Ticker

6/recent/ticker-posts

A Gyara Yau Don Gobe

Takardar da aka gabatar a bukin yaye ɗaliban karatun Islamiyya ta Aba Huraira da ke Yabo K’aramar Hukumar Yabo ƙarƙashin jagorancin mai girma Sarkin Kabin Yabo Alhaji Muhammadu Maiturare Yabo a harabar K’aramar Hukumar Yabo, Jahar Sakkwato, Asabar 25 ga Junairu 2014

Daga

Aliyu Muhammadu Bunza

Sashen Koyar da Harsunan, Nijeriya

Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina

Jahar Katsina, Nijeriya

Bismilaahir Rahmaanir Rahiimin

Wa sallal laahu alan nabiiyil karim.

Da sunan Allah mai rahama mai jinƙai. Tsira da aminci su dawwama ga fiyayen masoyin Allah shugaban bayin Allah Muhammad ɗan Abdullahi (SAW) da iyalan gidansa da sahabbansa da waɗanda suka yi koyi da su ya zuwa ranar sakamako.

Gabatarwa:


Da Allah na nufin bayinSa da rahamarSa da baiwarSa sai Ya turo musu manzaninSa da littattafanSa cike da saƙonSa domin raya zukatan waɗanda suka yi imani. Yin haka wata ishara ce ta kwaɗaitar da mu, da mu duƙafa ga koyo da neman sani mu da iyalanmu da ‘yan uwanmu domin idan ba ilmi hankalin tuwo kaɗai bai isa shiryar da mai shi zuwa ga tafarkin tsira ba. Fafitikar karance-karancen da almajirai da malamai da ƙungiyoyin addini daban-daban ke gudanarwa shi ya haskaka zukatan mutane suka yarda da wajabcin neman ilmi. Samun kai ga nasarar wannan faɗakarwar ita ce ta tara mu yau a garin Yabo, Allah Ya yi muna jagora.

Fa’idar Karatu:


Babbar fa’idar karatu ga ɗan Adam ita ce, ya gano ba shi ya yi kansa ba yin sa aka yi. Dalili kuwa komai toroƙan da yake yi da sunansa da ya ɗaukaka a fagen karatu kowace iri cikin tazara yake ga abubuwan da ilminsa bai kai can ba. Tabbas! Allah kaɗai ya gewaye komai da ilmi. Sanin mutun ya gane wani ɗan abu kawai ya sani wasu bai san su ba, wani karatu ne cikin faɗar mahaliccinmu cewa komai Ya sani. Duk kururuwan da ɗan Adam ke yi na ci gaban fasahar karatu da rubutu da sarrafa shi cikin nasara a fannonin rayuwa daban-daban, masani komai cewa ya yi bai ba mu komai daga cikin saninSa ba face ɗan kaɗan. K’a’idar ilmi ke haska wa ɗan Adam cewa dole akwai manufa ga wanda ya halicce shi a kan halittar da ya yi masa. Wannan tunanin zai yi canjaras da nassin ba mu halicci aljanu da mutane ba, don komai face don su yi wa mahaliccinsu bauta. Idan zuciyar karatu ta yi nasarar tabbatar da wannan ba za ta musanta saƙon mahaliccinta ba ta hannun kowa ya turo shi. Yadda ba ka san lokacin da aka yi ka ba, ba dole sai ka san wanda za a turo da saƙon yadda za a yi bautarsa ba. Cikin wannan haske muka gano a kowace irin al’umma Allah Ya turo manzanninSa da saƙonSa na a kaɗaita shi ga bauta a kafirce wa masu fito-na-fito da dokokinSa ɗagutai. Ba don hasken karatu ba, abu ne mai wuya wata dabba daga cikin dabbobin bangon ƙasa ta yi imani da abin da ba ta taɓa gani ba, ba ta taɓa jin labarin wanda ya yi ido-ido da abin ba, kuma a zamaninta ba ta taɓa ganin wanda ya ga abin ya ba ta labari ba. Wannan shi ne kirarin da Allah ke yi bayinSa muminai a farkon “Surar Raƙuma”.

Allah Akbar! Cikin wannan martabar ne aka zaɓa muna Musulunci ya zamo addininmu. Aka zaɓa muna Muhammad (SAW) manzaonmu. Aka saukar da Alƙur’ani ya zama muna jagora. Aka cusa hikima da basira da wadataccen hankalin a ƙirjin Manzonmu Muhammadu (SAW) domin ya yi muna fashin baƙin kuramen nassoshin zancen mahaliccinmu. Aka arzuta Muhammadu (SAW) da mabiyan da ba a taɓa samun irinsu ba gabaninsa, a bayansa har ya zuwa yau ba mu ji labari ba. Ilminsu ya sa suka yi adawa da duk wanda ya yi adawa da ilmin da Manzo (SAW) ya zo da shi komai kusancinsa gare su a jini ko soyayya ko siyasa. Bisa ga haka aka yabe su ga tsanantawa ga makafirta da rahama ga juna. Aka ɗebe tausai da jinƙai a zukatansu zuwa ga duk wanda ya yi adawa da Manzo (SAW) da saƙon da ya zo da shi yana a raye ko a mace! Waɗannan su ne ɗaliban ilmi na sunna na farko a haka suka rayu, a haka suka yi shahada.

Fa’idar Karantarwa:


Allah da Ya saukar da hasken karatu shi Ya ba da umurnin a yi tunatarwa domin koyar da bayinSa. Ba don koyarwa ba da ilmin addininmu ya tuƙe daga sahabbai. Mahaliccinmu Ya umurce mu da mu je gun masana mu koyi abin da Ya sanar da su. Wanda ya koyar da alheri zai samu sakamakon duk wanda ya aikata alherin. Don haka, ladar iyaye da suka tarbiyartar da ‘ya’ya da malaman da suka koyar da su Allah ɗai ke iya ƙididdige ta. Koyarwa kamar haihuwa take, idan ba haihuwa duniya ta gama ƙarewa tun gabanin wannan ƙarni. Haka yake idan ba a koyarwa da koyo da jahilci ya isa ya ƙare al’umma a yi zuwan sunge duniya. Alƙur’ani ne babban manhajar koyarwa domin Allah Ya ce, ba a ‘boye komai a cikinsu ba. Ta tabbata shi littafi ne wanda ya bayyana komai. Mai son ya san komai dole ya tunkare shi. Wanda bai san Alƙur’ani ba a wajen Allah ko da haƙora yake rubutu saboda ilmi jahili ne. Wanda duk aka koyar ba da Alƙur’ani ba an wahalar da shi. Wanda duk aka koyar da Alƙur’ani ya huta an huta da shi. Ilmin duk da bai yi canjaras da na littafin Allah ba, jahilci ne mai kai mai shi ga hauka tuburan.

A Gyara Yau Don Gobe:


Irin garaɓasar da ke tattare da ilmin da amfanonin da ke ƙunshe ciki ga wanda ya yi sa’ar samunsa, ya zama dole mu tashi tsaye ganin yaranmu sun same shi. Musibar da ke ci muna tuwo a ƙwarya ta fifita boko da addininmu ga yaranmu ita ta kai mu ga halin da ƙasarmu take ciki. Wautar da magabata da muka yi da girmamar da baƙin haure ‘yan ta’adda shi ne tushen ta’addanci da ke wakana a yau. Miƙa tarbiyar yaranmu ga hannun waɗanda suka ƙaurace wa tarbiyar da Allah Ya zaɓa musu su, shi ne musabbabin ɗurƙushewar tarbiyarmu da ta yaranmu. Tsinkayar haske cikin ɗakin da Allah Ya ce duhu ke ciki shi ne dalilin dunduminmu da yaranmu a yau. Kyautata hanyoyin da Allah ya ‘bata shi ya kai mu ga faɗa wa hanyoyin ‘bata a yau. Zaton da muke yi na ganin wayonmu ya isa ya tsirar da mu, shi ya sa aka sallaɗo muna abin da muka haifa da kanmu su zama fitina ga rayuwarmu.

Yadda za mu sha kan duk waɗannan musibu shi ne, mu gyara yau don gobe. Yadda za a gyara yau, shi ne a shagaltar da yara ga karatun addininmu da yi wa littafin Allah hidima da hardace shi da lugude shi a zukatansu ya yi langaɓu a harsunansu su samu abin yin munajati da Ubangijinmu domin Ya tausaya muna cikin tausayinSa. Da kwalayen digiri da manyan takardun shaidar boko ke gyara al’umma da Amerika da Ingila da Rasha da Jamus da ƙasashen Asiya ba su koka a kan tarbiyar yaransu ba. K’arni ɗaya da ya gabace mu a Nijeriya ta Arewa babu mai dogiri. Ku gaya mini ta’addanci nawa aka samu a lokacin?

A ƙarninmu hatta da karen ‘buki da biri da buzuzu an ba digirin digirgir amma zama lafiya ya buwaya safe duk gara jiya da yau. Yaran jiya su ne manyan yau. Na yau manyan gobe. Na gobe, su ne sabbenen jibi. Na jibi, a gata, su ne ranka ya daɗe. Na gata da citta, kama-kunnen na shekaran jiya ban da jiya ne, kun ko san duk gefen da sanuwar gaba ta sha ruwa nan ta baya za ta tsoma bakinta. Ku bar rena shekarun yaranku da wayonsu, idan ba ku ilmantar da su littafin Allah ba sai sun zama muku barkonon tsohuwa. Ku tambayi raƙumi da ya rena kunama ya take ta me ya ji? Shi da kansa ya ce: “Ana shaggu ƙasa”. Allah Ya tsare mu Ya tsaras muna. Amin!

Lokacin Abu A Yi Shi:


Hausawa sun ce, lokacin abu a yi shi. Duk ƙwazon koyar da yaranmu addini da tarbiya da gina ƙasa, ba zai ci nasara ba idan maƙiyansu sun rinjaye su. Halin da muke ciki a yau ƙasarmu na buƙatar addu’a ga kowa da kowa. A fagen zaman lafiya tura ta riga ta kai bango. Ko ba a faɗa ba mun kai ƙarshen tika-tika tik! Haƙiƙa mun shiga halin ɗaka zufa, waje sanyi, gado kazunzumi zani ga ƙyeya. Manyanmu sarakunanmu da malamanmu da shugabaninmu na siyasa da sana’a sun tabbata allonmu ya cike da rubutu, mun kai gaɓa ta ƙare karatu a fagen zaman lafiya an kai sin-waw-raa-taakuri. Yau ko muna son a ci gaba da karatun zama lafiya mun tabbata an kai, walan waladaina walaa malam na ƙiya. Me ya rage gare mu, mu ‘yan saura da ke raye gabanin a turo muna ‘yan uwanmu a laƙume mu, a tarwatsa wuraren ibadojinmu, a yi wa kaburan iyayenmu da kakaninmu fitsari, a shiga farautarmu ana kisa irin na CAR. Ga dukkanin alamu yaƙin BOKO HARAM yanzu aka sa hannu. A fashin baƙin kalmar BOKO HARAM duk wanda ya kaɗaita Allah ya yi imani da ManzonSa (SAW) ya miƙa wuya ga dokokinSa, a fassarar Nijeriya shi ne ɗan BOKO HARAM. Don haka, ruwa na ƙasa sai ga wanda bai tona ba. Gabanin a fito wa kusa Hausance, dole ne duk wanda ya yi imani da kalmar laa ilaaha illal laahu Muhammadur rasuulullaahi ya fara tunani yin hijira gabanin zaɓen 2015 domin ga dukkanin alamu manyan yau sun ce:

Cikin biyu sai a zaɓi guda a ɗauka

Walau tashi walau a bi Annasara.

In dai mu zaɓi tashi bayan ƙarni ɗaya mu dawo in da sauran zuriya. In ko mu zauna zaman bayi da baƙin haure a cikin ƙasarmu ta gado. In ba haka ba, mu tashi tsaye mu ga an ba kowa ‘yancinsa da haƙƙinsa da mutuncinsa na zama ɗan ƙasa. Ni a ganina zama lafiya ya fi zama ɗan sarki. Da a yi ƙunar baƙin wake, gara a yi twa-da-twa wankin ɗan kanoma mashaya a hura wuta kowa ya ga rabonsa. Yaya za a hura wuta? Ku biyo ni.

 

Naɗewa:


Idan ba a ɗatu da yaro to a ba shi daddawarsa. ‘Yan siyasarmu da ke da sauran hankali da suka ga an mayar da Arewa mayanka. Masalatanmu sun koma maƙabatar. Kasuwanninmu sun koma fagen arbatu. Gidajenmu sun koma kangaye. Ma’aikatunmu sun koma maɓuyar ƙadagaru da macizai. Yankinmu an yi kusan a kore shi daga ƙasarmu mu san inda dare ya yi muna sai suka fara tunanin sauya sheƙar siyasa abin kuwa ya fara tasiri. Irin wannan yaƙi shi ne yaƙin ilmi, yaƙin fahinta, yaƙin zamani, yaƙin kifi na ganin ka mai jar homa. Wanda duk ya ɗaura ɗamarar irin wannan yaƙi a yau ya cancanci mu naɗa shi kwamandan ƙwato wa masu haƙƙi haƙƙinsu. A kan wannan nike cewa, yau a Sakkwato ba mu da zaki da makaye da garnaƙaƙi da zagi da jagora irin mai girma Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Dr. Aliyu Magatakarda Wamakko Sarkin Yamma Sakkwato da ‘yan majalisarsa na gida da na tarayya. Fatarmu Allah ya ba ku nasara, ya ƙarfafa ku, ya jiɓinci al’amarinku. Mun gode. Dalilin wannan hasashe nawa shi ne falsafar malamin kiɗa Naranbaɗa da ya ce:


Jagora: Da mai hashin wuta

: Da mai kashin wuta

: Da mai rabon hwaɗa

: Da mai haɗin hwaɗa

: Su duk huɗu sun taru sun game

: Ba mu samu guda wanda yaf fi ba.

 

Yara: Narambaɗa komo ga gaskiya

: Mai kashin wuta ya fi mai hashi,

: Mai rabon hwaɗa ya fi mai haɗi,

: Ni kan ga irin wadda nag gani,

: Ka san jimina ta fi zarɓi

: Babban guru ko tai masassara.
 

Jagora: Ta tababta gwarzon uban gida

: Namijin jiya ka zarce ‘yan uwa.

Na gode, Allah Ya yi muna jagora ƙasarmu ta zauna lafiya. Amin!

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments