Ticker

6/recent/ticker-posts

Kacici-Kacici: Rumbun Fikira

Na

Abba Muhd Danhausa

07038838301

abbamuhddanhausa@gmail.com

MENE NE KACICI-KACICI?


Da fari a daidai wannan ga’ba, akwai buk’atar mu fahimci cewa, kacici-kacici na Hausa yana d’aya daga cikin rassan adabin baka na gargajiya. Wato yana k’ark’ashin zantukan azanci da ke fitowa a
maganganu na yau da kullum da Hausawa suke yi. Yawancin kacici-kacici tambayoyi ne da amsoshinsu wad’anda cikin salon da ke buk’atar zurfafa tunani kafin gane amsarta.
https://www.amsoshi.com/2017/07/01/kacici-kacici-da-amsoshin-wasunsu-cikin-hotuna/

A Kamusun Hausa Na Jami'ar Bayero, Kano (2006), an bayyana kacici-kacici da: “Za’bi ko kintata” Amma dangane da asalin Kalmar kacici-kacici kuwa, Yahaya (1991: 27) ya bayyana cewa:

“Kalmar kacici-kacici tana da ma'ana kashi biyu masu alak’a da juna. Da fari ya nuna an samo asalinta ne daga kalmar 'cinta', wato kintaci fad’i.”

Ya fito da haka ta nuna yadda yara sukan yi wasa a inda d’aya zai rufe wani abu a hannunsa ya buk’aci d’ayan ya cinta, wato ya yi kintaci-fad’in abun da yake a hannunsa. A kan haka, Almajir, (2013: 4) ya bayyana cewa, wannan wasa da yara suke yi tsakanin junansu shi ne ya gina wannan wasa ta kacici-kacici wanda ake yi da tunani da siffanta wasu abubuwa. Sannan akan yi ta ga yara cikin wata irin Hausa mai zuzzurfar ma'ana.

YADDA AKE AIWATAR DA KACICI-KACICI


Masana irin su Dangambo, (2008) da Almajir,  (2013:5) suna da ra’ayin cewa ana fara kacici-kacici ne da fad’in; "kulin kulifita."  A ra’ayin nasu, hakan na nuna wa abokan wanda ya yi wannan furuci cewa, ya zo ne da shirinsa na yin kacici-kacici. Su kuma sai su amsa masa da cewa "Gauta." Daga nan sai ya shiga ba su tambayar kacici-kacicin su kuma suna ba shi amsa. Idan ya kawo wata wadda aka rasa mai iya ba shi amsarta sai su ba shi gari (wato mik’a wuya cewa ya fad’i amsar da kansa), shi kuma sai ya faɗa musu amsar.

Irin amsar da za a tsammaci bayarwa dole ne mai sauraro ya yi zuzzurfan tunani kafin ya furta ta. Dole ta kasance k’wayar abun da aka siffanta a tambaya, walau siffantawa ta yanayi ce ko kuma
al'adar abun da aka san abun nufin (amsar) da ita. Tun asali yawanci yara ne ke yin kacici-kacici, bayan sun yi tatsuniya sun gaji.

https://www.amsoshi.com/2017/07/09/kacici-kacici-da-amsoshinsu-cikin-hotuna-4-2/

 

AMFANIN KACICI-KACICI GA HAUSAWA


A k’asar Hausa an rungumi kacici-kacici a matsayin wata hanya ta sanya shak’uwa tsakanin al'umma. Kacici-kacici na sanya kaifin basira da kuma iya fahimtar maganganun na gaba da shi. Sannan yana zama wani rumbu da ke adana kalmomin al'umma. Yana kuma sanya raha da annushuwa ga waɗanda suke yin sa.

MISALAN KACICI-KACICI


TAMBAYA: K’ulin k’ulufita.
AMSA: Gauta.

TAMBAYA: Shirim ba ci ba.
AMSA: Baba.

TAMBAYA: Takanda ba k’ashi ba.
AMSA: Kanwa.

TAMBAYA: Na ga saurayi da gemu.
AMSA: Masara.

TAMBAYA: Gwanda lili da liyo.
AMSA: Gwanda noma da awo.

TAMBAYA: Sikiti futata.
AMSA: Bazawara.

TAMBAYA: Kumbon Iya da Zak'i.
AMSA: Yalo.

TAMBAYA: Cikin cikin ma da ciki.
AMSA: Albasa.

TAMBAYA: Samarin gidanmu masu fararen kawuna.
AMSA: Ta’bare.

TAMBAYA: 'Yammatan gidanmu masu yawan zannuwa.
AMSA: Masara.

MANAZARTA.

Almajir, T. S. (2013). Kacici-kacicin Hausa. (Ba Jiha): (Ba madaba'a)

Dangambo, A. (2008). Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon Tsari). Zaria: Amana Publishers.

Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero, Kano (2006). K’amusun Hausa Na Jami'ar Bayero. Zaria: Ahmadu Bello University Press
www.amsoshi.com

Post a Comment

2 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.