Ticker

6/recent/ticker-posts

Kundin Ma’aurata 46: Kafin Ka Zama Maigida na Ƙwarai

15) 'Yan uwanka ka iyakance mata irin yadda kake so ta yi mu'amalla da su. In sun raina ta kai ka jawo mata. In ta wulaƙanta yayyinka ba ta ɗauke su komai ba duk kai ne sila...


Kundin Ma’aurata 46: Kafin Ka Zama Maigida na Ƙwarai

Baban Manar Alƙasom
Zauren Markazus Sunnah



1) Ka tabbatar da cewa aurennan saboda Allah SW za ka yi ba don kawar da sha'awa ba.

2) Ya zamanto cewa wace za ka auro za ta iya ba ka kariya daga fadawa abubuwan da Allah SW ya hana.

3) Kar ka dogara da bangaren sha'awa kawai wajen zabar wace za ka aura.

4) Uwar yara za ka auro, wace za ta tarbiyantar da diyoyinka mata,  ba wace ita ma take buƙatar tarbiyar ba, wanda bai da abu ba zai iya bayar da shi na.

5) Duk yadda za a yi ka dauko wace za ta girmama mahaifanka da 'yan uwanka kamar yadda kake girmama su kai ma.

6) Ka zabo wace za ta yi musu hidima ta taimaka musu da wani aikin kamar yadda ta riƙa taimakon nata kafin ta zo gidanka.
.
7) Ka zabo matar da za ta iya cuduwa da uwayenka a matsayin zuriya daya, ba tare da ƙyashi ko tsaginagini ba.

8) Ka yi tunani sosai wajen daukar wace za ka iya tanƙwara ta, ka saka ta a hanya ta ƙwarai, ba wace in ka gama biyan sha'awarka za ta wargaza maka gida ka dawo kana da-ka-sani ba.

9) Kar ka yarda ka yi mata ƙaryar mallakar  abin da ba ka da shi, girmanka zai fadi a idonta tun shigowarta gidanka in ba ta gansu ba.
.
10) Ka yi ƙoƙarin bayyana mata wasu abubuwan da ka san za su iya bata ka a idonta kafin ta ji su ta wata hanyar.

11) Tunda aurennan ibada ne, ka yi tunanin yin abin da Allah SW ya yarda da shi don ya sanya muku albarka, ka kiyayi abin da zai fusata mahalicci a ciki, kamar bukukuwan kide-kide da cakuduwar maza da mata da bayyana tsaraici zuwa shaye-shaye.

12) Ka yi ƙoƙarin yin walima wajen dafa abinci mai rai da motsi ka kira bayin Allah na gari su ci, wato waɗanda za su yi maka addu'a su yi wa mahaifanka.
.
13) Ka yi ƙoƙarin zama da iyalinka tun farko ku sabonta fahimtar juna, kowa ya san abin da junansa yake so da wanda ba ya so.

14) Ka nuna mata girman mahaifanka, kai ma ka girmama su, sai ita ma ta dauke su yadda ka dauke su.

15) 'Yan uwanka ka iyakance mata irin yadda kake so ta yi mu'amalla da su. In sun raina ta kai ka jawo mata. In ta wulaƙanta yayyinka ba ta ɗauke su komai ba duk kai ne sila.

16) Kar ka sabar mata da abin da ka san ba za ka iya jure kawo mata koda yaushe ba, kamar kudi, ko nau'in abinci, ko tufafin sakawa, ko matsuguni.
.
17) Ka sabar mata da ibada, kamar salla kan lokaci da azumi irin na nafila da sauransu.

18) In ka ga ba ka da lokacin koyar da ita addini ka yi ƙoƙari ka bar ta ta je inda za ta koya.

19) In ka yi mata alkawarin wani abu kafin ka aure ta, kamar ci-gaba da karatun boko ka yi ƙoƙari ka cika.

20) Ka fara kai ta wurin uwayenka ka gaya mata yadda za ta taimake su.

21) In ka ga ba ta iya wani abu na gida ba, ka samo hanyar da za a gyara cikin dabara da sauƙin kai.

22) Mace ba ta son hayaniya, ka san yadda za ka riƙa yi mata fada, da inda ya dace ka yi din.

23) Kar ka riƙa kushe ta idan ta yi maka abu.

24) Tana son in ta yi abu ka yaba mata, ka daure ka riƙa fadin ra'ayinka game da duk abin da ta yi maka.

25) Babban abin da ta fi buƙata shi ne a zauna da ita a saurare ta.

26) Komai shagulgulanka ka riƙa ware lokacin da za ka zauna da ita ku yi wasa da dariya.

27) Ka sani cewa mata da yawa ba saduwar aure ne kadai matsalarsu ba, har da rashin zama da su.

28) Idan iyalinka ta fara kawo maka kukan wani abu koda ka san shi ka saurare ta ta gama kafin ka fadi ra'ayinka.
.
29) Ka sani cewa ba wai mafita kawai take nema ba, tana ma son ka riƙa jin matsalolinta kuna tattaunawa.

30) In ta yi kuskure ka yi mata hanzari, dole hakan ya faru.

31) Kar ka riƙa raina hankalinta don ta saba maka, kamar ka ce mata yarinya ko maras hankali.

32) In ka ga kuskurenta sau daya ka tuna goma na arziƙi da take maka.

33) Ka riƙa kallon bambancin dake tsakaninku na shekaru da wayewa da wadata wurin yi mata hanzari.

34) Ka riƙa kallon cewa ita ma fa 'yar gata ce a wurin mahaifanta kafin ka rabo ta da su ka kawo ta gidanka.

35) Ka dauke ta a matsayin mataimakiyarka in kana gida, in kuma ba kanan ka ba ta kujerarka.

36) Ka sa ido sosai a yadda take mu'amalla da kowa in kananan ko ba kanan.

37) In kana da matsala da shimfida ka nemo magani.
.
38) Ki kiyayi wasu nau'o'in abinci da suke rage sha'awa kamar abubuwa masu tsami ko daci, ko shan zobo ko latas da 'yan mintuna kadan kafin jima'i.

39) In kana saurin kawowa ka koyi dabarar saduwa, ka riƙa tafiya mai tsayi a ƙasa, ka lura da nau'in abinci.

40) Ka ji tsoron Allah wajen saduwa, ka tabbatar ita ma tana biyan buƙatarta ba kai kadai kake biyan naka ba.

41) In ka zo saduwa ka yi ƙoƙari ta riga isa ƙololuwa don in ka riga isa sauka za ka yi.
.
42) In tana da juna biyu sai ka riƙa haƙuri, saboda tsarin da Allah ya yi mata a lokacin na tsananin buƙatarka, da saurin fushi ba dalili ko ninkuwar kwadayi.

43) Ka fahimci cewa haihuwa ta Allah ce, in matarka ba ta haihuwa ba haka take so ba, kar ka ƙara mata damuwa.

44) Kar ka bari uwayenka ko 'yan uwanka su wulaƙanta ta a kan abin da ba a hannunta yake ba.

45) Alhakin samun da namiji hukuncin Ubangiji ne, sannan kai ne kake iya fitar da ƙwan namiji ko mace ba ita ba, kar ka ce tana haifa maka 'ya'ya mata.
.
45) Ka sani cewa yawan haihuwa ba matsalarta ba ce, kai kake yin cikin.

46) Kar ka matsa mata sai ta yi tsarin haihuwa don abu ne da yake da jibi da lafiyarta, kai ma za ka iya yi in kana so, ka nemi yardarta kuma ka nuna mata illolin da suke tattare da hakan don kar ta zarge ka a gaba.

47) Ka taimaka mata a wurin tarbiyar yaran, ka riƙa daukar jaririnku za ta ji dadin yadda kake ba su kulawa.

48) Ka riƙa tambayarsu lafiyarsu kowani lokaci.

49) Ka tabbatar ta yi duk allurorin da yaron yake buƙata tun daga ciki har zuwa watannin da aka tsara masa.

50) Ka yi ƙoƙari iyalinka su fi sonka sama da kowa.

51) Duk abin da za ka yi musu ka san cewa haƙƙoƙi ne da Allah ya daura a wuyarka, ibada kake yi, kar ka ce za ka bari don sun baƙanta maka rai.
.
Ƙarshen dan wannan littafi kenan, ba zan iya ambato duk waɗanda suka ƙarfafa ni kan wannan aiki ba, amma ina miƙa saduwar gaisuwa ga Sani Abu-Unaisa, Maijidda Abdulƙadir, Albani Dabai,

Nura Ja'afar Dallaje, Muhammad Inuwa, Musa Bala Gwarzo, Abu Husari Rabiu Abdu, Imranatu M Usman, Muhammad Abu Muhammad Ramadan, Usouph Muh'd Sani, Fatima Ahmad, Falalu Abdullahi, Ibrahim Nasidi Baban Ilham, Kabir Ahmed Abubakar, Hauwa T Musa, Abdurrahman Mustapha, Baffa Adamu Safiyanu, Al Amin Rabiah, A'isha Mahmud Yusuf, Rukayya Haruna, Alfa Usman, Abdullahi Muhammad, Sadear Haidar, Pheenearh Isah, ba iyakarsu ba kenan, waɗanda na dan iya kawowa kusa kenan, Allah ya saka da alkhairi, ina godiya da ƙwarin gwiwar da kuke ba ni.

Post a Comment

0 Comments