Ticker

6/recent/ticker-posts

Hoton Maguzawa Da Maguzanci A Wasu Rubutattun Littattafan Adabin Hausa

Maguzawa Hausawa ne na asali da ke zaune a k’asar Hausa tun da dad’ewa.Tarihin Hausa da Hausawa ba zai kammalu ba sai an ambaci  Maguzawa domin ba su da wani harshe sai Hausa . A k’ok’arin wasu marubuta adabin Hausa wajen isar da sak’onninsu na adabi, sukan kawo hoton Maguzawa da Maguzanci cikin ayyukansu ta hanyar fito da wasu ‘bangarori na rayuwar  Maguzawa da suka had’a da amfani da harshe, da imaninsu na gargajiya, da al’adunsu wad’anda suka sa’ba wa na ‘yan’uwansu Hausawa. Wannan Mak’ala ta yi k’ok’ari ne wajen kawo  hoton Maguzawa da Maguzanci da ke fitowa cikin  wasu rubutattun adabin Hausa.


Hoton Maguzawa Da Maguzanci A Wasu Rubutattun Littattafan Adabin Hausa

Alamuna Nuhu
Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe
Jami’ar Jihar Kaduna, Kaduna Nijeriya
08030472882


Gabatarwa:

Hoton rayuwar wata al’umma takan fito cikin ayyukan adabi wanda adabin Hausa bai ke’banta ba. Hakan na faruwa ne idan marubuci ya ta’ba jin labari, ko gani, ko karanta wani aiki da ya shafi wannan al’umma. Wani lokaci kuma zamantakewa ke kawo nason rayuwar wasu al’ummomi na kusa ko na nesa cikin aikin adabi. Idan kuwa ba haka ba, hoton rayuwar da aka gani wadda marubuci ke bayani; yana yiwuwa jinin marubuci ne da ke da asali tun daga iyaye da kakanni. Kenan asalin marubuci yana iya tasiri cikin rubutu har a ga hoton rayuwar magabata ta kusa ko nesa na mai rubutu, ya sani ko bai sani ba.

Mak’asudin wannan mak’ala shi ne yin bayanin hoton Maguzawa da Maguzanci da suka fito cikin wasu rubutattun littattafan adabin Hausa. Marubutan sun yi k’ok’arin kawo rubutaccen adabin Hausa, amma sai ga rayuwar Hausawa ta asali ta fito. Littattafan da mak’alar ta duba su ne: Magana Jari Ce na uku (Labarin ‘Danhakin da ka raina), da K’arshen Alewa K’asa, da Malam Inkuntum. Muk’alar za  ta dubi yadda marubutan suka fito da wasu ‘bangarori na abin da ake kira Maguzawa da kuma Maguzanci a matsayin hoton rayuwar ta wannan al’ummar.

https://www.amsoshi.com/2017/10/14/makamin-dimokradiyya-falsafar-alada/

Rubutaccen Adabin Hausa:

Hausawa sun sami hanyar ingantaccen rubutu da karatu ne ta hanyar Larabawa da Turawa. Rubutun Ajami shi ne wanda Larabawa suka koya wa Hausawa. To sai dai rubuce-rubucen da Hausawa suka yi cikin ajami ya fi k’arfi a ‘bangaren wak’a. Rashin ayyuka game da zube da wasan kwaikwayo cikin ajami, ba zai rasa nasaba da alak’ar  ajami da musulunci ba. Zuwan Turawa k’asar Hausa ya kawo sauyi cikin rubutaccen adabin Hausa.A dalilin zuwan Turawa k’asar Hausa, sun kafa makarantun boko domin koyar da rubutu da karatun boko na bak’ak’e da wasulla a jere, (Yahaya :1988:72).

A ‘bangaren zube, yunk’urin Turawan Mishan a k’asar Hausa na mayar da adabin bakan Hausa a rubuce  shi ya wanzar da rubutaccen adabin Hausa, (Malumfashi 2009:36-37). Shi kuwa wasan kwaikwayo d’an auta ne cikin rukunin adabin Hausa rubutacce. A cewar Sun Xiaomeng (2013:59)  Malamai irin su: (Malumfashi 1984, da 1985, da 1987), da (Ahmed 1988) sun yi nuni da cewa, akwai sa’banin ra’ayi dangane da lokacin da aka fara samun rubutaccen wasan kwaikwayo wanda ke nuna ba na yau ba ne, tsaran zube ne. Duk da wannan dai, wasan kwaikwayo bai sami tagomashi irin na wak’a da zube ba.

3.0 Maguzawa da Maguzanci:


Maguzawa jam’i ne na kalmar Bamaguje (Namiji). Kalmar Bamaguza ko Bamagujiya kuwa na nufin Mace. Maguzawa su ne Hausawan asali wad’anda  harshen Hausa shi ne harshen da suke amfani da shi tun daga iyaye da kakanni, kuma k’asar Hausa nan ne mazauninsu na asali. Maguzanci ko Magurci shi ne yanayin rayuwar Hausawa da ta dogara  kan imani da tunani  a gargajiyance.

Maguzawa a Wasu Rubutattun Littattafan Adabin Hausa:

Kowace al’umma da ta shahara akwai wasu abubuwa da ake sa ran a ji game da ita a duk lokacin da aka ambace ta. Da zarar an ce Maguzawa, ka ji an yi shedarsu wajen wayau, da gwanintar harshe, da zama cikin daji, da sana’ar noma, da ma sunaye da suka ke’banta da su kad’ai. Duk wad’annan kad’an ne daga cikin hanyoyin   gane Maguzawa. Wad’annan abubuwa da aka lissafo, suna daga cikin abubuwan da muk’alar za ta kalla cikin fasalin Maguzawa da Maguzanci a wasu rubutattun adabin Hausa. Ga yadda hoton nasu suka fito:

4.1 Wayau:

Wayau yana d’aya daga cikin d’abi’ar Maguzawa (Abdullahi, 2008:4). Ana iya gane wayon Bamaguje idan aka yi mu’amala da shi, ko aka ji labarin wani abu da ya faru tsakaninsa da wani. A labarin ‘Dan Hakin da ka raina na cikin littafin Magana Jari Ce na uku, an nuna cewa Maguzawa mutane ne masu wayau. Ga dai abin da Anunu Mahauci da abokansa suke cewa:

Suka hanga, guda ya ce , Bahaushe ina? Kuna ganin Bamaguje, ku dubi irin kayan gogan mana, iya Magana yanzu nan ko d’an Kano.

Daga nan sai guda wanda ake kira Anunu ya ce : “Haba wane wayo ke ga Arne, daga dai an k’yale su”.Guda ya ce: A! Don wayo dai suna da shi.



A nan Anunu da abokansa sun tabbatar da cewa duk wani Bamaguje yana da wayau. To amma dai had’uwarsu a wannan wuri an yi wa Bamaguje hikima an cuce shi.

Shi kuwa marubucin littafin Malam Inkuntum ya nuna wayon Maguzawa ne a wurin da ya ambaci wani Arne da ke neman bawan Allah wanda zai ba d’iyarsa a matsayin miji.Arnen ya gwada wayonsa ga wasu musulmi da cewa:

Arne:Kai! Bawan Allah ne kai in kashe ka maimakon nawa da ya kashe jiya.

Ladan : Lallai  ni kam bawan Allah ne.In ka kashe ni ka kashe bawan Allah.

Arne: Kashe ka fa zan yi yanzu, ko k’yaftawa babu .

Ladan: Ai ta samu gare ka. Allah ya ba mu cikawa da imani, mu tashi da imani, amin.

Arne: (ya mai da gatarinsa a kafad’a, ya kama hannun Ladan ) Zo mu je gidana , kuma kwantad da zuciyarka, ba kashe ka zan yi ba.



Wannan misali ya nuna wayon da Arne ya yi amfani da shi domin ya tantance wanda zai ba d’iyarsa aure. A ‘bangaren su Anunu da Bamaguje kuwa, cutar da Anunu ya yi wa Bamaguje ya rama ta hanyar ‘bad da kama kamar haka:

To Bamagujen nan ya yi kamar ya k’yale, sai da ya bari an yi kamar kwana ashirin har an bar wannan Magana, sai ran nan ya sami kayayyaki farare irin na Hausawa  ya sa, ya nemi rawani ya bayar aka nad’a masa. Bamaguje ya nufi  wajen Anunu ya tarad da shi da kan akuya yana sayarwa. Da zuwansa sai ya dafa kan Anunu, ya dubi kan akuya ya ce: “wannnan kan nawa ne?” Anunu ya ciro ido ya dube shi ya ce: “ Mene ne kuma na dafa mini kai? Ku dai Malamai  kun raina mu..To ga shi nan fad’i abin da za ka biya.



Nan ma wayau Bamaguje ya yi wa Anunu domin ya dafa kansa a matsayin kan akuyar da ake ciniki. A k’arshen wannan ciniki dai sai da aka dangana da gaban alk’ali. Ko da alk’ali ya ji duk yadda aka yi tun lokacin da Anunu ya sayi San Bamaguje har ya zuwa cinikin kan akuya, ya san cewa, Bamaguje ya rama abin da aka yi masa ne. Ga shi kuma Bamaguje ke da gaskiya, don haka a k’arshe dai Anunu ya yi hasara fiye da wadda Bamaguje ya yi lokacin da aka sayi Sansa.

4.2 Muhalli:

A duk inda Maguzawa suke, sun fi son su zauna cikin daji, wato nesa da gari ba tare da mutane sun tsangwame su ba. Wannan ya sa suka ba noma muhimmanci a rayuwarsu fiye da duk wata sana’a. Cikin littafin K’arshen Alewa K’asa marubucin ya yi bayanin muhallin Maguzawan Tsaunin Gwano da cewar:

Wannan gari na Tsaunin Gwano yana da gidaje kamar guda d’ari biyu. A gefen garin akwai wani dogon tsauni wanda ta wajen ne garin ya sami suna. A da can ‘yan shekaru kad’an da suka wuce dukkansu suna zaune a kan tsaunin nan ne.Wannan kuwa ya faru ne saboda tsoron masu harin bayi suna sayarwa.



Nan ma nuni ne da muhallin Maguzawa tun lokacin da suke a saman duwatsu, har ya zuwa saukowarsu daga duwatsu, kuma a cikin daji. A cikin littafin Malam Inkuntum kuwa, an nuna wasu Filani wad’anda bisa d’abi’arsu ba Filani ba ne Maguzawa ne suka fito daga daji zuwa gari .An bayyana wurin da wad’annan mutane suka fito da cewa:

Ana ta rawa da wak’a sai ga wad’ansu Filani su uku sun fito daga cikin daji. Ashe sa’ad da suke can daji yunwa ta kama su har sun tarad da gawar bika sun gasa namansa sun ci.



4.3 Sana’o’i:

Sana’ar da ta fi kowace muhimmanci wajen Maguzawa ita ce noma. Ita suka gada kaka da kakanni, da ita suke alfahari fiye da komi a duniya, (Abdullahi 2008). Ya k’ara da nuna baya ga noma  Maguzawa suna da wasu sana’o’i irin su: k’ira, da farauta, da kiwo. Hoton sana’o’in wad’annan mutane  sun fito cikin littafin K’arshen Alewa K’asa inda marubucin yake bayanin yekuwar farautar shekara da za a yi kamar haka :

“Hyai, hyai!Ina mazajen Tsaunin Gwano, Sarkin K’ira ya gaishe ku . Bayan gaisuwa ya ce a fad’a maku lokaci ya yi wanda duk mai ji da kanshi ya shirya….”

Wani Saurayi wanda ake kira Mailoma yana zaune a kan wani buzu da aka yi da fatar biri ya mik’o hannu suka tafa. Sai ya yi wuf ya mik’e gaban hantsi yana gyaran lagen gwadonsa. Ya ce  bara kuwa an yi farauta da sa’a. Ka tuna lokacin da muka darkaki k’atuwar Barewar nan?

Shi wannan d’an tsoho sunansa Chiwake. Duk garin Tsaunin Gwano da kewaye an san shi da yin jima.Wannan sana’a da yake yi ta sa a kullum ba ya rasa abin yin kayan miya.



Wad’annan misalai sun kawo hoton sana’o’in Maguzawa da suka k’unshi farauta, da jima. To amma ba wad’annan sana’o’in ba ne muhimman sana’arsu ba kamar yadda ya zo cikin littafin , noma shi ne babbar sana’arsu.

Shi kuwa labarin ‘Dan Hakin da ka Raina na cikin Magana Jari Ce ya nuna cewa noma da kiwo suna daga cikin sana’o’in Maguzawa. Farkon labarin ya fara ne da bayanin sana’ar Maguzawa kamar haka:

Wata rana wani Bamaguje ya lafta wa takarkarinsa hatsi, ya kora zai kai kasuwa.Kasuwar da za shi kuwa ana d’am mudu k’warai , don kullum in ya kai kayan takarkarin nan, daga ya sayar sule talatin sai ya sayar talatin da biyar.



Haka ma a cikin littafin Malam Inkuntum, lokacin da Arne ya je neman bawan Allah, ya nuna cewa shi manomi ne inda ya ce:

Arne:Kai tsaya tambayarka zan yi. Akwai mutane cikin akurkin nan naku?

Malam Almu: Ai tukuna. Yanzu dai muke harama. Anjima kad’an za a taru. Sallar za ka yi yau?

Arne: Tir! Me ya kai ni wannan abin duk’e-duk’e ba wurin noma ba.



Wannan Arne ya nuna babu wani abu da zai sa ya dinga wasu duk’e-duk’e indai ba wurin noma ba. A ganinsa wurin noma ake yin duk’e-duk’e a nasa tunanin.

4.4 Sunaye:

Suna shi ne kalmar da ake amfani da ita wajen kira ko ambato ko wani abu, (K’amusun Hausa 2006:401).Akwai abubuwa da dama da kan ba da haske wajen sa wa yaro ko yarinyar da aka haifa suna. Cikin irin wad’annan abubuwa akwai: yanayi, da halin haihuwa, da yanayin haihuwa, da siffar mutum , (Yahaya 1979:5-8). A  wasu lokuta kuma, akan sa sunan wata dabbar daji ko ta ruwa a matsayin suna ga Maguzawa. Wasu daga cikin sunayen gargajiya da aka yi amfani da su cikin wad’annan littattafai guda uku  su ne:

Arne: Wanda ke yin tsafi, kuma ana kiran Maguzawa da wannan suna

Bamaguje: Suna ne na namiji tilo mai bin addinin gargajiya na Hausa

Dubu: Wadda aka haifa lokacin da ake yin bikin dubu da tambarci

Hantsi: Yaron da aka haifa lokacin da rana ta fito kafin ta kai tsakiya

Juda: Suna ne na wata dabbar daji mai kama da Mage.Ana samun turare daga wasu sassa na wannan dabba

Maguzawa: Jam’i ne na kalmar Bamaguje

Malka: It ace Yarinyar  da aka haifa lokacin da ruwan damina ya kai tsakiya

Sarkin Arna: Shugaban Maguzawa kuma mai jagorancin bautar gargajiya

Sarkin  Dodanni: Abin bautar gargajiya ne

Sarkin Noma: Mai yin jagoranci wajen harkokin noma

Sarkin Tsafi: Mai yin jagoranci wajen tsafi

Tayani: Sunan abin zama ne wanda aka sak’a da kaba tare da fatu, mata suke kad’i kansa

Tamu: Suna ne da ake saw a yaron da aka haifa shekarar da gyad’a ba ta yi kyau ba

Maguzanci a Wasu Rubutattun Littattafan Adabin Hausa:

Imani da tunanin Maguzawa na gargajiya shi ke jagoranci wajen tafiyar da harkokin rauwarsu.Wannan shi ne abin da ya bambanta Maguzawa da sauran ‘yan’uwansu Hausawa.Wannan fasali ya dubi wasu ‘bangarori cikin imani da tunanin Maguzawa a gargajiyance da suka had’a da bautar gargajiya, da cin mushe da sharholiya, da zagi da batsa da dai sauransu.

 5.1 Bautar Gargajiya:


Bauta da abin bauta a wajen Maguzawa suna da muhimmancin gaske, don haka suke kiyayewa da mutunta duk wani abu da ya shafe su. A tsarin bautar Maguzawa, akwai abin da ake yi wa bauta, da wurin bauta, da hidima ga abin bauta, da kiyaye dokokin abin bauta, da kuma sakamakon da ake samu ida an sa’ba ma abin bauta.

5.1.1 Abin Bauta:

Addinin Maguzawa addini ne na gargajiya ne da suka gada wajen iyaye da kakanni. Hanyoyin bautar Maguzawa su ne tsafi ,da bori, da mu’amala da dodo.Abubuwan da suke bauta ma kuwa su ne Aljanu, da Dodanni, da wata dabba da sukan ke’be, ko wani itace.Aljanu su ne abubuwan da suka fito a matsayin abin bauta cikin wannan aiki. Misali, a rigimar Bamaguje da Anunu Bamagujen na cewa:

Da ni dai na fi son kan da kome, don  in kai wa gunkinmu ya sha jinni.



Bayanin wannan Bamaguje ya nuna cewar gunki yake bauta ma, amma ba gunkin ba ne aljani yake nufi domin gunki ba ya shan jini. Shi kuwa littafin K’arshen Alewa K’asa Aljani ne aka ambata a matsayin abin da suke yi wa bauta. Ko da yake an ce yakan fito cikin siffar maciji ko wani abin daban, amma dai Aljani ne. An bayyana shi da cewa:

Wannan surin yana k’ark’ashin wata babbar tsamiya ce …… Sarkin Arna da jama’arsa Talakawa sun yarda cewa wai a cikin wannan surin akwai wani tsohon Aljani. Shi wannan Aljani an san shi a cikin siffar maciji, ko da yake an ce kuma ba abin da ba  ya rikid’a.

Shi ma wannan ya nuna babu tsayayyar sifar da abin bautar yake da ita, sai dai a iya cewa ya fi bayyana cikin sifar maciji.

Ana iya samun jinsin mata cikin aljanun da ake yi wa bauta kamar yadda Arnen cikin littafin Malam Inkuntum ya ce:

Ladan: Na ji na yarda, amma ina so a d’aura aure.

Arne: Ku yi can ruwa ga wuya, in ji mata.Ai ni tun da Uwar Dawa (aljana) ta yi mini izini, iyakar nawa ke nan.(arne ya koma gida).



5.1.2 Wurin Bauta:

Maguzawa ba kamar sauran mutane ba, sukan ke’be wani wuri na musamman domin yin bauta. Duk wurin da suka ke’be suna yin bauta nan ne mazaunin da abin bautar tasu yake. Suna kula da wurin fiye da makwancinsu ta fuskar tsaftacewa, da ba wurin kariyar da ta dace musamman ga wanda bai san darajar wurin ba. Irin wannan wuri na iya kasancewa d’aki a cikin gida, ko bishiya a k’ofar gida ko bayan gari. Misali cikin littafin K’arshen Alewa K’asa an ambaci wurin bauta da cewa:

Ita fadar Sarkin Dodanni wani irin wuri ne inda yake da wani irin babban suri wanda girmansa ya kai tsawon mutum uku dogaye.

Wannan surin yana k’ark’ashin wata babbar tsamiya ce, kuma a kowace rana Sarkin Arna yakan sanya yaran shi su share wurin nan fes. Su dai abin da suka ji kaka da kakanni shi ne: Wannan aljani sunansa Sarkin Dodanni. Haka kuma shi ne abin da za a bauta ma wa.



Lallai wannan wuri ya amsa sunansa wurin bautar gargajiya na Maguzawa kasancewarsa bayan gari, kuma ga suri jikin bishiyar tsamiya[1] wanda ake sharewa a duk safiya.

5.1.3 Hidima ga Abin Bauta:

A tsarin bautar gargajiya ana yin hidima ga abin da ake yi ma bauta. Hidimar da ake yi ta had’a da tsaftace wurin , da yin yanka ga abin bauta, da sagale k’asusuwan dabbar da aka farauto, da yin kyautar mutum ko dabba ga abin bauta. Cikin labarin Bamaguje da Anunu na Magana Jari Ce, an nuna inda Bamaguje ya so a bari ya yanki Anunu domin Gunkinsu ya sha jini .Bamagujen na cewa:

Da ni dai na fi son kan da kome, don  in kai wa gunkinmu ya sha jini.



A littafi K’arshen Alewa K’asa kuwa, an yi bayanin hidimar da ake yi wa abin bauta kamar haka:

A kowace shekara Sarkin Arna yakan zo ya yi sujada, kuma ya kawo wa Sarkin Dodanni ‘yar gaisuwarsu. Irin gaisuwar da Sarkin Arna ke kawo wa  tana da nauyi k’warai.Watau kyautar da ake yi ita ce rai guda na mutum.  



Ita ma wannan hidima masu gudanar da bautar sun gaje ta ne tun iyaye da kakanni ba sai cikin wani labari ba. A wajen wasu Maguzawan kuwa, ba sa bayar da ran mutum sai na dabba.Bayanin Maguzawan garin Jinjin Wawa na cikin K’arshen Alewa K’asa ya tabbatar da haka:

Jinjin Wawa wani gari ne wanda shi ma girmansa kamar na Tsaunin Gwano yake.Suna da Sarkinsu na tsafi, to amma shi ba a ba shi ran mutum sai na dabba.



5.1.4 Sakamakon Sa’ba Ma Abin Bauta:

A duk lokacin da ake gudanar da bauta a Maguzance, ya zama wajibi a kiyaye tare da mutunta wannan abin bauta. Idan ba haka ba za a ga sakamako wanda ba dad’i. A lokacin da Mailoma ya yi karambanin zuwa fadar Sarkin dodanni ya aikata abin da ba a yi kamar haka:

Da yake wannan yaro baya cikin hankalinsa, ko tufafinsa bai tu’be ba.

Da ya ji tarin ya k’i tsakaitawa sai ya tura d’an yatsa a mak’ogwaro ya yiwo aman giya a kan surin nan

Ya ce ma suri, “sha mana”

            Ya sake kecewa da dariya.



Wannan rashin kunya da Mailoma ya aikata ga Sarkin Dodanni na daga cikin abin da ba a yi a wurin tsafinsu. Yin haka kuwa kan haifar da mummunan sakamako ga wanda ya aikata. A dalilin wannan rashin kunya da Mailoma ya yi, wasu abubuwa sun faru da shi kamar haka:

Ai wannan babu shakka cizon maciji ne, don kuwa ga alamar d’an jini da kuma shaidar hak’ora.Maciji? Aha ga amsa a fili. Nan take ya fusata ya yi ruri cikin dajin nan yana kira, MACIJI. MACIJI! SARKI. SARKI! Kai  ne ka cinye Tayani.

To a tsammani na Sarkin Dodanni bai yi niyyar d’aukar ran wannan yarinya ba, domin wannan shi ne cikon kwana na bakwai da bayar da ita.Kai Mailoma kai ne ka tilasta ma Sarkin Dodanni har ya amshi wannan gaisuwar.Yau d’in nan bayan ka shawo giya ka bugu , ka shiga fadarsa ka yi ta shegantaka, haka ne?

https://www.amsoshi.com/2017/10/20/mene-ne-bori-fashin-bakin-maanarsa-cikin-taskar-harshe-adabi-da-alada/

Cikin wad’annan bayanai dai, an ji yadda Mailoma ya fahimci cewa maciji (Sarki) ne ya ciji Tayani, da kuma labarin da Akkati take ba shi domin ta tabbatar masa da wanda ya kashe matarsa a sakamakon sa’ba wa Sarki da ya yi.

5.2 Zagi da Batsa:

Zagi shi ne fad’a wa mutum bak’ar magana ko bacin iyayensa, (K’amusun Hausa 2006: 487). Zagi wani ‘bangare ne cikin lafuzzan d’aurin auren Maguzawa wanda a  wasu lokuta yake zuwa surke da batsa. Maguzawa suna sanya zagi cikin lafuzzan d’aurin aure domin wanda yake da niyyar k’alubalantar d’aurin aure idan ya tuna girman zagin, da kallon da jama’a za su yi masa ya fasa, (Abdullahi 2008: 5-7). Ko ba wurin d’aurin aure ba Maguzawa sukan yi ashar cikin magana ta yau da kullum, ko da kuwa zagin surke yake da batsa.A irin wannan yanayi, ba sa jin nauyi ko kunyar wani don sun yi irin wad’annan kalamai. Misali an sami zagi cikin litttafin K’arshen Alewa K’asa a yayin da Mailoma yake yin kirari kamar haka:

Ni ne na bara ni ne na bana

Mijin Tayani dogon yaro

Samun irinku sai an tona

Yaro ko kana musu in ci ubansa.



Haka kuma Mailoma ya sake kunduma wani ashar d’in lokacin da matarsa ta sheda masa tana da juna biyu inda ya ce:

Sai ni Arne tsaran manya na Chiwake da Tayani. Yaro ko kana shakka ne yanzu in ci k’undun durin uwarka.



Batsa ita ce maganar banza musamman wadda ta danganci ambaton al’aurar mace ko namiji. Ga Bamaguje, batsa ta zama jiki, domin tana cikin lafuzzan d’aurin aurensu. A maganganun yau da kullum, al’ummar Maguzawa ba sa jin kunyar yin batsa. Haka ma a littafin K’arshen Alewa K’asa batsa ta fito a wannan wurin kamar haka:

Dutsen nik’a: Kakir-kakir

Malka: “Ba ruwan ka da yaron kowa”

Malka ta sake maimaitawa.

            “Ba ruwan ka da yaron kowa

            To, zagayo ka ci gutsu,

            A hankali ba da garaje ba”.

Batsar da ke cikin wannan zance na Malka tana k’unshe da kalmomi wad’anda idan ba Bamaguje ba, babu wanda ke iya fad’i ba tare da jin kunya ba .Dalili kuwa, an ambaci al’aurar mace ba tare da jin kunya ba.

5.3 Cin Mushe:

Hausawa na cewa: “kyawun Bamaguje ya ci mushe”. Mushe shi ne naman wata dabba ko tsuntsu da ya mutu ba tare da an yanka ba. A wurin Maguzawa dabba ko tsuntsu da ya yi mushe nama ne mai kyau. Wasu Maguzawa da aka kira da sunan Filani cikin littafin Malam Inkuntum, an nuna cewa sun ci mushen Biri a cikin daji kafin su iso gari. Mrubucin na cewa:

Ana ta rawa da wak’a sai ga wad’ansu Filani su uku sun fito daga cikin daji. Ashe sa’ad da suke can daji yunwa ta kama su har sun tarad da gawar bika sun gasa namansa sun ci. Sun yi wa juna alk’awarin ba wanda zai fad’i wannan Magana har abada. Ko kafin su iso nan k’ishirwa ta kama su k’warai da gaske. Sai kuma suka ji durin kid’a ake yi, suka tona asirinsu.

Bafillace na Farko: Ho d’an Kare da ba da k’ishirwa

Bafillace na Biyu: Hala kana so ka fad’i.

Bafillace na Uku: He, ku fad’i, mun ci biri, mun ci biri, mun ci biri.

5.4 Sharholiya:

Sharholiya ita ce yin abubuwa na jin dad’in rayuwa da nufin more rayuwa da shak’atawa. Abubuwan sharholiya ga Bamaguje su ne shan giya, da wasanni, da auren mata da yawa, da yin bukukuwa, da sha’awar doki, (Abdullahi 2008:5) Daga cikin wad’annan d’abi’un, giya ita ce ta mamaye littafin K’arshen Alewa K’asa. A farkon littafin an fara  zancen giya lokacin da ake sanarwa domin gayyatar farauta da cewa:

Hantsi ya ajiye k’ok’on da ya gama shan burkutu da shi, ya yi wata doguwar mik’a ya yi murmushi.Hantsi ya k’ara ciko k’ok’onsa da giya ya ce: A wannan rana duk tsawon rai na ba zan iya mantawa da ita ba. Lallai da ban sa baki ba da ai da kun yi d’anyen aiki, ya mik’o masa giya cikin k’ok’o, Mailoma ya kar’ba….

Ko da ake yin wannan sanarwa, wad’annan samari suna cikin sharholiyarsu ne da giya. Wannan ya nuna cewa rayuwa ba ta gudana wurin Maguzawa sai da giya, kuma wa da k’ani suna iya had’uwa su sha ba tare da sun ji komi ba.A lokacin da Mailoma ya je yi ma Juda gaisuwar d’ansa, an nuna cewa ko a nan sai da ya sha giya ya yi tatul har aka ba shi wadda ya yi guziri da ita.Juda ya fara bayani da cewa:

Ku kawo masa giya nan, hankalin yaron nan ya tashi.” Ku yi sauri mana ku zubo, ka bar kukan nan.” Bayan an zubo giya a k’ok’o sai aka mik’a wa Mailoma don ya sha.Ya kar’ba.

Bayan da Mailoma ya k’are zaman gaisuwa , sai ya yi sallama da jama’a ya nufi k’auyensu. Ko da yake dai shi ya yi sallama da mutane, amma a gaskiya bai san lokacin da ya yi ba. Giyar da ya d’irka da kuma naman da ya ci duk sun yi masa babakere a ciki. Ga shi saboda buguwar da ya yi har da k’yar yake iya takawa.

Kuma tun lokacin da ya zauna gindin su Manje maikukuma yake d’aukar k’ok’o bisa k’ok’o na burkutu, wanda ma ba ya ko d’an saurarawa domin ya huta.

Ya tinkaro hanyar Tsaunin Gwano da wani goran giya mai girma a hannunsa. Wannan kyauta ce wadda Juda ya yi masa saboda ba a samu wani wanda ya kama k’afansa wajen shan giya ba.



Kusan kowane lungu da sak’o na rayuwar Maguzawa, giya ba ta rasa gurbi. Idan kuwa babu wata hidima, to haka nan ma sukan sha domin annashuwa.

6.0 Jawabin Kammalawa:


Maguzawa da Maguzanci tamkar ‘Danjuma ne da ‘Danjummai. Dalili kuwa shi  ne a duk wuraren da aka ambaci  Bamaguje, sai an had’a da wani ‘bangare na abin da ake kira Maguzanci. Ke nan hoton Maguzawa da Maguzanci cikin wasu littattafan adabi, rayuwa ce ta wata al’umma da wasu marubuta suka k’yallaro cikin fasaharsu a rubuce. Kowane littafi k’ok’arinsa shi ne, a fahinci su wane ne Maguzawa? Yaya rayuwars take? Binciken ya k’ara fito da bayani game da yadda Bamaguje ya d’auki abin bautarsa, da bin umarninsa, da kiyaye dokokinsa. Haka kuma an kawo cikakken hoton d’abi’un Maguzawa ta fuskar sharholiya, da tsafi, da bautar gargajiya. To sai dai a ‘bangaren littafin K’arshen Alewa K’asa, shi ya fi kawo hoton rayuwar Maguzawa a ‘bangarori da dama. Da alama marubucin yana da kusanci da Maguzawa fiye da Abubakar Imam, da Dogondaji. Dalili kuwa, rayuwar Maguzawa da Maguzanci ne suka mamaye littafin K’arshen Alewa K’asa. Littafin ya kawo fasalin wasu tsafe-tsafe na Maguzawa da suke gudanarwa a harkokin rayuwarsu. Haka kuma, littafin bai tsaya ga bayanin Maguzawa da Maguzanci a gargajiya kad’ai ba. Ya kawo rayuwar Maguzawa da Maguzanci a  zamanance, duk da ba a kansa ne muk’alar ta ginu ba.

https://www.amsoshi.com/2017/10/14/gudu-bahaushen-tunani/



 Manazarta

Abdullahi, I.S.S. 2008. Jiya  Ba  Yau  Ba: Waiwaye  a Kan Al’adun Matakan  Rayuwar  Maguzawa na Aure  da  Haihuwa da  Mutuwa. Kundin Digiri Na Uku. Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Abdullahi, I.S.S 2008. “Fitattun ‘Dabi’un Maguzawa”, Maiduguri Journal of Linguistics and Literary Studies, (MAJOS) Volume. x Department of Language and Linguistics, University of Maiduguri.

Abdullahi, I.S.S 2008. “Bamaguje da ‘Dan Akuya: Rashin K’auna Ko K’iyayya?” Departmental Seminar Series, Department of Nigerian Languages, Usmanu ‘Danfodiyo University, Sokoto.

Abdullahi, I.S.S  2012.  “Falsafar ‘Daurin Auren Maguzawa”. Muk’alar da Aka Gabatar a  Taron K’ara wa Juna Sani a Cibiyar Nazarin Hausa, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Abdullahi, I.S.S. 2014. “Matsalolin Koyar  da Maguzantattun Wak’ok’in Hausa”. Mak’alar Da Aka Gabatar A Taron Kara  Wa Juna Sani  Na K’asa da K’asa A kan K’alubalen Koyar Da  Harsunan Afirka, Niamey Jamhoriyar Nijer.

Bunza, A.M. 2006. Gadon Fed’e Al’ada. Tiwal Nijeria Limited, Lagos.

Dogondaji, A. 1995.Malam Inkuntum. Norla, Zaria.

‘Dangambo, A. 1984. Rabe-raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausa.

Triumph Publishers, Kano.

Gagare, B. 1982. K’arshen Alewa K’asa. Northern Nigerian Publishing Company ltd,      Zaria.

Ibrahim, M.S. 1982. Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan  Rayuwar Hausawa. Kundin Digiri Na Biyu.Sashen Harsunan Nijerya, Jami’ar Bayero, Kano.

Imam,A. 1939.Ruwan Bagaja.Literature Bureau,Zaria.

Magaji, A. 2002. Wasu Al’adun Hausawa: Yanaye-Yanayensu  A K’asar Katsina. Kudin Digirin Na Uku.Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Malumfashi, I. A. M, 2009.Adabin Abubakar Imam. Garkuwa Media Services, Kaduna.

Nuhu, A. 2014. Maguzantattun Karin Maganar Hausa. Muk’alar da aka Gabatar a Taron K’ara wa Juna Sani na K’asa da K’asa na Farko kan Nazarin Hausa a K’arni na 21,Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Sa’id, B. da wasu (ed) 2006. K’amusun Hausa. Ahmadu Bello University press Ltd, Zaria.

Umar, M.B. 1987. Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Gargajiya. Triumph Publishers, Kano.

Xiaomeng,S. 2013. Rubutaccen Wasan Kwaikwayo a Rukunin Adabin Hausa: Ha’bakarsa da Muhimmancinsa. Gidan Dabino Publishers, Kano.

Yahaya, I.Y.1979. Sunayen Hausawa na Gargajiya da Ire-iren Abincin Hausawa. Jami’ar Bayero, Kano.

Yahaya, I. Y. 1988. Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Northern Nigerian Publishing Company, Zaria.









[1] Itacen tsamiya yana d’aya daga wurin da Hausawa suka yi imani da samuwar iskoki tare da shi.Haka shi ma suri yana cikin wurare na musamman da iskoki ke zama.Don k’arin bayani, dubi Bunza, A. M. 2006. Gadon Fed’e Al’ada.Tiwal Nigeria Limited, Lagos.Shafi na 10-14.

Post a Comment

2 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.