke da sauran k’uruciya ko sha’awar kasancewa da namiji.  Galibi iyayen mace su kan fara tuntu’bar iyayen namiji tare da amincewar matar. Tsoron kada ’yar su ta shiga wani hali na ‘batanci ta ja musu abin kunya shi kan sa su fara bayar da shawarar raba auren. Daga lokacin da magabata suka yanke shawarar raba irin wannan aure, to ta zama bazawara, kuma ta fara zawarci.

 

  • BAYYANAR DA ZAWARCI


A wasu lokuta abu ne mawuyaci siffan jikin mace ya iya bayyanar da kasancewar ta bazawara. Hakan na iya faruwa ne saboda ko da a makon da budurwa ta tare gida miji suka rabu, ta zama bazawara. A irin wannan yanayin, halayenta ko d’abi’unta da yadda take mu’amala da mutane musamman maza su ke nuna cewa bazawara ce. Haka kuma al’ada takan haramta mata gudanar da wasu lamurra kamar gad’a a dandali da sauran sharholiyar da ’yanmata ko budare ke aiwatarwa. Hatta da yanayin irin mazan da za a ga bazawara tana mu’amala da su sukan bambanta da na budurwa.

 

 4.1 Huld’a da Maza


Bazawara takan saki fuska ga maza idan ta kusance su. Irin wannan sakin fuska ko kad’an ba za a same shi ga matar aure ba. Takan rik’a fara’a da ba’a da kuma son tsayawa a yi zance da maza ba lallai sai da dare ba. Ta haka akan fahimci bazawara ce musamman ga wad’anda ba su san ta ba ko ba k’auye d’aya suke ba.

 

4.2 Cin Kasuwa


Bazawara a muhallin Maguzawa takan yawauta cin kasuwa ko da ba ta zo sayar da komai ko sayen komai ba.  Dalili a nan shi ne, a ranakun kasuwa ne maza ke taruwa don saye ko sayar da abin da suka kawo kasuwan. Ga wanda ya sayar da wani abu, yana da ’yan kud’in da zai yi toshi ga bazawarar da ya gani ya nuna yana so. Ga bazawarar, wata dama ce da za ta had’u da maza iri-iri da suka taru don cin kasuwa. A irin wannan wuri, ta la’akari da irin damar da aka ba ta na mu’amala ko sayar da wani abu, akan gane cewa bazawara ce.

 

4.3 Samun abin sayarwa


Zawarawa sukan tsiri yin ’yan sana’o’i musamman na k’walama. Wannan kan sa maza su rik’a matsowa kusa da ita har su fahimci bazawara ce ta hanyar kalamanta ko d’abi’unta na ba’a da sakin fuska. Takan fahimci ra’ayin namiji gareta ne idan ya yawaita sayen abin da take sayarwa.

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/bukin-hawan-sadaka-na-maguzawa/

5.0       MATAKAN AUREN BAZAWARA


Had’uwa tsakani wanda ke son aure da wadda ake so shi ne mataki na farko na k’ulla irin wannan auren. A wurin gudanar da sha’anonin rayuwa a ko’ina bazawara tana iya had’uwa da masoyi. Daga cikin muhimman wuraren da aka fi wannan had’uwar akwai kasuwa da wurin buki ko wani sha’ani na taruwar jama’a

 

Idan bazawara mai farin jini ce tana iya samun manema fiye da goma. Kowane daga cikinsu zai rink’a k’ok’arin samun abin da ya ba ta don jawo hankali. Wasu daga kasuwar nan za su yi mata cefane iri-iri ta komo gida. Idan bazawara na son mutum daga kasuwar nan tana iya bin shi zuwa gidansa. Tana ma iya yin kwana biyu ko uku tare da shi. Daga baya ta kawo shi wajen iyayenta.[ii]

 

Bazawara takan ba da dama a zo zance a gidansu. Idan manemi ya zo zance zai gai da iyayenta, ta shimfid’a masa tabarma su yi zance. Haka kuma, yana iya zuwa da rana. Sai dai galibi suna zuwa da ’yan rakiya saboda gudun rikici. A al’adar neman bazawara a maguzance, ba lalle ne sai iyayen manemin sun zo ba. Idan an ba shi baki, nan take iyayenta kan ce, “Ka gaya wa magabata su zo rana kaza a d’aura aure.” Kafin a kai ga d’aura aure, iyayenta za su tambaye ta inda ta samo bazawarin. Idan hankalinsu ya kwanta da shi, sai a ce mata ta gaya masa ya fito. Idan kuma ba su amince ba, za su ba ta shawara. Sai dai ba a tilasta mata. In ta k’i jin shawarar, ruwanta.

 

Idan ya kasance bazawara tana da manema da yawa, kuma ta kar’bi kud’i ko kayan da yawa daga cikinsu, to ranar da ta tsayar da d’aya, ranar shi wanda aka tsayar zai biya sauran. Haka kuma ranar zai ba ta kud’in sayayya. Wato ta tanadi ’yan kayan da za ta tare da su. Idan daga cikin manemanta akwai wanda ya ba ta wani abu ba a biya shi ba, to ba zai ce komai ba sai ranar d’aurin aure. Sai an fara shirye-shiryen d’aura aure abokansa za su ce, “Kada a d’aura, akwai kud’in Wane.” Za a tsayar da hidimar d’aurin auren a bincika. Idan an tabbatar da haka, to nan take angon ko danginsa za su biya ko a fasa d’aura auren sai ranar da aka biya shi.

 

A auren bazawara ba a yi wasu hidimomi kamar yadda ake yi a auren budurwa. Illa dangin amarya da na ango kawai za su halarta, sai kuma wad’ansu mak’wabta da wad’anda ke kusa. Dangane da kayan d’aurin aure, akan zo da toshin uwa da uba da kud’in ajiya da dukiyar aure. Haka ma bayan d’aurin auren, bazawara tana iya tarewa kai tsaye. Wasu akan sami mata su yi mata rakiya zuwa gidan miji ta ci gaba da zaman aure.

 

Bazawara ita ma takan yi auren kissa musamman idan ta ci kud’in mutane da yawa a lokacin da take zawarci. Sukan shirya da wannda take so idan ba zai iya biyan kud’in ba. Sai ya ce ta yi auren bayan kwana biyu ta tabbatar da ya more ta dawo masa.

 

6.0       HUKUNCE- HUKUNCEN AUREN BAZAWARA A MAGUZANCE


Maguzawa suna da hukunce-hukuncen da suka tanadar dangane da abubuwan da kan biyo mutuwar auren mace da sake yin wani auren. Wad’annan k’a’idoji sun danganta ne da yanayin rabuwar auren. Haka kuma akwai tanade-tanaden da aka yi dangane da tsohon miji ko dukiyar aurensa a lokacin da tsohuwar matarsa ta kashe auren kuma ta tashi yin wani auren.

6.1 K’ayyade lokacin sake aure


A maguzance babu Idda.[iii] Hausawa sun sami wannan tsari ne bayan da suka kar’bi addinin musulunci. A al’adar Maguzawa, idan auren mace ya mutu, tana iya k’ulla wani auren a kowane lokaci ta ga dama. Wato babu wani k’ayyadadjen lokaci da za ta d’auka  ko dai tana jiran ta fara zawarci, ko tana zawarci kafin ta yi wani auren. Ba a la’akari da cewa auren mace na iya mutuwa da shigar cikin tsohon miji. idan bazawara ta yi aure da cikin tsohon miji, abin da aka Haifa na sabon mijin ne.

 

6.2 Sauya Miji


Bamagujiya tana da ikon in ta ji ba ta son mijinta, ta bar gidansa ta koma gidan wanda take so. Illa daga baya a zo a sasanta da tsohon miji dangane da abin da za a mayar masa na dukiyar aure. Idan sabon mijin ya kasa biyan dukiyar auren da tsohon miji ya yanke to dole ta hak’ura ta koma gidansa. Idan ya kasance mace tana da cikin tsohon miji, ta koma gidan sabon miji ta haihu, to abin da aka haifa ya zama mallakar sabon miji.

 

6.3 Kome   


Kome yana nufin mace ta koma gidan tsohon mijinta bayan aurenta ya mutu. Irin wannan lamari yana faruwa ne bayan mace ta rabu da mijin farko, ta yi wani auren, sai ta fahimci ba ta gamsu da mijin na biyu ba. A irin haka ta ga damar ta koma ga mijinta na farko kai tsaye ba tare da wani sharad’i ba. Sai dai sabon mijin ya hak’ura. Haka kuma idan ya kasance mace ta yi wani auren ne bisa dalilin ‘bacewar mijinta na farko, sai aka wayi gari ya dawo, to tana iya koma wa mijin na farko ba da wani sharad’i ba. An nuna wasu matan sukan koma gidan tsohon mijinsu ne saboda halin da ’ya’yan da ta bari kan kasance.

 

6.4 Auren Matar Mamaci


Matan da Bamaguje ya mutu ya bari sukan shiga takaba ne a ranar da aka share makoki, wato kwanaki bakwai da mutuwarsa. Ita dai takaba ga maguzawa, zama ne na kad’aici da haramcin yin aikace-aikace ko mu’amala da mutane kamar yadda aka saba na wani k’ayyadadjen lokaci da mace kan yi bayan miji ya nutu. Adadin watannin da matar mamaci takan kasance cikin takaba sukan bambanta daga wuri zuwa wuri. Ga misali, Maguzawan Lezumawa  wata biyar sukan yi, kamar yadda su ma na K’wank’i suke yi. Maguzawan K’wank’i sukan yi wa takabar lak’abi da shiga biyar, (idan za a shiga), ko wanke biyar (idan lokacin fita ya yi). Maguzawan Gidan Bakwai wata shida suke yi.

 

Bayan matan mamaci sun fita takaba, idan akwai masu sauran k’arfi ko sha’awar yin aure daga cikinsu, nan take sukan fara zawarci. To sai dai irin wannan zawarci yana da k’a’idoji da yawa. Daga cikin wad’annan k’a’idoji, ’yan’uwan mijinta da ya mutu su ke da alhakin d’aura wa mace aure. Don haka sai wanda suka ga ya dace. Ko da masoya suna da yawa, sai wanda suka yi shawara suka ga ya cancanta ya auri matar ubansu ko d’an’uwansu. Haka ma ko da ta aminta tana son bazawari, in su ba su amince ta aure shi ba, ba yadda za a yi wannan auren, dole ta hak’ura. Iyayen mace na ainihi ba su da damar su sa baki. Idan dangin mamaci suka bayar da auren matar da ya bari, sai aka wayi gari ta fito daga gidan wannan mijin, to duk wani lamari nata ya koma ga iyayenta ko danginta na jini. A wannan lokacin ba ruwan dangin mijinta da ya mutu wajen tsoma hannu ko sa baki a auren da za ta k’ara yi.

 

Dangane da mijin da matar mamaci za ta aura bayan ta k’are takaba, ba a yarda mutumin da ya had’a jini da shi (mamacin), ko mak’wabci ko wani amininsa ya aure ta ba. Hakan na faruwa ne wai saboda kunya da girmamawa ga mamacin. To sai dai an yarda dangin mamacin su nemo wani can wanda suka aminta da shi, su ce ya aure ta musamman don ya kula musu da k’ananan ’ya’yanta idan akwai su. Haka kuma suna iya had’a wannan aure don su sami wanda zai kare mutuncinta ba wanda zai wulak’antar da ita ba a matsayinta na matar uba, ko matar d’an’uwansu. Idan aka dace da mijin, to za a d’aura auren ne a k’ofar gidan mijinta da ya mutu. A nan za a yi duk al’adun da auren bazawara ya tanada. Haka ma daga nan za a d’auke ta zuwa gidan sabon mijin.

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/budurcin-maguzawa-faifan-nazari-darussa-ga-hausawan-zamani/

 

7.0       KAMMALAWA


Wannan nazari ya tabbatar muna da wasu al’adu da hukunce-hukunce na musamman da suka shafi zawarci da auren Bazawara a tunanin Maguzawa. Muhimmin abin lura da wad’annan al’adu shi ne damar da suka ba matan da suka fad’o a wannan rukuni na darjewa su za’bi abin da suka ga ya dace da su musamman da yake ana ganin sun d’and’ana rayuwar aure, sun san dad’insa da d’acinsa. Haka kuma wasu daga cikin wad’annan al’adu na auren bazawara, tamkar wata hanya ce na samar wa mace gata da kyakkyawar rayuwa sa’banin inda ta fito, ko d’orewar ingantacciyar rayuwa ga matar mamaci da abin da ya bari. Hak’ik’a wannan nazari wani haske ne manazarta na ganin irin sa’banin da ake samu na tunanin d’an Adam a kan sha’anin zamantakewa musamman idan an kwatanta da abin da aka wayi gari ana gudanarwa a alumar Hausawa a yanzu.

 

 

8.0       MANAZARTA


Abdullahi, M.  (1997), “Yanayi da Tsarin Al’adun Aure a Birnin Kebbi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato.

 

Abu, M. (1985) “Al’adun Aure da Canje-canjensu a Katsina,” Kundin Digirin farko (B.A. Hausa),  Jami’ar Sakkwato.

 

Adamu, M.  (1976), “The Spread of Hausa Culture in West Africa 1700 – 1900” Savanna No 5 Vol. 1, A  Journal of the Environmental and Social Sciences.  Published at  Ahmadu Bello University, Zaria.

 

Adamu, M.  (1977) “The Economics of Culture Among The Hausa during the Present Millenium A. D.” Culture Seminar Ahmadu Bello University, Zaria.

 

Akodu, A. (2001), Arts and Crafts of the Maguzawa and some Educational Implications. Gaskiya Corporation Limited. Zariya – Nigeria.

 

Alhassan, H. da Sauransu (1982), Zaman Hausawa (Babu Mad’aba’a).

