Ticker

6/recent/ticker-posts

Barazanar Zamani Da Mutuwa Ga Harshen Hausa



Hausawa na cewa zamani riga ce, wanda ya ƙi saka ta ya kwana huntu. Daga cikin wasiyyar marigayi Muhammadu Hambali Jinju akwai bincike, rubutu da talifi. Wanda duk ya zauni Farfesa Hambali zai san mutum ne mai kama jiki, mai kishin Hausa da Hausawa, mai ƙwazon ganin Hausa ta ci gaba, mai sha’awar koyar da Hausa da Hausa, mai ƙoƙarin ganin an fassara wasu ayyuka na wasu ilmuka zuwa Hausa domin amfanin Hausawa. A koyaushe  yakan gaya muna, ku kama jiki, ku yi bincike in mu ne yau, ba mu ne gobe ba. Yau 2014 maganarsa ta zama nashin ƙasa babu kure. Don haka nake son in jinjini wasiyar bisa ga barazanar zamani da mutuwa ga sha’anin bunƙasa da ci gaban harshen Hausa a duniyar karatun boko.

-------------------------------------------
Daga
Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan, Nijeriya
Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina
Jahar Katsina, Nijeriya
--------------------------------------------------
 
Takardar da aka gabatar a taron ƙasa da ƙasa domin karrama Marigayi Farfesa Muhammadu Hambali Jinju mai taken: The Challenges of Teaching African Languages and Association des Auteurs Nigeriens en Langues Nationales (ASAUNIL) due da Nigerian Indegenous Languages Writers Association NILWA suka shirya, ranar 19-21 Febrairu, 2014 a Emir Sultan, Niger Republic haɗe da bukin ranar Harshen Uwa International Mother Language Day (IMLD) da UNESCO ta ƙaddamar
Gabatarwa
Hausawa na cewa zamani riga ce, wanda ya ƙi saka ta ya kwana huntu. Daga cikin wasiyyar marigayi Muhammadu Hambali Jinju akwai bincike, rubutu da talifi. Wanda duk ya zauni Farfesa Hambali zai san mutum ne mai kama jiki, mai kishin Hausa da Hausawa, mai ƙwazon ganin Hausa ta ci gaba, mai sha’awar koyar da Hausa da Hausa, mai ƙoƙarin ganin an fassara wasu ayyuka na wasu ilmuka zuwa Hausa domin amfanin Hausawa. A koyaushe  yakan gaya muna, ku kama jiki, ku yi bincike in mu ne yau, ba mu ne gobe ba. Yau 2014 maganarsa ta zama nashin ƙasa babu kure. Don haka nake son in jinjini wasiyar bisa ga barazanar zamani da mutuwa ga sha’anin bunƙasa da ci gaban harshen Hausa a duniyar karatun boko.
Zamani
Zamani ga irin hangena kalmar Larabci ce daga “Zaman” aka Hausantar da ɗurin wasalin “i” ga nun guda ta ƙarshen gaɓarta. A Hausa ita ce “lokaci” ita ce “bana” ita ce “yau”. Za a ji Bahaushe na ambatonsu a taskar adabinsa da faɗar:
·         Zamani riga ce
·         Allah ne zamani ruwa ne kifi
·         Zamani abokin tafiya
·         Zamani ba ka jira
·         Kowa ya ƙi zamani ya ƙi Allah
·         Lokacin abu a yi shi
·         Kowa ya samu dama ya shanya garinsa
·         Komai na jiran lokacinsa
·         Lokaci ba wasa
·         Yau da gobe ba ta bar komai ba
·         Yau ake yi gobe sai labari
·         Karen bana maganin zomon bana
·         Yau da gobe ƙaryata boka
·         Jiya ba yau ba.
Abubuwan da Hambali ke yi muna kuka da su, zamani ne mai suna lokaci, yau, bana, da dai sauransu. Idan muka sa idon natsuwa muka dubi waɗanan zantukan magabata da idon nazari za mu tabbata cewa:
i)                   Kowane abu da lokacinsa idan aka yi kuren lokacinsa zaɓaɓɓe, to a sani ba a ɓari a kwashe daidai.
ii)                 Idan zamani abu ya zo gudunsa ƙauyanci ne, rashin karɓarsa wautar da kai ne, yaƙi da shi, rashin hankali ne, banga-banga da shi yana sa a bar mutum baya.
iii)               Lokacin da kake da damar yin abu shi ne lokacinka, idan ka bari ya salwanta sai ka zama ɗan kallo daga nan sai shiga kwandon tarihi.
Idan muka yi duba ga wasiyyar Hambali da tussanta cikin taskar adabinmu za mu ce, gare mu ɗaliban Hausa yanzu ya kamata mu ba ta irin gudunmuwarmu. Abin da za mu yi a yau, a gobe ɗalibanmu za su ƙarasa. A jibi ɗalibansu za su ci gaba, mu tamu ta ƙare sai juyayinmu kamar yadda muke yau muna juyayin malaminmu Farfesa Muhamamdu Hambali Jinju. Barazanar da zamani ke yi wa toroƙon da Hausa ke yi na kalle shi ta fuskoki kamar haka:
i)                   Murabus
ii)                 Sauya sheƙa
iii)               Mu sake nazari
iv)               Lokaci
v)                  Aron Hannu
vi)               Ana wata ga wata
vii)             Rangadi
Murabus
