Ticker

6/recent/ticker-posts

Dabarun Bayar Da Labarin Wasu Al’adun Hausawa A Bakin Makaɗa Dankwairo: Nazarin Wakar Ba Takura Kaurin Gaba

Citation: Maimota, A.S & Kabir, J. (2024). Dabarun Bayar Da Labarin Wasu Al’adun Hausawa A Bakin Makaɗa Dankwairo: Nazarin Wakar Ba Takura Kaurin Gaba. Algaita Journal of Current Research in Hausa Studies. Vol. 17, No. 1, December, 2024. Pg. 65-76

DABARUN BAYAR DA LABARIN WASU AL’ADUN HAUSAWA A BAKIN MAKAƊƊANƘWAIRO: NAZARIN WAƘAR BA TAKURA KAURIN GABA

Na 

Aishatu Shehu Maimota
+2348066054705
maimotaisha@gmail.com

Da

Hauwa Rabi’u Ɗanbappa
+2348035452399
Hauwadanbappa200@yahoo.com

Tsakure

Adabin Hausa hanya ce ta bayyana rayuwar al’ummar Hausawa, kama daga al’adu da tarihi da yanayin zamantakewa. Wannan Maƙala ta bibiyi yadda Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya yi dabara ya bayar da labarin abin da ya shafi masarautar garin Kano a waƙarsa mai suna “Batakura Kaurin Gaba”. Makaɗin ya bayyana yadda ake gudanar da hawan salla a wannan masarauta. Takardar ta gano yadda wannan mawaƙi ya saƙa basirarsa ya bayyana yadda ƙasaita ta mulkin sarkin Kano Alhaji Ado Bayero take, da yadda yake gudanar da haye-hayen salla, tare da yanayin kwalliyarsa da wuraren da yake ziyarta a yayin wannan hawa. A ɓangare ɗaya wannan maƙala ta yi fashin baƙi kan ɗiyoyin wannan waƙa. A yayin wannan fashin baƙi an bayyana ma’ana da amfanin wasu kayayyaki na al’adar wannan masarauta da mawaƙin ya zayyano. Haka zalika takardar ta yi ƙarin haske kan wasu abubuwa da Ɗanƙwairo ya bayyana a wannan waƙa. An gudanar da wannan bincike ta hanyar duba da ra’i da Gusau (2015) ya samar. Masanin ya bayyana daga cikin dabaru da ake gudanar da tarke adabi akwai inda ake ‘tarken al’adu a wasu sassan adabi’ da kuma ‘tarken fashin baƙi’, duba da haka ya sa wannan maƙala ta bibiyi al’adu da aka zayyano na masarautar Kano a wannan waƙa mai suna ‘Batakura Ƙaurin Gaba’, tare da yin fashin baƙi a kan ɗiyoyin waƙar. Wannan bincike ya gano cewa masarautar Kano ta keɓanta da wasu al’adu da ita kaɗai take gudanarwa a ƙasar Hausa. Haka zalika wannan masarauta tana da wasu kayayyaki na sarauta waɗanda su ma ita kaɗai ta keɓanta da su.

Kalmomin Bincike: waƙar baka, Bayar da labari, al’adu, fashin baƙi.

1.1 Gabatarwa

Mawaƙan Hausa na da dabarar bayar da labari a waƙoƙinsu inda suke bayyana labari na wani abu da ya faru ko yake zuciyarsu cikin waƙa. Iri waɗan nan waƙoƙi su ne da Turanci ake kira da narratiɓe poetry. Masana irin su Hess sun bayyana waɗannan waƙoƙi da cewa waƙoƙi ne da suke bayyana wani cikakken labari na wani abu da yake ɗauke da wata manufa. Irin wannan dabara makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya bi ya bayar da labarin wasu abubuwa da suka shafi masarautar Kano a zamanin mulkin marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Bayero. Haka zalika Hess ya bayyana cewa za a iya raba ire-iren waɗannan waƙoƙi zuwa kashi huɗu, ciki har da abin da ya kira ‘epic’, wato ‘kandamin labari’. Waƙa mai ɗauke da kandamin labari waƙa ce da take ɗauke da labari mai tsawo wanda zai iya zama tarihi. Wannan takarda ta bibiyi yadda Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya bayar da labarin hawan ƙaramar salla a masarautar Kano. A ya yin bayar da wannan labari ya fito da wasu al’adu da wannan masarauta take da su, ire-iren waɗannan al’adu wannan maƙala ta binciko a wannan waƙa tare da yin fashin baƙi a kai. An gudanar da wannan nazari ne ta duba da ra’i da Gusau (2015) ya samar. Masanin ya bayyana yadda ake tarken adabin Hausa, daga cikin dabaru da ake gudanar da tarken akwai inda ake ‘tarken al’adu a wasu sassan adabi’ da kuma ‘tarken fashin baƙi.

An kasa wannan maƙala zuwa kashi uku, kashi na farko gabatarwa ce tare da taƙaitacen tarihi makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun da bayanin waƙar ‘Batakura Ƙaurin Gaba’. Kashi na biyu kuma an yi bita kan ma’anonin al’ada da waƙar baka tare da taƙaitaccen bayanin ra’in tarken al’adu a wasu sassan adabi da kuma tarken fashin baƙi. Sai kashi na uku inda aka kasa shi gida biyu, an fara da bayyana haye-hayen salla da ake gudanarwa a masarautar Kano. A ɓangare na biyu kuma aka kawo al’adun da Ɗanƙwairo ya kawo a wannan waƙa tare da yin fashin baƙi wato bayani a kan waɗannan al’adu.

1.2 Taƙaitaccen Bayanin Waƙar ‘Ba takura Kaurin Gaba’

Waƙar Ba takura kaurin gaba tana daga cikin waƙoƙin sarakuna da Ɗanƙwairo ya yi wa marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Bayero wanda ya yi mulki daga shekarar 1963-2014. Ya yi wannan waƙa ne tsakanin shekarar 1975 zuwa 1978, domin makaɗƊanƙwairo ya nuna ya yi wannan waƙa ne a lokacin mulkin gwamnan Kano Kanal Sani Bello, kamar yadda ya bayyana a waƙar inda ya ce:

... Nan yaz zo ya sabka,

Gwamnan Kano Sani Bello.

yas sauko suka gaisa....

waƙar tana da ɗiya 27 kamar yadda suka zo a Gusau (2019)

1.2.2 Bitar Ma’anar Al’ada

Magaji (2002) ya bayyana al’ada kamar haka: “Al’ada ita ce hanyoyin da al’umma take bi domin gudanar da rayuwarta waɗanda suka haɗa da abinci da sutura da muhalli da gine-gine da sadarwa da sauran muhimman abubuwa na wannan al’umma.”

Haka kuma, an bayyana al’ada da cewa “…hanya ce da al’umma take gudanar da rayuwarta ta yau da kullum ta fuskar tsarin zamantakewa da abinci da muhalli da tufafi da gine-gine da bukukuwa da ma dukkanin wasu abubuwa da suka shafi al’umma da rayuwarsu ta yau da kullum.” (Mu’azu, 2013:1)

2.1 Taƙaitaccen Bayanin Ra’in Tarken Adabin Hausa

Gusau (2015) ya bayyana yadda tarken adabin Hausa ya samu da cewa;

Hausawa sun sami hanyar yi wa adabinsu tarke bayan da suka iya rubutu da karatu na haruffan Romanci wato karatun boko. Kafa makarantun boko da Turawa suka yi wa Hausawa da samar da hukumomi kamar hukumar fassara (1929) DA Hukumar Talifi (1933) da Gaskiya Corporation , Tudun Jukun Zariya (195) da Hukumar Yaƙi d Jahilci (1953) da Hukumar NORLA, wato Samar da Adabi (1954-1960) da Kamfanin Gasiya (1960-1966) da Kamfanin NNPC (Oktoba, 1966) sun taimaka wajen samar da ayyukan adabin Hausa. (Gusau, 2015:11)

Gusau ((2015) ya ƙara da cewa:

Ayyukan tarke na adabin Hausa, musamman daga ‘yan ƙasa Hausawa, da sauran masu sha’awar adabin Hausa sun ci gaba da ƙaruwa suna bunƙasa. Daga cikin dabaru na tarke da aka mai da hankali a kansu sun haɗa da:

§ Tarken gargajiya

§ Tarken ƙagaggen labari

§ Tarken al’adu a cikin wasu sassan adabi

§ Tarke na fiɗa ko sharhi

§ Tarken fashin baƙi

§ Tarken ƙalailaice adabi

§ Tarken adabin baka

§ Tarken sigogin adabi

§ da sauransu (Gusau, 2015:13)

A taƙaice a wannan littafi Gusau ya yi bayani dangane da ayyuka da masana tun daga Turawa zuwa Hausawa ‘yan ƙasa suka gabatar waɗanda za su zama jagora ga mai nazari ko tarken adabin Hausa. Domin samun cikakken bayani a duba Gusau (2015:11-19)

3.0 Bayar da Labari da Fashin Baƙi kan Wasu Al’adu a Waƙar Ba Takura Kaurin Gaba

Makaɗa Musa Ɗnƙwairo Maradun a waƙarsa ta ‘Batakura Kaurin Gaba’ ya bayar da labarin yadda ake gudanar da hawan salla a masarautar Kano, a ya yin bayar da wannan labari ya fito da wasu al’adu da suka keɓanta da masarautar Kanon. A wannan kashi an fito da yadda ya bayar da wannan labari tare da bayyana waɗannan al’adu tare da yi musu fashin baƙi wato ƙarin bayani.

3.1 Hawan Salla a Waƙar ‘Ba Takura Kaurin Gaba’

Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun ya bayyana ire-iren hawa guda huɗu da sarki Ado Bayero ya gudanar a bikin ƙaramar salla ƙarama. Ya yi bayanin yadda ya gudanar da waɗannan hawa.

3.1.1 Hawan Idi

Hawan Idi hawa ne da ake gudanarwa ranar ɗaya ga salla wato, 1 ga watan shawwal bayan an kammala azumin watan ramalana. Hawan idi shine hawa na farko a bukuwan salla.

Makaɗa Musa Ɗanƙwairo cikin gwanancewa ta iya waƙa ya zayyanoo hoton wannan hawa ta yadda ko da mutum bai taɓa halartar kallon wannan hawa ba zai habarto ya ya yake. Ya fara da zayyano tun daga fitowar sarkin daga gida inda ya fita ta ƙofar mata zuwa filin masallacin idi, inda ya ce:

Jagora: Ni Alhaji Musa Ɗanƙwairo

Na tahi Kano na yi salla

Nig ga hawan sarkin Kano

Da zai fita zai je idi

Ta Ƙofar Mata ya fita.

Bisa al’ada sarki kan tafi sallar idi a ƙafa sai ya dawo a doki, duk da makaɗa Musa Ɗanƙwairo bai fito ya bayyana sarki ya tafi a ƙasa ba amma ya bayyana da zai dawo ya hau doki, ya dawo ta Ƙofar Wambai, sannan ya faɗi cewa da zai koma gida ya shiga ta Ƙofar Arewa. Ga yadda ya zayyano:

Sarki ya hau doki

Ya shiga Ƙofar Wambai

-------------------------------

Ya shiga nan Ƙofar Arewa

Haka zalika makaɗa Musa Ɗanƙwairo cikin hikima da fasaha ya zayyana hoton irin shigar da sarki ya yi a ranar salla inda mai sauraro zai iya hasaso yanayin shigar sarkin a zuciyarsa:

Jagora: Bakan Dabo na ga hannunai

Ga kwarinsa ya rataya

Da anka sabko idi

Ya dogara shi yay yi huɗuba.

ɓangare ɗaya makaɗin ya zayyano yadda hakiman sarki da bayinsa suka fito domin raka sarki, in da ya ce:

Daudu: Hakiman sarkin Kano,

Su talatin da shidda ne,

‘Y/Amshi: Ga layin ‘yansanda,

Ga layin ‘yandoka,

Ga samarin sarki ‘yan baka,

Ga layin zagaigai,

Ga dawakin zage,

Ga raƙumi, farin doki,

An ka haɗa su wuri ɗai,

Kuma ga Shamaki Ɗanrimi

Manyan bayin sarki.......

Bayan ya gama zayyano waɗannan sai kuma ya bayyana yadda sarki a kan hanyarsa ta dawowa ya tsaya a Gwauron Dutse inda gwamna na wannan lokaci ke tsaye yana dakon zuwan sarki, sarki ya tsaya sun gaisa har gwamnan ya yaba wa sarki bisa irin hidimar da yake wa talakawansa.

Jagora: Har ya za ka Gwauron Dutsi

Nan yaz zo ya sabka

Gwamnan Kano Sani Bello

Yas sakko suka gaisa...

MakaɗƊanƙwairo bai tsaya a nan ba sai da ya labarto mana cewa bayan gaisawa da gwamna, sarki ya shiga Ƙofar Arewa ya tsaya ya yi wa talakawa jawabin salla tare da yi musu nasiha. Inda ya ce:

Jagora: Ya shiga nan Ƙofar Arewa,

Ya gode wa Allah,

Ya gode wa Rasulillahi,

An ƙare azumi lahiya,

An ƙare salla lahiya,

Kowa ya zo ya sauka,

Ya ce musu kowa ya zo ya sauka,

A so Allah da zumunta,

‘Yan’uwa a so Allah da zumunta.

3.1.2 Hawan Daushe

Hawan Daushe shi ne hawa na biyu a jerin hawan salla, ana gudanar da shi ne ranar biyu ga salla wato kashegarin idi. Kamar yadda tarihi ya bayyana hawan Daushe ya samu ne a lokacin da sarki ya sami labarin wani babban bawansa Daushe ba shi da lafiya,bai samu hawan idi ba. Da sarki ya tambayeshi sai yace ba shi da lafiya, da yamma ta yi sai Sarki ya sa aka buga kugen hawa aka hau sarki ya je Babban ɗaki ya gai da mahaifiyarsa daga nan suka kewaya wasu unguwanni domin gaisawa da talakawansa. Bayan an sauka Sarki yace da Daushe wannan hawa na ka ne. Daga nan aka samu sunan hawan ake cewa hawan Daushe.ganin bai zo fada ba da yamma da ya zo shi. Tun daga wannan lokaci ya zama cikin jerin hawan salla, sai ya zamana a ranar sarki kan tafi babban ɗaki, wato gidan mahaifiyarsa ya gaishe ta. A wannan rana da safe sarki kan zauna a fada da ya karɓi gaisuwar hakimai da wasu rukunan jama’a, sai kuma ya shiga gida, da an yi sallar la’asar sai ya hau doki a fita hawan Daushe, ya je ya gai da mahaifiyarsa daga nan ya biyo ta wasu unguwanni na nan cikin gari ya gaisa da talakawansa. MakaɗƊanƙwairo ya zayyana wannan zama na fada da hawan Daushe da ake gudanarwa a wannan rana. In da ya ce:

Jagora: Da azzahar tak kama,

Sarki ya yi hawan daushe,

Ya tafi babban ɗaki,

Ya zo ya yi ziyara,

Ya dawo ya sauka....

3.1.3 Hawan Nassarawa:

Hawan Nassarawa hawa ne na uku a jerin hawan sallar Kano. Ana gudanar das hi da safe ranar uku da salla, inda sarki kan fita da wuri. Sarki na fara sauka a gidansa na Nassarawa ya je ya kai ziyara kabarin iyayensa da kakanninsa sarakuna da aka binne a wannan gida. Daga nan sai ya ƙara hawa ya tafi gidan gwamna su gaisa sai kuma ya biyo ta unguwoyi da suke yankin nassarawa ya ga talakawansa su gan shi.

Cikin hikima da gwanancewa makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya zayyano yadda hawan Nassarawa ya kasance da yadda yake kai ziyarar ban girma ga gwammna da sauran wurare da yake zuwa a yankin nassarawa wato, wajen gari. Ga yadda ya ce:

Jagora: Da salla tak kwana biyu,

Sarki yay yi hawan Nasarawa,

Ya tafi can Nasarawa,

Sai ya zarce gidan Gwamna,

Sunka gaisa da Gwamna

Sai yah hau dokinai

Ya dawo ƙofar Nassarawa,

Sai yaɗ ɗau hanyar banki,

Mutanen da suke banki,

Sun yi layi a kan titi,

Suna gaisuwa ga sarki,

Allah sa ka yi jinkiri,

Ka kai bisa bisa Madi,

Alhaji ka kai bisa Madi, amin,

Das sabon gari ya zaka Fage,

Mutanen da suke Fage,

Sun yi layi a kan titi,

Suna gaisuwa ga Sarki,

Allah sa ka yi jinkiri,

Ka kai bisa Madi,

Alhaji ka kai bisa Madi, amin,

Daf Fage yas shigo birni,

Mutanen da suke birni,

Sun yi a kan titi,

Suna gaisuwa ga sarki.....

3.1.4 Hawan Fanisau

Hawan Fanisau shi ne hawa na huɗu kuma hawa na ƙarshe a jerin hawan salla a Kano. Ana gudanar da wannan hawa ne ranar biyar ga salla. Sarki kan fita da safe ya tafi gidansa na Fanisau ya yini sai bayan la’asar ya dawo.

Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya bayyana tarihin gidan sarautar Fanisau inda ya ce sarkin Kano Usman ne ya gina shi. Ga yadda ya ce:

Da salla tak kwana biyar,

Sarki ya yi hawan Fanisau,

Fanisau gidan sarauta ne,

Tun lokacin Sarki Usuman,

Shi nag gina shi,

Daudu: Na ji tun lokacin Sarksi Usuman

‘Y/Amshi:Shi nag gina shi,...

3.2 Wasu Al’adu na Masarautar Kano a Waƙar ‘Batakura Kaurin Gaba’

Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun, ya fito da wasu al’adu na masarautar Kano a wannan waƙa da ya yi wa marigayi sarkin Kano Alhaji Ado Bayero. Ya fito da al’adu da suka shafi suture da kayan ado na sarki, haka ya fito da al’adu da suka shafi sufuri. A ɓangare ɗaya makaɗa ya fito da sunayen wasu sarautu na bayin sarki.

3.2.1 Suturu da Kayan adon Sarki

A waƙar Batakura ƙaurin gaba, makaɗƊanƙwairo ya bayyana nau’ikan suturu da kayan ado na fada, kama daga waɗanda sarki yake amfani da su da na yaran sarki da na bayinsa. Ya bayyana su kamar haka:

Sarki mai kyautar riguna,

Sarki mai kyautar wanduna,

Sarki mai kyautar kuftoci,

Sarki mai kyautar alkyabba,

Sarki mai kyautar rawuna,...

sai kuma:

...Da zai fita zai je idi,

Bakan Dabo na ga hannunai,

Ga kwarinai ya rataya,..

Akwai kuma inda ya ce:

Daudu: Ƙwairo tafiya ƙarin ilmi

Na ga ƙawa birnin Kano,

Na ga hawan bayin sarki,

Kuma na ga hawan yaran sarki,

Kowane hakimi yai ado,

‘Y/Amshi: Da yaranai sun tunjum,

Su ko kayan doki,

Daga alkashafa, sai tunjumi,

Sai tumbas mai tsada...

Riguna da wanduna suturu ne na Hausawa, amma akwai nau’ikan na fada duk da Ɗanƙwairo bai fito ya bayyana ba, suna da riguna kama daga asake da saƙi da sauransu. Wanduna kuma akwai masu kamun ƙafa da buje da sauransu. Kufta riga ce da ake yi wa ɗinkin hannu. An sami kufta daga ƙasashen Larabawa musamman na Magrib irinsu Maroko da Aljeriya da Tunisiya da sauransu, sarakuna da hakimai da sauran mutanen fada suna amfani da kuftoci somin ado. Ko a ɗinki kuftocin fada sun fita daban, domin ana yi musu aiki mai yawa da zare na musamman. Alkyabba kuma riga ce doguwa mara hannu mai buɗaɗɗen gaba mai aiki sosai, sanna tana da hula a jikinta da ake kira ƙoƙuwa, ana yafa ta a kan riga. Ita ma alkyabba an same ta ne daga ƙasashen Larabawa amma sarakunan Hausa sun fi amfani da ita. Haka kuma sarki da hakimai ne kaɗai suke saka alkyabba, sai kuma wasu manyan bayin sarki kamar Shamaki da Ɗanrimi da Sallama da sauransu, waɗanda su ma ba koyaushe suke saka wa ba sai lokutan bikin salla ko wani biki.

Rawani kuma abin naɗi ne da sarakuna da hakimai da sauran mutanen fada suke amfani da su. Rawuna iri-iri ne kuma suna zuwa a launuka daban-daban, akwai nau’ikan rawuna na ‘ya’yan sarki, akwai na malamai da na bayin sarki. Shi rawani ana naɗa shi ne a ka. Rawuna akwai harsa fara da masu launi, akwai wanda ake kira kuskus da akwai dan Sakkwato wanda ake kira ɗan Sardauna, akwai ɗankura wanda ake cewa shuni.

“Bakan Dabo” da “Kwari”,kayan kwalliya ne da sarakunan Kano ne kaɗai suke da shi. Sarakunan Kano sun gaji wannan kwari da baka ne daga kakansu sarki Ibrahim Dabo, wanda shi ne sarkin Kano na biyu na daular Fulani. Duk wani sarki na Kano yana rataya wannan kwari na Dabo sannan ya dogara bakan kamar sanda. Amma ba kodayaushe sarki ke amfani da kwari da bakan Dabo ba sai lokacin sallar idi ƙarama da babba, sai kuma ko ranar juma’a idan za a buɗe masallaci. Yawanci ba a ganin kwarin saboda idan sarki ya rataya yana ɗora babbar riga da alkyabba a kai, sai dai bakan da yake dogarawa ake gani.

Idan aka ce ‘tunjum’, a fada ana nuni ne da wata kwalliya ko shiga wadda yawanci manyan bayin sarki masu zama a gefensa suke yi.haka zalika yaran hakimai ma suna wannan shiga. Shiga ce da ake yi bayan an saka manyan riguna sai a zuba hamilu a yi ɗamara a naɗa rawani ɗan’kura. Wannan shiga cikin ɗamara ake ce wa an yi ‘tunjum.’ Ko yara masu bin angwaye yayin hawan angwanci cikinsu akan sami waɗanda za su kasance a gefen ango sun yi irin wannan shiga.

‘Alkashafa’ kayan ado ne na doki ne da ake sa wa a ƙirjin doki mai kyalli tana da nauyi saboda akwai ’yan ƙarafuna masu kyalli a jiki. Amma yanzu ba a cika amfani da ita ba ana amfani da ‘yan ƙirji marasa nauyi, sai dai suna da zubin alkashafa ɗin.

‘Tunjimi’ ana kiransa ‘tunjima’ ita ma kayan ado ne da ake sa wa a gaban doki a kan goshinsa. Asali tunjima ta da tana ɗauke da ƙulaƙulai na ƙarfe yadda idan doki ya girgiza kansa za a ji suna ƙara. Amma yanzu ana yin tunjima da ƙulaƙulai na ƙyalli ba na ƙarfe ba, yadda ko doki ya girgiza kansa ba za a ji wannan ƙara ba.

Tumbas shi kuma sirdi ne amma na azurfa, yana da tsada ƙwarai ta yadda ba kowa ke iya mallakarsa ba, kasancewarsa azurfa.

3.2.2 Sufuri

A kan abin da ya shafi sufuri ma, Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya kawo kayan hawa na gargajiya kamar doki wanda ya ambace shi a wurare da dama, sai kuma raƙumi. Misali shi inda aka ce:

‘Y/Amshi: Mai nasara ya mirɗo.

Ga layin ‘yansanda,

Ga layin ‘yan doka,

Ga samarin Sarki ‘yan baka,

Ga layin zagaigai,

Ga dawaki zage,

Ga raƙumi, farin doki,..

‘Dawakin zage’ dawakai ne na sarki da suke gaban sarki waɗanda ake yi musu shiri da ƙawa kamar za a yi amfani da su saboda shirin ko ta kwana. Asali da sarakuna suna dogon zango idan za a tafi yaƙi ko fasa haraji, kuma suna wannan tafiya ne a kan dawakai, saboda haka ake tafiya da wasu dawakan ko da doki zai kasa ko kuma zai gaji a wannan lokaci sarki kan caccanza doki. Haka kuma ana lulluɓes waɗannan dawaki saboda girmama Sarki ba za a bar shimfiɗarsa a buɗe ba, ko da zai hau doki sai an kare saboda komai na sarki a al’ada ana buƙatar sirri da girmamawa.

Raƙumi kuma a masarautar Kano suna sa shi a gaba ne domin tuna yadda sarkin Kano Alu Maisango ya yaƙi Damagarawa a kan raƙumi. Sarkin Kano Alu ya yi bad da kama alokacin wannan yaƙin, domin ya yi shiga irin ta buzaye ya hau raƙumi maimakon doki. An ce a wannan yaƙin ya yi wa Damagarawa ɓarna sosai. Kuma shi wannan raƙumi kodayaushe yana gaban ‘yan baka ne wato suna biye das hi a baya, hakan alama c eta nasara.

Farin doki, doki ne na ƙawa da sarki yake amfani da shi ranar idi ko hawan juma’a. Amma kuma da alfadari ne a wurin farin doki, tarhi ya nuna a zamanin sarkin Kano Abdullahi Bayero ana amfani da alfadarin ne, ana zaton sarki Abdullahi Bayero ya kawo wannan alfadari ne daga gabas, daga baya ne sarakuna da suka biyo suka maye gurbin alfadarin da farin doki, wato bayan mutuwar wannan alfadari.

3.2.3 Wasu Sarautu da Muƙamai na Bayin Sarki

A wannan waƙa ‘Batakura kaurin gaba’ MakaɗƊanƙwairo ya ambato wasu yaran sarki da wasu manyan bayinsa. A wurin da ya ce:

‘Y/Amshi: Mai nasara ya mirɗo.

Ga layin ‘yansanda,

Ga layin ‘yan doka,

Ga samarin Sarki ‘yan baka,

Ga layin zagaigai,

Ga dawaki zage,

Ga raƙumi, farin doki,

Anka haɗa su wuri ɗai,

Kuma ga Shamaki da Ɗanrimi,

Manyan bayin sarkin Kano

‘Yan baka a masarautar Kano mayaƙa ne waɗanda suke gaban sarki, suna kasancewa a gaba ne domin zama kariya ga sarki, kuma suna ɗauke da kwari dab aka suna saka riga ‘yar shara da wando da hula haɓar kada launi baƙi da shuɗi. ‘Yan baka na jere da sauran jami’an tsaro na masarautar Kano, kamar ‘yan bindiga da sauransu., ‘yan baka ma’aikata ne da suke ƙarƙashin gidan Sallaman Kano.

Zagaigai su ne zagage da suke gaban sarki, su suna riƙe da wasu abubuwa masu muhimmanci da sarki zai yi amfani da su a gaba, irin su talha da butoci, waɗannan butoci an ce wasu na ɗauke da fura wasu ruwa. Ana kiran shugaban zagage babban zagi, shi babban zagi jagora ne ga sarki, wato inda ya taka ya cire ƙafa nan sarki zai taka ko dokinsa. Bayan babban zagi wanda shi ne sarkin zagage, akwai galadiman zagi da sauransu.

Shamaki shi ne babban bawan sarki, domin duk sauran bayin sarki irin su Ɗanrimi da sallama da kilishi suna ƙarƙashinsa ne. Shamaki shi ne tsani tsakanin sarki da hakimai da bayin sarki. Haka zalika duk wani abu da zai wakana a fada sai da hannun, shi ne yake shigar da hakimai gaban sarki, haka zalika duka wani gandu na sarki da dawakansa suna ƙarƙashin kulawar shamaki. Akwai ayyuka da dama na fada da shamaki ke gudanarwa. A taƙaice shamaki kamar wani hakimi ne a tsakanin bayin sarki domin yana da alkyabba da yake yafawa a wasu lokuta, musamman lokacin bukukuwa. Haka kuma yana da hakimansa, akwai ciroman shamaki da turakin shamaki da makaman shamaki da sauransu. A lokacin hawan doki kodayaushe a cikin giwar sarki shamaki yana daga grfen damar sarki. Ana yi wa shamaki kirari

Ɗanrimi yana daga cikin manyan bayin sarki. Za a iya cewa shi ke bin Shamaki a muƙami, domin akwai wasu abubuwa da Ɗanrimi yake gudanarwa idan shamaki baya nan. Haka kuma shima Ɗanrimi yana da wasu ayyuka da shi kaɗai yake gudanarwa. Daga cikin ayyukansa akwai kasancewa daga gefen hagun sarki a cikin giwar sarki, wato idan ana hawa. A zamanin da Ɗanrimi ke kula da ganuwar cikin birni, haka kuma daga dogon gida zuwa ƙofar Arewa duk wanda ya rasu shi yake kula da harkar jana’izarsa. Ɗanrimi yana da hakimansa irinsu Makaman Ɗanrimi da Galadiman Ɗanrimi da Ɗansarai da Turakin Ɗanrimi da sauransu. Shi ma Ɗanrimi kamar Shamaki yana saka alkyabba a lokutan hawa.

4.0 Kammalawa

wannan maƙala ta kalli yadda makaɗa Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun ya yi wa Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero waƙa. A wannan waƙa mawaƙin ya wassafa yadda ake gudanar da hawan salla a masarautar Kano ta yadda wanda bai taɓa halartar hawan ba zai ga kamar hoton hawan aka jiye masa. Haka kuma takardar ta bibiyi wasu al’adu da makaɗin ya kawo na wannan masarauta tare da yi fashin baki wato bayani a kan waɗannan al’adu. Daga ƙarshe takardar ta gano lallai masarautar Kano tana da wasu al’adu waɗanda ita kaɗai ta keɓanta das u. Ire-iren waɗannan al’adu akwai na hawan idi wanda duk masarautun ƙasar Hausa ke gudanarwa akwai hawan Daushe wanda masarautar Kano ked a hawa mai wannan suna, haka hawan Nassarawa da na Fanisau. A ɓangare ɗaya binciken ya gano masarautar Kano kaɗai ked a bakan Dabo da kwarinsa, haka zalika a ɓanagaren sufuri akwai wasu abubuwa na tarihi da wannan masarauta kaɗai ke da su, irin su raƙumi da dawakin zage. Takardar ta kuma gano har yanzu masarautar Kano na riƙo da waɗannan al’adu nata da ta gada tuntuni.

Manazarta

Gusau, S. M. (2015) Mazhabobin Ra’i da Tarke a Adabi da Al’adu na Hausa.

Kano: Century Research and Publishing Limited.

Gusau, S. M. (2019) Diwanin Waƙoƙin Baka Juzu’i na Huɗu. Wasu Waƙoƙin

Alhaji Musa Ɗanƙwairo Maradun (1909-1991) Sarkin Kiɗan Sarkin

Maradun Jihar Zamfara. Kano: Century Research and Publishing Limited.

Hess, G. R (2020) “Narratiɓe Poetry: Types, History, and use.”

www.poemofƙuotes.com

Khalil, N. W (2006) Bayi a Gidan Dabo Tarihin Shamakin Kaano Inuwa Ɗan Sarkin Zage

Amfani da Sauran Manyan Bayin Sarki (1819-2006 AD). Kano: Gidan Dabino.

Magaji, A. (1982) “Tasirin Adabin Baka A kan Rubutattun Ƙagaggun Labarai.” Kundin

Digiri na Biyu. Kano: Jami’ar Bayero.

Mu’azu, A. (2010) Jirwayen Baƙin Al’adu na Nesa a Ƙagaggun Labaran Soyayya na Hausa. Cikin Harshe 4 Journal of African Languages, pg 80-103, Zaria:A.B.U.

Muhammed, D. (1990) Hausa Metalanguage (Kamus na Keɓaɓɓun Kalmomi)

Volume I. Ibadan: University Press.

Mutanen da aka Tattauna

Shamakin Kano Alhaji Wada

Alhaji Usman Kofar Kudu

Garkuwan Sallama Ali

Wakilin Turakin Dogarai Halifa Aminu

Hajiya Ummi Wada maiɗakin Shamakin Kano

Hausa Novels

Post a Comment

0 Comments