Ticker

6/recent/ticker-posts

Wane Ne Ɗan Ta’adda?

Takardar da aka gabatar a matsayin babban baƙo mai jawabi a taro na musamman na haɗaɗɗiyar Kungiyar Musulmi MSSN, NACOMYO, FOMWAN, MSO, IMAN, WOMEN IN DA’AWA da MCAN, na Jahar Sakkwato. Ranar Litinin 14th Rabi’ul Awwal 1433 A.H. daidai da 6-2-2012 a babban ɗakin taro na FOMWAN, Sakkwato ƙarƙashin Jagorancin Mal. Muhammadu Bello Danmallam Shugaban Jama’atul Muslimin, Sakkwato.

Daga

Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu D’anfodiyo Sakkwato
Kibdau: mabunza@yahoo.com Waya 08034316508

GABATARWA


Gajeren tunanin da ke ga ɗan Adam shi ya sa Larabawa ke ce masa Insan wadda aka cirato daga kalmar Nisyan, mai nufin mantuwa. Mutum zai kafa dokar wani abu, da baya ya zo ya saɓa mata. Wannan dalili ne ya sa Hausawa ke cewa, mai dokar barci ya koma angaje. Matsalolin tsaro sai daɗa taɓarɓarewa suke yi, a koyaushe gara jiya da yau, shekaran jiya ta fi jiya, yau ta fi gobe. Babban abin nufi a nan shi ne , ƙoƙarin dangantawa wata al’umma da ke wata nahiya mai riƙe da wani addini alhakin ringingimun da ke wakana a duniyar zamaninsu. Yau, babu, ‘bata gari sai Musulmi. Babu ɗan ta’adda sai Musulmi. Babu ɗan ra’ayin riƙau sai Musulmi, don haka, a ƙasar nan sai Musulmi suka kasance marayu a kundin tsarin mulkin ƙasar da suka rinjayi kowane addini da ke cikinta. A kan haka nake son in ɗan ce wani abu a kan, wane ne ɗan ta’adda?

TA’ADDANCI:


Ta’addanci kalmar Larabci ce mai nufin shisshigi, da wuce gona da iri, da kece wa doka bante ta fuskar tsumbula cikin hane-hanenta a yi kane-kane ba tare da nuna wata damuwa ba. A fassarar ƙasashen Turai, ta keɓanta ta’addanci ga Musulmi masu ƙwazon neman haƙƙinsu da aka haramta musu, ko masu kare kansu da irin makaman da ake kai musu hari, ko masu ƙoƙarin tabbatar da dokokin addininsu a mu’amalolinsu. Idan wasu da ba Musulmi ba suka ɗauki wannan mataki, akan yi musu suna ‘yan gwagwarmaya ko ‘yan neman ‘yanci ko marasa rinajaye ko abokan hamayya ko ‘yan sari-ka-noƙe. Cikin dabara da yaudara, yau, a kafafen yaɗa labarai na cikin ƙasa da na waje duk da irin waɗannan fassarori suke amfani na shafa wa Musulmi da Musulunci kashin kaji.
Da za a tambayi wanda aka laƙaba wa suna “ɗan ta’adda” mene ne “ta’addanci”? Ba zai saɓa wa fassarar da addini ko harshe ya tanada ba. Idan aka tambaye shi aikin da yake yi, ko ya san ta’addanci ne? Ba zai yarda ba. Dalili kuwa shi ne, shi, yana ƙoƙarin kare kansa ne ga irin farmakin da ake kai masa, ko yana ƙoƙarin ramuwar gayya ne ga ta’addancin da aka yi masa da sunan tsaro ko neman zaman lafiya. Don haka, a ganinsa wanda ya kai masa farmaki shi ne “adda” shi da ke kariya shi ne “ɗanta” don haka wane ne ɗan ta’adda?
Ga dukkanin alamu, ana amfani da kalmar ne a yau domin a ɗebe tausayin waɗansu mutane da ake son a halaka ga zukatan jama’a. Ana amfani da kalmar ga mutanen da suka ƙi miƙa wuya borin Turawa ya hau kansu. Ana liƙa kalmar ga jama’ar da ke ganin kasawar Demokraɗiyya ga kare haƙƙin ɗan Adam. Ana danna ta ga waɗanda ke ganin rashin ingancin dokar ta yi takin saƙa da dokokin Allah (SWT). Ana sarkafa ta ga mutanen da suka ƙi kafirce wa al’adunsu don na wasu. Ana kururuwa da kalmar ga masu ra’ayin cewa, dokokin Allah ba su tsufa. Ana tabbatar da kalmar ga wanda ya yi ramuwar gayya da hushi. Ana sarrafa kalmar ga wanda ke ganin in an ɗebi na dahuwa yana iya ɗibar na gashi ga ban maƙiyansa. Ana taliyon kalmar ga waɗanda ke ganin cewa, da wulaƙanci gara shahada. A wasu lokuta, an fi saka ta ga waɗanda suka ƙi yarda a yi musu dodorido da makamai a tarwatsa musu fahinta.
Idan muka sa idon natsuwa sosai muka duba, za mu ga cewa, a duniyarmu ta yau za mu ga akwai:
i. ‘Yan fafitikar neman ‘yancin kai daga duniyar Turawa da mamayarsu irin su Nelson Mandela da ya yi kusan share rabin ƙarni a gidan Yari, da mutanen Namibiya, da Zimbabuwe, amma ba a yi masu suna da ta’addaci ba.
ii. Masu fito na fito da gwamnatin da ke ci a ƙasarsu. Cikin fafitakarsu sun kashe talakawa da sarakuna da waƙilan hukuma irinsu Saro Wiwa na ƙabilar Igonni, amma ba a kira shi da sunan ba.
iii. Akwai ‘yan gani-kashenin siyasa da suka kai fagen kashe talakawa da masu mulki. A ƙasar nan, an sami waɗanda suka kashe Ministan Shari’a bisa ga irin aƙidarsu ta siyasa ba a kira su da sunan ba.
iv. Muna da ‘yan bangar kare gonakin gado da suka fito da sunan Samarin Nija Delta, sun kashe ‘yan gida, sun kashe baƙi, sun talauta ƙasa, sun kashe sojoji da ‘yan sanda bila adadin, amma sai tukuici aka yi musu da albashi mai tsoka ga kowane ƙato marashi aikin yi aka kuma buɗe musu ma’aikata tasu ta kansu, wai su ba ‘yan ta’adda ba ne! ‘Yan kare gundumarsu ta gado ne.

