Ticker

6/recent/ticker-posts

Dabbobin Ruwa A Mahadin Magungunan Gargajiya

NA

MUSA SHEHU
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
07031319454
msyauri@yahoo.com

GABATARWA

Magani a sha ka a warke, har gobe ruwa na maganin daud’a. Hausawa al’umma ce da tun asali suke da hanyoyin neman waraka daga kowace irin cuta da kuma kariya daga kamuwa da ita tun kafin saduwarsu da kowace irin al’umma. Wannan hanya kuwa ita ce ta amfani da magungunan gargajiya. Ba komai ne wad’annan magungunan gargajiya ba face had’e-had’en wasu abubuwa da suke a muhallinsu ko suka mallaka, kama daga tsirrai da itatuwa ko k’wari ko ko dabbobi da makamantansu. Had’a itace da wasu albarkatun k’asa ko sama ko had’a wani ganye da wani, ko had’a wata saiwa da wata, ko gamin gambizar tsirrai da itace da k’wari da wasu abubuwa shi ake kira had’i a nazarin magani. Abubuwan da za a nemo, da lokacin da za a nemo su, da had’a su, da yanayin had’a su, shi ake ce wa mahad’i a nazarin magani. (Bunza 2006). A kan haka ne wannan mak’ala za ta yi k’ok’ari wajen nazarin wasu magungunan gargajiya wad’anda ake had’awa da sassan jikin wasu dabbobin ruwa, ko dai domin samun waraka daga wata cuta, ko domin kariya daga kamuwa da ita, ko domin saka ta ga jikin abokin gaba, ko don biyan wasu buk’atu na rayuwa.

2.0     MA’ANAR MAGUNGUNAN GARGAJIYA


Magani a sha ka a warke, kuma rashin yin magani ga maras lafiya wauta ce. A K’amusun Hausa (2006) an bayyana ma’anar magani da cewa, shi ne abin da ake sha ko shafawa a jiki ko d’urawa a jini ta hanyar yin allura don neman samun lafiya. (Bunza, 2006) ya bayyana ma’anar magani da cewa, wata hanya ce ta warkarwa ko kwantar da ko rage cuta ta ciki ko ta waje, ko wadda ake samu daga had’ari ko kuma neman kariya ga cutar abokan hamayya, ko cutar da su ko neman d’aukaka daraja ta hanyar siddabaru da sihiri na ban al’ajabi. Abdullahi (2013) yana cewa, kalmar magani na nufin duk wata hanya da d’an Adam zai bi wajen warkar da cuta ko rauni ko neman kariya daga cutar. Saboda haka ana iya cewa, magani shi ne duk wani abu da aka yi amfani da shi domin magance wata cuta, ko cutar da wani aka saka ta ga jikinsa. Maganin gargajiya shi ne amfani da itatuwa ko rubutu ko addu’a ko surkulle don warkar da wata cuta, ko neman wani amfani, ko gusar da sharri, ko haddasa  wani abu saboda biyan buk’ata (Musa da Zarruk’, 1982). Magungunan gargajiya sun kasu kashi-kashi. Akwai magungunan warkar da cutar jiki, akwai na kariyar jiki daga cuta da masharranta, akwai kuma magungunan waibuwa da tsafe-tsafe. Kashi na farko ba su da bi-ta-da-k’ulli mai muni k’warai, domin da ma cuta ce za a kawar. Kashi na biyu irin kashi na farko ne, domin jiki ne ake kariya daga cutar da ake yi masa barazana. Kashi na k’arshe shi ke da had’ari k’warai da gaske, domin harkokin da suka had’a da iskoki da neman taimakonsu da bauta musu domin biyan wasu buk’atu na rayuwa kawai. (Bunza, 2006).

MA’ANAR DABBOBI
A ma’ana ta k’amusun Hausa an kawo ma’anar dabbobi da cewa, dukkan halitta mai k’afa hud’u. Shi kuwa Abraham (1946:159) a cikin Mu’azu (2012) ya bayyana ma’anar dabbobi da cewa, duk wata halitta da ta shafi dabbobi masu jan ciki da k’wari da kifaye da tsuntsaye ana kiransu dabba, sannan akwai dabbobin daji da na gida. A fahimtata za a iya kallon dabbobi ta fuska biyu, wato dabbobin ruwa da kuma na tudu.

