Ticker

6/recent/ticker-posts

Maguzantattun Karin Maganar Hausa


Karin magana na  d’aya  daga cikin sassan adabin Hausa da ke  taskace  tantagaryar rayuwar Bahaushe. Wannan  ya  sa  da  wuya  a nemi  wani ‘bangare  na  rayuwar Hausawa a gargajiyance  a rasa  shi  cikin karin maganar su. Ke  nan, karin magana kandami ne da  ake iya  lek’awa don ganin rayuwar Hausawa ta  gargajiya  da  ma  wadda  take  da  tasirin had’uwarsa  da wasu  al’ummun duniya. A tak’aice  kafin  had’uwar Hausawa da wasu  bak’in al’ummu, suna gudanar da rayuwarsu ne ta hanyar amfani da  tunani  da kuma imaninsu  na gargajiya wanda suka  gada iyaye da kakanni.


ALAMUNA NUHU

Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe
Jami’ar Jihar Kaduna
Kaduna, Nijeriya.
Alamunan@gmail.com
08030472882

Mak’alar da aka  gabatar a taron k’ara wa juna sani na k’asa da k’asa na farko a kan Nazarin Hausa a K’arni na 21 wanda Sashen Koyar  da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano, ta shirya  daga ranar Litinin 10 zuwa Alhamis 13 ga Nuwamba, 2014. GABATARWA

Karin magana na  d’aya  daga cikin sassan adabin Hausa da ke  taskace  tantagaryar rayuwar Bahaushe. Wannan  ya  sa  da  wuya  a nemi  wani ‘bangare  na  rayuwar Hausawa a gargajiyance  a rasa  shi  cikin karin maganar su. Ke  nan, karin magana kandami ne da  ake iya  lek’awa don ganin rayuwar Hausawa ta  gargajiya  da  ma  wadda  take  da  tasirin had’uwarsa  da wasu  al’ummun duniya. A tak’aice  kafin  had’uwar Hausawa da wasu  bak’in al’ummu, suna gudanar da rayuwarsu ne ta hanyar amfani da  tunani  da kuma imaninsu  na gargajiya wanda suka  gada iyaye da kakanni.

Wannan mak’ala ta  k’udiri aniyar waiwayen hoton Maguzanci  cikin karin maganar Hausawa domin ta  fito  da imani  da  tunanin Hausawa a gargajiyance. Yin haka zai tabbatar da cewa,  karin maganar Hausa  ba, ta bar wannan rayuwa  ba.  Ta taskace su ta hanyar  fitowa da yanayin rayuwar da  ta gabata dangane  da imanin Hausawa a gargajiyance kafin su sami  saukakken addini. K’ok’arin  wannan muk’ala a nan shi  ne  ta  nuna  wasu rukuni na karin magana masu nuna imanin Hausawa dangane da halayensu, da  d’abi’unsu da abin bautarsu na gargajiya.

TUBALAN TAKE

Wannan fasali zai  yi k’ok’arin sharhi kan muhimman kalmomi  da suka gina taken wannan nazarin domin su yi  k’arin haske ga mai karatu. Kalmomin su  ne  Maguzanci  da  kuma Karin magana.


MAGUZANCI


Maguzanci  d’abi’a ce  ta Maguzawa. Su kuma Maguzawa su  ne Hausawan asali da ba  musulmi ba, wad’anda suka dogara rayuwarsu ga addininsu na gargajiya da al’adunsu da  suka sa’ba wa addinin musulunci (Sarkin Sudan 2008). Ta wata fuskar kuwa kalmar Maguzawa jam’i ne na kalmar Bamaguje (Namiji) ko Bamaguza/Bamagujiya (Mace).Saboda haka yanayin rayuwarsu wadda  ta   dogara  kan imani da tunani  na gargajiya  da  ya had’a  da addininsu  da  yanayin rayuwarsu na gargajiya, shi ne Maguzanci.
 • KARIN MAGANA
Wani sashe  ne na adabin baka da ake  amfani  da  shi  domin dunk’ule  zance  mai  yawa cikin tak’aitattun kalmomi wad’anda  idan aka  warware  su  sai  a  ga  cewa zance  ne  mai yawa aka  cure  wuri   guda. Karin magana na d’aya daga cikin wuraren da ake  ganin hoton rayuwar al’umma wad’anda aka  adana  a  cikin zantuka  na hikima masu buk’atar a san abin  da suka k’unsa. A tak’aice akan taskace  tarihin faruwar wasu abubuwa  cikin Karin magana don ta zama abin amfani  cikin zance  idan buk’atar hakan ta  taso  ga mai magana zuwa ga wani.