WANE NE D’AN TA’ADDA?


Masana addini sun aminta da tashin duniya kuma nassoshi sun inganta a kan cewa, lallai ranar Jumu’a za a sallame mu da aiki. Bincike ya nuna Jumu’ar ba ta da Assabar, sai dai sanin wace rana ce? An ‘boye muna. Duk da haka, daga cikin manyan-manyan alamominta akwai bayyanar ta’addanci a doron ƙasa. Fassarar ta’addanci a littattafan Shari’a yana banga-banga da fassarar Turawan mulkin kama-karya da ‘yan barandansu ‘yan bokon ƙarshen zamani. Mutanen da ke walawa da cin gajiyar ganimar duniya, da shan jinin moro, da tursasa wa marasa galihu, da maƙure mai ɗan ƙarfi, suna ganin duk abin da ke hana su miƙe ƙafafunsu, su baje kolinsu shi ne “ta’addanci”. Ban ga laifinsu ba, domin ƙolin tunaninsu daga duniya sai Abuja.
Idan ana biye da zaren tunanina, ta’addanci suna ne ƙirƙirarre na wannan ƙarni da ƙarya ke son ta yi garkuwa da shi ta yaƙi gaskiya. Tantance ɗan ta’adda a irin fassarar ‘yan bokon zamani yana da wuya saboda yaudarar da aka saka a ciki. Da dai za a tsaya a kalli kalmar da irin yanayinta da za a yi mata fassarar adalci a ce:
“Yin amfani da ƙarfi domin a turmuje mai ɗan ƙarfi, tare da bin kowace dabara ta rashin tausayi da keta haƙƙin bil Adam domin kai ga wata manufa da ake son a tilasta mutane su bi ta. D’an ta’adda shi ne, wanda ya fara takara, ya yi amfani da makamansa domin ya kai ga manufarsa. D’an ta’adda ba ya buƙatar zaman lafiya matuƙar ba a tsarinsa ba, kuma duk wurin da ya kafa tsarinsa da ta’addanci zai yi amfani ya rusa masu adawa da shi ya kare waɗanda suka bi.”

GANI YA KORI JI:


Na ƙirƙiro wannan ma’anar ta’addanci bayan na nazarci fassarorin da ‘yan boko ke ɗora ta’addaci a kai. A ganina, ba a iya gane ɗan ta’adda idan ba a bi silalen tarihi ba. A tsarin malaman usulu komai yana kan hukuncinsa matuƙar ba Shiri’a ta zo ta ɗora masa wani hukunci ba. Don haka, ƙasashen duniya duka lafiya lau suke zaune gabanin rigingimun ƙasashen yamma ya sunsune su. Tarihi ya tabbatar da cewa, ƙasashen Turai suka fara haihuwar ta’addanci suka rene shi, sai da ya zama samari sadauki suka aike shi sauran ƙasashen duniya don a san shi, ya san su. Wannan hasashen nawa, ana iya kallonsa da tubarau na tarihin duniya kaɗan daga ciki akwai:
i. Yaƙe-yaƙen da Turawan mulkin mallaka suka kai a ƙasashen Larabawa da Asiyawa da Afirka. Yaƙe-yaƙe ne na mamayar mutane a tilasta su, su bi dokar ƙasar da ba tasu ba. Su bi addinin da ba nasu ba. Su yarda da shugabanci da ba nasu ba. Su rungumi al’adun da ba nasu ba. Su rusa tsarin dokokinsu su bi waɗanda aka zo musu da ƙarfin soja, so da ƙi. Wanda ya miƙa wuya ya zama bawa, wanda ya ƙi ba da kai bori ya hau a kashe shi. Wane ta’addanci ya fi wannan a tarihin bil Adam?
ii. Mutanen da aka kashe, da waɗanda aka rataye, da waɗanda aka ƙona, da waɗanda aka sa cikin sahu, aka yi musu kisan takaici a ƙasar Libiya zamanin mulkin mallaka wa zai iya ƙididdige su? Haka aka yi wa Bagadaza sama ga Musulmi dubu ɗari biyu (200,000) aka kashe, aka ƙona litattafansu, wasu aka saka teku sai da ruwanta ya gurɓace halittun ciki suka mutu. K’asar Najad da Masar da Sudan duk sun ɗanɗani irin wannan ƙasaƙanci. Idan tarihi na da gurbi a bayanin ta’addanci, a fassarar ma’anar wannan, a ba masu aikin sunan da ya dace da su mu ji. Ai in maye ya manta mai ɗa ba ya manta ba.
iii. Mu waiwayi haɗaɗɗiyar daular Tanganyika an yi wa mata da yara da jinjirai da tsofaffi kisan kiyashi har sai da suka ari hauka domin su kakkaɓe wa tabarma kunya ƙura. Turawan mulkin mallaka sun kashe su har sai da suka gaji suka ajiye makamai domin su raga irin da za su taya su noma gonanki kakanninsu da iyayensu da aka kashe. Shahararru daga cikin yaƙe-yaƙen akwai Maji-maji da Mawo-mawo. Haka aka yi wa daulolin Bantu, aka karkashe ƙabilun Zulu aka kashe musu shuwagabanni Mzilikazi da Musheshe da Zwagendaba. Tsananin musibar bala’in kisan kai da ƙabilun Zulu ba su taɓa jin labari ba, balle su gani, shi ya sa suka kira zamanin Turawa Mfacane ma’ana; “zamanin bala’i da waba’i”. Kaico! Wai duk an yi wannan da nufin wayar da kan ƙauyawa in ji ‘yan mun waye.
iv. Idan muka waiwayi baya a nan cikin gida, laifin me daular Musulunci ta Sakkwato da Mujaddadi D’anfodiyo ya assasa ta yi? A yaƙin Giginya ba a iya ƙididdige shahidai. Aka je Burmi, aka yi kamar ba a yi wani abu a Giginya ba. Aka je Haɗeja aka yi kan mai uwa da wabi, fiye da mutum dubu goma sha biyar suka yi shahada. Ba a bar Satirawa baya ba, a 1906 su dubu goma aka ƙona cikin garinsu maza da mata yara da manya. Duk da tsananin wannan ta’asa, wai su ne ‘yan ta’adda. Haka kuma, an ƙone garin Raha da Bahindi da Kwantagora wai don a tauna tsakuwa a ba aya tsoro kawai. To! Tsakanin mai abu da marashi da ya zo da makamin yin ƙwace, wane ne ɗan ta’adda? Idan aka samu accakwama wa ya aikata ta’addanci?

Waɗannan musibu duka ba ‘yan gida suka jawo su ba. Baƙin haure da ke ganin, a ba manya fili ba don Allah ne ba. Wanda ya ƙi ba manya fili a ture shi ya faɗi a kashe, wanda ya ba da fili a bautar da shi na har abada. Wai, waɗannan kashe-kashe da babu tarihin da zai iya ƙididdige su an yi su ne da nufin neman wurin zama, da baje kolin sana’a, da kafa mulkin kama karya, da yaɗa addinin Yahudu da Nasara, da hana a ga tauraron kowa in ba nasu ba. A ganinka na ma’aboci hankali da wayo, wane suna ya fi dacewa da waɗannan mutane? Wa ya fara ta da zaune tsaye a duniyar bil Adam? Da wace hujja bunsuru zai hana wa akuya shan ƙasari?

NASON MIYAR JIYA GA SABON AKUSHI


D’an tsakuren da muka yi muke son mu daddage shi ga abubuwan da ke faruwa a duniyar ƙarninmu. Ga al’ada, kazar da aka yanka idan ta tashi cikin ɗaukar rai ta fi ban tsoro da firigirtawa da ban mamaki ga wanda ya yanka ta. Idan dai yana buƙatar cin namanta, idan ya kama ta ya danne, zai yi mata dannan takaici. Idan ya ga babu makawa sai ya sake yanka, zai yi mata yankan takaici sai ya raba kai da wuya. Irin haka ne yake faruwa a wannan ƙarni namu. A da, Turawan mulkin mallaka sun yi zaton sun gama da kowa. Don haka suka share wa jikokinsu wuri su zo su ci karensu ba babbaka. Da baya suka hango an yanka ta tashi, don haka jikokinsu na yau ke son su yi amfani da dabarun jiya domin su taushe kazar da kakanninsu suka yanke shekaranjiya.
Takaicin Yahudu da Nasara ga Musulmi na gado ne. Zama tare, da karatu tare, da auratayya, da maƙwabtaka, da boko, da demokraɗiyya, da buɗe ofisoshin jekadance, ba zai karkare shi ba. Bunƙasar addinin Musulunci ke ba su tsoro. Yawaitar malamai ke tayar musu da hankali. D’aukakar ƙasar da Musulunci ke shugabanci wani abin takaici ne a wajensu ko da kuwa bisa tsarinsu ya ɗora ƙasarsa. Yawaitar Musulmi a doron ƙasa ya fi gobarar gemu tashin hankali a wajensu. Don haka, duk hasarar da za su yi ta ganin an magance waɗannan abubuwa dole a bi ta, ba tare da ja da baya.
Na tabbata za ku gaskata ni, idan kuka tuna da Musulmi sama da dubu ɗari biyu tare da shugabansu Saddam Hussaini da aka kashe a ƙasar Iraƙi. Wa zai iya ƙididdige Musulmin da aka kashe a daular Musulunci ta Taliban, a ƙasar Afganistan? Dubi yadda aka rugurguza Musulmai da dukiyoyinsa a ƙasar Libiya? Aka sake biyo Musulman Egypt da baƙar yadiya don sun ce, a sa shari’a a tsarinsu na yanzu. Syria na cikin hayaƙi, an yi jinga da wasu mataulata su tayar da irin wannan fitinar a Saudi Arabia. Babu wata ƙasa da Musulmi za su yunƙuro da farfaɗo da addininsu face an yi musu taron dangi na ƙarfin soje an tarwatsa ƙasarsu, ko sun miƙa wuya ba a bari sai an ga baya ga shugabanninsu da malamansu da matansansu.
Abin ban haushi, hatta a fegen tsaron mutuncin ɗan Adam ba a ba mutane sarari ba. Ghana ta ƙi yarda da halasta kushili (luwaɗi) an jaye tallafin da ake ba ta. Zimbabuwe ta hukunta ɗan liwaɗi da ɗaurin gidan Yari, mai laifin ya ɗaukaka ƙara wata ƙasa ba tasa ba, Amurka ta tilasta a sake shi, kuma an sake shi tare da biyansa diyya, ba tare da an biya wanda ya yi wa luwaɗi diyya ba. Nijeriya ta ƙi sa wa dokar halasta luwaɗi da maɗigo hannu an ce, ta gyara dokarta ko a ɗebe ta cikin ƙasashe amintattu. Hausawa na cewa, sare-saren hauka zubar da yawu. Da jaye tallafi, sai a batse ƙasa, daga nan, sai a sa mata takunkumi, daga nan, sai kai mata sojojin tsaro, daga tsaro, sai tsokana, daga nan sai farmaki, don kare ra’ayin mutane ashirin a kashe mutum dubu ashirin. Wane suna ya fi cancanta da wannan salon Yahudu da Nasara na mamayar duniyar ƙarni na ashirin da ɗaya?

NIJERIYA INA AKA DOSA?


Ga alama ba a yi ƙasar da ta fi ƙasarmu zaman lafiya ba a faɗin duniyar jiya, mun yi suna ga kwnaciyar hankali, da lumana a nahiyar Afirka, yau abin na son ya sauya zani. A tarihi, al’ummar da ta fara wanzar da zaman lafiya a wannan ƙasar ita ce Musulmar al’ummar da aka riska da tsarin dokokinta na shari’a daidaitacciya. Ganin haka, Turawa suka ƙago muna mulkin “Shiga gaba in bi ka” (Indirect rule). A Kudu, aka ƙaga musu “Biyo ni a baya” (Direct rule). Dalilinsu a nan shi ne, sun tarar da Musulmi da tsarin da ba za a iya cire shi a kawo wanda ya fi shi ba, don haka dole a sa su gaba a bi su baya da baƙar yadiya. A Kudu, an tarar da su kara zube, dole aka yi musu jagora. Yaƙar daular Musulunci ta Sakkwato da aka yi da irin raddi mai gauni da suka sha a Sakkwato da Burmi da Haɗeja da Kwantagora da Satiru ya sa suke son sai sun mayar da raddi ko da bayan shekara dubu ne. Hanya mafi sauƙi a yau ita ce, a liƙa musu sunan ta’addanci a yaƙe su da shi, a kashe musu matasa da malamai sabon mulkin mallaka ya sake bayyana a Arewa. Ba daga waje aka yaƙe mu ba daga cikinmu aka yaƙe mu.

ZUBI DA TSARIN MUSULMIN NIJERIYA


Musulunci da ya shigo Nijeriya ba da yaƙe-yaƙe ko tsangwama ya zo ba, balle a ce, mun gaji abinmu. Wayewar Turai ta zo da faɗa, da yaƙi, da bauta, da zanga-zanga, don haka, fitina da tashin hankali a ko’ina ka gan shi baƙo ne cikin Musuluncin ɗan Nijeriya, ba a ba shi masauki ba balle ya shimfiɗa buzun zama.
A tarihance, Mazhabar Malikiyya ta fara ziyararmu, aƙidar Shi’a ta shigo ba ta samu karɓuwa ba ta rushe. Daga nan sai aƙidar Asha’ira ta biyo baya. K’adiryya ta zo, ba ta yawaita ƙwarai ba, Tijjaniyya ta zo ta karɓi tuta. Ana cikin wannan fafitikar Shi’a ta sake hudo kai da sabon salon na Mahajuba da Echo of Islam ana cikin wannan yanayi ƙungiyoyi irinsu Izala da Jama’atu suka ƙasura. Waɗannan ƙungiyoyin suka haifar da samarin Salafiyya masu ra’ayin ana iya yin tantagaryar addini irin wanda Manzo (SAW) ya yi, ba tare da an yi taƙalidanci da kowace mazhaba ko ɗariƙa ko ƙungiya ba. A yau, daga cikin waɗannan kashe-kashen wanda duk aka tsokana, aka hana masa ‘yancin addininsa, aka kashe masa malamai ko iyali ko mabiya, idan ya yi yunƙurin mayar da martani sai a sa masa sabon suna “Boko Haram”. Haɗarin da muke ciki shi ne, matuƙar ana son ɗebe tausayinka a zukatan Musulmin Nijeriya, a yi ma kisan gilla ko a yi ma ɗaurin rai-da-rai sai a ce maka ɗan “Boko Haram”. Shi ko wanda ba Musulmi ba da ya kai wa Masallatai da Coci hari, wane suna za a ba shi?

