Amososhi

DAGA


 


MUSA SHEHU


Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya


Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato


0703 131 9454


msyauri@yahoo.com


 


Takardar da aka gabatar a taron k’asa da k’asa domin karrama marigayi Farfesa Muhammadu Hambali Junju mai taken “The Challenges of Teaching African Languages” da k’ungiyar des Auteurs Nigeriens en Langues Nationales (ASAUNIL) due da Nigerian Indegenous Languages Writers Association (NILWA) suka shirya a ranar 19-21 ga Fabrairu, 2014 a Emir Sultan, Niger Republic had’e da bukin ranar International Mother Language day (IMLD) da UNESCO ta shirya.


 

Gabatarwa


          Zamantakewa a kowace irin al’umma gona ce mai fad’in gaske, sai dai a yau ana iya cewa, haki na k’ok’arin yi mata barazana na hana yabanya walwala. Hak’ik’a al’ummar Hausawa sun kasance masu kyakkyawar zamantakewa a tsakanin junansu. Gaskiya da rik’on amana da shi suke kwana suke tashi. Hak’uri da taimakon juna ya zama musu ruwan sha a ji sanyin rayuwa. Biyayya ga magabata da tausaya wa talakawa ga shugabanni ya zama ruwan dare game duniya. Sai dai kuma wannan kyakkyawar zama yana neman ta’bar’barewa a wannan zamani. Manufata da wannan mak’ala ita ce, fito da tsarin zamantakewar Hausawa a jiya, da kuma yadda zamantakewar ke k’ok’arin sukurkucewa a yau na rashin gaskiya da rik’on amana. A yau, taimakon juna da biyayya ga magabata, da tausaya wa talakawa daga shugabanni, da hak’uri da juna yana neman ya zama tarihi. Ga dai al’amurran nan suna k’ok’arin ta’bar’barewa a rayuwar Hausawa a yau.

Yanayin Zamantakewar Hausawa a Jiya


Tarihi ya nuna al’umma takan kafu ne a sakamakon wata yarjejeniya tsakanin wasu mutane wad’anda suka taru suka amince da kare kansu daga wasu abubuwan ban tsoro, ko hare-haren abokan gaba, ko namun daji, ko kuma su sauk’ak’a wa kansu wasu wahalolin duniya (Mar, 1980 a cikin Gusau 1999). Irin wannan zama na yarjejeniya yakan kawo sahihin had’in kai da yarda da juna, sannan da taimakon juna. A irin wannan yarjejeniyar zama aka sami wasu mutane daga k’abilu daban-daban suka had’a k’arfi suka samar da al’ummar Hausawa, masu ma’amala da harshe d’aya wato harshen Hausa, tare da samun daidatuwa ta wajen fannin d’abi’unsu da al’adunsu da muhallinsu da sauran kayayyakin ayyukansu duk sun zama fanni d’aya (Gusau, 1999).

Hausawa tun farko mutane ne da suka tashi da taimako da son juna, da ladabi da biyayya, da tsare gaskiya da rik’on amana, da aikata d’a’a da tsare hak’k’in shugabanci da mak’wabtaka da sadar da zumunci, da tausayi da sanin ya kamata, da sauran ayyukan alheri iri daban-daban. Kuma su mutane ne masu matuk’ar karimci da saurin amincewa da wasu mutane, wato bak’i. Sannan ga sakin fuska da shimfid’ar fuska wadda ake cewa ta fi shimfid’ar tabarma. Mutane ne masu kyakkyawan zamantakewa tsakaninsu da ma sauran bak’i masu shigowa. Duk da yake cewa, mun san akwai wasu halaye da d’abi’u munana da ake aikatawa tun wancan lokaci na farkon rayuwar Hausawa, domin Hausawa na cewa, mutum duka d’an tara ne bai cika goma ba.  A kan haka, za a iya kallon zamantakewar Hausawa zuwa wad’annan rukunnai:

Zamantakewa Tsakanin Mak’wabta


            Mak’wabtaka ita ce zama wuri guda da mutum dangane da sana’a ko wurin zama (Gusau, 1999). Ba shakka, akwai kyakkyawan zama da k’aunar juna tsakanin mak’wabci da mak’wabci. Idan wani abin farin ciki ya sami mak’wabci kamar harkar aure ko suna, yakan shaida wa mak’wabcinsa don a taru a yi murna. Hakazalika, idan abin bak’in ciki ne ya samu akan had’u a jajanta wa juna. Sukan kuma taimaka wa junansu idan wata hidima ta samu domin a rufa wa juna asiri. Mak’wabcin Bahaushe tamkar d’an’uwansa ne, ya san samu ko rashin mak’wabcinsa. Haka ma ya san farin ciki ko bak’in cikin mak’wabcinsa. Bugu da k’ari, zamantakewar ba ta tsaya a nan ba, galibi idan dare ya yi magidanta sun dawo gida, mak’wabta sukan fito da abincin dare daga gidajensu a zauna a ci tare ana tattauna lamurran da suka shafi rayuwar duniya. Ziyarar mara lafiya, da zuwa jaje ga wanda wani abu na bak’in ciki ya sama, da sak’onnin taya murna, duk Hausawa na gudanar da su ga mak’wabtansu na jini da na zaman unguwa ko gari ko sana’a, saboda ba da hak’uri da nuna tausayawa da taya murna. Idan wani rikici ya ‘barke tsakanin mak’wabta, akan had’u a tattauna a yi sulhu don samun masalaha.

Zamantakewa Tsakanin ‘Yan’uwa


        Zamantakewa tsakanin ‘yan’uwa na jini kamar ta mak’wabci da mak’wabci ce. Babu nuna bambanci tsakanin ‘yan’uba. Iyaye mata ko kishiyoyi ba sa nuna bambanci tsakanin ‘ya’yansu. A wani lokaci ma yaro bai gane mahaifiyarsa sai idan ya girma. ‘Yan’uwa kan yawaita sadar da zumunci tsakaninsu ta hanyar ziyartar juna daga lokaci zuwa lokaci. Kamar mak’wabta, su ma ‘ya’uwa kan taru domin taya juna murna ko farin ciki idan wani buki ya samu. ‘Yan’uwa kan yi iya k’ok’arinsu don ganin d’an’uwa bai ji kunya ba. Babu yaudara ko cin amana tsakanin ‘yan’uwa. Idan iyayen yara suka rasu, ‘yan’uwa kan d’auke su suna kulawa da su tamkar su suka haife su ta yadda rayuwarsu za ta inganta ba tare da sun tagayyara ba. Idan wata rashin lafiya ta sami d’an’uwa, babu maganar k’yama, ‘yan’uwansa na kusa da ma na nesa kowa yakan kawo tasa gudummuwa domin ganin wannan d’an’uwa ya sami cikakkiyar lafiya.

https://www.amsoshi.com/2017/09/27/kuka-faifan-nazari-laluben-diddigin-bahaushen-kuka-da-%c6%99unshiyar-lafazinsa/

Zamantakewa Tsakanin Masu Mulki da Talakawa


Hak’ik’a akwai kyakkyawar zamantakewa ta fahimtar juna a tsakanin masu mulki ko sarakuna da talakawansu. Abin da aka sani tun can azal a rayuwar Hausawa, sarki ko shugaba mutum ne wanda a koyaushe yake k’ok’arin tsare mutuncin sarautarsa ko shugabancinsa ta hanyar rik’e talakawansa da kyawo, ya d’ora su kan tafarki madaidaici wanda zai amfani rayuwarsu. Haka ma shugaba kan sa ido ya ga cewa, zalunci da cin amana da rashin gaskiya ko yaudara bai wanzu tsakanin talakawansa ba. Yakan kare mutuncinsu ga dukkan wani abu da zai kawo tarnak’i ga rayuwarsu. Shugabanni kan sa ido ga bak’i masu shigowa cikin gari don gudun saukar da ‘bara-gurbi. Haka ma a ‘bangaren talakawa, akwai d’a’a da ladabi da biyayya zuwa ga shugabanni. Sukan kuma taimake su wajen tabbatar da zaman lafiya mai d’orewa da kawo arziki da wadata a cikin k’asa. Haka kuma sarakuna sukan nemi shawarar talakawansu a cikin al’amurra daban-daban domin tabbatar da adalci ga jama’arsu.

Zamantakewa Tsakanin Malamai da ‘Dalibai


Malamai dai a cikin kowace al’umma su ne masu ilmantar da jama’a maza da mata, yara da manya sanin hanyoyin rayuwa tagari, da koya musu halaye masu nagarta, da nuna musu munanan halaye don su kauce wa fad’awa a ciki. Sannan su ilmantar da mutane ilimin addini da na zamani wanda zai shiryar da su zuwa ga rayuwar duniya da na gobe. Malami shi ne mai koya wa yara k’ima da girmama iyayensu, da yadda za su yi musu d’a’a da biyayya, da kuma yadda za su yi kyakkyawar huld’a da sauran jama’a. Su kuwa d’alibai suna matuk’ar girmama malamansu da yi musu d’a’a da biyayya da kauce wa duk wani abu da zai sosa rayuwarsu. Sukan kuma k’udurta kyakkyawar niyya game da malamansu. Ba su cin zarafin malamai ko yi da su, balle ma a gabansu. Haka dai wannan kyakkyawar zamantakewa take gudana tsakanin malamai da d’alibansu. Bugu da k’ari, ko da ilimin zamani ya shigo k’asar Hausa aka fara samun malamai da d’alibai ‘yan k’asa, wannan kyakkyawan tsarin zamantakewa tsakanin malaman zamani da d’alibansu bai sauya ba. Malaman sukan d’auki d’aliban kamar ‘ya’yansu na cikinsu. Haka su ma d’aliban sukan yi wa malaman ladabi tamakar iyayen da suka haife su. Akwai girmamawa da tsare hak’k’in juna tsakaninsu.

Zamantakewa Tsakanin Masu Arziki da Talakawa


Masu iya magana na cewa, kowa am mutum mutane ash shi. Zamantakewa tsakanin mai shi da mara shi abu ne gwanin ban sha’awa a k’asar Hausa. Masu arziki ba su walak’anta talakawa, hasali ma sukan jawo su ga jiki domin su ma su sami albarkar dukiyar. A wasu lokuta, masu arziki sukan rarraba wa talakawa jarin da za su gudanar da kasuwanci domin kowanensu ya amfana. Idan wata lalura ta sami talaka wanda ya shafi aure ko suna da makamantansu, talaka yakan kai kukarsa ga masu shi kuma a share masa hawaye gwargwadon iko. Su kuwa talakawa sukan kasance masu d’a’a da biyayya da gaskiya da rik’on amanar dukiyar da masu shi suka damk’a masu. Idan wata hidima ta samu mai shi, za ka tarar talakawa sun taru a k’ofar gidan mai shi don su taya shi murna idan abin farin ciki ne. Idan kuma akasin farin ciki ne ya auku, nan ma talakawan sukan taru domin taya shi juyayi da jajanta masa. Haka dai wannan kyakkyawar zamantakewa take tsakanin masu arziki da talakawa a k’asar Hausa, sai dai d’an abin da ba a rasa ba na sa’bani na yau da gobe. Da ma Hausawa na cewa, mutum duka d’an tara ne bai cika goma ba.

 

Zamantakewa Tsakanin Ma’aurata


        Hak’ik’a akwai kyakkyawar yanayin zamantakewa tsakanin miji da matarsa a k’asar Hausa. Miji yakan yi iya k’ok’arinsa na ganin ya tsare hak’k’in matarsa da ke bisa kansa. Yakan kula da ci da sha da lafiyar matarsa da sauran lalurorin yau da kullum gwargwadon hali. Yakan kauce ma wasu munanan halaye na cin zarafi ga matarsa ko wad’anda al’ada ba ta amince da su ba. Bugu da k’ari, miji kan sa hannu wajen tarbiyyantar da yaran da suka haifa don ganin sun rayu bisa turba tagari da yanayin zamantakewar duniya. Ita ma matar takan yi k’ok’arin tsare hak’k’in mijinta da ya rataya a wuyanta. Takan kasance mai d’a’a da biyayya ga miji da rashin k’etare iyakokinsa. Ita ce mai kula da harkokin gida na yau da gobe, da tsaftar yara da ba su tarbiyya tagari. Mace kan yi hak’uri da mijinta da tausaya masa game da harkokin rayuwa. Idan wata matsala ta shiga a tsakaninsu, sukan taushe zuciyarsu ga hana aikata d’anyen hukunci. Wannan ne ya sa yawaitar sakin aure bai samu gindin zama a tsakanin Hausawa ba. Hak’uri kusan shi ne jigon zamantakewar mata da miji, tare da bai wa juna shawara don samun mafita a rayuwa.

Zamantakewa Tsakanin Iyaye da ‘Ya’yansu


        A koyaushe burin mahaifa ko uwaye bai wuce ganin ‘ya’yansu sun tashi cikin halaye masu kyau da nagarta. Saboda haka suke koya musu d’a’a da ladabi da biyayya da bin kyakkyawar turba don su ribanci rayuwarsu, al’umma ma ta amfana da su. Uwaye sukan sanya yaransu makaranta irin ta addinin musulunci da ta zamani. Sukan nuna musu muhimmancin gaskiya da rik’on amana domin aiki da su. Sa’annan kuma da illar k’arya da cin amana domin su kauce musu. Sukan kuma nuna musu amfanin zumunci da ‘yan uwantaka ta hanyar yawaita aikensu a gidajen ‘yan’uwa da abokan arziki. Akan koya musu sanin darajar mutane da girmama su, ba wai sai iyayensu kawai ba. Saboda haka ne ‘ya’ya sukan kasance masu biyayya da jink’an iyayensu tun suna yara har zuwa girmansu.

A tak’aice, ana iya kallon yanayin zamantakewar Hausawa a jiya da wasu kyawawan abubuwa da al’ada da addini suka amince da su da kuma masu aikata su.

  • Gaskiya da rik’on amana

  • Zumunci da ziyartar ‘yan’uwa

  • Tsare hak’k’in mak’wabtaka

  • Taimako da tausaya wa juna

  • Ladabi da biyayya ga shugabanni

  • Girmama na gaba

  • Adalcin shugabanni ga talakawa

  • Tsare hak’k’in talakawa ga masu mulki

  • Hak’uri da yafe wa juna


https://www.amsoshi.com/2017/11/06/basarake-wakokin-sani-aliyu-dandawo/

Ta’bar’barewar Zamantakewar Hausawa a Yau


        Sanin kowa ne cewa, matsayin zamantakewar Hausawa ya kai inda ya kai a yau. Kyakkyawar tsarin zamantakewa da aka sani ga Hausawa a da, a yanzu ya d’auki sabon salo na koma baya. Kusan kowane rukunin tsarin zamantakewar Hausawa da aka ambata a baya, an sami ta’barwarewarsa a yau.

Kyakkyawar zamantakewa da ke tsakanin mak’wabta a da, ya fara yin nisa a yau. Sau da yawa za ka iske ba a ga-maciji tsakanin mak’wabci da mak’wabci, kowa ya kama mai fisshe shi. Maganar mak’wabta su had’u kowa ya fito da abinci a ci tare ya zama tarihi a yau, kowa ya yi gabansa. Sai mak’wabta su share mako d’aya ba su yi ido hud’u da juna ba balle a yi maganar gaisawa, sai dai idan an yi kici’bis da juna a bisa hanya. Hatta ‘ya’yan mak’wabtan da suke  had’uwa musamman da dare domin gudanar da wasanni, ya sha ruwa a yau, kowane maigida ya ja babbar k’ofa ya rufe ‘ya’yansa a cikin gida. Mak’wabci bai san halin da mak’wabcinsa yake ciki ba, na farin ciki ko akasinsa, balle su taimaka wa juna da shawara wajen samun maslaha a rayuwa.  Sau da yawa za ka iske mak’wabta na ta husuma a kan iyakokin gida ko haraba har zuwa wajen masu shari’a. Ga dai al’amurra nan sun cakud’e sai dai Allah ya gyara.

Shi kuwa harkar zamantakewa tsakanin ‘yan’uwa a yau ya zama abin da ya zama. Babu zumunci da taimakon juna, balle rik’on aman. Kowa ya kama gabansa, kansa kawai ya sani sai ‘ya’yansa. A yau, idan iyaye suka mutu suka bar marayu sai ‘yan’uwa su sa musu ido suna taggayara, babu ilimin addini balle na zamani, ba su samun tarbiyya balle su amfani kansu da al’umma baki d’aya. A yau idan ba ka da abin hannunka, babu d’an’uwa mai kusantarka domin ba a samun komai wurinka. Hatta shawara a kan wasu al’amurra na rayuwa ba a yi da kai balle ka san halin da ‘yan’uwa suke. Su kuwa ‘yan’uwa masu abin hannunsu sun ke’be kansu ba su buk’atar kowa ya ziyarce su don gudun  a  aza musu lalura.