 • KARIN MAGANAR KALMAR MAGUZAWA KO BAMAGUJE KAI TSAYE

Akwai  karin maganar Hausawa wad’anda  suka zo da  kalmar Maguzawa ko Bamaguje kai tsaye tare  da  nuna  wani ‘bangare  na abin da  ake ce  wa Maguzawa. Ga misalin wasu karin maganganu masu d’auke  da kalmar Maguzawa ko Bamaguje:

 • Duk d’aya, mara sallah ya  je  gidan

 • Wata daban, an ce da Bamaguje Bamaguje.

 • Maganin Biri Karen Maguzawa.

 • Komai tuban Bamaguje ba  a ‘bare masa

A cikin karin magana ta farko  an ambaci Bamaguje kuma aka  nuna  cewa Bamaguje  ba  ma’abocin yin sallah ba ne. Karin magana ta biyu tana bayani ne cewa Maguzawa ba  sa son a kira su da sunan Bamaguje, sun fi so a kira su Hausawa. Idan kuwa aka kira su da sunan Bamaguje  suna ganin ba a yi komai ba. Karin magana ta uku nan ma an ambaci Maguzawa har aka kawo bayani da ke nuna su mafarauta ne.  Karin magana ta hud’u ita ma ta ambato Bamaguje kai tsaye, to sai dai ta  yi k’arin bayani cewa ko da Bamaguje ya tuba ba  ya son katsalandan cikin harkokinsa.

 • KARIN MAGANAR MAGUZANCI

Maguzanci wata hanyar  rayuwa ce da ta yi takun sak’a  da  rayuwa  irin ta  addinin musulunci. Maguzanci  ya  k’unshi  wasu  al’adu  masu  sa’bani  da  koyarwar musulunci (Sarkin Sudan, 2008). Ke nan akan sami karin magana wanda ake  sa ran  a  ciki a ga abubuwan da  suka  yi takun sak’a  da koyarwar musulunci  wad’anda kai tsaye Maguzanci  ne suke  dauk’e da  su.

Maguzanci  bai  tak’aita ga   yanayin abinci  ko abin sha  ba,  hanyar bauta  ta   gargajiya  tana  daga  abubuwan  da  Maguzawa suke  ba  muhimmanci  a rayuwarsu. Hanyoyin bauta  ga  Maguzawa sun  k’unshi  tsafi,  da bautar iskoki (bori) (Ibrahim 1982). A ‘bangaren hanyoyin bauta  ana  samun karin magana  wanda  yake  bayyana ainihin rayuwar ta Maguzawa. Misali:

 • Duk bori d’aya ake wa tsafi,

 • Duhu d’akin bori,

 • An huta bori  ya kashe  boka,

 • K’arya ta k’are bori  ya kashe boka.

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/zawarci-da-auren-bazawara-maguzance/

Wad’annan misalai  sun  nuna wani ‘bangare na addinin Maguzawa  wato bori da  tsafi a karin magana ta farko. Karin magana ta biyu kuwa ta nuna cewa bori a wajen Maguzawa yana da wuri na musamman da ake aiwatar da shi kuma cikin sirri. Su kuwa biyun k’arshe  suna nuna yadda addinin gargajiya ke d’auke  da  tsari wanda idan aka sa’ba  shi, za  a sami mummunan sakamako ba  da ‘bata  lokaci ba. Har ila yau bokanci shi ma d’abi’a ce ta Maguzawa wadda ta  shafi bayar da magunguna ta hanyar bori.

