Ticker

6/recent/ticker-posts

Da Wasa Ake Gaya Wa Wawa Gaskiya

Bitar littafan SABO TURKEN WAWA na Halimatu Ahmad Umar Bunza wanda aka gabatar a bukin k’addamar da littafin ranar 1 ga Watan Junairu 2014 a babban d’akin taro na Tsangayar Sarkin Musulmi Muhammadu Maccid’o, Sakkwato k’ark’ashin jagorancin Ambasadar Shehu Wurno  da k’arfe goma na safe

Daga

Aliyu Muhammadu Bunza

Sashen Koyar da Harsunan, Nijeriya

Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina

Jahar Katsina, Nijeriya


Da suna Allah mai rahama mai jink’ai. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah Muhammadu d’an Abdullahi (SAW) da iyalansa da sahabansa da wad’anda suka yi koyi da su ya zuwa ranar sakamako.

Gabatarwa:


Sassan adabinmu na baka ba k’aramar rawa suka taka ba wajen daidaita muna akalar rayuwa a kowane k’arni muka samu kanmu. Lallai, ba don jiya ba, da yau ta yi masassara. Yunk’urin kyautata rayuwar yau kuwa, gobe ce ake yi wa shimfid’ar maraba. Sarrafa karin maganar “Sabo Turken Wawa” ya zama akalar jan zaren tunanin wannan littafi ya dace. Abin da aka saba da shi an san shi. Abin da aka sani dole an zaune shi. Abin da aka zauna, ya zama abokin rakiya sai a sake jiki, a mik’a wuya gare shi, har ya zama rak’umin makaho, kai ka gani ba ni ka gani ba. A ganina, burin littafin shi ne, a rik’a sara ana daban bakin gatari, domin a hangen zabiyar tashe cewa ta yi:

Jagora:       Bari wanka da tutu don a ga iska,

Yara:          Hadari yamma ba ruwa ke da shi ba.

https://www.amsoshi.com/2017/07/31/rahama-abdulmajid-jarumar-jarumai-mata-marubuta/

Bita:


An tsara littafin Sabon Turken Wawa cikin shafuka d’ari da arba’in da shida (146). Goshin aikin aka tsettsefe shi da shafuka ashirin da shida (26). Bayan shafin farko na sunan littafin. Shafin da ya bi masa aka sadaukar da aikin wurin da ya dace domin babu mai nunin gidansu da hannun hagu. An yi nagartacciyar godiya ga kagunan da aka sha madarar karatu. Daga nan aka samu tofa albarkar masana addini Sheikh Kabiru Haruna Gombe, da share fagen nazari daga Farfesa Salihu Bala Aljannare, Farfesa Abdullahi Bayero Yahya ya kakka’be wundin karatun domin abin aljihu na mai riga ne. Saboda cikon sunan makaho da waiwaya marubuciyar ta k’ara wata gabatawa ta daban. Yin haka, bai zama sabon salo ba, shik’a da daddare in ji kaza, domin malammamu cewa suka yi, mai sanda ke da fasalin bugu.

Ainihin k’unshiyar littafin an zuba ta cikin babuka goma sha biyu. Wad’annan babuka su suka ba da shafi d’ari da ashirin (120) na aikin. A hangen bita, na kasa su zuwa gida uku: Gida na farko babi na d’aya da biyu, su ne goshin aikin. Babi na d’aya ya ta’bo tarbiya ta addini da al’ada. A k’arshe, aka yi kwakkwahe da kunya domin ta zama madubi da ma’auni ga babukan da za su rako su. Babi na biyu ya kalli wayewa da wauta a idon masu ganin sun waye, ya kuma tabbatar da wautar wayayyin zamaninmu.

Kashi na biyu ya k’unshi babuka shida (babi na 3-7). Wad’annan babukan su suka yi wa aikin susa gurbin k’aik’ayi. An ta’bo sadarwar zamani da irin bi-ta-da-k’ullin da ke ciki. An kalli tauraron d’an Adam da idon tarbiya. An k’yallaro yanar gizo da hankalin tuwo da na addini. An waiwayi zaman banza da sunan majalisa da holewa ta mahangar tabaran Alhaji Muhammadu Sambo Wali Sakkwato, da ya ce:

Ga jin dad’in rayuwa samari ka bicewa,

Suna wasu ‘yan k’wange-k’wange don nuna ‘bacewa,

Su sa takalmin da ba wuya za a karewa,

Su shawo tabar da hankali zai juyewa,

Su gigice don su samu damar ‘bacinmu.

(Wak’ar Zaman ‘Banza).

 

Rukuni na uku ya k’unshi (babi na 8-12). A nan aka fito da sakamakon wayewa ga suturar mata da maza da kuma yankan ciki da ya yi wa matan wayayyi ma’aikatansu da wad’anda ke zaune gidajensu. Ga irin abubuwan da suka haddasu, aka nad’e karatun da fad’akarwa ga wad’anda abin ya shafa da kuma hukumar da ke kula da su, an dai gaji an dawo ga hasashen Alhaji Muhammadu Gambo Fagada da ke cewa:

Jagora: Wai ga maciji a d’ora biyas shayi da sanda,

: To ga ‘barayi, shi mib bid’i mai wak’ar ‘barayi?

 

Nazari:


Ga al’adar Bahaushe, idan aka ce sabo turken wawa, abin da zai bijiro ga tunanin Bahaushe na gidi shi ne, abin da aka saba da shi a koyaushe shi za a rik’a tunawa. Yadda aka san shi jiya, za a ga ko yau, yana nan ba sauyawa. Dad’in da aka sha jiya, gobe ana sa ran a sha irinsa ko wanda ya fi shi. Yadda duk ake d’aure dabbobi a turke, su mai da turke wurin zama na sakewa da jin dad’i, haka d’an Adam yake ga abin da ya saba. Wazirin Gwandu Alhaji Umaru Nasarawa ya kakka’be muna k’ura ga ma’anar kalmar “Sabo” yana cewa:

Na saba mik’a shed’ara

Ta tsaya tsaf babu tank’wara

Ai wak’a ba ta gagara

Muddin na tashi fassara

Wada duk nika so ina fad’i rarara.

(Wak’ar Yabon Sarkin Gwandu Yahya)

 

Don haka, sabo sanin abu ne na hak’ik’a domin Hausawa cewa suka yi, ido wa ka raina? Ya ce: “wanda na saba gani koyaushe”. Bisa ga wannan riwayar magabata ke cewa, sabo da ci kwad’ai yake sa wa. Idan aka nak’alci abu sosai su ce, hannu ya iya jiki ya saba. Dalili da haka ne suke ganin sanin asali kan sa kura cin kanjilo (k’onannen kashin shanu). Don me muke ganin, d’an gafiya ko bai yi sata ba yana dogon aro? Don ya saba da ganin banza koyaushe a gidansu. Ashe gaskiyar Bamaguje da ya shiga birni bai ga rumbu da masussuki da ya saba gani ba ya ce, “Ana zaman k’arya”. Tattara hankali wuri guda da k’uk’ewa ga ginan ‘bera da gafiya da yanyawa da tsari da damo, ba dare ba rana, ya sa makad’a Maitandu Shinkafi ke yi wa wani gwarzo take da:

Jagora: Tsohon tabuda tsohon sallatau

Yara: Uban na Nababa ya saba da gina,

Jagora: Na mai kid’i kwana suya yakai,

Yara: Kitsen burgu hak ya kamma shi gabanai na naso.

Gindi: Ya fito ma kusa Hausance

: Nababa ya saba da gina.

 

Ga al’adarmu, idan aka saba da abu, ba a gajiya da shi, in ji malamin kid’i Narambad’a:

Jagora: Uban Yari uban malami

Yara: Kowag gaji bai saba ba

Gindi: Koma shirin daga

: Gwarzon bahago d’an Iro.

 

Idan ana biye da zaren tunanina, za a ga, an fi son a saba da abin k’warai mai amfanin mai sabo ko jama’arsa. Idan abin da aka saba da shi, ba na kirki ba ne, ba a son a mayar da shi turke. Irin wannan turke shi Hausawa ke ce wa, turke mai ca’bo (ta’bo) marigayi Alk’ali Bello Gid’ad’awa ya tabbatar da:

Idan dabba tana sauri ga turke,

Da amfanin da tas san za ta iske.

(Bargon Hikima)

 

Marubuciyarmu ta hango turken da ca’bo, don haka take ganin wawa kawai zai saba da shi.

Wane ne Wawa?


Duk da yake an yi k’ok’arin a fayayce wawa sosai a littafin, ba zai hana a k’ara wa Borno dawaki ba. Wawa shi ne, wanda bai san ciwo kansa ba, bai san abin da ke cutar da shi ba, bale mai amfaninsa. Wawa shi ne, mai kallon mutane cikin wauta a ma’aunin wayonsa na wauta. Wawa ya fi mahaukaci ban haushi, da ban takaici, ga ayyukkansa, da lafuzzansa, da tunaninsa. A harshen Hausa, wawa ya fi kowane nau’i na mutane sunaye barkatai masu fito da sifarsa da d’abi’unsa da ayyukansa.

Bayan sunansa na yanka “wawa”, shi ne solo, sam’balto, satoto, hauge, sangala’be, shashasha, sususu, sakarai, bi-nan, dabba’uuna, haure, le’bo, sale’bo, hangaham, santo’bilo, talalla’biya, hoce, gabu, rak’umi, dambalalle, ji’bananne, makananne, ga su nan dai. Da wawa da mahaukaci da jahili, kakansu d’aya, iyayensu mata ne suka fito gidaje daban-daban. Rayuwar da yaranmu suke a kai yanzu ta yi canjaras da fad’ar wani makad’i Zari da ke cewa:

Jagora: Ina nika samun mahaukacin yaro wawa?

Yara: Ya tankwahe wando ya sa k’afa ramin kura.

 

Duk wani abu da ya shafi wauta a wajen Bahaushe abin zargi ne, abin kushewa ne, haraka ce ta komawa baya. Bahaushe bai tanada wa wawa wani gurbi ba a gurbin rayuwa, face na tir! Da assha! Da kayya! Da wayyo! Yaro ba ya son magaji wawa. Mace ba ta son miji wawa. Talakka ba ya son sarki wawa. Sarki ba ya son talakka wawa. Makad’a Sa’idu Faru cewa ya yi:

 

Jagora: Wawa bai san gacte ba

: Don an ce za a ba shi sarki

Yara : Hay yag gama da tuntu’be.

 

Gindi: Ya rik’a da gaskiya Muhammadun Muhammadu

: Karsanin gidan mai saje shirinka ya yi kyau.

 

Makad’a Narambad’a ya yi shakundun da cewa:

 

Jagora: Gidan ga mutum hud’u ba su sarauta

Yaro  : Da sam’balto da satootoo

: Shi wanga na ukku k’azami,

: Na cikon na hud’unsu hawaa’i.

 

Gindin: Shiri bajinin Mamuda

: Abu na Namoda tsayayye.

 

Wautar Yau a Hankalin Jiya


Hankalin jiya shi ne, tsararren tunani na girmama gabaci, da rik’on amana, da tsayar da gaskiya, da sanin ya kamata na kariyar mutuncin mutum, da gidansu, da zuriyarsa, da garinsu, da al’ummarsa. Hankalin jiya shi ne, kamalar mutum ta aiki da magana, a ji mutum, a ga mutum, a yarda da mutum. Hankalin jiya, wayonsa gudun kunya, da adawa da ita, da d’iyanta, da kowane bagire aka san mazauninta ne na dindindin da na wucin gadi. Hankalin jiya, ba ya shan iska wuri d’aya da k’arya, kuma bai ta’ba aminta su k’ulla zumunta ba, ko da ta hanya ce mai gamin zumuntar dole. Hankalin jiya, ba ya da kasala, bai yarda kwad’ai ba, ba su abota da rowa, ba unguwarsu d’aya da zaman banza ba, har ya k’aura, ba su ga-maciji da yawon dandi. Zanannen sunansa ladabi, lak’abinsa biyayya, don haka ake yi masa kirari da nagari na kowa mugu ko sai uwar da ta haife shi. Mutanen jiya sun saba da d’ansu sosai, suka wayi gari a yau, cikin wasu ‘ya’ya na daban, da babu nagari ga iccen kabari. Allah Ya shiryar da mu.

Wayon yau shi ne, ado da k’arya babba da yaro. Yaudara samun sa’a. Amana ta koma ganina. Gabaci ya koma wasan yara. Nagarta ta koma kasala. Kamun kai, ya zama k’auyanci. Sanin ya kamata ya zama wauta. Biyayya ga gabaci sunansa gidadanci. Tarbiyantar da yara da ladabtar da su ya zama dabbanci. Tsare mata a gidajen aure, da kare mutuncinsu, tsohon yayi ne, da tauye musu hak’k’i. Ba su damar gwada tsawo da k’atta, da za’ben abokin huld’a, da tanada musu ma’aikatun renon shaggun da suka haifa, shi ne cigaba, da ‘yancinsu, a wayon k’arshen zamaninmu. Tun gabanin Musulunci al’adunmu ba su yarda da hautsinan k’ato da k’atanya ba, bale yau da rana tsaka a yi muna sakiyar da babu ruwa. Sa’idu Faru ya tababtar da cewa, ko wurin buki a tsarin Bahaushe mata da maza zaman ‘yan marina suke yi a fad’arsa:

Jagora: Dogon sarki yana da kyawo

: Ranar da an ka je daba

Yara  : Ya yi kyau da riguna

 

Jagora: Shi wanga d’an gajere

Yara  : Ku a je shi gun rabon dawo

 

Jagora: Shi kai ma wanga dunk’ule

Yara  : Shi kai ma wanga dunk’ule

 

Jagora: Matuk’ar wurin akwai mata

Yara  : Hat tuman gadi shikai

 

Gindi: Ya rik’a da gaskiya Muhamamdun Muhammadu

: Karsanin gidan mai saje

: Shirinka ya yi kyau.

https://www.amsoshi.com/2017/10/30/sharhin-littafin-jarumtakar-maza-1-2-na-abdulaziz-sani-madakin-gini/

Me Ake Ciki Yau?


Ko kusa  , hankalin tuwo ba zai yarda da kushe ci gaban mai ginan rijiya da muke ciki a namu k’arni ba. Mai hankali duk ya nace ga karatun jaridunmu, da sauraren kafafen yad’a labaranmu, da tauraron d’an Adam da ke shawagi da hotuna da labaran duniyarmu, da wayar hannu da ta zama lalura gare mu, zai tabbatar da ba ta mutu ba ta ‘balgace. Mai wayo zai gano cewa, an tashi bisa k’asa an koma a kan da’be. Mai hankali duk ya san, da lauje cikin nad’i. Duk wani mai bincike zai gano, da walakin goro cikin miya. Masana sun tabbata an k’i cin biri an ci dila. Duk mai hankalin tuwo zai gano ko bayan tiya akwai wata caca. Matsalolin tarbiya da suka yi muna turnak’u a yau, na mugun mak’wabci ne, ba ka da mata ana haihuwan d’iya da kamar ka.

Daga cikin ribatarmu da Nasara suka yi cikin rigar wad’annan na’urori akwai: koya wa yaranmu k’azantattar tarbiyarsu ta neman abin duniya ido rufe, da bugun gaba da uwa, don a d’aure wa zina gindi. An koya wa yaranmu fashi da makami, da fashi da muk’ami, da tabanjamanci da d’an kamanci, da kwartanci da ak’idar kowa ya d’ebo da zafi bakinsa. Kyawawan al’adunmu na aure da haihuwa da mutuwa, an durmuyar da su. Tsarkakakkiyar ak’idarmu ta addininmu a ko’ina an yi mata ra’bo, an saka mu cikin d’emuwar da ta fi dogon suma had’ari. A cikin masalatanmu da mak’aabartunmu da makarantunmu muryoyin wayoyinmu ke cashe kid’e-kid’en arna da wak’e-wak’ensu na gumakansu da shaye-shayensu. An mayar da Alk’ur’ani da Hadisai da nassoshin shari’a busan sheshe a wayoyin hannu da sunan kishin addini. Mun manta da al’adunmu, wad’anda aka ara muna, mun kasa iyawa. Na tababta wad’annan abubuwa ne Halimatu ke yi wa shagu’be da: “Sabo Turken Wawa”.

Muradin taronmu a yau, gano irin illolin da suka haifar. Da iyaye da hukuma da masana su tashi haik’an fad’a da su. Ka da a aminta da kitsen rogo. A rege yaudarar k’awalwalniya (ruwan fak’o). A fahinci katawar Nasara ta zamani. A lura, kama da wane ba wane ba ne.

A da, cikin shege abin kunya ne, a yau, ya samu karin magana shege kowa ya Yi. A da, an ce, gaskiya ka fad’a ba sanda ba. A yau, mun ce, fad’a da faskiya tsaro ne. Magabata sun ce, namu namu ne, mu kuwa mun ce, in ka ji namu da mai shi. Addu’ar magabata a koyaushe ita ce, Allah da Ya ba ka rak’umi ya ba ni Zakara. Mu ko cewa muka yi, Allah da Ya ba ka rak’umi Ya ba mu wuk’a zakaran ya ci Ubansa. Duk wad’annan musibun da makanantansu cud’anyarmu da wad’annan na’urorin ya haddasa muna su.

Ina Mafita:


Hausawa sun ce, duk wurin da aka hau ice nan ake sauka. Tabbasa! Karen da duk ya yi cizo da gashinsa ake magani. Masu jihadin k’arni na goma sha tara Mujaddadi ‘Danfodiyo da mataimakansa sun ji muna wannan tsoro tun bai bayyana ba Uryanan (tsirara). Babu mafita face:

  • Girmama namu al’adu kamar yadda suke girmama nasu. Kowa ya yi doro da al’adun gidansu.

  • Yin garkuwa da addininmu ga duk wani bak’on abu da zai shigo mu.

  • Daina koyi da su a kan kowane irin sha’ani, dama kare jini biri jini aka rabu a goshin k’arni na ashirin. In babu k’ira me ya ci gawai?

  • Haramta wa rubuce-rubucensu da wasanni lek’a makarantun da muke koyar da yaranmu tarbiyarmu.

  • Fito da wani sabon salon yekuwar yak’ar rubuce-rubucensu da wasanninsu da suka yi kanta a zukatan matasanmu kamar irin yadda muka taru a yau.

  • Samar da Hukumma ta musamman da za ta fuskanci yak’i da rashin tarbiya da hana bak’in al’adu yin shigan kutse a k’asashenmu.

  • K’irk’iro darusa a kowane mataki na karatu da za su yi arangama da wad’annan abubuwa har sai mun ga baya gare su.


Ana cikin Gina ga wutsiya:


Sabon tsarin da ake son a tilasta a kanmu matsayin addini, wata dabara ce ta  yi muna kwanton ‘bauna. Cikin tsarin ake son a tilasta mu watsi da al’adunmu kyaawawa da addininmu ya halarta muna. Idan ba ku manta ba, da demokradiyya aka koya wa matan arewa karuwanci. Da ita aka haramta wa musulmi arewa da kudu kullin matansu. Da ita, aka la’be aka soke muna shari’ar mahaliccinmu. Da ita, aka la’be a yau (2013/2014) aka haddasa yak’i a arewancin k’asar nan da ba a ta’ba yin irinsa mai muni ba ga tarihin k’asar nan. Gare ta aka la’be, aka k’irkiro muna sunan da ba mu sani ba, ana yi muna kisan kyashi dare da rana. An tozartar da shugabanninmu. An hana muna ‘yancin addininnin da al’adunmu. An tarwatsa muna tattalin arziki. An mayar da mu saniyar wane cikin k’asarmu. An yi amfani da addini da k’abilanci da ‘bangaranci an raba k’asarmu, an sa himmar gamawa da mu gadan-gadan. Mun kasa ta’buka komai har sai da Allah Ya kawo rundunarSa ta rusa rundunar zalunci, duk da haka ba a daina kashe mu ba. Idan ba mu sa wa jikinmu gishiri ba, a za’ben 2015 tun ba a raba akwatunan za’be ba, za a rautsar da shugaban k’asa, ya k’ark’are regowar da guguwar BOKO HARAM da aka k’irk’iro muna ba ta ida ba.

