Ga alama abubuwan da magabata suka hanga bisa ga
nassohin bayyanar ƙarshen
zamani sun yi kere a zamaninmu. Manya da ƙananan alamomin tashin duniya sun yi wa
zamaninmu dumudumu. Maƙasudin
wannan waƙa jawo
hankalin masu hankali a kan sake bitar waÉ—annan
abubuwa da idon basira. Ganin irin nisan da muka yi ya sa na kira mu da muryar:
Anya Dai! Mu Taka Sannu. Na rubuta ta ranar alata, 28-01-2014, 11:38pm, a
Katsina.
Anya Dai! Mu Taka Sannu
Daga
1.
Na kiri wahidun
Ƙawuyun mai yau da gobe,
Mai baiwa dare da rana kuma ba shi zobe,
Mai rani da damina mai manyan gulabe,
Mai bunƙasa talikai bisa manyan gurabe,
Ba don sun buwaya sun
isa ne ba.
2.
Kurin taliki a
ce, yau shi ke iyawa,
Kamin an jima ka iske ya so gazawa,
Gobe a iske ya yi rauni daÉ—a sai macewa,
Babu abin da yar rage gu nai sai rufewa,
Allah Ka buwaya ba da
musu ba.
3.
Hauka ce ta
gaske kullum fifita kanmu,
Ko doro
da taƙamar asalin zuriyarmu,
Ko kuri
da hura hanci don É—an saninmu,
Wai yau
mu ka taƙama don kuɗɗin kashinmu,
Da gadara ga wanda bai samu ba.
4.
Son rai ya rufe
ido mun faÉ—a ga cuta,
Ba
tausai ga zuciya kullum sia mugunta,
Mun ɗebe sani da sabo har gun maƙwabta,
Ma su faÉ—a a ji su, su ne manyan macuta,
Fasiƙƙan da ba su ƙyamar zamba.
5.
Manya sun zamo
macuta me zai kasance,
Yara
suna gani karatu suka yi duƙunce,
Sannu a
hankali ƙasa daɗa ta zan makabce,
Ba
jagora dole za a yi mugun maraice,
Kowa ke cikinta bai tsere ba.
6.
Yau mai gaskiya
cikinmu abin zolaye ne,
Mai son
gaskiya cikinmu shi koma tsugunne,
In ya ba
da bai, mu bi shi da zagi da nune,
In ya
doshi dandali sai ka ga an yi done,
Cin zarafinsa ba da an fasa ba.
7.
Mai ƙarya a ba shi
tabarma tamatela,
An ƙunso ciki a
riga an karye hula,
Kowane
dandali da tabarna ga hilalla,
Ƙatti sun yi leme sun zama bayin sulalla,
Sun bautar da kansu ba da shiri
ba.
8.
Duk maganar da
mun ka yo, bar ta a nan a baki,
In ka ce
ka bincika, sai mun saka tsaki,
Daɗin baki ne da hila wane maroƙi,
Tsara
batutuwan ƙire, ƙulli ko masaƙi,
Babu shirin da ba da mu aka yi ba.
9.
In ka ji
rantsuwa ka É—auka duk gaskiya ce,
Sai an
kai ka an baro ka ga duk damfara ce,
Duk
tsarin da an ka yo ka ga duk tambaÉ—a ce,
Mai kuri
da hankali ka ishe ya makafce,
Bai sai inda kansa ke ciwo ba.
10.
Masu faɗin a ƙyautata su ke ɓarka cuta,
Mai
wa’azi ka iske ya gina ramin mugunta,
Wanda ka
taimaka shi yo maka tarkon asuta,
In ka zo
gida musibar cutar maƙwabta,
An shiga ukku ba da an shirya ba.
11.
Kukan kurciya
ba zai hana gero tumu ba,
Hurjin
dorina ba zai hana jirgi fito ba,
Kushe
mutum ba zai hana shi hawa martaba ba,
ZunÉ—e hasada ba za su tare É—aukaka ba,
Kun fayakunu na ga sarki babba.
12.
Mai rai in yana
tuni da zuwa duniyarsa,
Dole ya
girka tagumi ga tunin lahirarsa,
Kwana a
tashi gobe ba mai jin É—uriyarsa,
Sannu a
hankali ka iske a bar ambatarsa,
Ko kabarinsa ma ba za a tuna ba.
13.
Mun za ka
zamanin da yaz zo ga gaɓa ta ƙarshe,
Alfasha
da munkari duka yau ga su tarshe,
Masu
sani da jahilai duka an zan bisashe,
Samun
adili amini sai dai hasashe,
Ƙwarori cikinmu ba da yawa
ba.
14.
Yau algussu ta
zamo almiskin turare,
Duk wani
zaƙuno haramun aka yin kwarare,
Manya,
yara, ‘yan samari, hatta budare,
In aka
taru dandali ko a bukin amare,
Ba zancen a gyara gobe ake ba.
15.
Yara su kangare
su bar É—a’a gun iyaye,
Ba aiki
dare da rana sai shaye-shaye,
Babu
yinin da ba su sa tsofaffi hawaye,
Har an
alluhe hawayen duk sun tsiyaye,
Dole hawna jini musiba babba.
16.
Rowa ta yi
kwance kwancin kwana zukata,
Mai abu
ya fi son maras abu sai dai shi ƙwata,
Marashi
ya ƙi dangana sai ya laɓe ya sata,
An haÉ—u babu godiya da wadatar zukanta,
Ba marashi ba, ba ga mai samu ba.
17.
Maganar É—an’uwantaka yau ta zamto zance,
Yau
‘ya’yan ciki guda babu shiri da zance,
A wajen
‘yan uba faÉ—a had da ciro itace,
Shi
dangin uwa, uba, yanzu a kai shi kwance,
Kaka na gani ba zai magana ba.
18.
Tobashi ya zan
abokin yaƙi da gaba,
Ɗan wa ɗan ƙane ba za a yi auren zumu
ba,
Inna ka
wanke-wanke matan É—a bai kula ba,
A ci
irlinta É—a yana kallo bai muÉ—a ba,
Bone ya ci mu ba batun waƙa ba.
19.
Yau babba yana
gani yaro zai haye shi,
Girmama
hurhura da gemu wa ke kula shi,
Muddin
babu ta yi ma kanta ka yi gyashi,
Kuma
mulki na zamani an san, ba ka, ba shi,
Ban ga abin da za ka ce a jiya ba.
20.
Wanda ka wa ƙafa ya ruga shi
zai taÉ—e ka,
In kuma ɗalibinka ne ƙwazonai ƙure ka,
In
belinsa kay yi sai ya sa an tsare ka,
Ka yi
jinyarsa ka yi ciwo shi bai biya ka,
Bai ƙi a ce da safe ka shure ba.
21.
Suruki bai
ganin surukkai natsuwa ta samai,
Yanzu
talakka ba su ba sarki martabatai,
Girmama
mai gida ga yaro ƙannai da yannai,
Ga a
gaba-gaba da yaro zai kau da kainai,
A yi masa sallama ba zai karɓa ba.
22.
Yau rana kataa
ake yin sata da ƙwace,
‘Yan
boko ga dukiyar gwannati sace-sace,
Mata
babu godiya ga maza sun butulce,
Ga mai
hankali ga juji na tsince-tsince,
Ko ya kuwwata ba za a kula ba.
23.
In kun lura
shugabanci ya zan na wasa,
Domin
yara an ka ba dama sui ta gasa,
Yau
dattibe su ka fada gidajen matasa,
ÆŠan iska ya kwaso kaya tsoho shi amsa,
Shegen bai kula da na gode ba.
24.
Yau samunmu sai
ga matanmu É—iyan tsatsonmu,
Yannai
mu ka ƙwadagon dako shagon ƙanenmu,
Sai mun
haukace mu ƙwaci abin ɗan cikinmu,
DaÉ—a samunmu ya zamo kuka zuriyarmu,
Da takaici da rarrabe a yi gaba.
25.
Mai samun da
bai hana wa ubanai bara ba,
Bai hana
tsohuwarsa yawon ga-sussuka ba,
Bai É—ebe wa macce yunwar harjin ciki ba,
Bai hana
‘yan É—iyansa rokon suÉ—in miya ba,
Gara rashi da shi idan kun duba.
26.
Masu wa’azu
yanzu su ka takaicin mutane,
A
tsakaninsu ba shiri sai zagi da nune,
Mabiya
an haɗa su dambe da yin ƙone-ƙone,
Kuma su
za su ce wa gwannati duk ‘yan tasha ne,
Wa ka zubin adashi bai kwasa ba.
27.
Mai samu ba zai
yi laifi ba ga malumanmu,
Yai zina
yai ficen liwaÉ—i a gaban idonmu,
Ya yi
maye ya yo kisan kai mun kau da kanmu,
Ya yi
satan kuÉ—in hukuma kowa shi damu,
Ba ka taɓa ji a mumbarin huɗuba ba.
28.
Masu rabon faÉ—a a da, yau su ke haÉ—awa,
Masu faÉ—a a ji su da, yau wa ke kulawa,
Masu
kashin wuta a da, yau su ke hasawa,
Ƙarshen lokaci musibu ka yawan kitowa,
Ga mu cikinsu ba da mun tsere ba.
29.
Wa ka musun zamanmu
‘yan tsafi ‘yan ta’adda,
Hausawa,
Iyamurai, Yarbawa, Kakanda,
A yi
tsafi da É—an mutum farfesu da ganda,
An
tsotse jinin mutum an girke a randa,
Wai don jarrabara ta tara
kwababba.
30.
Ba wasa ba yau ƙabilanci ya
kashe mu,
‘Yan
gargajiya da masu aƙida dukanmu,
Yau
harshenmu ya zamo tamkar annabinmu,
Mu yi yaƙi saboda shi
muka fifita kanmu,
Kalimar laa illah ba za a kula ba.
31.
Imaninmu yau a
kai samu yankunanmu,
Tun daga can a mulmula su zuwa ƙanyukanmu,
In aka kai a sa gidajenmu na mallakanmu,
To daga nan gidan a ja su zuwa É—akunannan,
Kowa yar rasa ba za mu kula
ba.
32.
Fasiƙƙai da fajirai
bisa manyan kujeru,
‘Yan
iska da ‘yan daba su ka kira a taru,
Marasa
gaskiya ka wa muminnai dabaru,
‘Ya’yan
goruba da ‘ya’yan É—inya da faru,
Duk ba su kai abarba zaƙin sha ba.
33.
Koma baya yau É—iya sun ka zamo mahaifa,
Su ka
kira a zaburo har a yi sansarefa,
Su yi
tsawa mu kasa miƙe ƙafafu a rumfa,
Haka ƙarshenmu zai
zamo riƙa sanda da malfa,
Ba mu haifa wa kanmu albarka ba.
34.
Kai da É—iyanka ba ka tsawa balle bugawa,
In ka ce
ka tsaurara doka za a sawa,
In suka ƙaurace, gida
bariki ke tarawa,
Tsufa na
kiranmu ‘ya’ya na fandarewa,
Ba tausanmu za su ji su kula ba.
35.
Mata an ka ba
su ‘yancin yawo tsirara,
Aure bai
da dole zancen zina babu tara,
Kulle an
ka sa gudun hijira tun a bara,
Matan
zamaninmu ba kunya ko ta kara,
Ba a taɓa yin kamar su fajirci ba.
36.
Makarantun biɗar sani ƙatanya da ƙatta,
Ofis
kallabi da beje a tsakan macuta,
Ƙarshen gwannatinmu shaggu ke mallakanta,
Dole ƙasa ta durƙusa komai ɗaukakarta,
Ba ta dace da masu jagora ba.
37.
Tsarin namu mun
ke ce Allah bai iya ba,
DokokinSa
mun ka ce ba su za a bi ba,
ÆŠan ilminmu bai ci sa’ar kare Æ™asar ba,
Muka faÉ—a cikin faÉ—an basasa da gaba,
Ba a san lokacin da za shi lafa
ba.
38.
Muddin dai abin
da kan noma za ka girba,
Dole a
mai da sungumi aiki bai yi kyau ba,
Shukar
ta suƙe ga tausa ba a bar fari ba,
Ba
sauran iri batun noma bai tsaya ba,
Zancen cin tumu ba a fara ba.
39.
Duk shukar da
ta’ tsiro bisa juji ku lura,
Ga
yabanyarta ba kama nata kyawon tagara,
Tun ba ta
ja kara ba hoge zai tad da ƙura,
Dole a
bar tururuwa su yi aiki da fara,
Kwaj jiri amfalolo bai huta ba.
40.
Duk wani mai
jiran ɗiyan yau ƙarshensa hauka,
Balle
mai shiga faÉ—ansu ku mai she shi zakka,
Mai kuri
da su ina tunsan dambalarka,
Mai
bautar da kanka don su ban tufanarka,
Mai nema ba zai zaton ya rasa ba.
41.
Yau an bar
gudunmuwar tayyo ba a jin ta,
Kyauta
sai ga ‘yan siyasa a wajen masarta,
Haka
gayya da gangamin ajo haÉ—in zumunta,
An bar É—egiya tukuici in an yi kyauta,
Wa ka bukin da bai ciwo riba ba?
42.
Haka muka iske
zamani ya raba kan mutane,
Ya
gigita masu hankulla sun yi zone,
Wa da
suka san abubuwa an ce dambala ne,
An tsiri
sabuwar fahimta an kai tsugunne,
Ba ta fis she mu É—emuwar hanya ba.
43.
Iya bakinka
kakkacin yin zance guba ne,
Kere tsara
cikin abin taro dambala ne,
Nuna
sani a dandalin jahillai kure na,
Cin
zarafi da kushe girman manyan mutane,
Ba a taɓa yi a ba da labari ba.
44.
Zagin kasuwa
mafarinsa ake kulawa,
Ƙandume duniya ga zance ya zan ɓacewa,
Wawa ke
bugun gaba da kirarin ƙwarewa,
Duk mai
hankali yana jin ƙyamar zaƙewa,
Ba a taɓa shisshigi a kai ga sago ba.
45.
Bari tsoron
kira Alu tuna laifin kiranka,
In ka
shaida babu laifi É“arje guminka,
Ban ci ƙashi ba ban
aman tsoka kama kanka,
Tsorona
a zamaninmu a fis she ni zakka,
In ban hau ga godaben sunna ba.
46.
Duk mai
hankalin karatu in zai kwatance,
Da
fitinnun da ke wakana safe maraice,
Ga yaƙi da
zanga-zanga kullum rigince,
Mun za
ka lokaci na ƙarshe nassi rubuce,
Komi yab É“ata ba a gane ba.
47.
Ka da mu bi
lokaci mu shafa da ainin nagarta,
In ya
tarar da mu muna bisa aikin ƙazanta,
Mu muka
gayyato Nakini ga aikin mugunta,
Kowace
rai ta ƙuna sai ta yi kuka da kanta,
Ba aikin waninta za a awo ba.
48.
Mu ka faÉ—an abin da ba mu nufin aikatawa,
Alƙawalin da mun
ka yo ko É—aya ba cikawa,
Zantukkanmu
barkatai babu wurin riƙawa,
Kwaz
zaune mu sau guda bai fatar daÉ—awa,
Ba Æ™oshi mukai da ha’inci ba.
49.
In muka ce a yo
gabas, to tarbe mu yamma,
Mu yi
cuta da assuba tanzanko da yamma,
Hannu
gaisuwa ƙafa sata babu ƙyama,
Bayan
mun yaba mu koma tono da galma,
Ka da Allah Ya kai ka ba furta ba.
50.
Mai ƙaunar ganinmu
bai san siffarmu ne ba,
Mai ƙaunar zama da
mu bai taɓa jin mu ne ba,
Mai kuri
da mu bayani ab bai jiya ba,
Mai gaba
saboda mu bai ahumo da kyau ba,
Matuƙar ya sani ba zai fara ba.
51.
Dakance ni É—an uwa kar ka ga na tsananta,
Hujjojin
da ke gare ni idan na fasalta,
Zai zama
arashi da gugar zanar maƙwabta,
Ai ta
zato a faÉ—a giba É“annan zukata,
Maƙasudin ya zanto bai nasara
ba.
52.
Ita sandar
bugun kaÉ—e ba tada take ba,
Sandar
wawa ba ta tsallake yaro da babba,
Bisa kan
mai uwa da wabi na yi in ka duba,
Jifa ce
ta faÉ—a kan tsokai ban hana ba,
Kaina cikinsu ban É—ebe ba.
53.
Kai ko mai zato
da tawili can ga kanka,
Kai kuma
mai fashin baki ban hana fassararka,
Masana
Hausa masu fiɗar waƙa matarka,
Fatata
ku ganyato ni mu yo ga-ni-ga-ka,
A yi sharhin da ba cikin son rai
ba.
54.
Imaninmu
munzali nasa ba mu kai ga ci ba,
Muddin
mun ka kai ga mulki ba zan faÉ—i ba,
Ba mu taɓa cin karo da banza muka kau da kai ba,
In muka
tsundume cikin daula ba mu iya ba,
Ba ƙaramin kira ka sa mu jiya
ba.
55.
Ƙarya ba ta gargaɗar cuta ko
gwadawa,
Damben
tsegumi da tsince wa ke rabawa?
A yi É“anna da mu ina bakin tsawatawa?
Taratsin
fashin baƙi kanmu yake tsayawa,
Ba kan fasiÆ™ai da ‘yan bidi’a ba.
56.
Ba mu mun ka
fara yin wa’azi duniya ba,
Malamanmu
ba hisabi aka sa su yi ba,
In muka
ce mu tsabbace kowa bai iya ba,
ShaiÉ—an zai shigo da tarkon hasada da gaba,
Har maƙiya su farga ban mu kula
ba.
57.
Ta da gaba da
alfahar ga fahintar karatu,
Ko kuri
saboda samo shahadar rubutu,
Yin É—anga saboda boko manyan sarautu,
Ai ta
cuwa-cuwa tsakanin manyan ƙazantu,
Ba ƙarshen ƙwarai ake samu ba.
58.
Cewa ban da mu
ina wani babban kure ne,
Hana
mabiyinmu bin waninmu alamun É“ata ne,
Cewa
fassrarmu dai aka bi karkata ne,
Tilasta
mu bin fahintar wani dambala ne,
Wane ciwo gare mu ba wannan ba?
59.
Kukan kurciya
jawabi ne Bakatara,
Sai mai
hankali da mai wayo za shi lura,
In ya ƙiya a lahira
shi ji gyaran maƙera,
A buge
awwazu da kwanya a kare haƙora,
Ba su taɓa tausayin bugun ƙato ba.
60.
In don wagga duniya
ce tafi kama kanka,
Babu
gwani gare ta yaro bari koÉ—a kanka,
Magabatan
da sun ka bi mata ta sa su hauka,
Baƙon duk da yat
taho sai ta ba shi jikka,
In ya zazzage ba zai more ba.
61.
Nai shukura ga
Rabbana tammat na cika ta,
Bisa
murya ta Ayya Maitashe na’ a za ta,
“Borin
Goje” kun ji waznin gindin awonta,
Ali na
Bunza É—alibi shi yai bibiyanta,
Ku yi gyara wurin da bai dace ba.
[…] Anya Dai! Mu Taka Sannu […]
ReplyDelete