Dabbobin Ruwa: K’ofar Soro (2007) ya bayyana dabbobin ruwa da cewa, wasu halittu ne da Allah ya yi su bisa doron k’asa amma rayuwarsu a cikin ruwa take, sai dai daga cikinsu akwai wad’anda ke fitowa saman tudu. Ana samun dabbobin ruwa iri daban-daban kamar su dorina, kada ayyu, karen ruwa, da sauransu.

Dabbobin Tudu: Melinda (2008:18-19) a cikin Mu’azu (2012) yana mai cewa, dabbobin tudu wasu halittu ne da Allah ya halicce su a kan iyaka ba cikin ruwa ba. Irin wad’annan dabbobi suna gudanar da rayuwarsu a kan tudu ne, wato a gida tare da mutane ko a daji cikin rami ko kogo ko saman bishiya. Ire-iren  dabbobin da ake samu a daji sun had’a da zaki da kura da damisa da biri da ‘bauna da gada da karkande da sauransu. Dabbobin gida kuwa sun had’a da awaki da shanu da rak’uma da dawaki da raguna da dai makamantansu. Sai dai kamar yadda aka yi bayani a wajen gabatarwa cewa, nazarin zai dubi dabbobin ruwa ne kawai ba da na tudu ba domin a nazarci ire-iren magangunan gargajiya da ake had’awa da sassan jikin wasu daga cikin dabbobin ruwa.

3.0   DABBOBIN RUWA


Allah Ubangiji ya halicci duniya da kuma halittun da ke rayuwa a cikinta wad’anda suka had’a da halittun ruwa da na tudu. Akwai halittu iri daban-daban masu tarin yawa da ke rayuwa a saman tudu, kama daga d’an Adam da aljannu da dabbobi da k’wari da tsuntsaye da sauransu. Kamar yadda wad’annan halittu ke rayuwa a tudu, haka ma akwai halittu masu tarin yawa da ke rayuwa a cikin ruwa wanda kusan ake cewa sun d’ara halittun da ke bisa tudu yawa. Daga cikin dabbobi ko halittun da suka yi fice ko wad’anda Bahaushe ya fi sani da ke rayuwa a cikin ruwa akwai kifaye da kada da dorina da ayyu da karen ruwa da sauransu.

Bari mu dubi ire-iren wad’annan halittu ko dabbobi na ruwa d’aya bayan d’aya da kuma ire-iren magungunan gargijiya da ake had’awa da wasu sassa na jikinsu domin samun waraka daga wata cuta ko don biyan wata buk’ata ta rayuwar yau da kullum.

3.1  KIFI

A ma’ana ta k’amusun Hausa (2006) an bayyana ma’anar kifi da cewa, wata halitta a ruwa mai k’arni wadda ake ci, akwai su iri-iri kamar su tarwad’a, ko tsage ko lulu ko karfasa ko musko ko ragon ruwa ko sawayya ko k’araya ko minjirya ko ‘barya ko bargi ko madde ko halullu’ba. Kifi na d’aya daga cikin halittun da Allah ya halitta wad’anda ke rayuwa a cikin ruwa, kuma yana d’aya daga cikin abincin da d’an Adam yake sarrafawa domin ya ci, ya kuma biya buk’atar rayuwarsa. Amfanin kifi ga al’ummar Hausawa bai tsaya kawai a matsayin abin da za a ci a ji dad’in rayuwa ba, suna amfani da shi wajen sarrafa magungunan gargajiya iri daba-daban domin neman waraka daga wata cuta, ko domin kariya daga gare ta, ko domin cutar da abokin hamayya, ko don biyan wata buk’ata ta rayuwa. Akan yi amfani da wasu nau’o’in kifaye daban-daban ta hanyar amfani da wasu sassa na jikinsu kamar kawunansu ko ‘bawan jikinsu ko kitsensu ko ma fatar jikinsu, domin a had’a wasu magungunan gargajiya iri daban-daban. Bari mu kalli ire-iren wad’annan kifaye da ake amfani da sassan jikinsu wajen had’a wasu magungunan na gargajiya.

MAJIRIYA: Majiriya na d’aya daga cikin nau’o’in kifayen da ake samu a koguna da gulaben k’asar Hausa. Majiriya kifi ne mai ban al’ajabi wanda idan yana da rai ba a iya ta’ba shi, idan kuwa aka ta’ba shi ba za a sha da dad’i ba, domin kuwa ana ta’bawa za a ji majiriya kamar an ta’ba wayar lantarki. Hausawa suna amfani da sassan jikin wannan kifi su sarrafa magungunansu na gargajiya domin biyan buk’atunsu na rayuwa dangane da magani. Alal misali, ana amfani da fatar wannan kifi a sarrafa maganin dambe, ko a d’inka laya da fatar a rik’a shafa masa kitsen kifin a kai-a kai. Idan d’an dambe ya d’aura wannan laya ya bugi abokin karawarsa zai ji kamar wutar lantarki ta ja shi kuma jikinsa zai yi sanyi, sai ya mik’a wa abokin karawar nasa kai bori ya hau.

CINI: Shi ma cini wani nau’i ne na kifi mulmulalle d’an siriri kuma bak’i mai kama da maciji. An bayyana cewa ana amfani da wannan kifi ne wajen magance matsalar al’aura, wato ana sarrafa shi da wasu magunguna domin a yi amfani da shi ga namijin da al’aurarsa ba ta aiki.

KULLUME: Kullume wani nau’in kifi ne bak’i mai  santsin jiki da kuma k’aton kai. Ana amfani da kan kullume a jik’a wa yara su rik’a shan ruwan a matsayin maganin dussa ko gaida. Haka kuma akan yi amfani da kansa a saka wata laya a ciki a sake shi a cikin ruwa. A wannan lokaci duk wanda aka had’a ma wannan magani zai bi duniya ba tare da an san inda ya nufa ba, kamar dai yadda ba a san inda wannan kifi ya nufa ba, wato dai wannan magani kamar kurciya yake. Bugu da k’ari, ana amfani da kitsen kullume ana shafawa a jiki a matsayin maganin sanyi.

CIHAKI: Ana kiran ta da wannan suna ne saboda haki na daga cikin abincin da take ci a cikin ruwa. Dangane da siffarta kuwa, tana da d’an fad’in jiki da duhu da kuma d’an k’aramin kai. Ana amfani da kitsen wannan kifi wajen yin maganin firgitar yaro. Wato idan yaro na firgita ana amfani da man cihaki a had’a masa magani domin samun waraka ko sauk’i.

BALLI: Wannan ma wani nau’i ne daga cikin kifayen da ake samu a k’asar Hausa. Shi ma wannan kifi ana amfani da wasu sassa na jikinsa a had’a wasu magungunan gargajiya, kamar idonsa, da kuma ‘bawon jikinsa. Ana amfani da k’wayar idonsa a had’a maganin matsalar ido. Wato idan mutum ba ya gani sosai ana had’a masa magani da idon wannan kifi domin magance matsalar ko domin samun sauk’i. Har wa yau, an ce Fulani na amfani da idon wannan kifi ga shanunsu wad’anda ke da matsalar gani na idanu. Haka kuma an ce ana amfani da ‘bawon kifin a sarrafa magunguna iri daban-daban.

TALIBAMBAN: Talibamban wani nau’in kifi ne bak’i kuma mai k’aton ciki. Galibi masu ba da maganin gargajiya ba wai suna amfani da wannan kifi ba ne wajen maganin warkar da wata cuta ko kariya daga kamuwa da ita, a’a, suna amfani da wannan kifi ne wajen had’a maganin cutar da wani ko wasu. Sun bayyana cewa, idan aka had’a wa mutum wannan magani ko asiri da wannan kifi duk jikinsa zai kumbura ya k’abe kamar dai yadda wannan kifi yake, daga k’arshe mutum ya ce ga garinku.

BO’DAMI: Shi ma wannan wani kifi ne mai ban al’ajabi, domin an ce idan yana cikin ruwa sai ruwan ya jaye ya bar shi a cikin laka, an ce zai iya rayuwa a wannan laka har tsawon lokacin da wannan ruwa ya sake dawowa ya iske shi. Sun k’ara da cewa bindinsa na daga cikin abin da yake ci a cikin wannan laka. Dangane da maganin da ake had’awa da wannan kifi kuwa, an ce ana amfani da shi wajen had’a maganin ruwan nono. Ma’ana idan mace ta haihu ya kasance tana da k’arancin nonon shayar da yaro, ana amfani da wannan kifi a had’a mata maganin da zai taimaka mata don samun isasshen ruwan nonon da yaro zai sha ya k’oshi.

YAUNI: Shi wannan kifi ana amfani ne da bindinsa domin a magance matsalar ciwon kunne, ko idan kunne yana ruwa.