Wallahi! Sai mun d’ebe bambance-bambancen siyasar ta kowane fati, mun rungumi fatinmu mai suna, Addininmu, Al’adunmu, Yankinmu da ‘Yancinmu. Wanda duk ya kar’ba wannan kira, shi ne namu ko da bante ko guntun wando ya bak’unce mu. Wanda ya ce ba haka ba, ba namu ba ne, komai kaurin alkibbarsa da tsawon gemunsa. Idan tabbatar da tutar Biafara ya faskara. Kashe Sir Ahmadu Bello kwalliya ta kasa biyan kud’in sabula. Yunk’urin Gadion Orkah, ya zama kuwa baya ga yak’i. Almarar BOKO HARAM ba ta biyan buk’atu kudurin 2015 da yardar Allah. Marubuta, ga sabon fage nan na rubutu da ya fi fina-finai da na’urorin zamani zama annoba ga arewarmu da k’asarmu.

https://www.amsoshi.com/2017/10/30/sharhin-littafin-ragas/

Nad’ewa


A gai da Halimatu, a girgiza mata da k’wazonta da hasashenta. A gai da babanmu, kuma shugabanmu, mai Martaba Sarkin Musulmi ga yin tsayin daka ga jagorantarmu. Mu yi godiya ta musamman ga mai girma gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Dr. Aliyu Magatakarda Wamakko ga gagaruman ayyukansa biyu da ya yi wa takwarorinsa fintinkau a demokrad’iyar zamaninmu: Na farko, kare martabar Cibiyar Musulunci, Sakkwato na hana matarsa tallar kitso da beje da sunan First Lady. Allah Ya biya shi. Na biyu, yin fito-na-fito, da tawaye, ga k’arya da munafucci da zurmugud’d’u da kisisiniya ba tsoro ba ja da baya. A bisa wannan, Allah Ya yi masa jagora mu kar’be goriba ga hannun kuturu. Masu sauraro malamin kid’a na kiran ku da:

 

Jagora: Na hore ki gaskiya bari tsoron K’arya

Yara: Mai K’arya munafiki Allah su yak’ k’i

 

Jagora: Har yau ba mu ga in da

: An ka yi mai k’arya ba

 

Yara: Amma ita gaskiya

: Gani da mutane tay yi

 

Gindi: Gwarzon shamati na Malam taron giwa

: Baban Dado ba a tamma da batun banza.

Na gode

Manazarta


 

Banza, A.M. 2013 ‘Darussan Daular Sakkwato ga Musulman Nijeriya

na hijirar 1435 AH”. Takardar da aka gabatar a Joint Youth Islamic     Organazation, Zamfara Satate, J.B. Yakubu Secretariat, (Nuwamba, 4.)

 

Bunza, A.M. 2013 “Ido Mudu Ne: Ko Bai Ci Ba Ya San Abin Da Ke

Cika Masa Tumbi,” Takardar da aka gabatar don walimar Samun muk’amin Farfesa ga Farfesa Aminu Abubakar Illela, a Illela L.G Secretariat (Dec. 14,).

 

Bunza 2013 “Muhimmancin Hijira A Kwanan Watan Musulunci”,

Takardar da aka gabatar ga K’ungiyar ‘Dalibai Musulumai ta Najeriya, Jahar Kabi, a    masaukin Shugaban K’asa, BK. Dec, 19th.

 

Bunza, A.M. 2013 “Gurbin Ilimi ga Had’in kai da Cigaban Al’umma”,

takarda da aka gabatar a Zauro Development Association (ZADA) Disamba, 27.

 

Bunza, A.M, 2013 “Promotable Promotion Promotes Progressive

Professionalism”. Beingtext of paper presented at special Fishing Festival Organized in honour of    Justice Faruku Hassan Bunza as High Court Judge, Kebbi State, April, 28th.
www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments