YUNƘURIN SAMAR DA ZAMAN LAFIYA DA SASANTAWA: BINCIKE A KAN WAKAR ZAMAN LAFIYA TA BASHIR MUSA LIMAN
NA
MUSA SHEHU
Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya
Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato
msyauri@yahoo.com
07031319454
TSAKURE
Masu iya magana na cewa, “zaman lafiya ya fi
zama ɗan sarki”. Yunƙurin da ake ta famar yi na ganin zaman lafiya ya samu
inuwar hutawa a ƙasar Hausa da ma Nijeriya baki ɗaya bai bar sha’iran Hausa a
bayan fage ba. Akwai rubutattun waƙoƙin Hausa da dama da wasu sha’irai suka
rubuta domin ba da tasu gudunmuwa ga samar da zaman lafiya da sasantawa.
Manufar wannan takarda dai shi ne feɗe waƙar zaman lafiya ta Bashir Musa Liman
domin fito da hikimomi ko falsafar da ke cikin waƙar, wanda suka haɗa da
bayanin amfanin zaman lafiya, hanyoyin samar da zaman lafiya, dalilan da ke
haddasa rashin zaman lafiya, da illolin rashin zaman lafiya da sauransu.
1.0 Gabatarwa
‘Dangambo (1981) cewa ya yi “Waƙa wani saƙo ne da aka gina shi kan tsararriyar ƙa’ida
ta baiti, ɗango, rerawa, kari (bahari), amsa-amo (ƙafiya), da sauran ƙa’idojin
da suka shafi daidaita kalmomi, zaɓensu da amfani da su cikin sigogin da ba
lalle ne haka suke a maganar baka ba”. Giɗaɗawa (2006:174) cewa ya yi: “Waƙa
dai magana ce tsararriya wadda ake shiryawa a bisa wasu muryoyi na musamman,
wadda kuma ta bambanta da maganar yau da kullum. Tsara waƙa baiwa ce ta
Ubangiji sai wanda Allah ya hore wa ita zai iya. Hausawa sun fara rubuta waƙa
ne ta dalilin isar da saƙon Allah, wato domin yin wa’azi ga jama’a domin su
koma tafarkin Allah makaɗaici. Ladan (1975) ya bayyana cewa, marubucin waƙoƙin
Hausa yana nazarin abin da aka fi shagalta da shi, idan na zarafin duniya ne,
ya faɗi ra’ayinsa a kansa, idan kuma na addini ne ya yi wa mutane wa’azi.[i] Misali, a cikin ƙarni na 18 da na 19
lokacin da aka himmatu kan jaddada addini, waƙoƙin Hausa na wannan zamani duk
sun ƙunshi wa’azi ne. A wajen tsakiyar ƙarni na 20 kuwa, lokacin da aka
shagalta da yaƙin duniya na biyu, da ilimin zamani da siyasa da tafiye-tafiye
zuwa ƙasashen Turai, an sami haziƙan marubuta waƙoƙi da suka waƙe waɗannan
al’amurra, kamar Malam Sa’adu Zungur, Malam Mu’azu Haɗeja, Alhaji Mudin Sipikin
da makamantansu.
To sai dai kuma, wannan zamani na ƙarni 21 ya zo ne da rikice-rikice da
tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na ƙasar Hausa da ma Nijeriya baki ɗaya.
Zaman lafiya ya kasa samun gindin zama, don haka aka sami wasu marubuta waƙoƙin
Hausa waɗanda suka himmatu wajen waƙe sha’anin zaman lafiya, kama daga alfanun
zaman lafiya, da hanyoyin tabbatar da zaman lafiya, da hanyoyin kariya daga
aukuwan rikici, da illolin da ke tattare da rashin zaman lafiya, da
makamantansu. Waɗannan abubuwa ne wannan takarda za ta mayar da hankali wajen nazarinsu
kamar yadda marubuta waƙoƙin Hausa suka kalle su.
https://www.amsoshi.com/2017/11/08/makamin-dimokradiyya-a-falsafar-alada/
2.0 Ma’anar Zama Lafiya
Zaman lafiya a Bahaushen tunani shi ne, zama cikin natsuwa, da sakewa da rashin
fargaba da tashin-tashina ta kowace fuska. Zama ne da ba ka cuta ba, ba a cuce
ka ba. Zama ne na aminci ga ƙasa da waɗanda ke cikin ta, da waɗanda za su
ziyarce ta, da waɗanda za su fice daga cikin ta, da waɗanda ke maƙwabtaka da
ita. Zama ne da zai bai wa duk wanda ke cikin ƙasa ɗan asalin ta, da baƙnita na
arziki, da ‘yan gudun hijirarta, da masu zaman mafakar siyasa a ciki, natsuwa
da kuranye firgita a zukatansu. Zaman lafiya zama ne na ɗebe ɗammaha ga duk
wata hayagaga da ruɓushi da ta da zaune tsaye da wata halitta za ta haddasa ga
wanda ke cikin ta, face abubuwan da babu makawa aka ƙaddaro gare ta daga mai ƙaddarawa
(Allah)[ii].