Daga cikin ƙa’idojin ayyukan hukuma na ƙasarmu akwai yin murabus ga aikin idan aka kai ga adadin shekaru talatin da biyar ana yi ko a ka kai ga shekaru sittin da ‘yan  kai ana yi da mutum. A tanadin murabus, ba a kula da lafiyar jiki da tsufa da gazawa da gudunmuwar ma’aikaci. Da ya kai ga adadi dole ya ba da kai bori ya hau. Karatun Hausa a duniyar boko ba ya da gata kamar malaman da ke koyar da shi. Malaman su ne Hausa, kuma su ne masu renon waɗanda za su yi mata hidima. Ana cikin tsakiyar fafitikar sama wa Hausa ‘yancinta na har abada daga duniyar ilmi lokacin yin murabus na jigajiganta ya yi halinsa. Wannan guguwar ta ci muna masana da yawa, da wuya a samu bandejin da zai rufe mikin kuf-kuf-kuf! Dubi irin wannan hasara:
Farfesa Ɗandatti Abdulƙadir, PhD, 1975 Indiana, Adabin Baka
Farfesa Dalhatu Muhammad, PhD, 1977 SOAS, Rubutaccen Adabi
Farfesa Dauda Bagari, PhD, 1976 UCLA, Nahawu
Farfesa Ibrahim Mukoshy, PhD, 1984 Khartoum, Sudan, Nahawu
Farfesa Bello Ahmad Salim, PhD, 1981 York, Nahawu
Farfesa Bello Sa’idu PhD, 2002 BUK, Rubutaccen Adabi
Farfesa Abdulhamid Abubakar, PhD, 1982 London, Nahawu
Farfesa Abdulƙadir Ɗangambo, PhD, 1980 SOAS Rubutaccen Adabi
Dr. Abba Rufa’i, PhD, 1977 Georgetown, Nahawu
Dr. Tanimu Musa Yar’adua PhD, Nahawu
Daga cikin waɗanda murabus ya ci muna mai limancinsu ya karɓi PhD a shekarar 1975 a yau kimanin shekara talatin da tara (39) ke nan ana fafatawa da su. Waɗannan tsofafin kanu, tsayuwarsu a gaban ɗalibi yini ɗaya ya fi kwana talatin a ɗakin karatu ana bincike. Idan aka dubi tsarin shekarun da suka karɓi digirin PhD za a ga:
i)                   A lokacin babu jami’ar da ake karatun Hausa tantagaryarta a babban digiri. Sha’awarsu ce da kishin da suke yi wa Hausa suka ɗauke ta suka tallata ta, ta samu karɓuwa cikin gida da waje. Me za ka ce wa na yau masu ci da ita suna kushe ta?
ii)                 Har yanzu da sauran ƙarfinsu da su ake yi, in an yi ba da su ba ta tashi. Laifin me muka yi wa murabus da zai yi muna zamba cikin aminci? Da dai ta mu ne ɗalibai, ya kamata a ɗage murabus ga masana harsunan Afirka masu tasowa in ba son ake a yi haihuwan guzuma ba, ɗa kwance uwa ƙwance.
A fannin adabi akwai giɓi huɗu. A fannin Nahawu akwai shida. Nazarin waƙar baka Ɗandatti ya sari dajin. A fagen rubutattun waƙoƙin Hausa, Dalhatu ya kafa tubali: A fannin Nahawu, Abba Rufa’i ya assasa nahawun gargajiya. Idan aka ɗebe Bagari da Mukoshy da wa manazarci nahawu zai yi kirari a Hausa? Abdulhamid shi ne tauraron gabas na Hausa a ilmin sarfu. Bello Sa’id ya buɗe fagen nazarin waƙoƙin masu jihadin ƙarni na sha tara. Matarka salo da jigon waƙa da bazar Ɗangambo suke rawa. Ɗan autansu Tanimu ana cikin shan nononsa a nahawu aka cire bakin yara tun ba su iya yaye ba. Mu sake tunanin, yaya za mu ci gaba da cin gajeyar waɗannan jigajigai mu manta da murabus ɗan koren maƙiya Hausa ne.
Sauya Sheƙa
Ni dai ban ga laifin idan hagu ta ƙiya koma dama ba. Duk da haka, dole ne mu yi juyayin waɗanda duniyar ilmin Hausa ta yarda da ƙwarewarsu, an ci amfaninsu, an ci moriyarsu, da su aka taka rawar farko ana cikin dara sai dare ya yi. Malaman Hausa masu digirin MA da PhD na Hausa da suka sauya sheƙa zuwa wasu ayyuka na ilmi na daban ba koyar da Hausa ba, suna cikin giɓin da Hausa ke kuka da shi a koyaushe. Daga cikinsu akwai:
Dr. Isma’ila Junaidu, PhD, 1987, Indiana
Dr. Garba Magashi, PhD, 1982, BUK
Dr. Ahmadu Bello Zariya, PhD, 1982, Michigan
Dr. Hajara Mairukubta, PhD, 2009, UDUS
Mal. Adamu Aliyu Kiyawa, MA.
Mal. Muhammad Sani Aliyu, MA. 1982, BUK
Mal. Miko Ɗayyabu Ɗiso, MA 1984 SOAS .
Mal. Wada Hamza, MA, 1985, ABU
Mal. Abdurra’uf Tukur, MA,  BUK
Mal. Abubakar Dogo Mafara MA, 1979, Ibadan.
Kaɗan ke nan da ake iya tunawa a gurguje, na tabbata da za a zurfafa bincike a nunka haka fiye. Waɗannan a jami’a suke koyarwa sun kai ga babban digiri tun lokacin da babban digirin Hausa sai wane da wane. Mafi yawansu a wajen Nijeriya suka yi karatu. Da yake ƙaddara ta riga fata suka bar mu ba tare da muna so ba, ba suna so ba, lokaci dai ya yi halinsa. Idan irin haka ta ci gaba da aukuwa za a yi wa Hausa kashin mummuƙe ta mutu da tsaye. Yaya za mu shawo kan wannan matsalar? Na sa ku gaba.
Lokaci:
Hausawa na cewa, tafiya da waiwaya maganin mantuwa. Haƙiƙa in ta bi daga-daga na ƙurya ya sha kashi. In dai Bahaushe ya yarda da kaɗan gulbi ka cika. To, ka da ya ƙaryata Dakka na Umme (Dakarkari) da ke cewa lasa-lasa ba ya barin kunu. Murabus lokaci yake da shi, kuma ga shi an ce lokaci ba ya jira. Magabatanmu malamanmu managarta masu ƙoƙarin ka da bakin wuta ya mutu ga hannunsu lokaci na yi musu barazana. A koyaushe muka kalli agogon murabus sai mu ga yana ƙoƙarin nuna mana lokacin na nan yana ƙaratowa. Abin ban haushi, mu da ke ɗalibansu ba mu gama shan nono ba, suna ƙoƙarin harhaɗa kaya na kusantar gidajensu domin su haɗu da murabus can a tattauna. Daga 2014 zuwa 2024 shekaru goma da ke tafe malamanmu za su yi muna ban kwana musamman irin su:
Farfesa Munir Mamman, PhD, 1992, ABU
Farfesa Mu’azu Sani Zariya. 1983, SOAS
Farfesa Audu Yahya Bichi PhD, Pennsylvania,
Farfesa Ɗanladi Yalwa PhD, 1995 UCLA
Farfesa Maikudi Ƙaraye PhD 1990, Wisconsin
Farfesa Haruan Abdullahi Birniwa PhD, 1987, UNISOK
Farfesa Ahmad Haliru Amfani PhD, 1996, Ibadan
Farfesa Abdulhamid Ɗantumbishi PhD, 2003, UDUS.
Farfesa Abdullahi Bayero Yahya PhD 1987, UNISOK
Farfesa Isa Mukhtar PhD, 1986, BUK
Dr. Ahmed Magaji, PhD, 2002, BUK
Dr. Sani Yusuf Birnin Tudu, PhD, 2002, UDUS
Dr. Hamza Ainu, PhD. 2008, UDUS
Dr. Aminu Galadima Batagarawa, PhD, 2013, ABU
Dr. Magaji Tsoho Yakawada, PhD, 2002, ABU
Dr. Sa’adiyya Omar Bello PhD.
Dr. Bello Alhassan Sodangi PhD 1997, Frankfurt
Dr. Sammani Sani PhD.
Mal. Adamu Malumfashi MA, 1995, ABU
Mal. Abubakar Garba Ɗantsoho Abdullahi MA.
Ko maƙaho ya laluba ya san idan Hausa ta rasa waɗannan managarta zuwa shekaru goma da ‘yan kai daji ya ci wuta. Ya zama wajibi tun yanzu mu fara tunanin ya ya za a ci gaba da cin moriyarsu? Yaya za a samu mafita idan lokaci ya ƙi yi musu uzuri? Irin gudunmuwarsu mu ɗalibai na yau ba ma iya ta, bale na gobe da ake ɗari-ɗari irin ƙarfin guiwarsu. Gaba kura baya sayaki shi ya ba mu tsoro muka ga dole mu fuskanci ɗalibai da manazarta da masana Hausa da wannan matsala. Don haka, kura gare ku masu awaki! Mu dai kanmu ya ɗaure, ku yaya kuka gani?
Mu Sake Nazari:
Waɗanda lokaci ya tilasta suka yi murabus shekarunsu daɗa ƙaruwa suke yi. Za a kai ga lokacin da ko ana son taimakonsu ga wasu matsalolinmu dole a saurara musu. Dole mu sake nazarin wace hanya za mu sake fitowa da ita ta ƙara kusantarmu da su, mu ƙara amfana da abin da suka amfanu da shi?
Ka da a manta, waɗanda suka sauya sheƙa ba su yi laifi ba amma mun cutu da giɓin da suka bari. Ga alamar irin guguwar wannan lokaci namu tsohon ɗan boko duk ya dangane alƙalamin koyarwa da wuya ya dawo masa. Waɗanda ke ciki ma rashin kulawar hukuma ga buƙatocin jami’a ya fara ba su tsoro. Idan tsuntsu ya fara ɗaga kai sama tashi yake son ya yi. Tabbas! Idan ya samu reshe amintacce a wata bishiya, ya yi ban kwana da wadda ya tashi a kanta. Don haka, sai dai mu sake shirin yadda za mu yi mu ci moriyar abin da suka bari da wuraren da suke su sa muna hannu ba ga ido ba.
Idan zama ya yi tsawo aka tashi aka kakkaɓe riga ba za a hana mai ita ya ƙara gyara lankafarta ba. Hausawa na cewa, gani ga wani ya ishi wani tsoron Allah. Malamanmu da lokaci ke harara ba su laifi ba idan suka tunkare shi tun bai gwamatso ba. Duk da haka, ƙorafinmu shi ne, da sabuwar gina gara yabi. Mai hankali da basira duk ya san da gina sabuwar rijiya gara yaso. In so samu ne, mu fara tunanin yadda za mu yi yaso ka da mu bari ruwa su ƙofe, yashi ya cike ramin, mu shiga ɗawainiyar wani abu wai shi gina-yaso.
Aron Hannu
Wata musibar da ta fi ta murabus da sauya sheƙa da lokaci haɗari ga harsunanmu ita ce, ta “Aron Hannu”. Wai saboda faɗar zamani riga ce, ya sa wasu daga cikin ɗaliban nazarin harsunan Afirka ke son a riƙa koyar da harsunan da harsunan da suka reni ƙasashensu. Wannan wautar ta sa a koyar da Bayarbe Yarbanci da Turanci, Igbo da Turanci, zarma, Lelna, Fulfulde, Kanuri duk cikin Turanci. Wannan mazarin a duk wuraren da aka kaɗa shi ya kasa rawar da ake so dole aka daina. To, sai ga shi da rana tsaka, ɗaliban da suka karɓi digirinsu na BA cikin Hausa, da digirin suka samu kowane digiri suke da shi a duniya. Da shi suka sami hawa kowace irin kujera ta ɗaukaka. Da shi su ke ciyar da iyalansu da iyayensu da abokan arziki. Su ke ganin, wai, a riƙa koyar da Hausa cikin Turanci, gaba ta koma baya.
Wannan barazanar lokaci ya kawo ta. Na farko akwai rashin kishi. Na biyu akwai son a sani, a san na iya. Na uku akwai tiƙeƙen jahilci na son a burge, a ce an iya Turanci, ka ce Turancin wahayinsa aka yi. Wasu sun ce, akwai hasadar ka da wasu su samu digirin PhD kamar yadda aka samu. Gizagizan jahilci na mulkin mallaka su ke sa kan wasu ‘yan boko rawa da ƙarya, wai su karatun Hausa ba wata basira ba ce. Ka gaya wa sakarai, Baturen da ya koyar da shi Hausa, ɗaƙiƙi ne a Turanci? A wane bagire na ilmin duniya aka ce wani harshe ya fi wani? Abin takaici, waɗannan sakarkaru masu ɗaukaka Turanci kan Hausa, Hausa ta haife su, ta yi musu sutura, kuma bayan cikin Hausa babu wurin da za su je su sami na cefene. Wa zai nuni gidansu da hannun hagu a yi masa masauki a gidan wani? Musibar aron hannu ta fi yaƙin basasa muni ga ilmin harshen Hausa.
Ana Wata ga Wata