SUNA A FAGEN CIN ZARAFI


Idan ana son a gane a ina ta’addanci ya fito? Sai an bi tarihin yadda ake raɗa wa ɗaiɗaikun ƙungiyoyin Musulmin Nijeriya suna. A tarihi, magoya bayan ƙungiya ko mazhaba ba su ke ƙaga mata suna ba. Sunan na fitowa ne daga bakunan ‘yan adawa ko ‘yan jarida ko jahilai. Da wannan suna za a laɓe a yi ta kashe Musulmi har sai an ƙare mu gaba ɗaya bi-da-bi (Allah Ya kiyaye). Dga cikin misalan da zan bayar a nan sun haɗa da
a. Magoya bayan karantarwar Muhammad ibn AbdulWahab ‘yan Naƙshabandiyya suka sa musu Wahabiyawa. Ba su taɓa kiran kansu da sunan ba.
b. ‘Yan Mazhabar Malikiyya da Shafi’iyya da Hambaliyya da Hanafiyya da Zahiriyya, duk ba malaman da suka assasa mazhabar suka sa sunan ba. Malaman fahintocinsu suka fitar cikin gundarin nassi, ɗalibansu suka rungumi fahintar aka sa musu suna da fahintar malamansu.
c. Shehu Abdulƙadir Jelani da Shehu Tijjani ba su suka sa wa ɗariƙunsu suna ba. Abokan adawa da almajiransu suka sa sunan.
d. Muhammadu Marwa bai san da sunan “Maitatsine” ba ‘yan jarida da abokan hamayya suka sa sunan daga faɗar da yake yi “Allah Ya tsine wa maƙaryaci”.
e. ‘Yan ƙalaƙato ba su suka sa wa kansu sunan ba, daga faɗarsu ne na cewa “In an gabato aya babu sauran ƙala ƙato”. A nan, suna tsoratar da masu kawo nassoshin litattafai su gitta a kan nassin Alƙur’ani.
f. ‘Yan zando da K’ur’aniyyun duk suna ne da aka liƙa wa masu fahintar ba tare da saninsu ba, kuma galibi ba su yarda da sunan ba.

BOKO HARAM


Wannan ita ce ƙololuwar maganar da ake ciki a duniyarmu ta yau. Marigayi Malam Muhammadu Yusuf (Allah ya gafarta masa) bai kira da’awarsa suna Boko Haram ba, ɗalibansa ba su kira ta da wannan suna ba. Ni ina ganin ‘yan boko da boko ya zama wa dole, addini ya zama musu lalura, da su da ‘yan jaridar da ke son a turara hayaƙin rashin jituwa tsakaninsu da jama’a ke yi musu wannan suna. Gabanin a ci zarafinsu da wannan suna, ana ce da su “Ahalil Sunnah” kawai. Da baya wasu ‘yan adawa suke kiran su da Yusifiyya. Da suka yi wa aƙidojin boko na Yahudanci da Nasaranci hari gadan-gadan wanda ya tilasta wasu daga cikin masu da’awar barin aiki cikin gwamnati saboda gani babu wata hujja sahihiya da za a iya a tunkari Allah da ita idan an je gabanSa da Demokraɗiyya ko Gwannatin Tarayya suka yi murabus don ganin kansu. Ba a taɓa samun wurin da suka tilasta wani ya bar aikin gwamnati ba, ko ya bar boko, sai wanda ya gansu da hujjojinsu ya ɗauki fahintarsu. Duk da haka, ‘yan boko da ‘yan korensu suka bi su da suna Boko Haram.
A gaskiyar lamari, idan aka ce, al’amari boko gaba ɗaya halas ne an ci gyaran Alƙur’ani da wanda aka aiko da shi. Tun farko a dubi Tsarin Mulki, a dubi Dimukraɗiyya, a dubi fitar mata ‘yansanda, mata kwastan da soja da sauran ma’aikatan tsaro mata. A dubi mata masu aikin jinya da likita. A dubi cin hanci da rashawa. A dubi shugabancin mace da alƙalancinta, da dai sauransu. Me za a ce da su? Halas ko Haram? Me sunan wanda ya ba su suna ɗaya daga cikin sunayen da muka faɗa? Idan haka ne kuwa, ya zama tilas Musulmin Nijeriya su gaggauta zama su kalli wannan matsalar da idon adalci domin samun hanyar da za a samu zaman lafiya da juna. Wannan matsalar karatu ce ba ta amfani da ƙarfin bindiga ana kashe mutane ba.

IDAN BABU K’IRA ME YA CI GAWAYI?


Haƙiƙa hatta da masu mulkin ƙasa sun aminta da cewa tsaron ƙasa ya salwance. Akwai mamaki a ji shugaba da kansa ya yi iƙirarin cewa, akwai ‘yan ta’adda har a cikin gidansa kuma ya ayyana sunan waɗanda yake ce wa ‘yan ta’adda a bayyane. Wannan abin nazari ne sosai domin a gano ina ne salka ke tsatsa? Ana cikin wannan ruɗun wani ɗan siyasa ke cewa “Kodayake ba dukkanin Musulmi ne ‘yan ta’adda ba, amma dukkanin ‘yan ta’adda Musulmi ne.” Ko kusa ire-iren waɗannan lafuzza ba su dace ga ɗan siyasa ba, kowane irin addini yake biya. Ba a shugabanci da rashin ƙauna kuma ba a yin sa da rashin amincewa juna.
A tarihin Nijeriya, ba yau aka fara nuna wa Musulmi da Musulunci rashin gatanci ba. Matsalar Malam Muhammadu Marwa da aka yi amfani da ƙarfin soja ba a san adadin Musulmin da aka kashe a Kano ba. Aka sake yin irinta Bulunkutu a Maiduguri. Aka ƙara yin ta a ‘Yan’awaki a Kano. Idan an ce waɗannan an tsokane su sun rama ko suna da makamai, to su na Darus Salam na jihar Neja wa suka tsokana? Wane makami aka kama gare su? Da wace hujja hukuma ta tozarta su? An yi wa ‘yan Izala irin wannan cin zarafi da mutunci tun farko-farkon fitowarsu a ko’ina. ‘Yan Tijjaniyya ba su kuɓuta ga muzgunawar hukuma ba a Sakkwato da K’aurar Namoda da Gusau da Mungadi da Jega ga su nan dai. Wane makami aka kama gare su?
Babu shakka, waɗannan fitinu da rigingimu akwai masu tayar da su? Dole a wasu wurare a samu rahoton ƙarya, irin wanda Amerika ta yi amfani da shi ta rusa Iraƙi da Taliban a Afganistan. A wasu lokuta kuwa, a samu wakilan tsaro ke tsokanar tsuliyar dodo don sun ga bakin wuta a hannunsu yake. Ba zan musunta a samu siyasa a ciki ba, domin ɗan siyasa na iya shiga kowane rango na biyan buƙatarsa. Haka kuma, akwai laifin Musulmi su kansu na rashin haɗin kai, da kuma adawar da ke tsakaninsu sun yi ƙawance da hukuma domin a musgunawa abokan saɓanin fahintarsu. K’arancin Ilimi ga masu biya da son shugabanci ga masu wa’azi wani makamin jawo wa Musulmi fitina ne tsakaninsu har hukuma ta shigo ta yi musu kan mai uwa da wabi.

DA LAUJE CIKIN NAD’I


Duk wani kewaye-kewaye da za a yi na a goga wa Musulmi kashin kaji ga rigingimu da ke aukuwa a yau ba zai ci nasara ba domin:
i. An samu hannun waɗanda ba Musulmi ba tsamo-tsamo a cikin ƙone-ƙonen wurin ibadojin Kirista. To! A nan, me za a ce ga wanda ba Musulmi ba cikin kayan Musulmi ya aikata ta’addanci domin a ce Musulmi ne suka yi?
ii. Ire-iren makaman da ake sarrafawa sun fi ƙarfin a ce, wasu ‘yan ɗaiɗaikun mutane ne ke da hannu. Wanda ke cikin talauci, ina zai sami kuɗin sayen makamin da zai saya masa abincin shekara goma?
iii. Rahotannin da kafofin yaɗa labarai ke yawaita ambato na makaman da ake kamawa, musamman waɗanda aka sa shari’arsu a Ingila (yanzu) da waɗanda aka kama Ghana da Borno da makamantansu ba a bayyana masu su ba balle a san dabarun da za a ɗauka na zaman lafiya.

ME YA KAI MU A WANNAN HALI?


Wannan shi ne zuciyar abin da nake son in yi hasashe a ɗan bayanina. Yau mun shiga halin da kowa na buƙatar zaman lafiya. Don haka wasu ƙasashe na son su samu damar shigowa cikinmu ƙasarmu ta shiga wani hali. Babban abin da ya kawo mu a wannan hali shi ne:
i. Kisan gillan da wakilan tsaro ke yi wa shugabannin addini da masu addini a bayyane ba tare da an je kotu ba an tantance maras gaskiya. Ta yaya almajirai da muridai da mabiya da surukai da ‘yan’uwa da Musulmi za su yafe wa wanda ko waɗanda suka yi wa magabatansu kisan gilla na wulaƙanci da tozartaswa? Aikin hukuma ne ta lalabo waɗanda suka yi wannan aiki ta barranta kanta da aikin ta kai su kotu a hukunta su, a san ba da yawun hukuma suke kashe mutane ba. Idan hukuma ba ta ɗauki matakan hukunta masu laifi ba, kamar tana koya wa waɗanda aka zalunta ta’addanci ne. Kisan gillan da aka yi wa Malam Jafar a Kano da Muhammadu Yusuf a Maiduguri da D’anmaishiyya a Sakkwato (Allah ya gafarta musu), sun isa su zama abin misali a kan haka. Hukuma ta yi shiru kamar an aiki bawa garinsu. Me ake zato ga ‘yan’uwan mamatan?
ii. Rinjayar da aka yi wa wani addini cikin ma’aikatan tsaron ƙasa ya sa a koyaushe ake samun ire-iren waɗannan matsaloli. Wakilan tsaro wasu na amfani da su wajen kare addininsu. Don haka, addinin da duk aka fi yawa a cikin wakilan tsaron a koyaushe shi ne mai laifi, shi ake kawo ƙararsa a koyaushe, har sai an sa mai kai an cuta masa da sunan rahoton ƙarya. Wannan haƙƙin hukuma ne ta yi adalci a kan tsarin ɗaukar ma’aiktanta.
iii. Wakilcin galihu da alfarma da danniya na zaɓen shugabannin siyasa na ɗaya daga cikin mafarin yin haka. Da za a samu ‘yan siyasa ko da rubabi-rubabi ne waɗanda suka san addininsu da ƙasarsu da al’adunsu dole a yi wankin ɗa kanoma mashaya a kan kowace matsala da ta shafi ‘yan ƙasa. Matuƙar masarautu da ƙungiyoyin sa kai da jam’iyyun siyasa ke da babbar murya a zaɓen shugabannimu, muna da aiki baya, an bar kyau tun ranar haihuwa.
iv. Rinjayar da aƙidoji da dokokin wani addini a ƙasar da aka ce ta gamin gambiza ce, shi ke haifar da ta’addanci. Idan ƙasar gamin gambiza ce, to tsarinta gaba ɗaya ya zama gamin gambiza ba irin kashin dankali ba manya-manya su taushe ƙanana. A ce, kowane shugaba ya hau da tsarin addininsa za a yi aiki ko ba a faɗa a rubuce ba, a aikace an tabbatar. Waɗannan abubuwan ke sa masu kishin addnin da ba irin na shugaba ba, su ga gara komi ta banjama banjam! Da za a ɗora Nijeriya da tsarinta a kan sikelin addinin Musulunci ko Kiristanci ko makaho ya laluba ya san an ƙwari wani addini. K’in gyara wannan shi ke sa waɗanda ake shugabanta su kasa haƙurin walaƙanci, su da ƙasarsu a mayar da su bayi. Dole wannan ya haifar da saɓani a ƙasa hukuma ta fassara shi da sunan “ta’addanci.”
v. Burin wasu marasa kishin ƙasa da addini da sanin ya kamata na a raba ƙasar nan, su ci moriyar arzikin ‘bangarensu. Wasu na ganin kamar da arzikin da ke yankinsu ne aka gina Nijeriya. Bayan an fifita su ga rabon arziki wanda yake kure ne. Aka buɗe musu ma’aikatun tarayya na kansu cikin kuskure. Aka yanka musu albashin zauna-gari-banza mai tsoka ga matasansu marasa ilimi da aikin yi. Wataƙila ganin irin tsoronsu da ake ji, da reno na musamman da suke samu daga cikin gajiyar arzikin tarayya, wanda babu wani yanki na ƙasar nan da ya taɓa samun irin wannan gata, shi ya sa suke burin a dai raba ƙasa, a yanka musu tasu ƙasa, su gargaɗi baƙin haure daga yankunansu. Da yake ba addinin Musulunci suke yi ba, ba ‘yan ta’adda ba ne, samarin neman ‘yanci ne.
vi. Burin da wasu maƙiya Nijeriya ke yi na ta sake shiga yaƙin basasa domin su samu shigowa ciki su tarwatsa jama’arta da tattalin arzikinta ya kyautu a Harare shi. Tuni sun barbaza a kafafen yaɗa labarai na duniya cewa, a shekarar 2015 Nijeriya za ta barkace ta warwatse ta rarraba. Yanzu kuma sun gurgusa shi zuwa shekarar 2030 bayan an gama da mu duka. Da suka ga hasashensu ya ƙarato, abubuwan da suke son su wakana, ba su wakana ba. Waɗanda ake zaton su fito su yi aikin, wasu sun mutu, wasu sun kasa, wasu ba a yi da su, wasu an gane su, wasu sun ji tsoro sun tuba, daga nan sai bakin zaren hasashen lisafinsu ya ‘bata suka fito da sabon salon na yaƙi da ta’addanci a jiohohin Arewa da maƙiyansu suke.
vii. Cin hanci da rashawa da handama da babakere da shugabanni ke yi ya taka rawar gani na fitinun da ke wakana a yau. Yau arzikin ƙasa duka na masu mulki ne, wanda ba ya da mulki sai dai ya mutu. An mayar da matasa ‘yan ta’adda, an ba su makamai da tsaro domin su aikata abubuwan da ƙungiyoyin siyasarsu ke so. An mayar da malamai maroƙa. Sarakai sun zamo fadawa. An mayar da maza mata, mata sun koma maza. An cusa yunwa cikin talakawa, an ba masu arziki tsaro. An mayar da managarta lalatattu, lalatattu an mayar da su bayi. Waɗannan abubuwa duka cin hanci da rashawa ya haifar da su. Don haka, yau an kai mutane bango ko ba su bin kowane irin addini za su yi fito-na-fito da hukuma da ‘yan barandarta ko da za su yi hasarar rayukansu. Idan aka ƙi duban tashin hankali da ke aukuwa a Nijeriya ta wannan fuska an cuci ‘yan Nijeriya. Yaya za a ilmantar da matasa su rasa aikin yi, a hana su shiga wani hali? Ta yaya za a bar matasa babu ilimi babu abinci a hana su ƙunar Baƙin Wake ga kai ka muradinsu? Yaya za a tura talaka a bango, ba arziki, ba lafiya, babu abinci, babu matsagunni, babu tsaro, babu kulawa, babu kare haƙƙi, ba a sa ranar gyara ba, ya fito da gora don ya gyara a ce masa Boko Haram? Idan aka bi wannan fassarar wane ne ba ɗan Boko Haram ba a Nijeriya?
viii. Ina daga cikin masu ra’ayin cewa, babu Boko Haram. Wani samfarin yaƙi da Musulunci ne aka ƙirƙiro bayan da aka ƙirƙiro ciyon ƙanjamau na rage yawan jama’a a duniya musamman na Musulmi da suka ƙi yarda da ƙayyaje iyali na ba gaira ba saba. An ƙirƙiro Boko Haram ne, domin a tabbatar da an kawar da duk wani mai kishin addini da buƙatar ci gabansa. Martanin da ake zargin ‘yan Boko Haram suna kai an fara gano ba ma Musulmi ne ke kai shi ba. Waɗanda ke magana da yawun Boko Haram an gano ‘yan jeka-na-yi-ka ne da ake son a laɓe gare su a kashe Musulmi. Zargin da ake yi musu na haranta Boko an gano mafi yawansu ‘yan boko ne, wasu ‘ya’yansu na boko ga su nan dai. Ala tilas Musulmi su yi zama na musamman a kowace jiha cikin ƙasar nan a fuskanci wannan al’amari tun ba a ƙare mu cikin guguwar siyasa ba. Ba za mu yarda wani ya liƙa muna sunan da ba namu ba don ya kashe mu ya raya jama’arsa.

SAKAMAKON BINCIKE:


A fahintata hukuma da kafafen yaɗa labarai na cikin gida da na waje ba su taimaka wa ‘yan Nijeriya wajen samar musu zaman lafiya da lumana ba. A ‘bangaren ma’akatan hukuma wasu ƙabilarsu suke yi wa aiki. Wasu addininsu suke yi wa aiki. Wasu yankinsu suke yi wa aiki. Wasu ƙungiyoyinsu suke yi wa aiki. Wasu son ransu suke yi wa aiki. Wasu aljihunsu suke yi wa aiki. Wasu siyasarsu suke yi wa aiki. Waɗannan su suka taru suka yi ma’aikatan tsaro da farar hula da masu gudanar da mulkin ƙasarmu. Ta yaya za a samu zaman lafiya da haɗin kai alhali kowa da fuskar da ya kalla irin zaman ‘yan marina? Yaya za a yi wanda ke da ƙiyayya da wani addini a tura shi da makami ya kwantar da tarzomar ma’abota addinin da yake ƙiyayya, bai yi wa addininsa aiki ba? Yaya za a tura ɗan PDP sulhun auren ɗan CPC a ci nasara? A kan wannan tunani nake cewa
i. Idan dai da’awar hukuma da ‘yan jarida na danganta musibun da ke aukuwa a Nijeriya ta yau ga Musulmi wai Boko Haram! To, ai a Kudu can boko ya yanke cibi me ya sa ba a samu hare-harensu a can ba?
ii. Idan dai tabbas ne manufar Boko Haram a daina boko, yaya aka yi ba su kai hari a makarantun boko da ake haihuwar ‘yan boko ba?
iii. Kai! Hankalin tuwo ya isa ya yi hukunci manufa ita ce, ana son tarwatsa mu, a rage muna ƙarfi, a rage muna yawa gabanin a zauna teburin raba ƙasa da wasu ke da’awar a yi. Idan haka ne kuwa, ya kamata mu kama kanmu tun dare bai yi ba.
iv. Masu hangen nesa na ganin, da halastar da Luwaɗi da Maɗigo aka fara taya wa mahukuntar ƙasarmu. Da suka ƙi tayawa aka ƙago Boko Haram.
v. ‘Yancin mata na ƙarya da haranta auren mace ƙasa ga shekara 18 da tilasta wa mata boko da tilasta shugabancin mace da tabbatar da gado ga shege kaɗan ne daga cikin abubuwa da aka so a yi amfani da su a murƙushe mu. Da abin ya ci tura aka ba mu suna na dabam.

MAFITA


Ga zatona ko ban faɗa ba muna iya kirdadon mafita da kanmu. Ina ganin K’ungiyar Izala ta fara yada muna fitila. Idan muka yi koyi da tsarinta za mu gane ina ta’addanci yake. Mu taru mu duka kamar yadda Mazhabobinmu ba su hana mu salla wuri ɗaya ba, ba su hana mu son juna ba da yi wa juna ɗa’a da fatar alheri. Da yardar Allah ƙungiyoyinmu da ɗariƙoƙinmu ba za su hana mu zama abu ɗaya ba mu tunkari abin da ke tunkararmu. Duniya ba a taɓa samun wurin da ma’abota addini suka samu fahinta iri ɗaya ba, amma kuma su zama abu ɗaya a muryoyinsu da manufofinsu. Maganin wannan kawai gaggauta taro na dukkanin wanda abin ya shafa a yi zama na musamman na ganin an kai ƙarshen kowace irin fitina da sunan addini a Nijeriya. Ku tuna, a Kaduna ga zanga-zangar tsadar man fetur Musulmi da Kirista aka haɗe kai wuri ɗaya, Kirista ke gadin Musulmi idan lokacin salla ya yi, sai sun ƙare salla a ci gaba. To! Da aka yi haka ai ba a ji rahoton ‘yan Boko Haram ko jami’an tsaro sun kashe kowa ba. Wasu jahohi da ba a yi haka ba, yaya aka yi? Ban ga laifin shugaba ba idan ya ce cikin jami’an tsaro da wakilan hukuma Boko Haram suke, mun ko ga alama a Kaduna. Madalla da wannan haske. A hasashen shugabanmu Bobo Haram gamin gimbizar Musulmi ne da Kiristan Nijeriya su ne ma’aikatan ƙasa. To! In haka ne don me a jihohin Musulmi kawai ake kai hari da jami’an tsaro ana kashe Musulmai?

NADEWA

Shugabannin addinin da Sarakuna su daina suɓul da baka idan aka aikata wani ta’addanci aka jingina ga jama’arsu. Tabbas! Abubuwan da ke aukuwa a Nijeriya a yau na ta’addanci ba Musulmi ke aikata su ba. Yayatawar da ‘yan jarida ke yi na alhakin wasu ayyukkan ta’addanci ga wasu mutane bai isa a yi aiki da shi a kama kashe mutane ana tsare su ba, domin babu dasisar da maƙiya ba su yi wa Musulunci. Tursasa Musulmi da ake sa wakilan tsaro da ba Musulmi ba na yi wani ƙaramin ta’addanci ne mai sa ƙiliu ta tono balau!

www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

Post your comment or ask a question.