Tsafi  shi  ne  bin wasu hanyoyi  na gargajiya  musamman  yi wa iskoki  hidima, da  yanka, da bauta  domin biyan wata buk’ata  ko samun wani  amfani  ko tunkud’e wata  cuta (Bunza 2006). Ke nan tsafi yana  nufin yarda  da  hanyoyin bautar gargajiya  ta hanyar iskoki domin a sami  buk’ata   ta fuskar   cutarwa  ga wasu ko biyan buk’atar rayuwa. Idan  kuwa  haka  ne,  me  ke  ciki wad’annan karin maganganu?

 • Tsafi gaskiyar mai shi,

 • Ranar tsafi Bunsuru  ke kud’i,

 • Duk bori d’aya ake wa tsafi.
An kira  wad’annan karin maganganun Maguzantattu  ne saboda   tsafi  na d’aya daga cikin hanyoyin bauta  ta gargajiya  ga wanda   ya   yarda   da   ita.  Ga  masu  bin addinin gargajiya  na Hausa (Maguzanci) sun yarda  da tsafi. Wannan karin magana  ya   had’e bori  da  tsafi  wuri guda saboda suna  da  alak’a  ta kusa, wato dukkansu hanyoyi ne na amfani  da iskoki, da yi masu hidima domin neman biyan buk’ata. Tsafi ba  ya  yiwuwa  ba  tare  da  yin yanka ba. Daga cikin abubuwan  da  ake  yankawa wajen gudanar  da tsafe-tsafen Maguzawa  D’an’akuya  (Bunsuru) shi  ne kan ga’ba. D’an’akuya  ya  yi  tasiri  a tsafe-tsafen matakan rayuwar Maguzawa na aure, da haihuwa da mutuwa (Sarkin Sudan 2008).

Wani ‘bangare da  ya shafi hanyar bauta  a gargajiyance shi  ne imani da  Dodo. Bunza (2006) ya ce: “Dodo  a al’adar  Bahaushe  k’irk’irarren abu  ne da  ake  riyawa aka kuma yi  imani  da  samuwarsa. Ya k’ara da cewa Dodo ba isaka ba ne, kuma ba wani abin bauta ba  ne da  za a aje a yi bauta wurin da  al’ada  ta  aminta da samuwarsa”. To sai  dai  wannan nazari  ya fahinci cewa, Bahuashe ya yi imani da Dodo ne  tun gabanin zuwan Musulunci. Haka kuma dodo yana da kusanci da iska dangane da wasu ayyuka nashi.Wannan ya sa wasu karin maganar Hausa ke kawo ayyukansa, da  fahintar Hausawa kansa. Misali, ana samun karin maganar Hausa wad’anda dodo ya fito a cikinsu irin su:

 • Munafinci Dodo yakan ci mai shi

 • Mijin mai Dodo maganin wani kwarto
Manufar wad’annan karin magana ita  ce, dodo yana cin mutane. Haka kuma in dai  ba a  yin munafurci a fili, to shi  ma dodo  ‘boye shi ake yi  a wani ke’ba’b’ben wuri kamar yadda bori da  tsafi ke da nasu muhallai na gudanarwa. Baya ga haka, ana iya samun kyakkyawar fahinta  da  dodo ya  zama  ba  ya  cutarwa  ga  wanda  suka   yi aminci. Don  haka  ne  Bahaushe  ya k’irk’iri karin  magana  mai cewa:

 • Samun yarda ga Dodo ke  sa  a  shiga   ruwa gabagad’i

 • Ba a aminci da  Dodo  a  yi  fargabar shiga  daji
Wato dai akwai wasu wurare da ake sa ran cewa a nan Bahaushe ke ajiyar Dodo, ko kuma  nan ne ma’boyarsa. Har ila  yau, karin magana ta  biyu  na nuna cewa Dodo yana zaman luman da  mai shi, ko wani da  ke kusanci da Dodo yana  iya samun kariya a wasu lokuta. Wannan ya nuna cewa, amfani da irin wad’annan karin maganganu ‘bir’bishi ne na imanin gargajiya da aka yi a jiya yake bayyana  cikin zantukan Hausawa (Musulmi) a yau. Wannan imani na gargajiya kuwa, ba wani abu ba ne illa Maguzanci

 • KARIN MAGANA MAI HOTON LAFAZIN BAMAGUJE

A muhallin da Hausawa suke zaune da Maguzawa, akan gane su kai tsaye daga lafazinsu.  Irin wad’anan lafuzza suna nuna Maguzanci ne a cikin su ta yadda idan ba Bamaguje  ba, babu wanda zai  yi  irinsu. Misali.