A can da, masana Hausa na asali da suka assasa karatunta, a digirinsu na farko Turanci ko Larabci suka karanta. Wasu daga cikinsu da suka je Turai sun karanto Linguistics, Folklore, Anthropology, Sociology ko Philosophy. Don tsananin son su ga Hausa suka dawo gida suka ci gaba da yi wa Hausa aiki. Yalwatar fannonin karatu a jami’o’i a yanzu ya sa lokaci ya fara yi wa Hausa barazana. Fitattun jami’o’in da ake Hausa tsintsa an fara buɗe sassan Liguistics, Philosophy Hausa ta fara masassara. A ABU Zariya, an buɗa Philosophy, shugaban Hausa na da aka ba shugabancinsa. A UDUS, an buɗa Linguistics, babban gwarzon Hausa Dr. Dahiru Argungu ya mayar da ruwa rijiya. A BUK, an buɗa Linguistics fitattun jagororin nahawun Hausa sun koma gida irin su Farfesa Bello Salim, Farfesa Bagari, Farfesa Mukhtari, Dr. Aliyu, Dr. Hafizu, Dr. Chamo da Dr. Azare. A Maiduguri, Hausa ta kasa zama sosai duk da namijin ƙoƙarin Farfesa Abdulhamid da Farfesa Ahmad Baba Tela da Farfesa Munkaila da Farfesa Zulyadaini, da Hausa da Linguistics kusan a yi canjaras! Yaya za ka ce, mutum na kukan bai ƙoshi ba an haɗa shi ci da kare? Wannan ma wata barazana ce da ke son mu yi nazarin sosai.
Rangadi
Masu yawon rangadi sun kawo wa garuruwan da suka ziyarta abubuwan ci gaba da waya. A wasu wurare ga ‘yan rangadi za a fara ganin wasu abubuwa a ara a samu alfanu sosai a ci. Idan ɗan rangadi ya tsaga ya ga jini zai agaza wa ‘yan gida sosai. Buƙatar ‘yan gida ga ɗan rangadi ita ce, idan ya ga jini ya tsaya a ci a suɗe da shi. Wasu ‘yan rangadin sukan yi haka wasu kuwa ba sa yi. ‘Yan bokon farko na Arewa a fannonin fasaha sun yi wa Hausa biki a kundayen digirinsu na PhD irin su:
Yusuf Bala Usmanu PhD, 1974, ABU
Mahdi Adamu Ngaski PhD 1973, Birmingham,
Alhaji Garba Nadama Gusau PhD 1975, ABU.
Bello Alƙali Argungu MA 1969, ABU
Abdullahi Rafi Augi PhD 1984, Georgetown
Ahmad Baƙo PhD, 1990, BUK
Abubakar, Sokoto PhD, 1982, ABU
Murray Last, PhD 1967, Ibadan
Tabenderana, PhD 1974, ABU
Philips J. Shea, PhD 1975, Wisconsin-Madison
Kofoworola, PhD 1982, ABU
Bashir Ikara, PhD, 1975, London
Mansur Abdulƙadir PhD, 1998, London
Bello Daudun Bada PhD 1995, UDUS
Aminu Mode PhD, 2005 UDUS
Asabe Kabir PhD, 2003 UDUS
Malami Buba PhD, SOAS
Baba Waziri PhD, 1996, Ilorin
Philp Wall PhD, London
Abdallah Isma’ila PhD, Wisconsin
Puwdden PhD, 1977, Wisconsin
Berbaly Mark, PhD, Wisconsin
Sa’idu Baɓura, PhD 1986, London.
Omar PhD, 1998, London
Aleiro PhD, 2000, UDUS
Abdurrahman Adoro PhD, 2010, Sudan
Aliyu Muhammad PhD, 1977, London
Edward, B.F. PhD, 1971, Colombia
King, A.V. PhD, 1967, London
Barazanar da lokaci ya haddasa gare mu ga abokan aiki da suka kawo muna rangadi suka yi abin azo a gani ita ce, mun kasa kafa ingatar da cibiyoyin Nazarin Hausa da wadatattun kayan aiki. Mun kasa raya cibiyoyin. Mun daina kiran masu rangadi kusa da mu, mu ci moriyar su. Ba mu kirari da su ƙwarai kamar yadda muke kirari da malamanmu ‘yan gida. Ba abin mamaki ba ne, su fara yin tunanin mai da himma ga ɓangaren da suka fito, su sa muna ido da kayanmu. Mu tuna wannan hajar ba mu kaɗai muka yi tallarta ta samu karɓuwa ba. Idan muka ce, sussuka ɗaka shiƙa ɗaka, kowa ya tsira da karatun bakinsa, to, mu sani hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka. Yaya za mu mai do da martabar rangadi ga sassan ilmi daban-daban zuwa namu? Wannan ita ce, barazanar da lokaci ya haifar kuma dole mu yi amfani da lokaci mu tunkare ta.
Haba Mutuwa!
Babu shakka kowace rayuwa sai ta ɗanɗani mutuwa. Ba fannin karatun Hausa kawai ba, kowane fannin karatu a yau mutuwa na yi wa bunƙasarsa barazana. Wanda ya mutu gudunmuwarsa ta yanke daga ranar da ya mutu. Idan muka yi li’irabin irin aibin da mutuwa ta yi wa harshen Hausa na jigajigan masananta, dole a yi tagumi a kasa ta cewa:
Farfesa Muhammadu Hambali Jinju PhD, 1967, Mascow
Farfesa M.K.M. Galadanci, PhD 1969, SOAS
Farfesa M. Hisket, PhD 1969, SOAS
Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya PhD, 1979, ABU
Malam Isa Kurawa, BA, 1950, London
Malam Habib Alhassan Gusau, BA, BUK
Malam Mahbub Aminu Alƙali MA, 1989, BUK
Dr. Aliyu Abubakar Ambursa PhD, 1987, London
Dr. Abdullahi Garba Wurma PhD, 2000, ABU
Malam Umar Abubakar Zagga MA, London
Malam Ahmad Bala Jadaɗi BA, UNISOK
Malam Jafar Sulaiman MA.
Malama Aisha Ahmad Gandi, MA, 1981 SOAS
Malam Abdullahi Umar Kafin Hausa, MA,1985, ABU
Malam Abubakar Adamu Kafin Hausa MA, 1983, ABU
Malam Rabi’u Ahmad Zaruƙ
Malam Attahiru Umar Sanka BA, 1983
Malam Muhammad Abu Katsina BA, 1985, UNISOK
Malam Muhammad Sani Ibrahim MA, 1982, BUK
Malam Muhammad Balarabe Umar MA, 1984, ABU
Malama Rabi MA, ABU.
Malam Abdurra’uf, MA, 1995, ABU.

Madugu Muhammadu Hambali Jinju:
A tarihin karance-karance da rubuce-rubucen ilmukan harsunan Afirka Hambali ya cancanci a kira shi madugu. Hambali Bahaushen asali ne gaba da baya, manazarci makaranci masani Hausa. Wayayye ne a fagen Larabci. Ba a yi masa lungu a lugar Turanci. Ya shahara a fagen Zabarmanci Kakaki ne a harshen Azbinanci. A ko’ina malami ne a lugar Farasanci. Ya yi zurfi a nahawun Rashanci. Gaba da baya, a aikace da a rubuce Hambali malamin ilmin Harsuna ne. Daga cikin abubuwan da suka ɗagar da tutar Farfesa Muhammadu Hambali sama fiye da ta sauran malamai da masana Hausa su ne:
i)          Farfesa Muhammadu Hambali Jinju shi ne Madugun karatun Nahawun Hausa a duniyar baƙar fata, domin shi ya fara karɓar digirin PhD a Mascow, a 1967. Duk wani masani Hausa a duniya ƙasa ga wannan shekara ya karɓi PhD nasa.
ii)         Farfesa Hambali shi ne baƙar fata na farko a duniya da ya ratsi hazo zuwa Turai karatun digirin PhD a wajajen shekarar 1960.
iii)        Hambali shi ne masanin Hausa na farko da ya raɗa wa CSNL, BUK suna da “Cibiya” can da sai dai a ce “Santa” ko “Tsangaya”. Shi ya nace da kiran ta “Cibiya” har sunan ya bi ta.
iv)        Shi ya assasa binciken magungunan gargajiya na Bahaushe a duniyar baƙar fata, yana a Jami’ar Lagos (legas/Ikko).
v)         Farfesa Hambali ne madugun ƙirƙiro fassara kammalallen tarihin Afirka zuwa Hausa. Da su aka yi fafitikar kafa ofishin fasara JAKADIYAR UNESCO cikin harsunan Afirka da Hausa aka fara yin karan gwajin dahi.
vi)        Farfesa Hambali Jinju ya raya karatun Hausa a Jami’ar Ikko. Ya ɗaukaka ta a Jami’ar Ahmadu Bello. Ya inganta ta a Jami’ar Bayero, Kano. Ya bunƙasa ta a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato. Ya assasa ta Jami’ar Mascow. Da su aka share mata wurin zama a Jami’ar Cairo, Masar. Su suka yi mata tsayin daka a Nijar a IRSH da CEHLTO. Da bazarsa ake rawar taliyon asalin Hausawa. A kan buzunsa ake ɗaure wa karatun Hausa cikin Hausa gindi.

Masu Jiran Gado:
Idan aka dubi ta’adin da murabus ya yi. Aka waiga aka hangi zagon ƙasa sauya sheƙa. A sake sa wa ta’addancin aron hannu ido sosai. Matuƙar ba a ja wa rangadi linzami sosai ba, sabon salon yaƙin ana wata, ga wata bai yi niyyar barin kwamandojinmu ba. A kan wannan hasashen, masu jiran gado an raba musu hankali biyu an ce wa raggo ya sha fur aya je gona. In dai an sha fura ba noman kirki za a yi, in ko an je ciki wayam! Inuwa mai gulɓi za a yi wa biki. Idan muka shimfiɗa matasan masananmu irin su:
Farfesa Muhammad Munka’ila
Farfesa Ahmed Baba Tele
Farfesa Atiku Ahmad Dunfawa
Farfesa Salisu Ahmad Yakasai
Farfesa Ibrahim Aliyu Malumfashi
Farfesa Muhammad Lawal Aminu
Farfesa Balarabe Zulyadaini
Dr. Aminu Lawal Auta
Dr. Bello Bala Usman
Dr. Bashir Yusuf.
Matsalar bokon zamani da an ɗaura rawanin zama shaihin malamin sai ka ga an jingine rubuce-rubuce da wallafe-wallafe an shiga siyasar neman kujerin mulki. Idan masu jiran gado ba ce yanƙuri suka bi sahun magabata ba, rawunnan da ake naɗawa za su koma wasan yara. Wane abu aka yi sabo? Wane gyara ake yi wa tsohuwar tafiya? Wane ƙwazo ake ciki na ganin Hausa ba a bar ta a baya ba? A halin yanzu, Hausa na ƙamfar koyan aiki. Wallafa littatafai ingatattu na bincike salihi shi muke so. Sukan magabata da ɓata aikinsu, ba mu fito da namu ba, kuwwa baya ga yaƙin ne mai muzanta ko da masu sauraren ka.

Ina Mafita?
Matsalar karatun aku ga boko shi ke sa a koyaushe tattaro matsaloli ake yi a kasa dabarun da za a tunkare su. Irin barazanar da lokaci da zamani da aron hannu da sabuwar rawa ke takawa a cikin karatun Hausa ya kyautu a ce mun ɗan fara jarraba wannan:
i)                   Daukan matakan gaggawa na wallafa kundayen digirin PhD da aka yi na Hausa a ko’ina suke domin ɗakunan karatunmu su daina ƙamfarsu.
ii)                 Tattara ayyukan magabata masana Hausa da suka yi wa Hausa hidima a fagen ilmi da suka riga mu gidan gaskiya a wallafa su a taskace su.
iii)               Tilasta kowane sashen Hausa mai cin gashin kansa a jami’a da ya kira taron ƙasa da ƙasa na ƙara wa juna sani a ƙalla sau ɗaya a shekara.
iv)               Kira ga manyan makarantun COE da FCOE da su kira taron ƙasa a ƙalla sau ɗaya bayan kowace shekara biyu.
v)                  Fito da gudunmuwar wallafa PhD mafi rubutuwa da tantagaryar Hausa da kyauta mai tsoka ga ɗalibin.
vi)               Fito da tsarin inganta kyautukan da ake bai wa ɗaliban NCE, BA, MA da PhD na Hausa. A samu wata hukumar da za ta kula da shi da inganta shi.
vii)             Kyautata zumuntar masana da manazarta da mawallafa da ƙungiyoyin Hausa na duniyar Bahaushe.
viii)           Tabbatar da karatun Hausa da Hausa da rubutun kundayen kowane matakin karatu daga NCE-PhD cikin Hausa.
Naɗewa
Mutuwa ta yi muna girshi ba ta yi muna sauri ba, domin ba ita ta kawo kanta ba aiko ta aka yi. Haƙiƙa, tauraronmu bai yi zuwan sunge duniya ba, domin sai da ga sauke kayan da ya ɗauko, ya ce muna ga garinku. Mun tabbata mutuwa nama da ƙassa da jini ta ci, amma ruhin masani na nan cikin rubuce-rubucen da ya bari da zukatan ɗalibansa. Hausa ta yi rashin uban da ya yanka mata ragon suna. Ta yi hasarar mai son ta mai ƙiyayya da mai ƙiyayya da ita. Giɓin da Hambali ya bari, ko ba a gwada ba linzami ya fi bakin kaza. Gurbin da ya yi, ko ba a faɗa ba, sawun giwa ya take na raƙumi. Ba ka makara ba, lokaci bisa hanya ya tarar da kai. Da kuka yi canjaras da shi ba gaggawa ka yi ba, lokaci ne aka buƙace ka. Mu da ka bari, ba mu makara ba, lokacin ne muke jira. Da mu, da kai, da na jiya da na gobe, Allah Ya ƙaddare mu da samun rahamarSa. Amin! Duk! Abubuwan da suka wakana zamanmu na duniya mun yafe, Allah Ya yafe muna.  Amin! 
Manazarta
Abdullahi, M.D. 2011. A Study of Writing and Development of TAFI,
Fatima Publishing, Katsina.

