Ticker

6/recent/ticker-posts

Zumuntar Bahaushe A Zamanin GSM

A halin yanzu ma kusan rayuwa ba ta tafiya sai da ita, (musamman a biranenmu) in har kana son ka san abin da duniya ke ciki. A taƙaice, wannan fasahar zamani ta GSM ta buɗe wa Bahaushe sabon salon gudanar da dangantaka da ma’amala a sauƙaƙe, tare kuma da samun biyan buƙata gwargwado...

Muhammad Mustapha Umar
Department of Nigerian Languages Usmanu
Danfodiyo University, Sokoto
Email: mustaphahausa@yahoo.com
GSM: 08065466400

1.0 GABATARWA

Wayar salula hanyar sadarwa ce ta zamani wadda al’ummar Hausawa ke amfani da ita wajen biyan buƙatunsu na yau da kullun kama daga abin da ya shafi sada zumunci tsakanin ‘yan’uwa da abokan arziki, ta hanyar kira ko magana ko ta amfani da wani sashe na wayar mai ba mutum damar shirya rubutaccen saƙo ko bayani domin isarwa ga wani ko wasu cikin ƙanƙanin lokaci, ba tare da Ƃata kuɗi masu yawa ba. Salula ko wayar hannu ko hanset ko wayar tafi da gidanka ita ce wadda take yayinta a yanzu. Wannan maƙalar za ta yi ƙoƙarin ƙyallaro gudunmuwar GSM wajen zamanantar da kyakkyawar ma’amala ta zaman tare tsakanin al’ummar Hausawa, musamman ta fuskar yin amfani da sabon salon ganawa ta magana baka da baka da wani, wanda yake nesa, ko ta musayar rubutattun bayanai ko saƙonni waɗanda ake da damar ajiyewa ta yadda ba za su salwanta ko lalace ba. Wannan kimiyya da fasahar sadarwa ta GSM ta taimaka wajen ƙara danƙon zumunci a zamantakewar Hausawa, musamman a tsakanin zumai waɗanda suka rungume a matsayin hanya mafi sauƙin don sauke faralin da Allah ya ɗora musu na zumunta da ke rataye a kansu.

2.0 ZUMUNTAR BAHAUSHE A ZAMANIN GSM


Al’adar Bahaushe abu ce wadda ta ƙarfafa zumunta da neman sadar da ita a ko da yaushe. A kowacne hali ana son mutum ya zama mai ziyarar ’yan’uwansa, ya kasance mai taimako da kyautata musu gwargwadon hali. Hausawa na cewa “Zumunta a ƙafa take” wato zuwa wajen zumu don sada zumunci ko gaisuwa ko aika saƙo na musamman ko kuma halartar lalurar juna idan ta samu. A taƙaice, irin wannan dangantaka ita ce kusan ƙashin bayan kowace al’umma. Don a da mun saba amfani da hanyar gargajiya ta zuwa wajen dangi, don kai saƙo na musamman, da gane wa ido halin da ‘yan’uwa suke ciki ko kai goron gayyata ga musamman waɗanda ke zaune a wurare masu nisa.
Sabuwar hanyar sada zumuncin Bahaushe a yau ta samu ne sanadiyar cuɗanya da baƙin al’ummu, da bayyanar sauyin zamani da ci gaba waɗanda suka tilasta Bahaushe gudanar da kyakkyawar ‘yan’uwantaka ta amfani da sabbin hanyoyin sadarwa na zamani tsakaninsa da dangi ko abokai, don gaisuwa da bayan rabo da hulɗa irin ta zumunci. A yau Bahaushe na iya sada zumunci ta hanyar waya ko saƙo a rubuce komai nisan wuri, kuma cikin ƙanƙanin lokaci. Maimakon zuwa da kai wanda a wani lokaci bai zama dole ba. Wannan bunƙasa ta kimiyya da fasahar sadarwa ita ake yayi, kuma da ita muke sanar da halin da ake ciki, da yin sanarwa irin ta gayyata na wani al’amari wanda ake buƙatar halartar ‘yan’uwa. Daga cikin sabbin hanyoyin sadarwa da Bahaushe ya runguma a wannan zamanin namu akwai: rediyo, da talabijin, da jarida, da mujalla, da intanet sai wayar salula wadda ta shafi aikinmu wanda kai ƙoƙarin bayanin yanayin sadarwar Bahaushe ta amfani da kira da waya ko aika saƙon waya a rubuce.

3.0 WAYAR SALULA (CELLULAR PHONE)


Wayar salula na’ura ce da ake riƙewa a hannu domin yawatawa da ita, takan taimaki mutum yin magana da wani tamkar tarho inda kowa ke jin muryar juna rangaɗaɗau, kuma tana ba da damar aika rubutaccen saƙo kamar yadda ake buga shi a kwamfuita. Wayar salula ta ƙumshi muhimman abubuwa kamar: Batur, da agogo, da kwanan wata, da kalkuleta (calculator), da bulutut (Bluetooth), da memorikad (memory card), da rediyo, da bidiyo, da kyamara, da fitila, da layi mai ɗauke da lambar mutum ta waya da kuma damar adana lambobin mutane da ake hulɗa da su ko wasu bayanai. Sai dai ba kowace waya ke cin moriyar waɗanna abubuwa da muka ambata ba, don haka ma ya sa ake iya kallon rabe-rabenta ta fuskar aikinta, ko girmanta ko kuma sunanta.

4.0 SAƘON GSM


Saƙon GSM bayani ne taƙaitacce wanda aka rubuta wa wani domin ya fahimci abin da ake so ya karanta, ko ya gani ko ya sadu da abin da ake so ya karƂa ya kuma gan shi cikin akwatin saƙon wayar salula. A taƙaice, saƙon GSM rubutaccen matani ne da ake turawa ta sabis da GSM ya tanada domin musaya a tsakanin masu amfani da wayar salula. Saƙon GSM yana da muhimmin hali irin wanda ake ciki, kamar na daidaituwa ko shiryiwarsa a cikin wayar salular Hausawa. Wannan saƙo yana iya kasancewa taƙaitaccen saƙo ko saƙo wanda ba a taƙaita ba Ta fuskar Hausa ko harshen saƙon GSM kuwa, ana samun Hausawa masu amfani da damar aika saƙo cikin harshen Hausa zalla ko Ingilishi zalla ko kuma ta hanyar yin ingausa . Sannan akwai hasashe da ke nuna cewa masu tu’ammuli da kafar aike da saƙon waya a tsakanin al’umma sun haɗa da: masu ilmin Boko, ko waɗanda suka yaƙi jahilci ko kuma ‘yan biri Boko

