Amsoshi

Abba Muhd Danhausa


07038838301abbamuhddanhausa@gmail.com


 

1. Allahu na sa a farkon fari,
Don ku aminta ba zan yi shirme ba.

2. Yarda a yanzu na tsara baitoci,
Don AnnabinKa ba don mutane ba.

3. Zan yi batu kan gidan sarauta ne,
Masarautar Kano nake duba.

4. Wa za ya cewa cikin gida soro?
Sai ku bige shi ba wai hani nai ba.

5. In na kira dawa sai ya ce kango,
Sai ku sake shi ba hankali ne ba.

6. Sarauta ta Kano akwai girma,
Har tsawon tarihi ba wai ba.

 

https://www.amsoshi.com/2017/06/21/hausa-fasaha-rarrafe-masomar-tashi/

 

7. Ta zagaye Afirika nahiyya,
A sarauta ita ake duba.

8. Fadarta a wajen batun girma,
A Afirika ba ai kama tai ba.

9. Can a farkon fari mulkarta,
Ai Haɓe ne ba su yi wasa ba.

10. Sarkinta cikin Haɓen farko,
Ku ce Bagauda da bai yi wasa ba.

11. Ya sa tsaro a cikin Kano kwata,
Ya faɗaɗa ta bai shuka cuta ba.

12. Ali Yaji Sarkinta jan gwarzo,
Musulunci bai k'i karɓa ba.

13. A cikinsu na ce akwai Rumfa,
Sarki Muhammadu bai yi sanya ba.

14. A lokacinsa na ce ku yo duba,
Shari'a ba ta k'i tsayawa ba.

15. Shi ne ya yo kasuwa ta Kurminmu,
Duk duniya an san ta ba wai ba.

16. Shi ne ya yo figini da alkyabba,
Har a yau ba a rushe wannan ba.

17. Sarakunan na haɓen akwai tari,
Amma kaɗan na faɗo su ku yi duba.

18. Su suka yo aiki dare, rana,
A saurata su ake duba.

19. An ture Sarkinmu Alwali,
Na Haɓe ban ɓoye wannan ba.

20. Sai Daula ta Fulani tat taso,
Sarauta ta Kano ta sa ɗamba.

21. Sarki na Kano cikin Fulɓe,
Suleman bai shuka cuta ba.

22. Shi ne Sarkinmu tun farko,
A Fulani cikin Kano babba.

23. Kayan faɗa, kundi da ma tuta,
Danfodiyo bai k'i bashi wannan ba.

 

https://www.amsoshi.com/2017/08/22/duniyata-kashi-na-farko/

 


24. Ibrahim Dabo Sarki ne,
Na biyu a cikin Kano duba.

25. Sarki Usmanu ɗan Dabo,
Shi ne na ukunsu ba wai ba.

26. Abdullahi Maje Karofi ma,
Na huɗunsu bai shuka ɓarna ba.

27. Sarkin ga Muhammadu Dabo,
Na biyar ne ba da gangan ba.

28. Sarki Tukur na shida cikin Fulɓe,
Sai Aliyu Sarkinmu ne babba.

29. Sarkin Kano na takwas Muhamman ne,
Muhammad Abbas da bai gaba.

30. Usman na ɗaya shi ne Sarki,
Na taransu ban saya wannan ba.

31. Abdullahi Bayero shi ne,
Ya zo a na goma ba su ba.

32. Muhammad Sunusi ma na ɗaya,
Ya yi sarauta ba da wasa ba.

33. Sai Sarkinmu na goma sha biyu ma,
Muhammad Inuwa da bai gamba.

34. Yanzu ko na zo gaɓa babba,
Zan yi tinawa ba zana manta ba.

35. Zan yi batu kan shi don amana ne,
Sunan shi ba wai faɗi nai ba.

36. Gwarzo, hazik'i, fasihi ne,
Tun rasuwarsa ban bar hawaye ba.

37. Domin na zo a mulki nai,
Na gan shi, ba za na manta ba.

38. Kun ji giye ginshik'i na daulata,
Dagumi bai bar mak'eta ba.

39. Indai taro na kairan ne,
Za ka gan shi ba zai ɓacewa ba.

40. Indai tuggu don a k'ulla ne,
Ga talakan shi ba za ya je gun ba.

41. Ya rik'e sakali ya ja daga,
Kan Musulunci bai ji tsoro ba.

42. Kanonmu ya ce ta Malam ce,
Ba su fada ko gumaka ba.

43. Shin wane? Tambaya ce na yi,
Kar ku ce ba ku san shi bai zo ba.

44. Zuciyarsa fara take fes-fes,
Bai san ya zai yi cuta ba.

45. Sarkin ga na goma sha uku ne,
Sunan shi ba zan rufewa ba.

46. Ado Bayeronmu zaki ne,
Rusa Kano bai bar magauta ba.

47. Sarki mai martaba kun ji,
Bai san fa ya tada k'ura ba.

48. Don tuna shi na tsara baitina,
Zani PIN ba zan k'i gasa ba.

49. Na yi hawaye na yi shasshek'a,
Don kamar shi ba za a sama ba.

50. Yau gashi ina ta darawa,
Ya mace bai k'i bar magaji ba.

51. Muhammad Sunusi ne na biyu,
San Kano bai ɗarsa tsoro ba.

52. Shi ne Sarki na goman nan,
Sha huɗu bai zo da wasa ba.

53. Ya san ilimi na addini,
Da na zamani, bai k'i wannan ba.

54. Maganarsa kawai a gyara ne,
Kan talakka bai k'i kulawa ba.

55. Shugabanni kansu hakk'un ne,
Ya faɗa musu, ba da tsoro ba.

56. Lale murna nake ni dai,
Shekara uku bai k'i kaiwa ba.

57. Allah Kai ke da ikon nan,
K'arfafe shi ba don hali nau ba.

58. Don Muhammadu don ak'ida tai,
AnnabinKa da ban k'i k'auna ba.

59. Danhausa nake ku dudduba,
Abba Muhammadu ba da wasa ba.

60. 'Dan Kano nake kun ji daulata,
Unguwa-uku ban rufewa ba.
`
61. Duba dubu biyu har da goman nan,
Sha bakwai ban je kushewa ba.

62. Na yi wak'e na rera wak'ata,
Na gama ban tuɓe warki ba.

63. Sanya haske ya haske daulata,
Allah, ba don halina ba.