Ticker

6/recent/ticker-posts

Ci Gaban Mai Ginar Rijiya: Illolin Dimokuradiyya A Rayuwar Hausawa A Yau

Takardar da aka gabatar a taron kara wa juna sani na kasa da kasa na farko a kan nazarin harshen Hausa a ƙarni na 21 da Jami’ar Bayero Kano ta shirya a ranar Litinin 10 - Alhamis 13 ga Nuwamba, 2014.

CIGABAN MAI GINAR RIJIYA: ILLOLIN DIMOKURAƊIYYA A RAYUWAR HAUSAWA A YAU

NA

MUSA SHEHU
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato
07031319454
msyauri@yahoo.com

1.0  Gabatarwa


          Hausawa na ɗaya daga cikin al’ummomin duniya da ke a sahun gaba idan aka yi batun tarbiyya da kyawawan tsarin zamantakewar al’umma. Tsarin zamantakewar Bahaushe ya taimaka wajen samar da kyawawan ɗabi’u da al’adu abin alfahari ga mai su. Hausawa sun ci gaba da tafiya bisa waɗannan kyawawan ɗabi’u da al’adu waɗanda suka zama musu abin ado a tsakanin mutane.
[i] Daga cikin kyawawan ɗabi’un Hausawa na zamantakewa akwai gaskiya da riƙon amana, da zumunci, da tarbiyya tagari ga ‘ya’yansu maza da mata, ga ladabi da biyayya, da taimakon juna, da kyautata wa maƙwabci, da makamantansu da dama. Sai dai kuma, dukkan waɗannan kyawawan ɗabi’u da halaye na al’ummar Hausawa sun wanzu ne tun kafin tasirin Turawa na samuwar dimokuraɗiyya a ƙasar Hausa, domin a yau al’amurra sun sassauya, kyawawan ɗabi’un da aka sani ga Hausawa sun yi rauni matuƙa. Zama lafiya ya kau, biyayya ga iyaye da magabata ta salwanta, tarbiyya tagari daga iyaye ta sha ruwa, zumunci ya kama gabansa, wai duk da sunan ci gaban dimokuraɗiyya, wanda nike ganin cewa, ci gaba ne amma irin na mai ginan rijiya. Kar dai in cika ku da gafara sa ku kasa ganin ƙaho. Maƙasudin wannan takarda shi ne, nazarin illolin da dimokuraɗiyya ta haifar a rayuwar Hausawa a yau, da dalilan faruwarsu, da kuma hanyoyin magance su ko kuma rage musu ƙarfi ta yadda rayuwar Hausawa za ta iya sake ginuwa kamar inda aka fito ko fiya da haka. A sakamakon shigowar dimokuraɗiyya a ƙasar Hausa a yau, kyakkyawar rayuwar Hausawa ta sukurkuce ta yadda take neman agaji daga mawuyacin halin da ta shiga a yau. Tarbiyyar yara maza da mata ya sukurkuce, sai shaye-shaye da ayyukan ta’addanci ga matasanmu. ‘Yan siyasa sun tsunduma cikin tsafe-tsafe domin samun nasara. Zalunci da rashin gaskiya da amana da adalci ya share fili ya shimfiɗa tabarmarsa a rayuwar shugabanninmu, abin dai sai wanda ya ji ko ya gani. Allah Ka yi muna agaji.

2.0  Ma’anar Kalmar Dimokuraɗiyya


          Kalmar dimokuraɗiyya asali ba kalmar Hausa ba ce, ararriyar kalma ce daga harshen Ingilishi, woto “Democracy”. A ma’ana ta Mac Millan Dictionary, kalmar tana nufin, wani tsari na gwaunati wanda jama’a ke jefa ƙuriar zaɓen waɗanda za su shugabance su.
[ii] A ƙamusun Hausa kuwa, dimokuraɗiyya na nufin, tafarkin mulkin da mutanen ƙasa ke zaɓar shugabanninsu ta hanyar jefa ƙuri’a.[iii] Dimokuraɗiyya tsari ne da ke ba kowa ‘yancin shigowa a dama da shi a fagen neman shugabanci matuƙar ya samu amincewar al’ummar da yake son shugabanta dangane da kyawawan halaye da ɗabi’unsa. Haka ma akwai ƙayyadadden wa’adin da aka shata na tsawon lokacin da mutum zai yi yana gudanar da shugabancin. Saboda haka, idan wannan wa’adi ya cika zai sauka daga wannan matsayi a sake zaɓen wani. Sai dai tsarin ya ba mutum damar sake neman shugabancin, ma’ana mutum zai iya sake nema karo na biyu, a wani matsayin ma mutum zai iya nema fiye da haka har sai sa’ad da wani ya fito ya kayar da shi. Saboda haka, irin wannan tsari na shugabanci sabon al’amari ne ga rayuwar Hausawa, domin ba haka lamarin yake a tsarin al’adun rayuwarsu ba. Shugabanci a al’adar Hausawa gadon sa ake yi, ko dai a wajen iyaye ko kuma a wajen kakanni. To sai dai kuma, irin wannan tsari na dimokuraɗiyya tsari ne mai alfanu da kuma ba kowa ‘yancinsa ba tare da wata tawaya ba, amma fa idan an yi amfani da shi kamar yadda waɗanda suka shigo da shi suka tsara.

https://www.amsoshi.com/2017/11/06/1355/

3.0  Rayuwar Hausawa Kafin Shigowar Dimokuraɗiyya


Kamar yadda aka bayyana a cikin gabatarwa, rayuwar Hausawa kafin shigowar dimokuraɗiyya ta kasance gwanin ban sha’awa. Shugabanni sun kasance masu adalci da riƙon amanar talakawansu. Iyaye suna kula da tarbiyyar ‘ya’yansu kamar yadda ya kamata. Talakawa suna biyya ga shugabanni gwargwadon hali. ‘Ya’ya sun kasance masu ladabi da biyayya ga iyaye da ma magabata saboda kyakkywar tarbiyyar da suka tashi da ita. Iyaye sun sa ido ga ilimn ‘ya’yansu, da kuma aza su ga tafarkin yin sana’a. Babu mai zaman kashe wando balle ya sa ido ga abin da ba daidai ba. Zama lafiya ya wanzu a ko’ina, al’amarin dai gwanin ban sha’awa ga mai sauraro da ɗan kallo. Bari mu dubi bayanin yadda rayuwar take dalla-dalla domin feɗe biri har wutsiya.

Zaman LafiyaMasu iya magana na cewa, zama lafiya ya fi zama ɗan sarki.`Kafin gurɓatar dimokuraɗiyya, ƙasar Hausa ƙasa ce da aka sani da zama lafiya da kwanciyar hankali. Babu tashe-tashen hankula balle a samu salwantar rayuwa da dukiyoyi. Zalunci da babakere ba su sami gindin zama ba balle su baje kolinsu. Shugabanni suna kwatanta adalci, don haka ba su fuskanci tawaye daga talakawansu ba. Saboda yanayin zama lafiya da ke akwai a ƙasar Hausa, ya sa al’ummomi daban-daban suke yin tururuwar shigowa ƙasar domin a ci gajiyarsa da su. Hakan ya sa duk ɗan wata ƙabila da ya ɗanɗani zama a ƙasar Hausa bai iya komawa ƙasarsu domin ya ga wurin zama, sai dai ya riƙa zuwa ganin gida daga lokaci zuwa lokaci. Faɗace-faɗace da ayyukan ta’addanci sai dai Hausawa su ji labarinsu a wasu ƙasashe. Rayuwa a ƙasar Hausa in dai babu sa albarka, babu ko Allah wadai.

Ladabi Da BiyayyaLadabi da biyayya manyan ƙusoshi ne a cikin tarbiyyar Hausawa, wato muhimman halaye ne da Bahaushe yake so ya ga ana yi. Girmama na gaba da kyautata wa na baya su ne halayen da ake kira ladabi da biyayya (Alhassan da wasu 1982). A kullum burin iyaye ba ya wuce ganin ‘ya’yansu sun girma cikin halaye kyawawa masu nagarta, don haka suke koya musu yin ladabi da biyayya ga iyaye da ma na gaba gare su. Sukan koya musu ladabin magana wanda ya shafi koya musu tausasa murya lokacin magana da babba, kuma kar a tsura masa ido da kallo kamar yadda tumaki suke yi. Haka ma ba a gai da iyaye ko magabata a tsaye sai an duƙa musamman idan suna zaune. Ba a ƙetare umarnin iyaye ko ba daɗi, sai dai a daure a aikata yadda suke buƙata.

Kare ‘DiyauciBahaushe bai san karuwanci ba balle masu yin sa.’Ya’yan Hausawa mata tun suna ƙanana akan yi ƙoƙarin cusa musu al’adar nisantar maza da kuma illar da ke tattare da kusantar su. Don haka ne ko a wasannin dandali ƙungiyar mata daban na maza ma daban. Wannan tarbiyyar ba ta tsaya a nan kawai ba, hatta idan aka yi wa mace aure akan kai ta da wani farin ƙyalle da ake kira bante wanda za ta fara kwanciya da shi. Ta wannan ƙyalle ne za a gane ta kare ɗiyaucinta ko akasin haka. Idan aka yi nasara ta kai bante wato ba ta taɓa sanin ɗa namiji ba sai ga mijinta na aure, iyayenta kan yi murna da kasancewa masu alfahari da ita. Idan kuwa aka sami akasin haka, to yarinyar ta bar abin faɗe da zubar da mutuncin iyayenta. Wannan al’ada ya yi tasiri ainun ga ‘yan mata wajen ganin ba su zubar da mutuncin gidansu ba, da kuma barin abin faɗe a baya.

Gaskiya Da Riƙon AmanaHausawa mutane ne da suke da kyakkyawar tarbiyya da himmatuwa zuwa ga ɗaukar halaye nagari irin su gaskiya da riƙon amana. Babu yaudara ko cin amana a rayuwar Hausawa. Wato mutane ne masu karimci da shimfiɗar fuska wadda aka ce ta fi shimfiɗar tabarma. Duk wanda ya haɗa hulɗa ta kasuwanci ko na zamantakewa da Hausawa zai tabbatar da cewa Hausawa mutane ne masu gaskiya. Wannan ne ya samar wa Hausawa kyakkyawar dangantaka ta kasuwanci tsakaninsu da al’ummomi daban-daban na cikin gida da ma sauran ƙasashen duniya.

ZumuntaƘoƙarin kusantar ‘yan’uwa da abokan arziki da ziyartar su a kai-a-kai, ita ce zumunta (Alhassan da wasu 1982). Tarbiyyar Hausawa tana jaddada ziyarce-ziyarce tsakanin ‘yan’uwa da abokan arziki. A tsarin rayuwar Bahaushe, maƙwabci tamkar ɗan’uwa ne, domin idan aka wayi gari sai an gaisa kafin kowa ya fita tasa harka. Don haka, idan wani abin farin ciki ko akasinsa ya samu maƙwabcin mutum, za a zauna a taya juna murna ko juyayi idan mara kyau ne. Haka ma duk wani abu da ya samu ‘yan’uwa na murna kamar haihuwa ko aure akan taru domin a sada zumunci kuma a ƙarfafa shi. Har ta kai ga Bahaushe kan ɗauki ɗansa ya ba ɗan’uwansa riƙo domin ƙarfafa zumuntar da ke tsakaninsu.

Mallakar Sana’a: Al’ummar Hausawa tun asali al’umma ce wadda ta dogara da kanta wajen samar da hanyoyin tattalin arzikinta. Ta haka ne ya zama a kowane gidan Bahaushe za ka tarar yana da sana’o’in da yake aiwatarwa. Don haka, yakan yi ƙoƙarin gina yaransa bisa wannan sana’a domin su girma da ita, su kuma kauce wa zaman kashe wando da sa ido da yawon gararanba a cikin unguwa.

4.0  Illolin Dimokuraɗiyya a Rayuwar Hausawa a Yau


          Da ma ana cewa, duk wani abu mai amfani ba za a rasa illa a cikin sa ba. Dimokuraɗiyya wani tsari ne na tafiyar da rayuwar al’umma mai alfanu matuƙar dai an yi amfani da shi kamar yadda aka tsara shi. To sai dai kuma, lamarin Dimokuraɗiyyar a Arewacin Nijeriya a yau ya ɗauki sabon salo wanda ya sha bamban da na waɗanda suka kawo shi, wato Turawa. A dimokuraɗiyyar da ake gudanarwa ƙasar Hausa a yau, an cakuɗa gaskiya da ƙarya, an mayar da gaba baya, ta yadda al’amurra suka kasa zuwa gaba sai dai baya. Wannan matsalar ta yi tasiri ainun a rayuwar Hausawa a yau, inda ‘yan siyasar ƙasar Hausa suka mayar da dimokuraɗiyya in ba ka yi ba ni wuri. Sukan bi duk wata hanya mai kyau ko akasinsa, galibi hanyoyi marasa kyau domin cimma burinsu na wani matsayi da suke nema. Hakan ya sa tsafe-tsafe ya samu gindin zama. Safarar miyagun ƙwayoyi domin bai wa matasa ‘yan bangar siyasa ya baje hajarsa. Ƙungiyoyin ‘yan daba suka mamaye unguwanni. Fitintinu da tashe-tashen hankula da salwantar rayukar al’umma da dukiyoyinsu ya zama ruwan dare game ƙasar Hausa. Ga dai bayanin irin illolin kamar haka:

4.1  Rashin Zama Lafiya

Zama lafiya da aka sani a ƙasar Hausa inda har wasu al’ummu kan shigo domin cin gajiyarsa, a yau ya yi ɓatan dabo. Tashe-tashen hankula ya wanzu a kusan kowane ɓangare na ƙasar Hausa. Allah kaɗai ya san adadin rayukan Hausawa da dukiyoyinsu da suka salwanta tun bayan gurɓacewar dimokuraɗiyya. A yau za ka ji an kai hari a wannan sashe an kashe mutane masu tarin yawa da hasarar dukiyoyi, gobe ka ji an kai a wancan ɓangare, haka dai lamarin ke ci gaba da aukuwa fiye da shekaru huɗu da suka gabata duk da sunan ci gaban dimokuraɗiyya. To sai dai kuma, duk da irin waɗannan matsaloli da Hausawa ke huskanta a ƙasashensu, sai ka iske ‘yan siyasa sun miƙe suna bayyana irin ci gaban da aka samu na tafarkin dimokuraɗiyya, Allah dai ka yi muna magani.

4.2  Taɓarɓarewar Tarbiyya

          Kyakkyawar tarbiyyar da aka san matasan Hausawa da shi a da, a yau lamarin sai dai a shafa fatiha a watse. ‘Yan siyasa sun yi ruwa da tsaki wajen tabbatar da gurɓacewar tarbiyyar matasa a yau. Sukan sawo miyagun ƙwayoyi da miyagun makamai da ɗan kuɗin da bai taka kara ya karya ba su raba wa matasa don su yi musu bangar siyasa. Saboda haka, a duk lokacin da waɗannan matasa suka sha waɗannan ƙwayoyi sukan fita hayyacinsu, daga nan sai ayyukan ta’addanci su wanzu na kai wa abokan hamayyar ubangidansu da ma junansu hare-hare da lalata dukiyoyi, da yi wa mata fyaɗe da makamantansu.  A wani lokaci ma har hayan matasa ake ɗauka domin su hallaka wani abokin hamayya. Don haka, maganar mallakar sana’a ya sha ruwa, sai dai tunanin haɗa ƙungiyoyin daba iri daban-daban. Haka ma lamarin karatun zamani (boko) da na addini (Musulunci) ga matasa ya yi rauni, domin ‘yan siyasa sun yi awon gaba da kyakkyawar tunanin matasan suka bar musu gurɓatacce, don haka maganar neman ilimi ko sana’ar dogaro da kai bai taso ba. A sakamakon haka, matasa da yawa sun sami taɓuwar hankali, wasu sun zama musakai, wasu ma sun rasa rayuwa baki ɗaya. Duk waɗannan matsaloli ne da ke faruwa da sunan ci gaban dimokuraɗiyya, Allah ya kiyashe mu da irin wannan ci gaba na mai ginan rijiya.

4.3  Taɓarɓarewar Zumunci

           Mulkin Dimokuraɗiyya ya zama ummul-haba’isin taɓarɓarewar zumunci a yau. Siyasa ta shiga tsakanin ‘yan’uwa ta ɗaiɗaita su. Ta shiga tsakanin abokai ta yanke musu ƙauna. Ta raba soyayyar da ke tsakanin ma’aurata. Ta shiga tsakanin maƙwabta ta haddasa gaba a tsakaninsu, ta bi komai ta hargitsa. Sau da yawa za ka taras ana uwaka-ubaka tsakanin ‘yan’uwa, ko wa da ƙani, ko mata da miji, ko aboki da abokinsa, ko ma ka iske an yi hannun riga tsakanin ɗa da mahaifi kowa ya kama gabansa. Haka ma sai ka iske ba a ga-maciji tsakanin maƙwabta, sai maƙwabci ya yo hayar ‘yan daba a kawo wa maƙwabcinsa hari a lalata dukiyoyinsa, duk kawai saboda bambancin jam’iyyar siyasa. Saboda haka, tilas zumunci ya taɓarɓare, taimakon juna da ziyara da jinƙai suka nufi inda dare ya yi musu tun lokaci bai ƙure ba. A yau kowa kansa kawai ya sani, ya nufi inda zai sami arziki a ƙarƙashin wata jam’iyya, duk mai mutuwa ya rage nasa.

4.4  Wanzuwar Ƙungiyoyin Daba na Matasa (Area Boys)

          Saboda irin taɓarɓarewar da Dimokoraɗiyya ta yi a ƙasar Hausa a yau, har ta kai ga wanzuwar ƙungiyoyin ta’addanci na matasa waɗanda ake kira “Area Boys” daban-daban biranen ƙasar Hausa da ma ƙauyukansu waɗanda ke ƙarƙashin kulawar wasu ‘yan siyasa. Wasu ƙungiyoyin ma har albashi ake yi musu a ƙarshen kowane wata kamar sauran ma’aikatar gwaunati. Saboda haka, a duk lokacin da za a tafi yawon kamfe, za a kwashi waɗannan matasa (‘yan daba) cikin motoci a ba su miyagun makamai don ko ta kwana. Haka ma idan ana buƙatar cin zarafin wani abokin hamayya ko ma a kawar da shi a doron ƙasa, irin waɗannan matasa ‘yan siyasa kan samu su biya musu buƙata. Don haka, duk irin ta’adin da suka aikata komai ba a yi musu, saboda ko hukuma ta kama su sai iyayen gidansu su shiga su fita sai sun ga an sake su. Alal misali, a kwanakin baya ‘yan daba suka riƙa tsayawa a tsakiyar randabawul  a cikin garin Sakkwato suna tare motocin mutane wai sai an ba su rabonsu ko mutum ya huskanci walaƙanci.

4.5  Yawaitar Tsafe-Tsafe                                                                                                                 A riwayar Bunza (2006) ya bayyana tsafi da bin wasu hanyoyi na gargajiya musamman yi wa iskoki hidima, da yanka, da bauta, domin biyan wata buƙata, ko ko wani amfani, ko tunkuɗe wata cuta.
[iv] Ya ci gaba da cewa, Tsafi ya yi rawar gani wajen tabbatar da Bamagujiyar rayuwa ta Hausawan jiya. Da shi ake tinƙaho don tsare kai da kaya. Da shi ake kuri wajen kariyar martabatar abin da aka gada kaka da kakanni. Da shi ake yin fice wajen wasanni da bukukuwan gargajiya da ake aiwatarwa a ko’ina a ƙasar Hausa. Sai dai zuwan Musulunci ya taka masa birki ta yadda ya kasa motsi balle ya wataya. To sai dai kuma, a wannan zamani da ake ciki na tsarin dimokuraɗiyya yana neman ya mayar da hannun agogo baya, domin a yau ‘yan siyasa sun tsunduma dumu-dumu cikin harkar tsafe-tsafe domin neman matsayi na siyasa. Sun ba Allah baya, sun fuskanci malaman tsibbu da miyagun bokaye domin biyan buƙata. Saboda haka ake tura su zuwa ga sace-sacen yara ana cire wasu sassa na jikinsu, ko a tafi maƙabarta a tone ƙabari a ɗibi wani sashe daga jikin mamaci, domin haɗa miyagun asirrai wai a samu nasara.

 

4.6   Handama da Babakere

A ma’ana ta gaskiya, ba komai ne Dimokuraɗiyya a Nijeriya ba face zalunci da rashin gaskiya da handamar dukiyar talakawa. A yau ‘yan siyasa suna neman matsayi ne ba don kare haƙƙin waɗanda suke wakilta ba, a’a, sai don kawai handamar dukiyoyinsu da kuma barazana ga rayukansu idan suka nemi su yi tawaye. Hakan ya sa suke bin duk wata hanya na ganin sun kai ga baitil-malinsu. Talakawan jiha ba su amfana da arzikinsu na aƙalla kashi talatin cikin ɗari da ake ware musu, an yi ruf-da-ciki da saura. Lamarin ƙananan hukumomi kuwa sai wanda ya ji ko ya gani, domin da zarar an yi albashi da abin da bai wuce kashi talatin cikin ɗari ba, sauran sai dai kawai ‘yan siyasa su yi tonton kowa ya kwashi rabonsa a hari wani wata mai zuwa. Talakawa sun shiga halin ƙaƙa-nika-yi, abin da za su ci ma ya zama lalura balle a kula da lafiyarsu da sauran buƙatun rayuwarsu. Allah ya kiyashe mu da irin wannan ci gaba na dimokuraɗiyya.

4.7  Cuɗeɗeniyar Maza da Mata

Cuɗeɗeniyar maza da mata wuri ɗaya abu ne da al’adar Hausawa da ma addininsu (Musulunci) ba su aminta da ita ba, sai dai idan lalurar hakan ta kama. Amma a yau tsarin mulkin Dimokuraɗiyya ya nuna cewa, mace za ta iya fitowa neman wani matsayi na shugabanci a fafata da ita kamar yadda namiji zai iya fitowa. Sau da yawa za ka iske an kwashi ‘yan mata da zawarawa har ma da matan aure cikin mota ana yawon kamfe da su kamar yadda takwarorinsu maza suke yi. A yanzu ma har an fara samun matan Hausawa suna fitowa takara suna tsayawa gaban dubban maza suna kamfe wai a zaɓe su a matsayin wakilan maza. A faɗar wasu, wai duk abin da namiji zai iya yi, mace ma za ta iya yin fiye da haka. Wannan mummunan tsari da tunani a yau ya ratsa ƙwaƙwalwar matan Hausawa na ganin  cewa za su iya gwagwarmaya da maza ta kowace fuska, don haka lamarin sai dai kawai addu’a Allah shi yi muna magani, ya kuma sa mu gane tafarki managarci.

5.0  Musabbabin Matsalar


          A duk lokacin da al’amurra suka sukurkuce suka sauya kamanni ba kamar yadda aka saba da su ba, tilas akwai dalilan da suka jawo haka. Don haka, akwai abubuwa da dama da suka zama ummul-haba’isin waɗannan matsaloli da suke ci wa rayuwar Hausawa tuwo a ƙwarya a yau. Ga wasu daga cikinsu:

Rashin Amfani da Doka da OdaBa shakka, rashin amfani da doka da oda na daga cikin abubuwan da suka haddasa wasu daga cikin illolin da aka bayyana a sama. A yau kowa na cin karensa ne babu babbaka musamman ‘yan siyasa ko masu wani muƙami ko masu hannu da shuni. A yau idan kana tare da manya, duk laifin da ka yi hukunci ba ya hawa kanka. Don haka, duk dukiyar da ka sata na al’umma ko wani ha’inci ko kisan kai ko wani ta’addanci, ko an gane ba a yi ma komai, ka ci bilis. Haka ma, idan ‘yan ta’adda suka aikata wani ta’addanci aka kama su, sai ka iske wasu ɓara-gurbin mutane sun yi ruwa sun yi tsaki sun hana hukuma aikinta. Idan ka ga doka ta yi aiki a yau, to ga talakawa ne waɗanda ba su da kowa sai Allah.

Sakacin IyayeHaƙiƙa akwai sakacin iyaye wajen lalacewar tarbiyyar matasa a yau. Sai ka iske iyaye sun haifi ‘ya’ya sun sake su kamar tumaki ba su tsare hakkin da Allah ya ɗora musu na tarbiyyansu da ta danganci addini da al’ada. Sau da yawa za ka iske iyaye ba su damu da sa ‘ya’yansu makarantar addini ba balle na zamani. Saboda haka, duk yaron da ya tsinci kansa cikin irin wannan yanayi rayuwarsa na cikin haɗari. Daga nan ne sai ka iske yaro ya haɗu da miyagun abokai, sai shaye-shaye da haɗa ƙungiyoyin daba, shi ke nan rayuwa ta lalace.

6.0  To Ina Mafita?


          Masu iya magana na cewa, ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba. Ba shakka, duk yadda al’amurra suka taɓarɓare ba za a yanke ƙauna ga samun mafita ba. A kan haka nike ganin akwai hanyoyi da yawa waɗanda idan aka jaraba amfani da su wataƙila a sami maslaha a ceto rayuwar Hausawa daga bala’o’in da ke ƙoƙarin ganin baya gare ta. Daga cikin waɗannan hanyoyi akwai sa hannun gwaunati, da iyayen yara, da kuma malaman addini.

6.1  Gwamnati


          Haƙiƙa gwaunati ce a sahun farko na waɗanda za su iya ba da tasu gudummuwa wajen samar da mafita dangane da waɗannan matsaloli na dimokuraɗiyya da suke ci gaba da addabar rayuwar Hausawa a yau. Gwunati za ta iya daidaita al’amurra su dawo cikin hayyacinsu ta hanyar fito da wasu hanyoyi na daƙushe bangar siyasa da amfani da matasa wajen ayyukan ta’addanci. Dole ne a yi amfani da doka da oda wajen hukunta duk wani ɗan siyasa ko ɗan bangarta da aka samu da hannu wajen aikata abubuwan da suka saɓa wa doka. Dole ne gwaunati ta samar da wasu shirye-shirye na faɗakar da matasa illolin da ke tattare da bin ɓara-gurbin ‘yan siyasa, da kuma irin haɗurran da ke tattare da shaye-shayen miyagun ƙwayoyin da suke yi wanda ke iya kai su ga halaka.

6.2  Iyaye

          Iyaye su suka fi cancanta da kula da halin da yaransu ke ciki, domin su ne Allah ya damƙa wa ragamar tarbiyyar rayuwarsu tun suna ƙanana har zuwa girmansu. Tilas su tsaye tsayin daka wajen ba su ilimin addinii da na zamani domin su ci moraiyar rayuwarsu ta duniya da ma ta gobe ƙiyama. Dole ne iyaye su ɗora ‘ya’yansu bisa turba ta sana’a domin kauce wa zaman banza wanda shi ke kai su ga faɗawa cikin miyagun hanyoyi. Dole su sa ido ga ire-iren abokan da ‘ya’yansu suke hulɗa da su don kauce wa faɗawa hannun ɓata-gari.

6.3  Malaman Addini

          Duk da cewa, malaman addinin Musulunci suna iya ƙoƙarinsu wajen wa’azantar da al’umma a kusan kowane lokaci, kuma ana yayata faɗakarwar tasu a kusan dukkan kafafen yaɗa labarai kama daga rediyo da talabijin da jaridu da mujallu da tauraron ɗan Adam da intanet da makamantansu, zai kyautu su ƙara ba da ƙarfi a kan wannan matsala da mulkin Dimokoraɗiyya ya haifar a rayuwar Hausawa a yau. Su riƙa bayyana wa jama’a musamman masu ruwa da tsaki a kan lamarin siyasa irin mummunar sakamakon da ke jiran duk wani mai ƙoƙarin cutar da al’umma, yake barazana ga rayuwarsu, ko yake lalata tarbiyyarsu, ya haddasa musu bala’i, ya hana su zama lafiya balle su bauta wa mahaliccinsu kamar yadda ya kamata.

Jawabin Kammalawa


          Tsarin dimokuraɗiyya a ƙasar Hausa a yau ya zama tamkar wani mulki na kama-karya da danniya da babakere da rashin tausayin na ƙasa wanda ya gudana a zamanin jahiliyya, inda sai yadda shugabanni suka ga daman yi da talakawa. An gurɓata tunanin matasa ta yadda ba su iya fitar da suhe wuta. An talautar da jama’a domin a juya akalar rayuwarsu yadda aka ga dama. Aka kuma haddasa fargaba da rashin zama lafiya a rayuwarsu. Kowa son yake yi ya shiga harkar siyasa domin a ci karen da babu babbaka tare da shi. Al’amurra a rayuwar Hausawa a yau musamman talakawa ya zama abin tausayi ga duk wani mai imani na gaskiya. Tilas mu tashi tsaye mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin ganin bayan wannan bala’i da ya kewaye kusurwoyin rayuwar Hausawa domin sake dawowa da kyakkyawar rayuwar da muka gada daga kaka da kakanni.

 

 

https://www.amsoshi.com/2017/11/08/makamin-dimokradiyya-a-falsafar-alada/

 

 

MANAZARTA


Alkali, B. 1968. “Hausa Community in Crisis: Kebbi in the 19
th Century”, MA Thesis, Ahmadu Bello University, Zaria.

Birniwa, H. A. 1987. “Conservatism and Dissent: A Comparative Study of NPC/NPN and NEPU/PRP Hausa Polical Verse from Ca 1949 – 1983, PhD Thesis, Usmanu ‘Danfodiyo University Sokoto.

Birniwa, H. A. 1987. “Ra’ayin Riƙau da na Kawo Sauyi Cikin Waƙoƙin Siyasa”, Maƙalar da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa na Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,  Jami’ar Bayero Kano.

Bunza, A. M. 1996. “Gaskiya Ina Laifinki? Tsokacin Diddigin Musabbabin Karyewar Arzikin Nijeriya Cikin Waƙar Gaskiya Mugunyar Magana, Ta Alhaji Muhammadu Sambo Wali Basakkwace,” Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato.

Bunza, A. M. 2000. “A Daɗe Ana Yi Sai Gaskiya: Laluben Gurbin Gaskiya Cikin Adabin Hausa”, Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo Sakkwato  .

Bunza, A.M. 2006 Gadon Feɗe Al’ada. Tiwal Nigeria Limited, Surulere, Lagos.

Bunza, A.M. 2013. “Makamin Dimokuraɗiyya a Falsafar Al’ada” Takardar da aka gabatar a

taron  ƙara wa juna sani na ƙasa na farko a kan  Harshe da Adabi  da  Al’adun

Hausawa na Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano.

Burji, B. S. 1997. Gaskiya Nagartar Namiji. Baraka Press Limited, Kaduna.

Msutapha, S. 2003 “Gurbin Gaskiya Cikin Adabin Hausa”, kundin digirin MA, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

Nasidi, Y. & Igoil, I. (ed)1997Culture and Democracy. Zaria: Ahmadu Bello University Press

Sarkin Gulbi, A. 2013 “Tsafe-tsafen Dimokraɗiyya” Takardar da aka gabatar a taron ƙasa na

farko kan Harshe da Adabi da Al’ada, wanda Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya

Jami’ar Bayero Kano ta shirya.

[i]  Dubi Bugaje 2013, “Tarbiyya da Zamantakewar Hausawa Jiya da Yau”. Maƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa da ƙasa kan Taɓarɓarewar Al’adun Hausawa a Yau, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina.

[ii]  Dubi Mac Millan English Dictionary for Advanced Leaners, International Edition, shafi na 369.

[iii]  Dubi ƙamusun Hausa, 2006,  wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano shafi na 104

[iv]   Domin ƙarin bayani game da lamarin tsafi, sai a dubi Bunza 2006, Gadon Feɗe Al’ada, shafi na 35-57.

 www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.