Zamantakewa tsakanin masu mulki da talakawa kuwa ya sauya fasali a yau. A maimakon kare hak’k’in talakawa da mutuncinsu, masu mulki sun sanya k’afa sun shure wannan d’awainiya da ya ratayu a kansu. Sun kasa tsare mutuncin talakawa, sai cin amana da danne hak’k’ok’insu da ma barazana ga rayukansu.  Masu mulki sun k’i su jawo talakawansu ga jiki domin sanin halin da suke ciki. A dalilin haka, su kuwa talakawa sun bijire ba su ganin mutunci da darajar masu mulki balle su yi musu biyayya. Talakawa sai muguwar addu’a suke yi wa masu mulki saboda danne hak’k’ok’insu da ake yi. Zamantakewa ya ta’bar’bare ta yadda sai an kashe haki kafin yabanya ya sami walwala.

Dalilan Ta’bar’barewar Zamantakewar Hausawa a Yau


A bayanin da ya gabata, an bayyana cewa, kyakkyawar yanayin zamantakewar Hausawa a jiya ya samu gindin zama ne saboda rik’o da wasu d’abi’u da al’ada da addini suka amince da su, kamar gaskiya da rik’on amana, zumunci, hak’uri, taimakon juna, da makamantansu. A duk lokacin da al’umma suka rasa ire-iren wad’annan al’adu, ko suka yi rauni a rayuwarsu, tilas halin zamantakewar wannan al’umma ya ta’bar’bare. Wasu daga cikin abubuwan da nake ganin sun taimaka wajen haifar da wannan ta’bar’barewa na zamantakewar Hausawa a yau sun had’a da:

Yawaitar Zalunci: Sa’banin inda aka fito, a yau galibin al’ummar Hausawa burinsu bai wuce tara abin duniya ko ta halin-k’ak’a (halat ko haram). Masu kud’i sun daina taimakon na k’asa gare su wai don gudun k’arewar dukiyar ko raguwarta. Su kuwa masu mulki sai danne hak’k’in talakawa idan sun shigo hannunsu. Shugabannin yanzu sun daina wakiltar talakawansu, babban burin akasarinsu shi ne su wawari dukiyar talakawa da suka shigo hannunsu a matsayin amana ta yadda ko bayan sun sauka ba za su talauce ba daga su har jikokinsu. A kan haka, a yau matsananciyar adawa ta wanzu tsakanin shugabanni da wad’anda ake shugabanta, sai kallon-kallo ake yi wa juna. A yau, a gida guda ma idan wani abin amfani ya shigo hannun wani daga cikin gidan wanda za a raba kowa ya amfana, sai ka iske wannan da kayan ya shigo hannunsa ya wawari wanda ya fi na saura.          

Rashin Hak’uri da Juriya: A yau rashin hak’uri da juriya ya yi tasiri ainun a tsakanin al’ummar Hausawa. Tashin hankula ya yawaita a tsakanin ma’aurata, koyaushe sai an yi sulhu saboda yawan fad’ace-fad’ace. K’arin tabbatar da wannan zance shi ne, a lek’a kotunan alk’alai za a ga yawan k’ararrakin da ake shigarwa a kowane yini wad’anda suka shafi ma’aurata ne (Gusau 1991). Zawarawa sun yawaita a kowane sashe na gari. A unguwa d’aya sai ka sami zawarawa bila’adadin an sako su, wanda galibi saboda rashin hak’uri da juriya ne.

Rashin Gaskiya da Amana: ‘Yan kasuwa sun bijire wa gaskiya, sai son cin amana da yaudara da cin ‘batacciyar riba da ‘boye abubuwan sayarwa sai sun yi tsada. A yau, idan mai dukiya ya jawo talaka cikin arzikinsa domin kowa ya amfana, sai talakan ya sa rashin gaskiya da cuta, ko kuma shi mai arzikin ya rik’a danne hak’k’in yaron nasa. A yau idan ka ba wani sak’on kaya ko kud’i ya kai ma wani wuri ko ya adana maka har na tsawon wani lokaci, sai ya ci amanarka ya k’i kai sak’on ko ya salwantar da ajiyar da ka ba shi. A yau mai gaskiya bai cika tasiri a mafi yawan kotunan shari’ummu ba, sai dai wanda ya fi k’arfin ba da abin hannunsa. Mata ta ci amanar mijinta, miji ya ci amanar matarsa. Masu mulki da shugabanni sun murje ido sun yi babakere da handamar dukiyar talakawa da aka ba su amana. Babu gaskiya da amana tsakanin abokai da ‘yan uwa, ga abubuwa nan dai duk sun ta’bar’bare. Ba manufata ba ne da wannan bayanai cewa, babu kyakkyawar zamantakewa baki d’aya a k’asar Hausa a yau ba, sai dai don yin hannunka-mai-sanda ga al’ummarmu domin a farga ta yadda za a shawo kan matsalar tun abin bai yi muni sosai ba.

Hanyoyin Farfad’o da Zamantakewar Hausawa


        A tunanina, ta’bar’barewar da zamantakewar Hausawa ta yi a yau bai yi munin da za a kasa samar da hanyoyin da za a warware matsalar ba muddin an himmatu da gaskiya. Dole iyaye su farga wajen cusa kyakkyawar tarbiyya tagari a zukatan ‘ya’yansu ta yadda za su rayu bisa turba madaidaiciya da za ta amfani al’umma, kamar gaskiya da mana, ladabi da biyayya ga na gaba, sai kuma uwa-uba hak’uri wanda aka ce shi ne gishirin zaman duniya.

Su kuwa malamai tilas su taka irin nasu rawa wajen gargad’i a kan hani da horo na koyarwar addini da al’ada a kan irin zalunce-zaluncen da ya yi katutu a rayuwarmu ta yau. Haka zalika su ci gaba da bayyana wa jama’a irin mummunar sakamakon da ke tattare da aikata miyagun d’abi’u da al’adau ga masu aikata su. Har wa yau, dole gwamnati ta sanya ido ga harkokin shari’a ta yadda za a daidaita adalci ga kowa, da kuma hukunta duk wanda ya aikata ba daidai ba. Su kuwa sauran mutane kowa ya tsaya ya tsarkake zuciyarsa da halayyanrsa ta yadda rayuwarmu za ta sake komawa ga turba mai tsarki da muka gada daga magabatan da suka wuce.

 

 

Kammalawa


        Zamantakewa abu ne da ya shafi illahirin rayuwar mutane, idan ya inganta, rayuwar al’umma ce za ta kyautatu, idan kuma ya lalace, rayuwar al’umma ce za ta ta’bar’bare baki d’aya. A tak’aice ana iya cewa, tun asali al’ummar Hausawa suna da ingantaccen tsari na zamantakewa a tsakaninsu da kuma sauran jama’a masu mak’wabtaka da su. Sai dai kuma, babban abin takaici a yau shi ne, wannan kyakkyawar halayya tana fuskantar gagarumar barazana na ta’bar’barewa. Wannan kuwa yana faruwa ne saboda son kai da kwad’ayin tara abin duniya, da rashin gaskiya da amana da hak’uri da ya mamaye al’ummarmu ta wannan zamani. Sai dai ana cewa, ruwa na k’asa sai ga wanda bai tona ba, ma’ana za a iya bin wasu hanyoyi da aka ambata a baya watak’ila a shawon kan matsalar ta yadda al’ummarmu za ta sake ginuwa kamar inda aka fito.

 

 

 MANAZARTA


Alhassan  H. da wasu  (1982) Zaman  Hausawa.  Islamic Publications Bureau, Mushin, Lagos

Alkanawy A.S.  (2004) Finafinan   Hausa:  Fad’akarwa  ko Shagaltarwa. A cikin Hausa Home

Videos:  Technology, Economy,  and  Society, Jami’ar  Bayero  Kano.

Bunza A.M. (2006)  Gadon Fed’e Al’ada. Tiwal Nigeria Limited, Surulere  Lagos.

Chamo I.Y. (2004) Tasirin  Al’adun  Turawa  a  cikin  Finafinan  Hausa. A cikin Hausa Home

Videos: Technology, Economy,  and Society,  Jami’ar Bayero Kano.

C.N.H.N.   (1981)   Rayuwar   Hausawa.  Littafin  da  Cibiyar  Nazarin   Harsunan  Nijeriya

Jami’ar Bayero Kano ta wallafa.

Gusau S.M.  (1999)  “Tarbiyya  a  Idon  Bahaushe”. A cikin Algaita Journal of Hausa Studies.

Jami’ar Bayero Kano. Volume 1 No 1.

Ka’oje U.I.  (2006)  Tarbiyya  a  K’agaggun  Labaran  Hausa : Nazari  kan  ‘Ya’yan  Hutu na

Malama  Bilkisu  Funtuwa. Kundin  digirin  farko, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo

Sakkwato.

K’amusun Hausa (2006) Wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya na Jami’ar Bayero Kano

Magaji, A. (1999)  “Kunya  da  Mutunta Mutane a Al’adar Bahaushe” A cikin Algaita Journal

of Hausa Studies, Jami’ar Bayero Kano.