 

Anchau, M. D. (1986), “Tasirin Zamani Da Illolinsu Kan Al’adun Auren Hausawa A Lardin Zazzau, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Sakkwato.

 

Fletcher, D. C. (1929) “The Kai-na-Fara.” Extract from Re-assessment  Report on ’Yand’aka District, Katsina Emirate, Zaria Province. M. P. No K. 8833 National Archives and Monuments, Kaduna.

 

Furniss, G. (1999), Poetry, Prose and Popular Culture in Hausa, Edinburgh University Press, London.

 

Gennep, A. V. (1960) The Rites of Passage The University of Chicago Press, USA.

 

Greenberg,  J. (1946) The Influence of Islam on a Sudanese Religion: Monographs of the American Ethnological Society. J. J. Augustin Publisher, New York.

 

Gwarjo, Y. T. da  wasu  (2005)  Aure a Jihar Katsina Hukumar BincikenTarihi Da Kyautata Al’adu ta Jihar Katsina, Hausa Vocabulary, Oxford University press, London

 

Ibrahim, M. S. (1982), “Dangantakar Al’adu da Addini: Tasirin Musulunci Kan Rayuwar Hausawa”, Kundin Digiri na Biyu (M.A. Hausa), Jami’ar Bayero, Kano.

 

Ibrahim, M. S. (1985), Auren Hausawa: Gargajiya Da Musulunci, Cyclostyled Edition – Hausa Publications Centre – Zaria.

 

Kado, A. A. (1987), “Kainafara Arnan Birchi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Sakkwato.

 

Krusius, P. (1915), “Maguzawa” in: Archiu, Anthropologies, NF Vol. XIV.

 

Lawal, A. T. (1986), “Al’adun Hausawa Jiya da Yau”, Kundin Digirin farko (B. A. Hausa) Jami’ar Sakkwato.

 

Madauci  I. da  wasu (1968) Hausa  customs Northern Nigerian Publishing Company, Zaria.

 

Magaji, A. (2002) “Wasu Al’adun Hausawa: Yanaye- yanayensu a K’asar Katsina.” Kundin digiri na uku (Ph.D Hausa) Ja’mi’ar Bayero, Kano.

 

Maikano, M. M. (2002), Maguzawan Yari Bori: Tarihinsu Da Al’adunsu”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

 

Malumfashi, A. A. (1987) “Hausa Language Speech Usage Norms: A Case Study of Maguzawa Society in Malumfashi Area” (B. A. Hausa Project), Bayero University, Kano.

 

Mashi, B. U. (2001), “Maguzanci Da Zamananci: Nazari A Kan Al’adun Maguzawan ‘Bula A Gundumar Mashi”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

 

Morel, E. D. (1968), Nigeria Its Peoples and Problems, Frank Cass and Company Limited London.

 

Nyamwaya, D. and Parkin, D. (1987) Transformation of African Marriage. Manchester

University Press, United Kingdom.

 

Ottenberg, P. and Simon (Ed.) (1960), Cultures and Ethics of Africa, H. Wolff Book Mfg.Co., Inc. U.S.A.

 

Robinson, D. (2004) Muslim Society in African History  Cambridge

 

Safana, Y. B. (2001), “Maguzawan Lezumawa (Babban Kada) Gundumar Safana”, Kundin Digiri na farko (B.A. Hausa), Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

 

Saulawa, I. A. (1986), “Yanayi da Tsarin Al’adun Aure A K’asar Katsina”. Kundin Digirin farko (B.A. Hausa), Jami’ar Sakkwato.

 

 

Sufi, A. H. (2001) “Hanyar Kiran Maguzawa Zuwa Ga Addinin Musulunci.” Mak’alar  da aka gabatar  a  taron Kwamitin Yad’a Addinin Musulunci na Jihar  Kano.

 

Temple, C. L. (ed.) (1965), Notes on the Tribes, Provinces, Emirates and States of the of the Northern Nigeria, Frank Cass and Company Limited London.

 

Tremearne, A. J.  N. (1913) Hausa Superstitions And Customs.  John Bale, Sons and Danielsson,  LTD Oxford.University Press United Kingdom.

 

Yusuf, A. B. (1986), “Wasannin Maguzawan K’asar Katsina”, Kundin Digirin farko, Jami’ar Sakkwato.

 

[i] Maguzawa su ne Hausawan da ba Musulmi ba kuma addininsu da al’adunsu na gargajiya  sun yi tasiri a

kansu.

[ii] I rin wannan ba a tsammanin saduwa a tsakanin su. Takan yi haka ne kawai don ta tabbatar masa tana son shi.

[iii] Idda na nufin mace ta yi tsarki na wani lokaci bayan mutuwar aurenta, kafin ta yi wani auren. Wannan

umurni ne na addinin Musulunci