A Ƙamusun Hausa (2006) ba a kawo ma’ana ɗaya da ta shafi kalmomin biyu ba, wato
‘zama da lafiya’, sai aka kawo ma’anonin kalmomin daban-daban kowane yana cin
gashin kansa. Don haka aka bayyana ma’anar zama da “kasancewa zaune”, wato
kishiyar tsayuwa, lafiya kuma aka bayyana ta da “rashin tashin hankali da
hargitsi a wuri.” Saboda haka, idan aka dubi ma’anonin kalmomin biyu za a ga
suna bayyana ma’anar zaman lafiya da kwanciyar hankali da rashin rigingimu da
fitina a cikin jama’a.
Ibeanu (2006) ya kawo ma’anoni kamar guda biyar da suka shafi fannoni
daban-daban na ilimi a kan zaman lafiya, ga su kamar haka:
Zaman lafiya na nufin rashin wanzuwar yaƙi; yaƙi kuma na nufin rashin wanzuwar
zaman lafiya. Don haka, a koyaushe kalmomin biyu ba sa haɗuwa wuri ɗaya, dole a
kiyaye su da yadda suke wakana a rayuwa.
A ma’ana ta ilimin falsafa kuwa (Philosophical definition), zaman lafiya na
nufin rashin wanzuwar cin hanci ko rashawa a cikin al’umma kamar yadda Allah Ya
tsara. Haka ma, ana iya cewa, zaman lafiya yanayi ne na kyakkyawar rayuwar
al’umma a doron ƙasa da bai riga ya gurɓata ba.
A fannin ilimin walwalar rayuwa (Sociological definition), zaman lafiya na
nufin yanayin haɗin kan al’umma na rashin tashin-tashina a tsakaninsu. A wata
faɗar kuma, zama lafiya na nufin wani yanayi ne na rashin wanzuwar
rikice-rikice a tsakanin ɗaiɗaikun mutane ko ƙungiyoyi ta yadda za su iya samun
damar biyan buƙatun rayuwarsu cikin lumana.
A fannin siyasa kuma (Political definition), kamar yadda Jami’ar zaman lafiya
ta bayyana, zaman lafiya shi ne tsarin siyasa da ke tabbatar da wanzuwar adalci
ga al’umma. Daga nan kuma marubucin ya bayyana ra’ayinsa kan ma’anar zaman
lafiya yana cewa, zaman lafiya al’amari ne da ya shafi al’amurran da suka shafi
bunƙasa da ci gaba kai tsaye ko a fakaice, da rage rikici a cikin wata al’umma
da ma al’ummomin duniya baki ɗaya.[iii]
Francis (2006) yana cewa, zaman lafiya na nufin rashin wanzuwar yaƙi, tsoro,
rikici, fargaba, wahala, da ta’addanci, da kuma wanzuwar lumana. Wato abu ne da
ya shafi samuwa da ɗorewar adalci a cikin al’umma da kuma sasanta rikici ta
hanyar ruwan sanyi.[iv]
3.0 SASANTAWA
Sasantawa (Conflict Resolution) wani al’amari ne mai muhimmancin gaske a
rayuwar kowace al’umma. A duk lokacin da wasu rikice-rikice ko yaƙe-yaƙe ko
tashin-tashina suka wanzu a tsakanin al’umma, hanya mafi dacewa da ya kamata a
yi amfani da ita domin warware su cikin ruwan sanyi da kuma dawo da zaman
lafiya mai ɗorewa ita ce hanyar sasantawa ko yin sulhu a tsakanin masu husuma.
A ƙamusun Hausa (2006) an bayyana ma’anar sasantawa da shiga tsakanin masu
husuma biyu, ko kuma sulhu.[v] A cikin Ƙamusun Oxford an kawo ma’anar
sasantawa da cewa, yanayi ne na warware ko daidaita matsala, jayayya, da
sauransu.[vi]
4.0 Musabbabin Rikice-Rikice
Duk wata matsala ko rikici da ya auku a rayuwa akwai musabbabin aukuwarsa, ko
dai kai tsaye ko a fakaice. Marubuta waƙoƙin Hausa daban-daban sun bayyana wasu
dalilai da ke haddasa rashin zaman lafiya a waƙoƙinsu na “zaman lafiya” waɗanda
suka haɗa da:
Rashin Adalcin Shugabanni: Ba shakka, rashin adalcin shugabanni na
taushe haƙƙin talaka, da tursasa shi, da yin ko-oho da muradun rayuwarsa, sun
taka muhimmiyar rawa wajen rashin samuwar zaman lafiya da ake fama da shi a yau
a ƙasar Hausa. Shugabanni sun kasance marasa gaskiya, da rashin amana, da
rashin cika alkawali musamman ga ‘yan siyasar wannan zamani, da uwa-uba
barazanar da ake yi wa rayuwarsu a kullu yaumin. Bashir Musa Liman a waƙarsa ta
“zaman lafiya” a baiti na 10 da 11 da 12 da 17, yana cewa:
Baiti na 10 Masu iko sun yi ƙi-mudu-gus
Wajen bai wa talaka hatsin gus-gus
Su kuwa suna ta tauna gurus-gus
Hakan ya haifar da zaman ƙiyayya
Baiti na 11 ‘Yan siyasa suna alkawartawa
Idan sun ci zaɓe za ai morewa
Suna ci sai su zam ɓacewa
Hakan ma na jawo hatsaniya
Baiti na 12 Masu mulki suna sheƙa mulki
Wanda ya sa wasu ke take hakki
Almundahana, danniya da zulaƙi
Wanda ta sa talaka yin gogayya
Baiti na 17 Masu iko na fashi da muƙami
An bar talakawa cikin jimami
Da warin jiki mai tsabar hamami
Ga ruwan hawaye na zuba a idaniya
Talauci da Rashin Aikin Yi: Talauci da rashin aikin yi na daga
cikin abubuwan da ke kassara rayuwar al’umma, wanda a mafi yawan lokuta idan ba
a kai zuciya nesa ba, sai a faɗa ga aikata miyagun ayyuka waɗanda za su iya
haddasa fitina da rashin zaman lafiya. Farfesa Aliyu Muhammad Bunza a waƙarsa
ta gasar waƙoƙin zaman lafiya a baiti na 57 da 58, ya bayyana rashin aikin yi
na haddasa rashin zaman lafiya a cikin al’umma, yana cewa:
Baiti na 57 Rashin aikin yi shi ka kawo
Zaman banza a yi gardama
Baiti na 58 Da sannu abin ya game gari
Har ya watsu ƙasa ya ƙudan zuma
Bashir Musa Liman a waƙarsa ta “zaman lafiya” a baiti na 18 da na 19, ya
bayyana talauci da rashin aikin yi daga cikin musabbabin hana zaman lafiya a
cikin al’umma, yana cewa:
Baiti na 18 Talauci ya sanya fashi da makami
Kana gida ka ga ɓarayi da makami
A kan hanyar tafiya ma da makami
Ka bayar da kuɗi ka zauna lafiya
Baiti na 19 Matasa ba aikin yi sai zaga gari
Ba su da ko sule, balle zancen ɗari
Hakan kuwa ya sa su cikin garari
Wanda ya sa suke ta hatsaniya
5.0 Illolin Rashin Zama Lafiya
Rashin zaman lafiya babbar
musiba ce a rayuwar al’umma, domin yakan haddasa talauci da fargaba da taɓarɓarewar
tattalin arziki, da hasarar dukiyoyi da ma rayuwa baki ɗaya. Farfesa Aliyu
Muhammad Bunza a waƙarsa ta “zaman lafiya” a baiti na 81 da na 82 da na 99 da
na 100, ya bayyana irin illolin da ke tattare da rashin zaman lafiya a cikin
al’umma, wanda ya haɗa da taɓarɓarewar ilimi da tattalin arzikin ƙasa, yana
cewa:
Baiti na 81 Kashe ilmi fitina ka yi
Duk ta ƙare manyan maluma
Baiti na 82 Takan ƙare jama’ar ƙasa
Duk su tsere ba mai sallama