 • Za a sami alheri a wannan  gona, Bamaguje  ya rufe jan Bunsuru a gonar dawa.

 • Allah ya yi Allan nasa, Bamaguje ya iske Biri  ya  mutu a gonarsa.

 • Ana zaman k’arya, Bamaguje ya  zo  gari  ya iske ba

A tak’aice,  bayanan da  ke  k’unshe cikin wad’annan karin magana suna  nuna Maguzanci ne. Dalili kuwa, Bamaguje  ne ke ta’ammali  da Bunsuru musamman a wajen tsafi. Haka kuma noma  yana daga cikin abin  da  ba  a raba  Maguzawa da  shi. Hasali  ma, noma babbar sana’a  ce  ga  Maguzawa wadda suka gada iyaye  da  kakanni. Ta hanyar noma ne Bamaguje yake  kaiwa  k’ololuwar shahara har  a yi masa bukin dubu. Batun tsintar mushen Biri a gona  ga  Bamaguje  kuwa tamkar kara ma Barno  dawaki  ne  domin nama  ne mai kyau  a gare shi. A wata   fuskar  kuwa sai a  ce  lallai  tsafinsa  na uwar gona  ne ya kama Biri a yayin da  ya  zo yi  masa ‘barna.

Idan kuwa ana  zancen noma  Maguzawa ba  baya ba, don haka ne ba  sa  iya  zama  wurin da  ba  zai  ba su  damar  yin noma ba wanda da  shi  ne  rayuwarsu  ta dogara. Kenan a wajen Maguzawa, zama wurin da ba  a yin sussuka  zama  ne marar amfani  a nasu gani.

Idan aka  ji wani  yana  magana  sannan  ga batsa  yana  kutsawa cikin zancensa  ana  iya  cewa akwai ‘bir’bishin Maguzanci  tattare  da wannan zance. Abu  mafi  kusanci da  batsa wanda  Maguzawa ke  yi  shi  ne  ashar. Suna yin ashar ne  a  yayin d’aura   aurensu  wanda  wani  ashar d’in ma  surke  yake  da batsa. Ambaton wani sashi na al’aura kai tsaye ko a kaikaice na  iya  zama batsa kamar  yadda ya  zo cikin wad’annan karin maganganu:

-  An takalo tsuliyar Dodo

-  Dole/Tilas zama da d’uwawu

-  Ba a had’a gudu da  susan d’uwawuAbubuwa biyu ne ke  k’unshe cikin karin magana ta farko wato kalmar tsuliya wadda  batsa ce  kai   tsaye. Ambaton Dodo da  aka  yi shi kuwa  ya nuna imanin Bamaguje ne. To amma sai ga shi irin wannan karin magana tana zama abin kwatance da wani abu da zai wahalar a yayin zance. Haka kuma kalmomi irin su d’uwawu  da aka yi amfani da  su a misali na biyu da  uku  fad’arsu zai sa k’imar mutum ta ragu ga masu saurare, saboda kalmomin sun shafi al’aura.

https://www.amsoshi.com/2017/11/05/1267/

6.0  KAMMALAWA


Tsafi da bori da Dodo hanyoyi ne na  bauta  da  suka shafi addinin  gargajiya  wad’anda idan  ba Bamaguje ba, babu mai yin su  a matsayin bauta. Wasu lafuzzan  kuwa  ba a sa  ran  jinsu  bakin kowa  sai  Maguzawa, su  ma d’in  sai don  kasancewarsu  masu bin tsarin gargajiya  a harkokin  rayuwarsu. Rayuwar Maguzawa ta yau da kullum ta fi karkata wurin noma, wannan  ya sa ba  sa iya zama nesa da gonakinsu. Samuwar karin maganganun Hausa masu d’auke  da  Maguzanci cikin zantukan  Hausawa  a yau  kuwa wani  abu  ne da  wannan muk’ala  ta  gano  a matsayin  hoton rayuwar Hausawa ta  gargajiya  a wasu ‘bangarori. Idan har za a  rik’a amfani  da wad’anan karin maganganu, yana da kyau a lura da  abin  da  suke  k’unshe a ciki don kauce  wa Maguzanci.