4.1 SADARWA DA GSM A MATAKAN RAYUWAR BAHAUSHE


A cikin matakan rayuwar Bahaushe da aure da haihuwa da mutuwa sun ɗauki wani sabon salon ci gaban zamani, sanadiyar rungumar wayar salula da Hausawa suka yi cikin gudanar da al’adunsu na auratayya da zumunta da sauran nau’o’in zaman tare ga musamman abin da ya shafi sanarwa da kiran mutane domin yin wani abu tare kamar yadda al’ada ta tanada. A taƙaice, wannan sashe zai duba yadda Hausawa ke amfani da wayar salula don sanar da lalurar ɗaurin aure ko rashi na rayuwa da aka samu da gayyatar halartar zanen suna da kuma gaisuwar Jumu’a. Sannan za mu doshi wata manufarmu ta sosai, wato mu bayyana mayar da martani ko taya murna ko gaisuwa da jajantawa a musamman saƙonnin da ake musaya a lokutan waɗannan shagulgula. Sai dai ya kamata mu san cewa a irin wannan ma’amala zumunci shi ne ƙashin bayan al’umma masu zaune cikin tsari da ingantattun al’adunsu.
Hausawa na da al’adar taya juna murna idan wani ya sami ci gaba ga rayuwa, ko lokutan aure da samun ƙaruwar haihuwa ko ƙarin matsayi a wajen aiki. Da kuma lokutan bukukuwan sallah inda saƙonnin GSM ke riƙa shawagi tsakanin wannan wayar hannu zuwa wata wayar salula. Ta saƙon GSM mutane ke nuna farin cikinsu da nishaɗin da ya mamaye zukatansu a lokutan shagulgula da dama. Dubi waɗannan saƙonni.
‘Ina taya k murnar samun ɗ nmj Allah SWT y ry muna sh bisa hnyr mslnci. Ita km madam Allah y bt lfy. Kai km madugu Allah y ƙr hore m abin llr. Wallahi N y farin ck mtƙ. Sai n zo ganin baby boy.’
Alhamdulillahi Allah ya albarkace mu da samun ‘ya mace yau 6/06/2013, kuma madam da baby duk suna cikin ƙoshin lafiya. Na gode. ‘D’Dahiru Muhammad.ɗ
Allah SWT has blessed us with a baby boy yesterday @ 11pm. Thanks for your support nad prayers. ‘DSama’ila Daniya.ɗ
‘Za a ɗaura min aure ranar Assabar 27th November, 2010 da ƙarfe 2:30 na rana a gidan Alhaji Abubakar Garba Fana. Number 2 federal low cost Arkilla kusa da masallacin Jumu’a na Arkilla. ‘DMustapha Umar.ɗ
You are invited to attend the wedding fatiha of Yazeed Abubakar and Sadiya Malami Boɗinga. Which will take place at Boɗinga Central Jumu’at Mosque on Saturday 4/05/2013 by 12pm. ‘DYazeed Abubakar.ɗ
Kasancewar kowace rayuwa tana tare da jarabawa, shi ya sa idan abin baƙin ciki ya sami wani akan yi masa jaje, wato a taya shi baƙin cikin abin da ke damunsa, ta hanyar zuwa da kai, ko ta amfani da wayar salula domin kira a yi magaba da shi ko aika saƙon kalmomi masu kwantar da hankali da nuna tausayi, da kuma ba da haƙuri. Akan tura saƙonnin jaje ga musamaman mutanen da ke zaune a wurare masu jayawa, ko kuma kasancewar wanda zai je taya baƙin ciki yana fama da ƙarancin lokacin kai ziyara, saboda yanayin aikinsa da makamantansu. Ga yadda saƙon ta’aziyya ke bayyana a shafin wayar salular Hausawa.
‘Salam, Ashe wani abu ya faru haka to, Allah ya gafarta masa, yasa ya huta. Allah ya ba da haƙurin jure rashinsa. Allah ya sanyaya. Mu kuma Allah ya kyautata tamu idan ta zo. Sannunmu Baffa a yi ta masa addu’a.’
Aslm alykm. !! Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un!! Allah SWT ya yi wa gwaggon Usman Gwiwa rasuwa jiya, da fatar a yi mashi ta’aziya. Allah ubangiji ya yi mata gafara amin.
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’una Allah ya yi wa mahaifiyata rasuwa yanzun nan kuma za a yi jana’iza ƙarfe 8am. Muna baran Addu’a. ‘DMuhammad Abdullahi.ɗ
Kasancewar duk wanda ya rayu a duniya, to babu shakka wata rana zai rasu, ya bar ta. Saboda haka, waɗannan saƙonnin waya sun bayyana muna yadda wanda aka yi wa rasuwa ke sanar da rashin da ya yi, da kuma yadda masu ta’aziyya ke masa gaisuwa da addu’a ga mamaci. Wani lokaci ma, akan sami sanarwar rasuwa ba daga bakin wanda aka yi wa rasuwa, sai dai daga wani ɗan’uwa ko abokanin arziki.

https://www.amsoshi.com/2017/09/27/nahawun-ke%c6%83a%c6%83%c6%83un-kalmomin-intanet-na-hausa/

4.2 SADARWA DA GSM A WASU ƁANGARORIN MA’AMALAR BAHAUSHE


Bahaushe na cewa zumunta a ƙafa take, yau an wayi gari al’umma ta rungumi sada zumunci ta hanyar wayar GSM. Hausawa na kira ko musayar saƙonnin GSM tsakaninsu da ‘yan’uwa, da abokan arziki, da maƙwabta ko waɗanda ake aiki tare da su. Mafi yawan maganganu ta wayar GSM ko saƙon sada zumunci kan ƙumshi gaisuwa da fatar alheri, musamman tsakanin waɗanda suka daɗe ba su haɗu ba. Saboda haka, muna iya cewa amfani da fasahar wayar GSM ya taimaka wajen ƙara daƙon zumunci tsakanin zumai na kusa da musammam waɗanda ke zaune a wurare masu nisan gaske. Dubi yadda ‘yan zamani ke sada zumunci tsakaninsu.
‘Hi, y kake, y gd, y iyl? I hope komai yn tfy nomal. Wai bros y zancen auren Tima baby ne, amma y kmt a y sh b4 azumi man. Pls. k turo man credit ko n #100 garin ne y yi zafi. N gd. Allah y bar zmnc.’
A wannan zamani ana samun musayar saƙonni tsakanin Hausawa, musamman ranar Jumu’a ko lokutan shagulgulan Musulunci kamar ranakun sallar Azumi da ta layya. Akwai kuma saƙonnin da ake musaya a lokuta daban-daban.
Idan kana cikin damuwa ko wata masifa to, ka lazimci ‘Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un’ Idan ka samu biyan buƙata a kan wani al’amari sai ka riƙa cewa ‘Alhamdulillahi’ Idan kana neman gafarar ubangijinka to, ka riƙa lazimtar ‘ Astagfirul Lahul Lazi La’ilaha Illa Huwal Hayyul Ƙayyumu Wa A Tubu Ilaika’ Idan za ka roƙi Allah ka ce: ‘Allahumma Salli Ala Muhammadin Wa Sallim’ ka haɗa da Allahumma Assir Auratina Wa Ammir Rau’atina’ da kuma ‘Allahumma La Sahala Illa Ma Ja’altuhu Sahala Wa Anta Taj’alal Huzuna Iza Shi’ita Sahala’ Allah ya sa mu dace.
Narrated Abu Hurairah (R.A) The prophet (SAW) Said: ‘Adulterer fornicator, at the time he is committing illegal sexual intercourse is not a believer; and a person, at the time of driking an alcoholic drink is not a believer; and a thief, at the time of stealing, is not a believer.’ (Sahih Al-Bukhari, vol. 7, Hadith No 484) Jumu’at Kareem.
Salam, an yi sallah lafiya. Allah ya maimaita mana, ya nuna mana ta baɗin baɗaɗa. Allah ya karƂi ibadodin da muka yi, ya sa muna cikin waɗanda aka ‘yanta daga wuta zuwa aljannah. A gaida mutanen gida, sai mun kawo muku ziyasa. Kuma kar ka manta da kabarbarin da ake yi. Barka da Sallah.
Masu tura saƙonnin nishaɗi kan shirya su saboda ba da dariya da yin raha ko ba’a ga wani ko domin shammatar wani ko ma domin yaɗa wata taƂargazar da wata ƙabila ta yi. Waɗannan saƙonni kamar yadda ake rubuta su sukan ɗauki sigar barkwanci, ko tsokana ko kuma domin kawai sada zumunci tsakanin ‘yan’uwa da abokan arziki. A taƙaice, su ma saƙonnin nishaɗi kan yaɗu daga wata waya zuwa wata.
Wani yaro ya ɗauko namijin tantabara a cikin kwali ya zo police check point, sai police ya ce: “Kai yaro, sauke kuma buɗe abin da ke cikin kwalin nan.” Yaron ya ajiye kwali, amma yana tsoron buɗewa. Sai police ya daka masa tsawa: Buɗe mana! ‘Sai yaron ya fara kuka amma yana ta ƙoƙarin buɗe kwalin; yana cewa: “WALLAHI IN NA BU’DE TASHI ZAI YI.” Ai kuwa kafin ka ce kobo, police kowa ya kama gabansa!
Wani Bafulatanin daji ne ya je birni. Da ya tashi dawowa sai ya sayo wa matarshi tsarabar madubi domin ba su taƂa gani ba. Tana kallo sai ta ga fuskarta a ciki. Sai ta yi fushi ta yi yaji…. Da mamarta ta tambaye ta dalilin yaji sai ta ce mijinta ya yi mata kishiya a birni mai kama da biri ya kuma kawo mata hotonta. Uwar ta ce mu gani, tana dubawa sai ta ce “ Wannan tsohuwar banza zai auro miki? Lalle dole ki yi yaji.”
Babban manufar waɗannan saƙonnin nishaɗantarwa ita ce domin gaisuwar sada zumunci, ta hanyar ba da dariya a tsakanin al’ummar yau.
Tsokana na nufin jawo magana, ko yin wani abu da zai jawo hankalin wani, da zimmar Ƃata masa rai ko don tsokanarsa wasa (Umar,2013:6) Saƙon GSM hanya ce da ake yaɗa zantuka ko labaran da ba su da tushe. Mafi yawan masu shirya waɗannan saƙonni suna yi ne domin tada hankalin mutane, ko tsokana, ko don nishaɗantarwa. Ana samun saurin yaɗuwar irin waɗannan bayanai da mutane ke ƙagowa na ƙarya, saboda duk wanda aka tura wa saƙon yakan yi ƙoƙarin baza shi ga mutanensa. Saboda haka, muna iya cewa yaɗa ji-ta-ji-ta al’amari ne da akasari ba gaskiya ba, kuma ya rigaya ya zama ruwan dare tsakanin ‘yan Nijeriya.
Ko ka san da cewa yanzu ‘yan ƙungiyar asiri na amfani da wasu lambobin waya waɗanda ba su cika ba, domin shan jinin mutane. Kuma an samu rahotannin hasarar jini da ta rayuwar mutane da dama daga kowane Ƃangare na ƙasar nan. Don Allah a sanar da ‘yan’uwa da su yi hattara su san lambobin da za su riƙa amsa kiransu.
It has been reported that all palm oil coming to North from South this week is being mixed with a large quantity of poison that kills instantly. Please do not use any palm oil or its kind transported from southern part of this country. Pls pass this information to ur family and friends. Tanq
Waɗannan saƙonni sun tabbatar da zaman saƙon GSM wata fitacciyar hanyar baza ƙarya da ji-ta-ja-ta, domin kawai samar da nishaɗi, ko don samun wata biyan buƙata.

5.0 KAMMALAWA


Lalle bayyanar fasahar zamani ta wayar salula da fanninta na saƙon GSM sun yi tasiri matuƙa a zamantakewar Hausawa. Hasali ma, sun mamaye ilahirin fannonin rayuwarmu ta kowace fuska, musamman saboda kasancewar mu cikin zamanin amfani da na’urorin kimiyya wajen tafiyar da al’amurran yau da kullun. Sannan bincikenmu ya nuna yadda samuwar fasahar GSM ya ƙara kawo wadatuwa da gamuwa ga jama’a wajen sada zumunci. A halin yanzu ma kusan rayuwa ba ta tafiya sai da ita, (musamman a biranenmu) in har kana son ka san abin da duniya ke ciki. A taƙaice, wannan fasahar zamani ta GSM ta buɗe wa Bahaushe sabon salon gudanar da dangantaka da ma’amala a sauƙaƙe, tare kuma da samun biyan buƙata gwargwado.

MANAZARTA


‘Dantumbishi, M.A. 2004. “Harshe, Al’umma da Kuma Zamananci”: Takardar Ƙara wa Juna Ilimi da Aka Gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo.
Galadanci M.K.M Da Wasu. 1990. Hausa: Don Ƙananan Makarantun Sakandare 1. Lagos: Longman Nigeria Plc.
Jami’ar Bayero. 2006. Ƙamusun Hausa. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Skinner, N. 1965. Ƙamus Na Turanci Da Hausa-English, Hausa Illustrated Dictionary (Babban Jagora Ga Turanci). Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Ltd.
Umar, M.M. 2012. “Nazarin Saƙon G.S.M a Wayar Salular Hausawa.” Kundin Digiri na Biyu, Sakkwato: Jamai’ar Usmanu ‘Danfodiyo.
Umar, M.M. 2013. “Hausar Masu Ƙwallon Ƙafa a cikin Garin Sakkwato” : Maƙalar Aka Gabatar a Taron Ƙara wa Juna Sani a Sashen Harsunan Nijeriya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu ‘Danfodiyo.
Umar, M.M. 2013. “Nazarin Ingausa a Sakon GSM.” Dundaye Journal of Hausa Studies. Department of Nigerian Languages. Sokoto: Usmanu Danfodiyo University, Volume 1 No 5. June, 2013 Page 77-82. ISSN: 0189-7802
Yakasai, S.A. 2012. Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Services.
Yule, G. 1985. The Study of Language: An Introduction. Australia: Cambridge University Press.
Zarruk, R.M Da Wasu. 1986. Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa. Don Ƙananan Makarantun Sakandare, littafi na ‘Daya. Ibadan: University Press Limited.
Zarruk, R.M Da Wasu. 2006. Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa. Don Ƙananan Makarantun Sakandare, littafi na Uku. Ibadan: University Press Limited.
Wayoyi

Post a Comment

3 Comments

Post your comment or ask a question.