Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Waya: 0803 431 6508
KibƊau: mabunza@yahoo.com
Tarihi: 13/01/2013, Kano, BUK
1. Ya mai rahama da tausayi ya mai jinƙai,
Ya mai ikon da babu mai kai ga irinai,
Kai ka yi kurma kaza makafi da kutare.
2. Kai ka yi mata maza ƙanana
da manyansu,
Kai ka yi mai hankali taɓaɓɓu naƙasassu,
Ka yo mai ji da wanda sai ya yi mamare.
3. Kai kay yi garinmu Bunza, Zogirma da Tilli,
Kay yo Digi, Gayi, Kalgo ga Jega da jalli,
Kay yo Yarawal da ƙeta
Kay yo Mutuɓare.
4. Roƙon da nikai gare ka Ka
san niyata,
Tanzanko nai nufi ga tsarin waƙata,
Kan babban malaminmu Bellon Mutuɓare.
5. Allah Kai kay yi Bello Kai kag ƙaga shi,
Kai mishi baiwa mudarrasi ga shi matashi,
Yaz zama wata ɗaukaka ga sunan Mutuɓare.
6. Kai masa naci ƙididdigan
gane karatu,
Ba alfahari ba Bello ya gane rubutu,
Mai li’irabin fashin baƙi
ɗan
Mutuɓare.
7. Zancen Fuƙaha’u
Bello ka san sirrinsa,
Tun ga Iziyya Mudawwana can ƙolinsa,
Ka darzaje su gwargwado babu marare.
8. Ka san Shu’ara wajen Luga ka zan babba,
Zancen nahawunka gwargwado ba mu ɗeɓe ba,
Ba ka da malam a Bunza balle Mutuɓare.
9. In an zo gun fashin baƙi,
kai ne Shago,
Ko an sa hasada, a ce maka Gojirgo,
Nassin aya ka feɗe nassi jejjere.
https://www.amsoshi.com/2017/09/27/kaska-wakar-farfesa-aliyu-muhammad-bunza/
10. ɗalibbai mui rashi haƙiƙan kuma babba,
Mun rasa mai ba da lokacinai a yi kwamba,
Ai ta karatu, ana ibada tattare.
11. Mun rasa Malam talakka bakin halinmu,
Mai ɓoye kurakuranmu don
tsananin sonmu,
Bai katsalandan, bale shi sheƙo
a ci tare.
12. Kowa aɗ ɗalibin
sani birnin Bunza,
Yai kuka ya yi jan ido ya mummurza,
Dole hawaye zuba walau an shasshare.
13. Ni kukana guda rashin in tar da ka,
Ko dai a gadon da kam mace in iske ka,
Ko ai sutura gare ka in fesa turare.
14. Kaicona! Sai cikin waya muka yin zance,
Har yau in na tuna da muryarka a kwance,
ƙirjina zan ji ko’ina ya ɗaɗɗaure.
15. Kwancin jinya ga mumini fa ibada ne,
Ciwo sanadinsa, ko’ina daga Allah ne,
Ga annoba zama guda a wuce tare.
16. Roƙon da nikai gare Ka, ya
Sarkin jinƙai,
Na yarda da yin Ka, wanga bawa Ka ɗaukai,
Roƙon rahama mukai ga Bellon
Mutuɓare.
17. Ka fi mu saninsa hakaza da ayyukansa,
ɗan namu sani zama da shi ga aƙidarsa,
Ba bidi’a babu shirka, gun ɗan Mutuɓare.
18. Mun san ba tsegamu, da giba, ba cuta,
Ba shi siyasa, bale a sa masa laɓonta,
Bai sha’awar ratsa godaben ga na Gulmare.
19. Shaidar ga da mun ka yo, saninmu da shi ke nan,
Kai ko Ka san abinka ko bayan sannan,
Mu dai rahamarKa ɗai muka daɗa
saurare.
20. Gafarta mai kurakuransa da Kas shaida,
Manyansu da ‘yan ƙanana
duk sai Ka yarda,
Ya Algaffaru gun Ka ne za mu kwarare.
21. Ya Algaffaru ceci malam gafartai,
In so samu, a kai shi can inda Sahabbai,
Duk bai da wuya gare Ka, shi muka saurare.
22. Na sa son kai Ilahu ni ma a saka ni,
Ba ni da zaɓi ga ko’ina
aka raɓa ni,
ɗan Modiɓɓere kana ga ɗan
Mutuɓare.
23. Duk mai roƙonKa
Rabbana bai taɓewa,
Mai tauhidin saninKa shi ke roƙawa,
In ka yafe, kurakurai sai su tarare.
24. Roƙon da mukai wajenKa Bello
ya zan babba,
In Ka yafe shi, an gama, ba wai ne ba,
Dole sikeli ya bar khaɗaaya su zurare.
25. Son rai ka rufe sani ya sa bawa hauka,
Har ka yi gaba da wane, wai kar ya wuce ka,
Ustazawa ana faɗa har da taɓare.
26. In mai raba gardama ta zo, an kai ƙarshe,
Sauraren tamu dole ne, ga mu a tarshe,
Sai zare ido kamar ruwa sun ci kutare.
27. Wagga hasara ta Bello babban giɓi na,
Ya zama walle ga Bunza hat ta gurfana,
Ga ɗalibban sani ido ya
daddare.
28. Malam ɗan Ghana, Bello Allah Ya
riƙa ma,
Duk wani tsoro da fargabanka, Ya yaye ma,
In ga kana murmushi, haƙoranka
farare.
29. Allah Ya yi ma rabo da Firdausi shi sa ka,
Ni ko bisa ƙaddara Alu in iske ka,
Karya kumallonmu, kullu yaumin mu yi tare.
30. Me zan wa Bello ban da roƙa
mishi wannan,
Bai aje komai ba, ban da ilimi shi ke nan,
Kwas shiga kabari da ilmu ba shi zama bare.
31. Mai marsiya Aliyu jikan Inta ne,
Baban su Imamu Hali, in ga kwatanci ne,
Hali yai canjaras da Bellon Mutuɓare.
32. Ga hoton Bello mai buƙatar
siffatai,
Jajir yake ko Bala Fari bai tsere mai,
Bai da tsawo ko kaɗan Muhammadun Mutuɓare.
33. Ya ɗara Liman Alu fari, don a
kiyaye,
Liman ɗandauda, gun tsawo sun ka
kuranye,
ɗanmarina ga ɗammaha tsawonsu ya zo
tare.
34. Mamman ɗan’audi, ko a ce Usman
Arbi,
Ko ɗan Sala Papa gun tsawo in
kad dubi,
Ko Malam Buba dut tsawonsu a jejjere.
35. Ya ɗara welkom fari ga tsarin
fatatai,
Shi Bellon Maidihimi kowa yad dubai,
Can ga wushirya kamar Muhammadu Mutuɓare.
36. Amma ga zubin jiki da ƙirar
ƙassansa,
ƙara da farin jiki da aukin namansa,
An ce, tangam sukai da shi, da Alu Sure.
37. Tammat roƙon da nay yi Rabbu Ya karɓa min,
Mai sauraro da mai karatu ce Amin!
Allah yafe ni, ni da Bellon Mutuɓare.
2 Comments
Allah shi biyya Aliyu Muhammadu Bunza,
ReplyDeleteYajjikan Shi ko Malamin Mutubare,
Amin,amin don isar shi (saw) Maceci,
Annabin mu Babba......
abin bidar kowannen mu.
Amin malam. Mun gode.
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.