Adamu, M. 1975. Hausa Factor in West African History, Zaria: ABU, Press.

Amfani, A.H. (da wasu) 2012, Champion of Hausa Cikin Hausa A
Festschrift in Honour of Dalhatu Muhammad, ABU Press, Zaria.

Bagari, D.M. Bayanin Hausa, Rabbat, Morocco.

Bangbose, A. 1977. Language and Nation: The Language Question in Sub-
Saharan Africa, Edingburgh, University Press.

Birnin-Tudu, S.Y. 1990, “Nazari Kan Rubutun Ajami a {asar Hausa,”
Kundin digirin MA, Jami’ar Usmanu [anfodiyo, Sokoto.

Bivar, A.D.H. 1960. “A dated Qur’an from Borno” Nigerian Magazine, No.
65, Lagos: Federal Ministry of Social Development, Youth, Sprots and Culture, Lagos.

Bunza, A.M. 2000, Rubutun Hausa, Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa,
Don Masu Koyo Da koyarwa, Ibrash, Lagos.

Bunza, A.M. 2008, Naramba]a, Ibrash, Lagos.

Bunza, A.M. 2013. “Don Me Ake Karatun Hausa?” Cikin Harsunan
Nijeriya, Volume XXIII, 2011-2013 CSNL, BUK, Kano.

Clarke, P.B. 1982, West Africa and Islam, London.

Dressler, W. 1981, “Language Shift and Langauge Death, a Protean
Challenge for the Linguist”. Folia Linguistica.

Dorian, N.C. 1981a, Language Death: The Life Circle of a Scottish Gaelic
Dialect, Philadelphia.

East, R.M. 1952. A Vernacular Bibliography for the Languages of Northern
Nigeria. Zaria: NNPC.


Fagge, U.U. Ire-Iren Karin Harshen Hausa Na Rukuni, Benchmark
Publishers Limited, Kano.

Fischer, S.R. 2000. A History of Writing, Reaktion Books.

Galadanci, M.K.M. 1976, An Introduction to Hausa Grammar, Longman
Nigeria.

Gazali, K.A.Y. 2005, The Kanuri in Diaspora, The Contributions of Kanen-
Borno ULAMA to Islamic Education in Nupe and Yorubalands, CSS Press, Lagos.

Jinju, M.H. 1981, Rayayyen Nahawun Hausa, NNPC Zaria.

Miller, W. 1971. “The Death of Language or Serendipity Among the
Shoshani.” Anthropological Linguistics 13:114-120.

Omar, S. 2013, Modibbo Kilo, ABU Press, Zaria.

Oyetade, S. 2007. “Language Endangerment in Nigeria.” Perspectives on
Akolo Languages of the South-West” Dorian, N. (ed) International Journal of Society and Language, 184, pp. 169-184.

Rufa’i, A. 1977 “Grammatial Agreement in Hausa”. PhD Thesis
Georgetown University, USA.

Rodney, W. How Europe Underdevelop Africa.

Sakkwato, A.B. 2011 Ginin Jimlar Hausa, Jagora ga Mai Nazarin Harshe,
Mathi Production Sakkwato.

Sani, M.A.Z. 2011, Gamayyar Tasrifi da Tsarin Sautin Hausa, ABU, Press
Zaria.

Spender, D. 1980. Man Made Language, London Rutledge and Kegan Paul.

Tsafe, B.A da Sadi, S.A. 2010 Hanyar Binciken Ilmi a Hausa, Farin Batu
Press Gusau.

Ubah, C.U. 2001, Islam in Africa-History, Baraka Press, Zaria.

Yakasai, S.A. 2012. Jagoran Ilmin Walwalar Harshe, Garkuwa Media,
Services Sokoto.
Yar-Aduwa, T.M. 2008, The Syntactic adn Semantic Description of the
Hausa Quantifiers, Clean Impression Ltd, Kano.

Zariya, A.B. 1981, Nahawun Hausa, NNPC, Thomas Nelson, Nigeria
Limited.

Zaru}, R.M. Aikatau a Nahawun Hausa.



Post a Comment

1 Comments

Post your comment or ask a question.