GWANDO: Gwando wani kifi ne mai d’an duhu kuma mulmulalle ne mai kama da sifar maciji, kuma yana da ‘bawo mai kauri. Saboda haka idan za a yi amfani da shi sai swale ‘bawonsa tare da fatar sannan a dafa a ci. Ana amfani da ‘bawon wannan kifi a dake shi a had’a shi da wasu magunguna ana shafawa ga jiki domin magance salewar jikin mutum.

ZANGAI: Shi wannan kifi an ce ba a samun sa a k’asar Hausa sai a k’asar Mali. An ce ana amfani da idon wannan kifi domin samar da maganin dundumin ido.

RAMBOSHI: Ramboshi kifi ne mai kama da kullume ainun. Sai dai shi ramboshi yana girma k’warai fiye da kullume, kuma ya fi kullume k’aton kai. Bayanai sun nuna cewa, ana amfani da kitsensa a sarrafa magunguna iri daban-daban.

GIWAR RUWA: Giwan ruwa wani kifi ne babba wanda aka ce da wuya a sami kifin da ya kai shi girma a cikin gulabe da rafukan da ke k’asar Hausa. Ana amfani da ruwan idon giwar ruwa a sarrafa maganin matsalar rashin gani sosai.

TARWA’DA: Ana amfani da tarwad’a wajen rufe bakin mutane idan ba a son a tona wani sirrin wani al’amari, wato dai magani ne kamar shashatau.

K’WAN KIFI: Shi kuwa k’wan kifi ana amfani da shi ne a sarrafa maganin samun haihuwa ga mace idan ta d’auki lokaci ba ta samu haihuwar ba.

https://www.amsoshi.com/2017/11/08/littafin-ruwan-bagaja-maaunin-matakan-rayuwar-bahaushe/

3.2  AYYU

 Ayyu wata dabbar ruwa ce wadda ba kasafai ake samun ta a kowane gulbi ko rafi na k’asar Hausa ba. Bayanai sun nuna cewa, wannan dabba (wato ayyu) tana kama da saniya matuk’a, domin an ce idan aka cire kanta aka aje gefe d’aya ba tare da mutum ya ga gangar jikinta ba zai rantse cewa saniya ce aka yanka. Abin da kawai aka ce ya bambanta ayyu da saniya shi ne k’aho, domin shi ayyu ba shi da k’aho irin na saniya. Bugu da k’ari, an nuna cewa ayyu dabba ce mai tsananin ji, wanda hakan ya sa take da wahalar kashewa sai an yi mata kyakkyawan shiri kafin a tunkare ta. Dangane da amfaninta kuwa, baya ga namanta da ake sarrafawa domin a ci, akwai wasu magungunan gargajiya da ake sarrafawa da wasu sassa na jikinsa, kamar zakarinsa ko maniyinsa, da kitsensa da k’ashinsa da bayansa da makamantansu.

ZAKARI/MANIYIN AYYU: Bayanai sun nuna cewa, ana amfani da zakari ko maniyin ayyu a sarrafa yaji da shi domin maganin k’arin mazakuta. Wannan kusan a ce a bayyane yake, domin sau da yawa za ka ji masu tallar maganin gargajiya suna yawo suna tallata zakarin ayyu a matsayin maganin k’arin mazakuta.

K’ASHIN AYYU/KITSENSA: Akan yi amfani da k’ashin ayyu da kitsensa wajen sarrafa maganin amosanin k’ashi.

GASHIN BAYAN AYYU: Bayanai sun nuna cewa akwai wani gashi da ke akwai a bayan jikin ayyu. Ana amfani da wannan gashi domin a yi maganin k’yasfin jiki.

FATAR AYYU: Ana amfani da fatar jikin ayyu a sarrafa maganin sanyin jiki gaba d’aya.

3.3   KADA

 A ma’ana ta k’amusun Hausa (2006), kada wata halitta ce dangin k’adangare, k’ato, da ke zaune a cikin ruwa, yana da ‘bawo-’bawo mai k’arfi a bayansa. Kada na d’aya daga cikin manyan halittun da ke ruwa wanda aka ce yakan iya had’iye mutum kai tsaye ya koma ya yi kwanciyarsa. Galibi manya da yara kowa ya san kada, saboda sau da yawa za  ka iske wasu masu ba da maganin gargajiya sukan rik’a yawo da shi kasuwa kasuwa suna tallata maganinsu. An ce yana da hak’ora masu tsananin dafi wanda idan ya ciji mutum ba a d’auki matakin gaugawa ba tsutsa za ta fara fitowa daga wurin da ya yi cizon. Kada kamar d’an’uwansa ayyu yake ta fuskar amfani da wasu sassa na jikinsa da Hausawa ke sarrafawa a magungunansu na gargajiya. Daga cikin sassan jikin nasa da ake had’a magungunan gargajiya akwai watan kada da hak’oransa da suhensa da kitsensa da kashinsa da dutsensa da sauransu.

WATAN KADA: Watan kada wani kitse ne da ake samu a cikin tumbin kada bayan an fafe cikinsa. Dangane da maganin da ake had’awa da wannan kitse kuwa, an ce ana amfani da shi ne wajen had’a maganin bindiga ta yadda ko an halbi mutum bindiga ba za ta tashi ba, ko ba za ta kai ga jikin mutum ba.

DUTSEN KADA: Wannan wani dutse ne ko duwatsu wad’anda ake samu a cikin cikin kada wad’anda yake had’iyewa a lokacin da yake kalaci. Ana amfani da wannan dutse a had’a shi da bauri ana ba yara k’anana wad’anda ba su fara hak’ora ba suna sha a matsayin maganin hana wahalar da yara ke sha ta rashin lafiya a lokacin da hak’ora za su fito musu.

K’ASHIN KADA/KITSENSA: K’ashin kada da kitsensa ana amfani da su wajen had’a maganin sanyin k’ashi.

HAK’ORIN KADA: Shi kuwa hak’orin kada ana amfani da shi ne wajen had’a maganin ciwon hak’ori.

KASHIN KADA/BAYANSA: Bayanai sun tabbatar da cewa, ana amfani da wad’annan abubuwa biyu wato kashi da kuma bayan kada musamman wajen had’a maganin k’arfe ko kuma tauri.

SUHEN KADA/ZUCIYARSA: Ana amfani da suhen kada a sarrafa maganin tari. Zuciyarsa kuma ana amfani da ita a had’a maganin ciwon k’irji.

https://www.amsoshi.com/2017/11/08/barazanar-zamani-kan-magungunan-hausawa-na-gargajiya/

 

3.4  DORINA

 A ma’ana ta k’amusun Hausa (2006), dorina wata k’atuwar dabba ce mai zama a ruwa. Dorina wata dabbar ruwa ce mai girman gaske, domin ta fi ayyu da kada girman jiki. Dorina dabba ce mai abin al’ajabi musamman a cikin ruwa, domin kuwa sau da yawa takan taso saman ruwa d’auke da d’anta a baya tana wasa saman ruwa jama’a na kallo suna shewa da ta’bi har na tsawon wani lokaci. A wasu lokuta takan baro cikin ruwa ta tako tudu ta yi kiwo musamman a fadama, idan ta k’are ta koma ruwa. Ita ma dorina kamar takwarorinta ayyu da kada, baya ga amfani da namanta da ake yi ana had’a abinci, bayanai sun nuna ana amfani da wasu sassa na jikinta wajen had’a magungunan gargajiya kamar kitsenta da zakari da ‘bargo da sauransu.

ZAKARIN DORINA: Ana amfani da zakarin dorina wajen had’a maganin k’arin k’arfin mazakuta.

KITSEN DORINA: Shi kitsen dorina ana amfani da shi ne a rik’a shafawa a jiki musamman ga masu zuwa d’iban sak’ar zuma. An ce idan mutum ya shafa kitsen dorina ga jikinsa zuma ba ta halbinsa.

‘BARGON DORINA: Ana sarrafa ‘bargon dorina domin a had’a maganin sanyin fadama.

3.5   KAREN RUWA

          Karen ruwa wata dabba ce daga cikin dabbobin ruwa da ba kasafai ake samun ta a k’asar Hausa ba, kuma an ce yana da kamanni irin na karen tudu. An ce karen ruwa yana da saurin ‘bacewa a cikin ruwa, domin idan aka gan shi kafi k’yaftawar ido ya ‘bace. Karen ruwa ba kowa ne ya san shi ba kamar yadda aka san kada ko dorina, domin masunta ma ba su faye ganin sa ba balle mutanen gari. Shi ma karen ruwa ana amfani da sassan jikinsa kamar fatarsa da zakarinsa wajen had’a magungunan gargajiya.

ZAKARIN KAREN RUWA: Zakarin karen ruwa ana amfani da shi a had’a yaji a matsayin maganin k’arfin maza.