MANAZARTA


Abdullahi, I.S.S 2008. Jiya  Ba  Yau  Ba: Waiwaye  a Kan Al’adun Matakan  Rayuwar  Maguzawa na Aure  da  Haihuwa da  Mutuwa. Kundin Digiri Na Uku, Jami’ar Usman D’anfodiyo, Sakkwato.

Abdullahi, I.S.S 2008. Fitattun D’abi’un Maguzawa, Maiduguri Journal of Linguistics and Literary Studies, (MAJOS) ‘Bolume. d’ Department of Language and Linguistics, University of Maiduguri.

Abdullahi, I.S.S 2008. “Bamaguje da D’an Akuya: Rashin K’auna Ko K’iyayya?” Departmental Seminar Series, Department of Nigerian Languages, Usmanu D’anfodiyo University, Sokoto.

Abdullahi, I.S.S  2012.  “Falsafar D’aurin Auren Maguzawa”. Muk’alar da Aka Gabatar a  Taron K’ara wa Juna Sani a Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu D’anfodiyo, Sakkwato.

Abdullahi, I.S.S  2014. “Matsalolin Koyar  da Maguzantattun Wak’ok’in Hausa”. Mak’alar Da Aka Gabatar A Taron Kara  Wa Juna Sani  Na K’asa da K’asa A Akan K’alubalen Koyar Da  Harsunan Afirka, Niamey Jamhoriyar Nijer.

Bunza, A.M. 2006. Gadon Fed’e Al’ada. Tiwal Nijeria Limited, Lagos.

D’angambo, A. 1984. Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausa.  Triumph Publishers, Kano.

D’anyaya, B.M. 2007. Karin Maganar Hausawa. Makarantar Hausa, Sakkwato.

Gusau, S.M. 2008. Dabarun Nazarin Adabin Hausa. Benchmark Publishers, Kano.

Gusau, S.M. 2011. Adabin Hausa a Sauk’ak’e. Century Research and Publishing Limited, Kano.

Ibrahim, M.S. 1982. Dangantakar Al’ada da Addini Tasirin Musulunci Kan  Rayuwar Hausawa Ta  Gargajiya. Kundin Digiri Na Biyu, Jami’ar Bayaro, Kano.

Koko, H.S. 2001. Hausa Cikin Hausa. Sokoto Nijeriya.

Magaji, A. 2002. Wasu Al’adun Hausawa: Yanaye-Yanayensu  A K’asar Katsina. Kudin Digirin Na Uku, Jami’ar Bayero, Kano.

Malumfashi, I.A. da Ibrahim, N.M 2014. K’amusun Karin Maganar Hausa. Garkuwa Media Ser’bi’bes, Kaduna.

Umar, M.B. 1987. Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Gargajiya. Triumph Publishers, Kano.

Post a Comment

7 Comments

 1. Sannunku da kokari Malamanmu.

  ReplyDelete
 2. Muna gaishe da Malama Zainab. Da fatan za a sanar da dalibai da malaman Hausa game da wannan kafa.

  ReplyDelete
 3. TAHEER M Dalhat11 March 2018 at 03:39

  Wannan abu akwai burgewa sosai amma mu dalibai ne da malamanmu zamu raya wannan kafa....

  Amma ina Neman tallafi akan
  Karin maganar da duka fandarewa ko suka bsabawa addinin musulunci guda 50....
  Abu ubaida Allah ya kara jagora

  ReplyDelete
 4. Abu-Ubaida Sani11 March 2018 at 05:04

  Muna godiya Malam Taheer.

  Game da karin magana, za ka yiya duba littafi mai suna K'AMUSUN KARINMAGANA na Farfesa Malumfashi da Nahuce. Insha Allahu za ka dace.

  Mun gode.

  ReplyDelete

Post your comment or ask a question.