Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma’aurata 45: Tambayoyin Neman Ƙarin Haske


13) In ka ba ta izinin ta taɓi kuɗinka tana da hankalin taɓar yadda ya dace komai yawansa?...


Kundin Ma’aurata 45: Tambayoyin Neman Ƙarin Haske

Baban Manar Alƙasom
Zauren Markazus Sunnah


Wannan karon maza nake son su amsa min waɗannan tambayoyin, babu laifi in wata ta amsa don ƙarin haske (a- koda yaushe, b- galibi, c- wani lokaci, d- ba koda yaushe ba e- bai faruwa):-

1) Tana maka biyayya in ka yi mata umurni a kan abin da bai saba Sharia ba?

2) In ka kalle ta tana faranta maka rai?

3) Tana gamsar da kai a komai ba ta bari ka yi fushi da ita?

4) Takan kubutar da ramtsuwarka?

5) Takan kare kanta in ba ka?

6) Takan sanya diyoyinka a turba ko ba kanan?

7) Takan yi tattalin dukiyarka ba ta almubazzaranci?

8) Ba ta yarda wani ya bi shimfidarka?

9) A kullum ƙamshimta kawai kake ji?

10) Ta iya harshenta a lokacin da take magana da kai?
.
11) In ka kawo wani abu ba ta yi maka gardama?

12) Ta tsare maka gida yadda ba mai shiga sai wanda kake so?

13) In ka ba ta izinin ta taɓi kuɗinka tana da hankalin taɓar yadda ya dace komai yawansa?

14) Takan yi maka ado a gida ko ba za ta fita unguwa ko wurin aiki ba?

15) Takan tafi inda ba kai mata izini ba?

16) Takan yi maka zancen wasu 'yammatan?

17) Takan yi maka nasiha da ciyar da su da halal?

18) In ka dawo takan tarbo ka da murna da farin ciki?

19) In ka baza takardu ko littafai ko jaridu takan yi ta surutu?
.
20) Takan ƙarfafa maka gwiwa kuwa tare da yaba maka a kan ayyukan gida?

21) Takan gaya maka maganar da take so in ta fusata ko a gaban uwayenka ne da 'yan uwanka?

22) Gwana ce a wurin dafa abinci ko tsaftar gida?

23) Takan nesanci abubuwan da ta san ba su da amfani?
.
24) Takan tashe ka ko yaran gida don tafiya masallaci salla kuwa?

25) Tana ibada sosai, masamman salla?

26) Tana kula da kayayyakin wuta don gudun lalacewarsu?

27) Takan zabi kyawawan kalmomi lokacin da za ta yi maka nasiha?

28) Da wani irin sauti take magana da kai, mai taushi ne ƙwarai kuwa?

29) Idan za ka yi tafiya takan yi ta yi maka addu'a?

30) Takan riƙa taimaka maka a ayyukan jiki waɗanda suka dace ita, kamar wanke abin hawa a cikin gida?

31) Tana ƙoƙarin bin diddigin sirrorinka kuwa?
.
32) Ka taba kamata tana maka binciken waya ko computer?

33) Ka taba jin tana bambayar wasu a kanka?

34) Tana biyo ka wasu wurare don ta ga me kake yi?

35) Takan gaishe ka da safe?

36) Takan sanya diyoyinka su zo su gaishe ka?

37) Tana ƙoƙarin fitar da girmanka a gaban 'yan uwanta da naka?

38) Tana ajiye 'yan uwanta a inda ya dace?

39) tana yi wa uwayenka ladabi da biyayya?

40) Takan ziyarci uwayenka akai-akai?
.
41) Ka taba jin cewa tana taimakon mahaihiyarka aiki?

42) Takan dan yi wa mahaifanka wani dan ihsani kamar yadda take yi wa nata?

43) Kukan sami sabani don ka ce ba za ka taimaki wani dan uwanka ba?

44) Takan tunasar da kai mahimmacin bin uwaye?

45) Takan nemi ku je wurin uwayenka tare?

46) Takan fifita uwayenta a kan naka?

47) Takan nemi  shawararka kan wasu matsalolinta?

48) Takan sami sabani da mahaifiyarka?

49) Takan kawo maka kukan yaranka da ba ita ta haife su ba koda yaushe?
.
50) Tana ƙoƙarin yin adalci tsakanin yaran da suke gabanta a magana da abinci da tufafi da wurin kwana?

51) Takan zabi lokutan gaya maka matsalolin gida?

52) Indai kana gida kakan lura da wani jindadi tare da ita?

53) Komai na gidan takan ajiye shi inda ya dace?

54) Ban-dakinta da kicin da tsakar gida komai zanzan ne?

55) Takan zabi farintinka da cokalinka da kofinka na masamman ko wanda kowa yake ci kai ma kake ci?

56) Kullum butarka da ruwa ko kai kake zubawa in za ka yi aiki da ita?

57) Takan dan yi maka ƙari a cefane?

58) Takan rage cefanenka ta yi adashe da shi?

59) Tana yawan jawo maka matsaloli kamar fada da maƙwabta?

60) Ta san cewa ibada take yi da zaman aure ba taimakonka take yi ba?
.
61) Takan karbi abin da ka ba ta ba ta rainawa?

62) Takan wanke maka kayan ciki kamar kamfai da dingileti da kanta?

63) In ba ka da lafiya takan iya barin komai a dalilinka?

64) In tana da kishiya tana yin adalci kuwa?

65) Tana ƙaunar abokiyar zamanta kamar 'yar usarta musulma?

66) Tana hada kan 'ya'yan a matsayin 'yan uwa don su yi zumunci nan gaba?

67) Tana yawan kawo maka gulmammakin jama'a?

68) Takan matsa maka ka yi abu ko ba ka da shi?

69) Ka lura tana yawan yi maka addu'a?

70) Akwai lokacin da za ka ba ta abu ta ajiye don aikin gida don ta hutar da kai.

Post a Comment

0 Comments