Baiti na 99 Jidali na tauye darajar ƙasa
Ga idanun al’uma
Baiti na 100 Ya toshe tafarkin arziki
Ba zama na lumana an gama
Shi ma Bashir Musa Liman a waƙarsa ta zaman lafiya a baiti na 5 da na 7 da na
15, yana bayyana irin illolin da rikicin Arewaci da Kudancin Nijeriya suka
haifar, wanda suka haɗa da hasaran rayuka da dukiya, yana cewa:
Baiti na 5 A Kudu maso gabas ana ta
hatsaniya
Suna fasa bututun mai da hauragiya
Tattalin arziki ya zama koma baya
Muna cikin talauci ba zaman lafiya
Baiti na 7 A Arewacin ƙasata har da Maiduguri
Ana ta rikici na addini babu tsari
Rayuka da dukiyoyi sun ɓata ba iƙirari
Wanda hakan ya haifar da ƙiyayya
Baiti na 15 Rayuwa ta zam taɓarɓarewa
Al’amurra sun zam rikirkicewa
Komai da komai yai ƙazancewa
Sai lahaula a ƙasata Nijeriya
6.0 Matsayin Mai Hana Zama Lafiya
Babu wata al’umma da ta
aminta da mai tayar da ƙayar baya, balle ma ta yi masa tarbon arziki. Wannan ya
sa duniya take kiran masu tayar da zaune tsaye da suna ‘yan ta’adda. Don haka
ma Hausawa ke da karin maganar da ke cewa: “Maso faɗa wawa” da kuma “Fitina
kwance take, Allah ya la’ani mai tayar da ita”. Malam Sambo Wali ya bayyana
irin wannan matsayi na mai tayar da zaune tsaye a waƙarsa ta “Ku bar faɗa ku
bar son yaya” a baiti na 13 da na 19, yana cewa:
Baiti na 13 Faɗa halin matsiyaci ne don ba shi da komi
Baƙin cikin mutan kirki sun tattara komi
Shi bai aje ba ɓanna ba ta cin shi da komi
Mai arziki ka tsoron fitina ko bisa komi
Don ba ya son abin da duk ka lalata biɗatai
Baiti na 19 Dut ‘yan ƙasarmu Afirka ban ɗebe guda ba
A bar faɗa a bar son yaya ba falo na ba
Mai hankali tunani yaka yi ba sababi ba
Faɗa halin matsiyaci na hauka shika wo ba
Ko mace na iza shi ga ɓannatai ya ga daidai
Shi ma Hamisu Lamiɗo wanda aka fi sani da Hamisu Iyantama, ya bayyana matsayin
mai ta da fitina a cikin mutane a waƙarsa ta “zaman lafiya” a baiti na farko
kamar yadda Malam Sambo Wali ya bayyana, yana cewa:
Baiti na 1 Fitina kwance take hankali kwance ne
Duk wanda ya tashe ta shaiɗani ne
Tsinuwar Allah yai la’anta ne
Ga wanda duk ya ta da hankalin juna
7.0 Hanyoyin Zama Lafiya da Sasantawa
Rubutattun waƙoƙin Hausa ba a
bar su baya ba wajen ƙoƙarin bayyana hanyoyin da suka dace mutane su riƙa
amfani da su domin ɗorewar zaman lafiya da sasantawa. Daga cikin waɗannan
hanyoyi da marubuta waƙoƙin Hausa sukan bayyana a waƙoƙinsu akwai: Haƙuri da
taimakon juna da son juna da kauce wa ruɗin duniya da neman ilimin addini da
ilimin kimiyya da sauransu.
Haƙuri: Haƙuri muhimmin sinadari ne da za a yi amfani da shi wajen
samar da zaman lafiya da ɗorewarsa a rayuwar al’umma. Da mutane za su riƙa sa
haƙuri a dukkan al’amurran rayuwarsu, da wasu fitintinu ba su addabe su ba. A
waƙarsa ta “zaman lafiya”, Bashir Musa Liman ya kawo bayanin haƙuri a baiti na
25 a matsayin hanyar zaman lafiya musamman dangane da rikice-rikicen siyasa da
ya mamaye Hausawa a yau, yana cewa:
Baiti na 25 ‘Yan siyasa su san cewa
A zaɓe akwai ci da faɗuwa
In sun faɗi su zan haƙurewa
Haka zai haifar da zaman lafiya
Wannan baiti yana kira ne musamman ga ‘yan siyasa da ‘yan bangarsu da ke tayar
da ƙayar baya idan ba su samu nasara ba. Kamata ya yi su bar wa Allah su ɗauki ƙaddarar
faɗuwa, wata rana za su iya samun nasara.
Adalci ga Shugabanni: Duk al’ummar da ta ribantu da samun adilan
shugabanni masu ƙoƙarin kyatata wa mabiya da kare martabarsu da ba su kariya ga
duk wani abu da ka iya barazana ga zamantakewar rayuwarsu. Yin hakan zai sa
zaman lafiya ya sami sukunin walwala, yayin da tashe-tashen hankula da
rikice-rikice za su ƙaranta. Farfesa Aliyu Muhammad Bunza a waƙarsa ta gasar waƙoƙin
zaman lafiya a baiti na 13 da 27, yana cewa:
Baiti na 13 A tabbata duk sha’anin ƙasa,
‘Yan ƙasa kowa ya tsunduma.
Baiti na 27 Hukuma ya zama wajibi gun ki,
Dole ki tashi ki ɗau tsuma.
Bashir Musa Liman a waƙarsa ta “zaman lafiya” a baiti na 26, kira ya yi ga
shugabannin siyasa da su sauke nauyin da aka aza musu na kare martaba da haƙƙoƙin
talakawan da suke wakilta, domin yin hakan ne zai kawo ɗorewar zaman lafiyar
al’umma. Ga abin da yake cewa:
Baiti na 26 Su kuma waɗanda suka kai ga ɗarewa
Ga muƙami, kujera suna masu lilawa
To, su sauke nauyi da haƙƙin talakawa
Don a samu kyakkyawan zaman lafiya
Taimakon Juna: A duk lokacin da al’umma suka haɗa kansu wuri ɗaya
wajen taimaka wa junansu domin warware wasu matsaloli na rayuwa, ba shakka
rayuwarsu za ta kyautata, kuma zaman lafiya zai sami filin baje kolinsa a
tsakaninsu. Ga abin da Bashir Musa Liman ke cewa dangane da taimakon juna a
baiti na 28 da na 30:
Baiti na 28 Masu kuɗi ku zan taimakawa
Kayan masarufi ku zam bayarwa
Taimakon talaka ku ci gaba da yowa
Wannan zai sa a samu zaman lafiya
Baiti na 30 Mu so juna, mu ƙaunaci juna
Mu ji tausayi, mu taimaki juna
Mu agaza, mu kyautata wa juna
Yin haka zai sa a zauna lafiya
Kawar da Bambancin Addini da Ƙabilanci: Nuna bambancin addini da ƙabilanci
na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rikice-rikice da ruɗani a ƙasar
Hausa, waɗanda suka jima suna ci wa mazauna ƙasar tuwo a ƙwarya. Sha’iri
Farfesa Aliyu Muhammada Bunza a waƙarsa ta gasa mai suna “mu zauna lafiya” a
baiti na 35 da 36 da 44 da baiti na 45, kira ya yi da a kauce wa
tashin-tashinar addini da ƙabilanci domin jama’a su zauna lafiya, yana cewa:
Baiti na 35 Dukkan masana a cikin ‘Dariƙa
Izala Shi’a na gama
Baiti na 36 Ku daina jidalin ƙungiyoyi
Da jayayya don mai sama
Baiti na 44 Ƙabilanci cutarsa ya ƙaiƙayi
Tsami wane rama
Baiti na 45 Yana kawo yaƙi ƙasa sai,
Ta tarwatsa babu wurin zama
Shi ma, Muhammadu Sambo Wali a waƙarsa mai suna “ku bar faɗa ku bar son yaya..”
a baiti na 8 da na 11, kira ya yi da a guji nuna bambancin addini da ƙabilanci
musamman tsakanin Musulmi da Kirista. Ya nuna cewa, tun da Allah ya riga ya
halitto mu wuri ɗaya, kamata ya yi mu haƙura mu zauna tare don mu amfana da
juna. Ga abin da yake cewa:
Baiti na 8 A bar faɗan ƙabilanci ban yarda da shi ba
Faɗan a tsarkake jinsi bai sahi da mu ba
Ubangijinmu yay yo mu ƙasa ɗai fa ki duba
Da yai nufin mu watse da bai yo haka nan ba
Nufin yakai mu amfana da junanmu gaba ɗai
Baiti na 11 Nan da ɗai Musulmi muke mun tsere tsara
Bisa dole an ka mulke mu ga mulki na Nasara
Ku riƙe faɗin Lakum Dinukum ba ta da gyara
A nan akwai Kiristoci na bayyana saura
Ga zamantakewa kowa tashi ta fissai
Bashir Musa Liman a waƙarsa ta “zaman lafiya” a baiti na 31, ya bayyana kawar
da nuna bambancin waɗannan abubuwa biyu (addini da ƙabilanci) a zukatan
al’umma, wani mataki ne na zaman lafiya da kawar da rikice-rikice, yana cewa:
Baiti na 31 Idan muna so mu zam walawa
ɓangaranci ya zamto mun wullarwa
Yarenci da ƙabilanci, mu zam kaucewa
Hakan zai sa a yi daddaɗar dariya
Kauce wa Ruɗin Duniya: Ko shakka babu, duk wanda ke biye wa ruɗin
duniya zai iya faɗawa cikin halaka ko da-na-sani. Wannan ya sa da yawa daga
cikin rikice-rikicen da ke addabar mutane akwai ruɗin duniya na biye wa son
zuciya suna aikata masha’a ba tare da tunanin abin da zai biyo baya ba, mai
kyau ko akasinsa. Wannan ya sa Bashir Musa Liman a waƙarsa ta “zaman lafiya” a
baiti na 33 da 34 da 35, yake gargaɗin mutane da su guji irin wannan ruɗi na
duniya don a samu zaman lafiya mai ɗorewa:
Baiti na 33 Jama’a mu guji ruɗin budurwar duniya
Ƙazamiya, mamugunciya, makauniya
Asharariya, ibilishiya, mayaudariya
Maƙaryaciya, mahillaciya, mazambaciya
Baiti na 34 Ruɗinta ke haifar da ƙiyayya
Har ya zamto ana ta bugayya
Yaudararta ta wuce sanayya
Ta wani, bare a yi zancen dubayya
Baiti na 35 Ya kamata mu yo tunani
Don tantance yanayin zamani
Don guje wa sharrin shaiɗani
Wanda ba ya son zaman lafiya
Ilimi: Samuwar ilimin addini haɗi da na zamani yana taimakawa ƙwarai
wajen wanzar da zaman lafiya da sasantawa. Haka ma, rashinsa a cikin al’umma
yana haifar da ruɗanin tashe-tashen hankula da wanzar da ƙiyayya. Haka kuma,
samuwar tarbiyya tagari ga al’umma wani sinadari ne na dauwamar da zama lafiya
a cikinsu. Wannan ya sa duk al’ummar da ta rasa kyakkyawar tarbiyya musamman ga
matasa, tilas ayyukan ta’addanci da rashin zama lafiya su addabe ta. Har wa yau,
Bashir Musa Liman a waƙarsa ta “zaman lafiya” a baiti na 37, yana gargaɗin
al’umma da su tashi tsaye wajen neman ilimi da kuma samar da tarbiyya domin
rayuwa ta sami walwala da sakewa, yana cewa:
Baiti na 37 A yi ilimin addini da na kimiyya
Kuma a ƙasa idan aka samu tarbiyya
Mu lura ƙasa za ta zauna lami lafiya
Da rayuwa ba kwan gaba, kwan baya
Dakta Aliyu Tilde ya yi irin wannan gargaɗi a waƙarsa ta “zaman lafiya” a baiti
na 35 ya ce a nemi ilimin addini da na zamani domin a sami zama lafiya da ci
gaban tattalin arziki:
Baiti na 35 Mu rungumi ilmu na dini da duniya
Ci gaba rizƙu don zaman lafiya
Haɗin Kai: A yayin da kawunan al’umma ya rarraba, kowa ya kama
gabansa, tilas fitintinu da rashin zaman lafiya su wanzu a tsakaninsu. Haɗin
kansu wuri ɗaya kuma, shi zai kawar da duk wata gaba da zogin zuci da kuma duk
wani tashin-tashina da kawo zaman lafiya. Da ma Hausawa na cewa: “Hannu ɗaya ba
ya ɗaukar jinka” Farfesa Aliyu Muhammad Bunza a waƙarsa ta gasa mai suna “mu
zauna lafiya” a baiti na 9 da na 10, ya bayyana haɗin kan al’umma daga cikin
abubuwan da ke zaunar da su lafiya, yana cewa:
Baiti na 9 Ku zamto ƙasa ɗai zuriya ɗaya
Zaman daɗi tamkar zuma
Baiti na 10 Irin haka shi ke sa ƙasa
Haɓaka ya zamo ta kankama
Hamisu Iyantama a waƙarsa ta “zaman lafiya” ya fito da wannan jigo na haɗin kai
domin samun zaman lafiyar al’umma a baiti na 4 da na 10, yana cewa:
Baiti na 4 Mu dena raba junanmu babu ci gaba
Ta kowace siga mu bar yin gaba
Idan Allah ya so ba zai bambanta mu ba
Halittarmu sai ya yo kamannin juna
Baiti na 10 Mu haɗa kai al’umma ɗaya kar mu rarraba
Muna kira mu jure wa halin juna
Mu zauna lafiya, mu zauna lafiya
Mu zauna lafiya tsakanin juna
Addu’a: A duk lokacin da wani al’amari ya zama tarnaƙi ga rayuwar
Hausawa, ya ƙi ci ya ƙi cinyewa, za ka iske an mayar da lamarin ga hannun
Ubangiji ana yawaita addu’ar samun mafita domin kuɓutar da rayuwa ga irin
barazanar da ake yi mata. Wannan ya sa marubuta waƙoƙin Hausa bayan sun bayyana
irin hanyoyin zaman lafiya, sai kuma su biyo da addu’a ga mahalicci domin ya sa
hannu cikin lamarin. Wannan shi ya haifar da yawaitar amfani da karin maganar
Hausawa da ke cewa: “Allah ya ba mu lafiya da zaman lafiya”. Bashir Musa Liman
a waƙarsa ta “zaman Lafiya” a baiti na 39 yana cewa:
Baiti na 39 Roƙona ga Ubangiji Makaɗaici
Mai halitta har da iccen maɗacci
Wanda ya sa har abinci nakan ci
Ya sa ƙasata a yi zaman lafiya
Baiti na 40 Tammat a waƙe na zo ƙarshe
Don alfarmar Annabin ƙarshe
Dace da ganinsa shi ne ƙarshe
Allah ya sa a samu zaman lafiya
Shi ma Aliyu Tilde ya yi makamancin wannan addu’a na samun zaman lafiya mai ɗorewa
a cikin al’umma, a waƙarsa ta “zaman lafiya” a baiti na 30 da 31 da 34 da 87,
yana cewa:
Baiti na 30 Ta’ala mashiryi ga ni gare ka
Ina zan ka roƙon zaman lafiya
Baiti na 31 Gare ni da ‘ya’ya da mata dukkanmu
Da dangi abokai ga baki ɗaya
Baiti na 34 Fitintinu na baya kaza na zamanu
Ka kare mu Jalla mu zam lafiya
Baiti na 87 In yi sujuda in gode Allah
Ta’ala ka zaunar da mu lafiya
8.0 Amfanin Zama Lafiya
Haƙiƙa babu wani abu ɗaya mafi alfanu a rayuwar al’umma da ya kama
ƙafar zaman lafiya. Sai da zaman lafiya basarake zai gudanar da mulkinsa a
tsanake. Mai arziki ba ya more wa dukiyarsa idan babu zaman lafiya. Walwala ba
ta samuwa ga talaka idan ba a zaune lafiya. Wannan ya sa Hausawa ke cewa: “Zama
lafiya ya fi zama ɗan sarki, ko ma ya fi zama sarkin.” A kan haka ne marubuta
waƙoƙin Hausa suke bayyana alfanun zama lafiya domin al’umma su rungume shi ta
yadda za su ribanci rayuwarsu. Sha’iri Farfesa Aliyu Muhammad Bunza a waƙarsa
ta zaman lafiya, ya yi bayanin amfanonin zaman lafiya a cikin al’umma a baiti
na 61 da na 62 da na 63, yana cewa:
Baiti na 61 Ku bi ni da kyau in lisafo
Fa’ida ga zama bisa lalama
Baiti na 62 Yana bunƙasar da ‘ya’yanta
Al’amurranta su kankama
Baiti na 63 Sana’o’i su yawaita don
arzikinmu
Ya zan ya dauwama
Idan aka yi nazarin waɗannan baituka za a ga suna nuni da cewa, idan aka samu
zaman lafiya a ƙasa, komai zai haɓaka a samu ci gaba, kama daga tattalin arziki
da abubuwan more rayuwa da sauran al’amurra.
Shi ma Dakta Aliyu Tilde a waƙarsa ta “zaman lafiya” ya fito da amfanin zaman
lafiya a matsayin arzikin da babu kamarsa a faɗin duniya a baiti na 32 da baiti
na 33, yana cewa:
Baiti na 32 Musulmi, Kirista Ta’ala Karimu
Haɗa mu zumuncin zaman lafiya
Baiti na 33 Daɗe mu fahimta ta juna mu gane
Cikin arziki ba kamar zaman lafiya
Auwalu Anwar a waƙarsa ta “zaman lafiya” a baiti na 4 da baiti na 8 da ke cikin
littafin Gadar Zare, shi ma yana bayyana cewa, dukkan wani ci
gaban ƙasashen duniya da za a iya samu ya ta’allaƙa ne ga zaman lafiya. Ga abin
da sha’irin ke cewa:
Baiti na 4 Batun ci gaban duk ƙasashe haƙiƙa
Yana nan ga samun zaman lafiya
Baiti na 8 Ku gane batun tattalin arzikinmu
Gudan ginshiƙinsa zaman lafiya
https://www.amsoshi.com/2017/11/06/lokacin-abu-yi-shi/
Naɗewa
Babu shakka, zaman lafiya wani al’amari ne da ke da matuƙar muhimmanci da
amfani a tarihin rayuwar ɗan Adam. Babu wani mutum ɗaya mai arziki ko moro,
basarake ko talaka ko mai mulki da zai sami ingantaccen rayuwa mai ɗorewa da
sakewa ba tare da zaman lafiya ba. Babu wata al’umma da za ta sami ɗaukaka ko
bunƙasa da ci gaban tattalin arziki da siyasa da zamantakewa da walwala face
tana gudanar da rayuwarta cikin ƙoshin zaman lafiya. Saboda haka ne za a iske
duk wata al’umma da ta sami ci gaban rayuwa, haƙiƙa tana bisa turba ta zaman
lafiya. Haka ma, duk wata al’umma ko ƙabila ko ƙasa da rikice-rikice da yaƙe-yaƙe
da tashin-tashina suka mamaye ta, za a tarar al’amurranta sun taɓarɓare ko ma
sun durƙushe baki ɗaya.
MANAZARTA
Bunza, A.M. (2015) “Labarin Zuciya a Tambayi Fuska: Saƙon Dariya ga Sasanta Tsaro
a
Farfajiyar Karatun Hausa”. Takardar da aka gabatar a Makarantar Harsuna, Sashen
Hausa na Kwalejin Ilimi ta Adamu Augie, Argungu.
Bunza, A.M. (2015) “Zama Lafiya Ya Fi Zama ‘Dan Sarki: Shirin Tunkarar Zaɓen 2015
2015 a Nijeriya” Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani kan kyautata
zama
lafiya a zaɓen da za a gudanar a shekarar 2015 wanda ƙungiyar Orphans
and Huffaz
Educational Foudation Birnin Kebbi ya shirya.
Bunza, A.M. (2015) “Zaman Lafiya da Tsaro a Daular Musulunci ta Sakkwato: Abin
Koyi ga
Shugabannin Zamaninmu”. Takardar da aka gabatar a taron yini ɗaya da Centre
for Intellectual Services on Sokoto Caliphate ta shirya na faɗakarwa a
kan muhimmancin tsaro da zaman lafiya.
Ezirim, G.E. (2009) “The Role of Civil Society in Conflict Management” in Peace
Studies
and Conflict Resolution in Nigeria: A Reader, Edited by Ikejiani-Clark
M. Spectrum
Books Limited, Ibadan.
Francis, D.J. (2006) “Peace and Conflict Studies: An African Overview of Basic
Concepts” in
Introduction to Peace and Conflict Studies in West Africa, Edited
by Shedrack Gaya
Best Published by Spectrum Books Limited, Ibadan.
Sani, S. (2007) The Killing Fields: Religious Violence in Northern
Nigeria. Ibadan: Spectrum Books limited, Spectrum House.
[i] Alhaji Abubakar Ladan 1975:ix, Waƙar Haɗa
kan Al’ummar Afirka. Ibadan: University Press Limited.
[ii] Aliyu Muhammad Bunza 2015. “Zaman Lafiya da
Tsaro a Daular Musulunci ta Sakkwato: Abin Koyi ga Shugabannin Zamaninmu.”
Takardar da aka gabatar a taron yini ɗaya da Centre for Intellectual Services
on Sokoto Caliphate ta shirya na faɗakarwa a kan muhimmancin tsaro da zaman
lafiya a ƙarƙashin koyarwar shugabannin Daular Musulunci ta Sakkwato ranar
Asabar 31 ga Janairu, 2015 da ƙarfe goma na safe.
[iii] Oke Ibeanu 2006 “Conceptualising Peace” a
cikin Introduction to peace and conflict studies in West Africa,
[iv] David J. Francis, “Peace and conflict studies:
An African overview of basic concepts” a cikin Introduction to peace
and conflict studies in West Africa, 2006.
[v] Ƙamusun Hausa Wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Bayero Kano, shafi na 393.
[vi] Oxford Advanced Leaners’ Dictionary Seventh
Edition, shafi na 1244.

1 Comments
[…] Yunk’urin Samar Da Zaman Lafiya Da Sasantawa: Bincike Kan Wak’ar Zaman Lafiya Ta Bashir Musa Lim… […]
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.