FATAR KAREN RUWA/KITSENSA: Ana amfani da fatar karen ruwa had’i da kitsensa a had’a layar ‘bata. Bayani ya k’ara da cewa wannan magani na ‘bata da ake had’awa da fatar karen ruwa ko kitsensa bai rasa nasaba da irin saurinsa da kuma ‘bacewar da yake yi nan take idan yana cikin ruwa. Bugu da k’ari, ana amfani da fatarsa a yi laya da shi mace ta d’aura a wuya don maganin wabi.

3.6  MACIJI DA KUNAMAR RUWA: Kamar yadda ake samun macizai da kunamu a tudu kuma nau’o’i daban-daban, hakanan ma akwai macizai da kunamu da ke rayuwa a cikin ruwa. A gargajiyance, bayanai sun nuna cewa, maharban tudu sukan yi amfani da dafin maciji da kunamar ruwa ga makaman halbinsu kamar bindiga da kibau da sauransu, ta yadda  makaman halbin za su k’ara dafi ga jikin dabbar da aka halba. Haka kuma ana amfani da kitsen mesar ruwa ana shafawa ga baya a matsayin maganin ciwon baya.

Kammalawa

Ba shakka wannan nazari ya tabbatar mana da cewa, akwai hanyoyi da dama da Hausawa suke  amfani da su domin sarrafa magungunansu na gargajiya tun zamanin zamunna. Duk da cewa an sami ci gaban zamani da wayewa da tasirin addini ta fuskoki daban-daban a rayuwar Hausawa, amma hakan bai hana har gobe ana amfani da wannan hanya ta gargajiya wajen neman waraka daga wata cuta ba. Hasali ma sau da yawa idan wata cutar ta gagari magungunan zamani dole sai an koma wa magungunan gargajiya domin neman waraka. Su kuwa magunguna irin na kariyar kai da kaya ko na cutar da wani ko neman wasu biyan buk’atoci na rayuwar yau da kullum, har gobe suna ci gaba da gudana musamman ga masu alak’a da su.  Bugu da k’ari, nazarin ya bayyana muna cewa, amfanin dabbobin ruwa bai tak’aita ga sarrafa abinci kawai ba, ana amfani da su wajen neman lafiya da tsarin jiki da sauransu, duk da cewa wasu dabbobin ba kasafai ake samun su ba idan buk’atar amfani da su ta taso.

MANAZARTA


Abdullahi, I.S.S  (2013) “ Muhallin  Magani  a  Adabin  Bakan Bahaushe”, A cikin ‘Dund’aye

Journal of Hausa Studies, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Alhassan, H. da wasu (1982)  Zaman  Hausawa  Bugu  na  Biyu.  Islamic Publications Bureau

Lagos.

Bunza, A.M.  (1990)  “Hayak’i  Fid  Da  Na  Kogo: Nazarin  Siddabaru  da Sihirin Hausawa”,

Kundin digiri na biyu, Jami’ar Bayero, Kano.

Bunza, A.M.  (1995)  “Magungunan Hausa a Rubuce: Nazarin  Ayyukan  Malaman Tsibbu”,

Kundin digiri na uku, Jami’ar Bayero, Kano.

Bunza, A.M. (2006) Gadon Fed’e Al’ada. Tiwal Nigeria Limited Surulere Lagos.

Bunza, A.M. (2008)“Asirran Sata a Riwayar Gambo” Takardar da aka gabatar a taron k’ara wa

juna  sani  na sashen koyar da harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Datti,  B.M. (2012) Tasirin  Magungunan  Gargajiya a Cikin  Fina-finan  Hausa. Kundin digiri

na d’aya, Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo, Sakkwato.

Gulbi, A.S.(2013) “Tsafe-tsafen Demokorad’iyya”, Takardar da aka gabatar a taron k’asa na

farko da Cibiyar  Nazarin Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero, Kano ta shirya a kan

Harshe da Adabi da Al’ada.

Madabo, M.H.  (1979)  Ciniki da Sana’o’i  a  K’asar  Hausa. Printed in Great Britain, Thorbay

Press Limited Rayleigh Essex.

Wadanda aka yi hira da su:

Adamu Bakane Sokoto. 20-01-2013

Bala ‘Dankano Sokoto.   20-01-2013

Umaru Ciyaman na masu magani a garin Yauri. 31-01-2013

Muhammadu Sani Kullume. 31-01-2013

Babaruda Yauri. 02-02-2013

‘Danhajiya Yauri. 02-02-2013

Alhaji Ibrahim Taraba Yauri. 02-02-2013

 www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments