LALURAR KI'DA A BAKIN MAKA'DA
(Hasashen ďaliban Al’ada ga Makomar WaƘoƘin Baka)


DAGA


ALIYU MUHAMMADU BUNZA
SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA,
JAMI’AR USMANU ďANFODIYO SAKKWATO
mabunza@yahoo.com 0803 431 6508

TSAKURE


An yi bincike abin a zo a gani a kan makaďa da mawaƘan Ƙasar
Hausa. Ni a nawa sani babu wani fanni na Hausa da ya samu
tagomashin bincike kamar na waƘa. A iya sanina an gabatar da fiye da
kundayen digirin PhD 16 na fannonin waƘa daban-daban da kundayen
MA fiye da 50 amma babu wanda ya himmatu ga ƘwaƘwalo tunanin
makaďa a kan kiďa da waƘa. Ganin haka, wannan ďan bincike ya taƂo
mawaƘan baka 11 domin ya ji ta bakinsu. An ciro ďiyan waƘa 17 daga
bakunan makaďan da suka furta matsayin kiďa a wajensu. An raba
wannan nazari zuwa sassa 13 domin a bayyana ma’anonin matanonin
ďiyan waƘar da aka kafa hujja da su. A wajen makaďan Hausa
musamman ‘yan shige/haye kiďa wata Ƙaddara ce da ta riske su. A
Ƃangare ďaya kuwa, waďanda suka gada burinsu su aje su tuba. An
gano abubuwa bakwai da ke sa makaďi ya aje kiďa ya tuba. Ga alama,
nan gaba kaďan, Hausa za ta yi hasarar fitattun makaďan gargajiya ta
fuskar tsufa, tuba da mutuwa. Da za a taskace ayyukkan fitattun
makaďa tun dare bai yi ba, da an huta da ďirkaniya mota cikin randa.

GABATARWA


Babu wata al’ummar duniya ta za ta yi bugun gaba da cewa, da saukakken
addininta ta samu kanta. Bayan da aka zauni Ƙasa, aka miƘe Ƙafafu, aka more wa
Ƙuruciya, da yaranta, da tsufa, da zamani, saukakkin addinai suka riski ďan Adam.
Gabanin su, mutane sake suke ba Ƙaidi, bakin gudunka bakin ladarka.Bayyanar
addinai ya zo da rarrabe al’adu miyagu, da na gari, da yardaddu, da harantattu.
Bahaushe na daga cikin al’ummar da wannan guguwar ba ta tsallake ba. Gabanin
hasken saukakkin addinai a Ƙasar Hausa, addinan gargajiya ke jagorantar
zamantakewa. Cikin addinan da al’adun, kiďa da rawa da waƘa wasu sinadaran
rayar da al’umma ne. Ai don haka Bahaushe ke ce wa makaďa: “Makaďa ran gari”.
Da ba don kiďa ba da gari ya watse, a bar kangayen gidaje. Duk da yake ko bayan
da musulunci ya miƘe Ƙafafunsa Ƙasar Hausa ba a daina kiďa ba, amma ana
kallonsa wata lalura ta daban.

KI'DA A MA’AUNIN BAHAUSHE JIYA


Manufata da jiya shi ne, jiya mai nisa tun gabanin Bahaushe ya sunsuni
addinin littafe. Gobe a ma’aunin manazarta al’ada tana ďaukar ma’anar ranar
haďuwar bawa da mahillicinsa. Idan kuwa suka ce, “Yau”, to zamani ne mai tsawo
daga yanzu da muke magana har zuwa ranar da za a kwanta kushewa. Don haka, a
jiyar Bahaushe kiďa babbar sana’a ce da ta keƂanta ga gidaje na musamman da
suke taskace tarihin al’umma. A jiya, makaďa a Ƙasar Hausa mutane ne zaƂaƂƂu,
fitattu, Ƙwararru kuma amintattun al’umma da koyaushe ake kishin kare su da
martabarsu. Makaďi ba Ƙyalle ba ne a ko’ina yake zaune a garin Bahaushe. In ba su
ba gari, in kuma sun yi yawa gari ya haƂaka. Garin da ba makaďi matacce ne,

kurman gari ne mutanensa ba su da wata alfarma ta dole da maƘwabtansu za su sa
masu hannu. Bukukuwan matakan rayuwar Bahaushe uku, aure, haihuwa da
mutuwa kiďa ne gishirin haďa su.
A tsarin rayuwar jiya ta Bahaushe tsaron Ƙasa da kiďa yake tafiya, don haka
ake da kiďin yaƘi da kiďin tauri. Siyasar Ƙasa, kiďa ke fitar da amonta da
martabarta, don haka ake da makaďan fada. Tattalin arzikin Ƙasa kiďa ke inganta
shi, don haka ake da makaďan noma, farauta, Ƙira, fawa, su, da sauransu. Walwala
da sakewa kiďi ke kyautata su, kiďin gambara da gumbe da zari sun isa misali.
Addinin kansa da kiďa ake aiwatar da shi bisa ga amon goge da garaya da Ƙwarya.
Sadarwa ta cikin gida da unguwa da gari, da gari da gari, kiďa ke taka rawar gani ta
fuskar tambari da Ƙaho da kuge da gwarje da makamantansu. A Ƙasar Hausa ta
jiya, babu wata rawa da za a taka ba da makaďa ba. Don haka nake ganin kiďa wata
lalura ce babba da Bahaushe ya samu kansa cikinta wadda ta yi masa tarnaƘi a
rayuwarsa.

KI'DA A SIKELIN YAU NA BAHAUSHE


Yau ta Bahaushe ta Ƙunshi abubuwa masu yawa. A taƘaice, tana ďaukar,
bayan saduwar Bahaushe da wasu al’ummomi da can da bai san su ba. Bayan
saduwar Bahaushe da saukakkin addinai. Bayan fitar Bahaushe Ƙangin mulkin
mallaka. Bayan da addinin musulunci ya zauni Ƙasar Hausa ba zama na tsangwama
ba. Na so in ba da Ƙarfi ga bayanina na Ƙarshe, wato addinin musulunci da
Bahaushen yau.
ShaƘuwar da Bahaushe ya yi wa addinin musulunci ba ‘yar kaďan ba ce. Irin
kamun kai na nisantar Ƙarya da sharholiya da masha’a da kare mutunci da martabar
kai da ta zuriya da ta waďanda ke ƘarƘashinsa, kiďa bai tazarar shiga a wurin. Da
yawa daga cikin kaďe-kaďen Bahaushe musulunci ya saka su ciki tarkacen

hululuwa na tsallake dokokin iyakokin addini. Da sannu, makaďan da suka rage da
wannan ďan hayaƘin, da suka rungumi musulunci suka aske kiďa suka tuba suka
kama hanyar karatu kai tsaye. Waďanda ba su tuba ba shari’a ta hana su miƘe
Ƙafafunsu irin na jahiliyyar farko. Duk da yake shari’a ta kau da kai ga wasu kaďekaďe,
irinsu kaďa dundufa don bukin aure ko kiďin yaƘi. Haka kuma, wasu
musulmi suka shigo da kiďa a wuraren aiwatar da ibadojinsu kamar kiďin mandiri
da ire-iren su. Wannan duk bai sa makaďa suka yi watsi da fassarar farko ba,
domin sun san da kiďa wani abin kai gida ne da Annabawa Allah zai fara umurta
da shi. Da wannan hujja ce wasu makaďa suka fara tunanin tuba daga kiďa/kiďi.

ƘUNSHIYAR KI'DA


Kiďa sauti ne mai jan hanakali da yin gangami a zo a sheƘe aya. Ya fi
burgewa idan an haďa shi da rawa da ihe-ihe. Ya fi Ƙawata fage idan an haďa mata
da maza. Yana da jan hankali idan ana tafiyar da shi a waƘa. Idan ya kankama da
makaďa da ‘yan rawa sukan fita hayyacin kansu, musamman idan kiďin bori ne da
noma da farauta da tauri da Ƙira da su da sarauta. Kirare-kiraren da ke cikinsa da
masu yin kiďa da wanda ake yi wa kiďa da na sanƘira cike suke da turnuƘun
maguzanci na sauran danshen addinan jiya na gargajiya da ke nesa-da-nesa da
aƘidojin musulunci. Gaskiyar Bala Ganďo da ke cewa:
Jagora: Kiďan duma farauta
:Goge ka kiďan bori
:Dum mai salati
:Garkan Malam yaka komawa
Gindi: Ba a gane manya
:Sai ci ya samu

Ta tabbata cewa, kiďa ka tayar da tuban arne domin Ƙunshiyarsa cike yake
da zuga da washi da salon ingiza mai kantu ruwa mai haddasa santsi da Ƃarin baki
daidai yadda ďan’anace ke gaya wa Shago:

Jagora: Wandara in kana biyat ta kiďina
:Wallai ina halaka ka
:Sai na kai ka inda ba ka hitowa
Yara: Sai mu rage kiďi mu sassauta mai
:Don kar ya haukace baki ďai

Waďannan rubabi-rubabin zantuka da ke kai mai furta su, da wanda ake yi
wa su, da mai sauraren su ga da-na-sani su ne haďarin kiďa ga aƘidar addinin
Bahaushe na yau “musulunci”.
A hasashen Bahaushe, kowa na iya ya yi waƘa kamar yadda kowa na iya ya
zama mawaƘi. WaƘar ba ta fi damuwar Bahaushe ba kamar kiďa. Wannan shi ne
dalilin da ya sa idan mawaƘi/makaďi ya tuba, akan ce: “Ya tuba da kiďa”. Ida ana
son a fayyace sana’arsa akan ce: “Ai makaďi ne” domin kiďin ya fi fice da wuya a
ce, “Ai mawaƘi ne”. MawaƘi na iya ya kasance malami masani, amma makaďi da
wuya a same shi haka domin kiďa bai dace ga malami ba.

LALURAR KI'DA


Hausa gabanin karƂar addinin musulunci idan wani na aikata wani aikin da
shi kansa ya san ba ya son aikata shi, sukan kira irin wannan da sunan “kaya”.
Wani lokaci su ce, ya zama ‘alaƘaƘai’. Da musulunci ya zo, kalmar “lalura” ta
maye gurbinsu. Idan Bahaushen yau ya yi amfani da kalmar ‘lalura’ yana nufin abu
kamar dole-dole, ga shi ba a son aikatawa kuma ba a daina aikatawa ba. Idan mai
aikata abin ya kai ga faďar abin a bayyane cewa, ya damu da abin, ko yana son ya
daina abin ko bai gaji abin ba ga uwa bale uba, da rana tsaka Ƙadara ta riske shi,

abin ya zama “lalura”. Wannan nazarin na ganin haka sha’anin waƘa yake ga mafi
yawan mawaƘan Hausa.
A ďan binciken da na yi, da hirar da na yi da wasu mawaƘan Hausa, da hirar
da na ji ana yi da su, ko aka gaya mini an yi da su, sukan nuna Ƙyamarsu ga waƘa.
Da yawa daga cikin mawaƘanmu na Hausa idan aka bi diddigin tarihin rayuwarsu
za a ga:
i. Ba su gaji waƘa ba ga uwa da uba ta-tsaka ce ta rutsa da su.
ii. Ba sa sha’awar a ce ‘ya’yansu su gaje su.
iii. Wasunsu tun ana so, suna so, sai su tuba.
iƂ. Wasu na nuna sha’awarsu ga tuba tun ba su yi ba.
Ƃ. Wasu kan nuna damuwarsu na mutuwa suna kiďa.
Ƃi. Wasu kan nuna nadama kan kasancewarsu makaďa.
Ƃii. Wasu kan yi fatar sauya fasaha daga kiďa zuwa makaranta.

Ire-iren waďannan abubuwa da ake tsinta a baukanan mawaƘan baka ya
kyautu a ce an keƂe musu wani wuri da za a nazarce su. Yana kyau manazarci ya
san ba kowace magana ake yin banza da ita ba. Hangen waďannan abubuwa na ga
ya kyautu a kalle su da idon nazari bisa ga yadda su makaďan ke kallon su.
Makaďan da ke da ire-iren waďannan kalamai sun ďauki kiďa wata lalura da ya
kyautu a ce sun aje, sun dangane, sun tuba, sun nemi wata hanyar gamawa lafiya
da duniya. Wannan hasashen ya sa na yi wa binciken taken: ‘Lalurar Kiďa a Bakin
Makaďa.’ Ga yadda abubuwan suke:


GADON KI'DA


A al’adance, Bahaushe na bugun gaba da gado sosai. Wanda ya gaji abu
daga mahaifinsa ko kakansa, ya fi wanda bai gada ba, ko da kuwa wanda bai gada
ba ya fi suna da sanin abin. Wannan ne dalilin Hausawa na yi wa ďan gado suna
‘ďan asali’ wanda bai gada ba kuwa ‘ďan haye’ ko ‘ďan shige’. Ashe gaskiyar wani
yaron Garba ďanwasa Gummi (mai kiďin tauri) da ya tsima wani ďan gado sai ya
yi kirari da cewa:

“Kai Garba! Kai Garba!
Mu ka tauri,
Mu tauri ka so,
Mu mun ka gadi tauri,
Mu tauri yaz zama ma dole.”

'Dan tauri ke nan ke bugun gaba da gadon tauri da ya yi. Dubi Ja’e ďan
Dikko Canda (Ƃarawon tumaki), da mahaifinsa Canda ya rasu, Gambo ya kai
yawon waƘa gidansu yana gaya wa Ja’e:

Jagora: Ja’e na san Canda ba shi nana,
:Ga matata tana da ciki,
:Yac ce “Baba tahi yawon duniyakka”
:In kana kusa sa aka yankewa da rago
:In ba ka nan kusa, sa aka yankewa da rago
:Sunan da haramun za a yin shi
:Gambo ban kashe ko sisin kwabo ba.”

Ga ďan Ƃarawo na bugun gaba da ya gaji sata, to bale ďan malami ko ďan
Sarakai. SaƂanin haka, dubi yadda makaďi ke nunawa a bayyane cewa, shi bai gaji
kiďa ba duk da kasancewarsa a halin da yake bayanin waƘa yake yi, ana
saurarensa, ana yi masa kyauta, da kari, amma yana cewa:

Jagora: “Ni ban gadi in yi kiďi ba,
:Zaman gadon gidanmu karatu
:Da yin salla da yin alwalla.
:Ihm!”
(J. B. Zauro: WaƘar Sa’adatu)
Da kiďa bai zama wa J. B. Zauro lalura ba, da ba zai furta wannan ďan waƘa
ba. Wannan ďan waƘa ba tuntuƂen baki ba ne, domin ya ambaci abin da ya gada
daga iyayensa. Ga alama, yana burin ya koma ga turken iyayensa ya daina yin
sharholiya, ďirkaniya mota cikin randa.
Wanda bai gaji kiďa ba, ko ya shiga sana’ar kiďa komai zurfin da ya yi a ciki
rashin asali ke rage masa kuzari. Wani makaďin ‘yan-dandi mai suna ďantaro a
waƘarsa ta sharar fage yana cewa:

Jagora: “Kiďi gado ne
:Amma ďantaro
:Bai gada ba.”

Wai me ya sa suke son su kuƂutar da iyayensu cewa ba su gaji kiďa daga
gare su ba? Dalili kuwa shi ne, kiďa wata sana’a ce da ba ta bajinta ba, kuma tana
da Ƙura-Ƙura a fuskar addini da rage mutunci da Ƙima ta cika kamala irin ta
‘yantaccen mutum ga mai yin ta. Idan mutum ya sami kansa ciki da rana tsaka don
haka zai so mutane su san ba daga iyaye abin ya samo asali ba. Yana dai son a
gane abin Ƙaddara ce ta riske shi, ba tarbiyar iyaye ce ba.


ƘADDARAR KI'DA


A al’ada, Hausawa na gani idan yaro na karatun allo aka ba shi naƘalin
samun karatu, idan karatun bai samu ba sai basirar ta koma ta azancin magana da
waƘa. Wata Ƙila, shi ya sa ake samun ‘ya’yan manyan malamai cikin wannan
lalura a kasa gane da ina suka tsince ta. Marigayi Garba Maitandu Shinkafi na daga
cikin ‘ya’yan malaman da wannan ta-tsaka ta risga da su, ga yadda bayanin yake:
Jagora: Ban gadi kiďi ba
:Ni kiďi azanci na
:Yas sa ni yi nai
:Kaina zan wasa
:Garba ďan Jibo
:Dogo ďan baba Makau
Yara: Nufin Allah shi yas sa
:Abubakar waƘa
:Yas samu taushi
Gindi: Yana roƘon manyan mutane
:Mun bi ciki dajin Kwale
:Garba mun ishe kura na ta wasa

Garba gidan malamai ya tashi a Shinkafi, a faďarsa azanci ne ya sa shi waƘa.
A faďar wasu, fahamin karatun da aka yi ya yi yawa dole a sama wa magana wani
wuri da za ta fita in ba ga allo ba ga takarda ko ga turun waƘa. Don haka Ƙaddara
ce ta riske shi ba da gado ba.


MAKAďA A BAKIN MAKA'DA


Hausawa sun ce, mutum ba ya nuni gidansu da hannun hagu. Kowane
ma’aboci sana’a yana so ya ce, “Ni ne wane.” Idan har abokin sana’a na nuna
damuwarsa da kasancewarsa cikin sana’ar da yake yi, abin ya zan wata lalura ta
daban. A bincikena na samu wasu makaďan da ke bugun gaba da fannin kiďansu,
amma kuma a wata fuska su nuna kiďan an Ƙaddarto ne a kansu ba da son rai ba.
Alhaji Gambo Fagada, duk da cika bakin da yake yi na zama limamin mawaƘan
Ƙaddara da hasara yana yawaita faďar:

Jagora: Haliku Allah san da yay yi ni,
:Ban aza in zan mai kiďi ba,
:Yau ga ni, ina yawo da ganga.

Makaďa in ba ďan gado ba ne, ba ya son a ce wa mahaifinsa makaďa. Ga shi
makaďi, yana kuri a ce masa makaďi amma ba ya son a ce ďan makaďa. Da
malamin kiďa Narambaďa na jereƘe cikin bakandamiya faďa yake:

Jagora: Kyawon ďan mallami
Yara: Ya zan ka zuwa makaranta
Jagora: Shi ďan runji
Yara: Shi ďauki yuƘa daidai an nan
Jagora: Shi dillali
Yara: Da an saye shi bari ad daidai
Jagora: Shi kau makaďi
Yara: Ya gyara turu
:Daidai an nan
Jagora: Ni kam kun gane ni
Yara: Na gyare turuna
:Sai zuba waƘa nikai
:Kama da ta Alfa Zazi
Gindi: Gwarzon Shamaki na malam toron giwa
:Baban Dodo ba a tamma da batun banza.

Narambaďa fitaccen makaďin Sarauta ne, bai gaji kiďa ga mahaifinsa ba.
Mahaifiyarsa ta gaji kiďa ga mahaifinta Sarkin Kiďan Badarawa. Don haka ne bai
ce: “ďan makaďi kau.”Domin shi ba ďan makaďi ba ne, fasaha ce ta huje shi ya ci
gaba da zuba waƘa irin ta Shehu Alfa Zazi, madahan Annabi (SAW). A nan ma, da
alamun kiďa lalura ne gare shi.

https://www.amsoshi.com/2017/09/27/kaska-wakar-farfesa-aliyu-muhammad-bunza/


SAKAMAKON MAKADI


A shari’ar musulunci kiďi bai samu gata ba sosai yadda mawaƘa ke son ya
samu, wanda shi ne dalilinsu na yi ďari-ďari da shi. Nassi ya zargi kiďin hululuwa
da jahiliyya ya kuma hukunta shi. Ga saƘon wani shararren Shehi na addinin
musulunci Ibn Ƙayyim (Allah Ya yi masa rahama):

Nassi: “Wa tikraaru nushi minnaa lahum,
Li ya’azira fiihim ilaa rabbinaa.
Falammas tahaanuu bi tambihinaa,
Raja’ana ilal laahi fii amrinaa.
Fa’ishnaa alaa sunnatil Musďafaa,
Wa maatuu alaa tintinaa-tintinaa.”
Fassara: Yawaitar nasiharmu kullum gare su,
Kwaďaitar rabon Jalla don wajibina.
WulaƘanta zance yawan kau da huska,
Mu koma ga Allahu komai mu daina.
Mu rayar da Sunna mu bar bin hululu,
Tafashen kiďa tintinaa-tintinaa.
(Fassarar: A. M. Bunza, marubuci)

Bayanin Shehin malami Ibn Ƙayyim na nuna Ƙyamar kiďa ga shari’a da
buƘatar a nisance shi. Bayanin ya yi canjaras da fahintar Bahaushe na ganin munin
sana’ar kiďa a addini. Wani fitaccen mai wa’azi a Jamhuriyyar Nijar a wajajen
shekarar (1975 – 80) Malam Muhammadu mai Zabura ya fassara amon babban
kalangu da kurkutu (Ƙwazagge) kamar haka:
Kalangu sautinsa: Muna ganin Annabi dai!
Kurkutu sautinsa: Ko kusa! Ko kusa! Ko kusa!

A ganin Hausawa, kiďi ko ya zan na lalura lokaci gare shi, don haka ba sai
makaďi ya mayar da abin sana’a ba. Rashin aikin yi da lalaci ke sa bin makaďa ana
shan kiďa. Duk wanda wani abu mai amfaninsa ya shagaltar da shi, shi da makaďa
sai dai karin dole don kar a yi masa zambo. Wani makaďin samari ya tabbatar da
wannan a waƘarsa ta Ƙattan gari da ke cewa:

Jagora: Kai mai kiďi kiďa in jiya
:Ba ka da aiki ni ba ni da
:Mu taru mu lalace mu duka
:Kain! Kakanni ka tingan tigan!

Malam Mu’azu Ƙanen Hali Argungu ya tsoratar a waƘensa da cewa:

“Bale kan makaďin kalangu
Wasar ‘yan mata
Ba shi ganin Sidi lahira sai ya tuba.”
Waďannan abubuwa ne makaďan da suka musulunta ke hange su razana.
Hali Rayya mai gurmi ya yi wannan tunanin wurin da yake cewa:
Jagora: Ga ni ina kiďi cikin mata
:Matan aure suna kallona
:Ka san mai kiďi in naz zo
:Ni, ba ta da lalama sai kamtsa.
(WaƘar Wanakiri Dodon Kwanya).

Da wuya a yi kiďi ba a hautsina maza da mata ba, don haka duk wani
makaďin da ke tunanin makomarsa ya san ya saƂi Allah. Wannan ke sa, wasu na
bayan fage ke sa bakinsu cikin sha’anin kiďa su furta miyagun kalamai har ya
shiga ga kunnen makaďa su razana. Yaro Hore mai kiďin noma na cewa:

Jagora: An ce Yaro ya nakkashe
:An ce zunubin waƘa garan
:To! In zunubin waƘa garan
Yara: Ga wani can zunubin mata garai
SanƘira: Zunubinai ya hi naka Yaro!
Gindi: Aiki yai mai daďi Ƙwarai
:Gungaman noma ďan Bala
Babu wai, mawaƘa na sane da irin kallon hadarin kaji da al’umma ke yi
musu don haka suke son su ga sun bar lalurar kiďa da ransu.


DANGANE KI'DA DA TUBA


Hausawa na cewa, abin da duk ke gidan sarki yana cikin kasuwa. Yadda duk
mutane ke kallo makaďa haka makaďa ke kallon kiďa. Domin kuƂuta daga tarkon
lalura, za a ji makaďan na begen barin kiďa a zantukansu. Gambo Fagada na cewa:

Jagora: In nit tuna da Ƃarayi
:Waďanda nam mutu
:In ji awa in bar kiďin ga.

Makaďa ďan’anace na jan wannan batu a bakandamiyarsa ta Shago yana
faďar:

Jagora: Wata rana ka iske
:Ba mu kiďin ga
:Au walau mun mace
:Walau tsohewa

Wasu lokuta sukan fito Ƙarara su nuna buƘatarsu ga tuba tun mutuwa ba ta
riske su da ganga ba. Dubi faďar Gambo:

Jagora: San da nay yi nuhin
:Hajji mijin Kulu
:Na yi nuhin in tuba dac can

Da yake abubuwan da suka wakana, suka wakana bai tuba ba can, sai ya
dawo gida Allah Ya nufe shi da tuba. Lallai Narambaďa ya furta niyyarsa ta tuba
Ƃato-Ƃato a waƘar Sardaunan Isa, da yake cewa:

Jagora: Fatata ka yi Sarki Isa
:In yi ma waƘa
:Kowa shi jiya
Yara: Yannan in yada kiďi
:In tuba
Gindi: Na riƘa ka da girma
:Abdu Ƙanen mai daga
:Kan da mu san kowa
:Kai mun ka sani Sardauna


TUNA BAYA


Hausawa na cewa, in ana cin Ƃorai a daina tonon cikinsa. Don haka gyartai
ya ce, a bar tuna baya da ya ci sarauta. Adon tahiya waiwaye. Makaďa sukan yi
waiwaye ga asalinsu na iyayensu idan ba gadon kiďa suka yi ba. Idan makaďi ya
tuna baya, ya hangi wurin da aka sa gaba, sai ya karaya, ya yi fatar zama wani abu
ba makaďi ba. Marigayi Garba Maitandu na cewa:

Jagora: Kiďin ga nas soma
:Rabbana ka sa duka
:In mai she shi waƘe
:Ina begen Mamman na Dije
Yara: Zucciyata ta koma inda Mustafa
:Turu sai in aje shi
Gindi: Mun bi cikin dajin Kwale
:Garba mun ishe kura na ta wasa.

Tuna bayan da Maitandu ke yi a nan shi ne, ya san gidan karatu aka haife
shi, ga al’adar gidan karatu kuwa yabon Annabi Muhammadu (SAW) shi ne
madararsu. Da Allah Ya dubi Maitandu da idon rahama ya Ƙaddare shi da tuba,
kuma ya tuba yana kan gadon gidansu malanta. Allah Ya yafe masa. Irin wannan
tuna baya Alhaji Gambo Fagada ya yi shi da ya ga ana dubansa da gefen ido na
zamansa makaďi ya ce:

Jagora: Ko gidan giya nike
:ďan Liman za a ce mini
:Jikan Liman za a ce min
:Don Liman yah haifi Gambo
:Ka ga bai ci amanar mai kiďi ba
:Don ko ya aika ni Borno
:Shekarata goma sha huďu
:Sha huďu ko nar ratci sittin
:Yau ga ni ina yawo da ganga

Tunawa da Gambo ya yi na cewa, ya ratsi hizo sittin na AlƘur’ani, ga shi
ďan Liman, jikan Liman, kuma rungume da ganga, abin takaici ne. yadda aka
kwakkwahe ďiyan waƘar daga Ƙarshe, akwai alamun nadama ga kasancewa
makaďi wanda ke nuna ana kyarkyarar tuba. Haka kuma, aka yi, Allah Ya Ƙaddare
shi da tuba, 2008.

ME KE HADDASA TUBAR MAKA'DI?


Ga ‘yan abubuwan da muka tsinta daga ďiyan waƘoƘinsu za mu iya mu yi
hasashen tubar makaďi a fagen waƘa. Kaďan daga cikin fitattun makaďan da suka
tuba akwai:
i. Makaďa Abubukar Akwara Sabon Birni (1876 – 1962) ya tuba da
kiďa 1945 bayan ya dawo da aikin Hajji. An ce, ya tarar da an tuƂe
sarkin da yake yi wa kiďa Sarkin Gobir Shawai. Ya koma waƘoƘin
madahu.
ii. Makaďa Muhammadu Inyaga Argungu ya tuba da kiďa a shekarar
1975 bayan ya dawo daga aikin Hajji. Shi ne makaďin Sarkin Kabi
Muhammadu Mera 1959 – 1996.
iii. Makaďa Jibril ďan Dodo Mai Tabshi ya rabu da kiďin taushi ya koma
makaranta ya zama babban malami.
iƂ. Alhaji Muhammadu na Jankiďi ya tuba da kiďin taushi ya koma
makaranta ya zama babban malami a garin Gusau.
Ƃ. Makaďa Manu ďakin Gari (Ala Suddan) ya tuba da kiďa ya kama
salati yanzu ya tsufa Ƙwarai.
Ƃi. Hajiya ‘Yarkana Sakkwato, ta tuba kuma ta ce wani mafarki ta yi ba
ta gaya wa kowa, don haka ta dai tuba (2009).
Ƃii. Garba ďanwasa Gummi Makaďin Tauri, ya tuba da waƘa, shekarar da
aka kafa shari’ar musulunci Zamfara, ya rasu shekarar.
Ƃiii. Alhaji Muhammadu Gambo Fagada mai waƘar Ƃarayi ya tuba da kiďi
shekarar 2008.
iď. Makaďa Garba Maitandu Shinkafi ya tuba da waƘa, ya koma
makaranta. Ya zama babban malami a birnin Kano gabanin ya rasu.
Ya rasu Gusau, an binne shi a Shinkafi.
ď. Amadu Doka ya tuba shekarar 2011 a hirar da aka yi da shi Asabar,
11-11-2011 a Ƃ.O.A. (Muryar Amurka) ya ce, saboda wa’azin da ake
yi ya ji ya tuba, yanzu yana nan yana Sarauta a Jahar Kaduna.

Idan muka nazarci waďannan makaďa goma (10) da dalilin tubarsu da
abubuwan da suka biyo baya ga tubarsu, za mu iya hasashen dalilin da ke sa
makaďa tuba ga lalurar waƘa kamar haka:

i. Aikin Hajji: Al’adar musulman Ƙasar Hausa ce, da duk suka ci nasarar
zuwa Hajji lafiya akan tuba ga kowane aikin da addini ya zarga kamar
dambe da kokuwa da kiďa da sauran wasanni.
ii. ShauƘin komawa makaranta a yi karatu na daga ciki. Da ma makaďa
haziƘai ne, sun Ƃata basirarsu a fagen sharholiya. Da sun tuba sai su
kama karatu har su kai ga zama shaihunan malamai.
iii. Tsufa na daga cikin mafarin tuba. Za a kai ga shekarun da basira ke
rufewa, murya ta kasa, gaƂoƂi su nemi a rage musu kaya. Daga nan
sai a tuba, irin yadda ta auku ga Alhaji Musa ďanƘwairo, Maradun.
iƂ. Rasuwar jagoran Ƙungiya na sa yaransa su dangane kiďa su tuba,
musamman idan suna da kyakkyawar hulďa kuma suna da masaniyar
ya taƂa taya musu tuba gabanin ya mutu. Wannan ce ta faru ga yaran
Ibrahim Narambaďa, hatta da Maisa’a da ya raya Ƙungiyar da baya ya
tuba.
Ƃ. Mutuwar uban gidan mawaƘi wani mafarin tubar uban kiďansa ne. an
ce, da Sarkin Kabin Argungu Sama ya rasu, Jada ďantanoma ya tuba
da kiďa, ya koma Kamba ya rasu.
Ƃi. Yi wa uban gidansa marabus daga gadon da yake bisa, na sa uban
kiďansa ya tuba da kiďa. Makaďa Abubakar Akwara, bayan ya dawo
Hajji ya tarar da an tuƂe Sarkinsa Sarkin Gobir Shawai, sai ya tuba.
Ƃii. Wayewar kai irin ta addini na sa makaďa tuba, musamman waďanda
babu gehen da tawilin wani nassi zai kare tuntuƂen harshensu. Ina
ganin a yau, babu sauran makiďa Sata da Caca da Kwartanci da Giya
da Bashirwa da Shawai, ďan abin da ya ďan rage shi ne kiďin tauri da
bori. Tubar Alhaji Muhammadu Gambo Fagada na iya shigowa a
wannan rukunin.
Bisa wannan bincike za mu ce, lalurar waƘa babba ce a kan mawaƘan Hausa
musulmai musamman idan aka kalli dalilan shigansu kiďa da dalilan da ya sa suka
tuba.

SAKAMAKON BINCIKE


Babu al’ummar da ba ta yi jahilliyar irin nata zamani ba gabanin kanta ya
waye ta shiga sahun wayewar Ƙarninta. Larabawa sun yi irin wannan zamani, ya
wuce, sun taskace adabinsu har yanzu ba a Ƙoshi da shi ba. Turawa sun yi irin tasu
ta wuce, adabin da suka taskace su ne suke kai Ƙasashen da suka rena a matsayin
karatun boko. Sinawa da suka taskace nasu, ya zama wata ďaukaka gare su a yau,
musamman a fannin kiwon lafiya da kasuwanci. Babu shakka guguwar jaddada
addinin Musulunci, da tsarkake zukata, da Ƙasa, da al’adun mutane, da wuya ta bar
itaciyar kiďa da wani sansami mai amfani a jikinta. Tsofaffin makaďa sun rasu,
Ƙungiyoyinsu sun mutu, yaransu da suka rage sun tsufa, masu masƘi ga jiki sun
tuba, sauran da suka rage yau ‘yan kame-kame ne kawai. Sabon salo na kaďekaďen
zamani da ya shigo mu, bushaƘin iska ne, haka zai mutu kamar mutuwar
adabin kasuwar Kano. Babban aikin da ke gaban duk wani manazarci da masani a
fannin Hausa shi ne, ƘoƘarin taskace waƘoƘin bakanmu, ta fuskar rubuta su, da
tace su a fayafan radiyo, da nazarinsu, a kundace su, a wallafa su a bar wa na baya
kayan nazari kamar yadda sauran al’ummomin duniya suka yi. In ba a yi haka ba,
akwai alamar salwantar karuruwan harshenmu da kalmominmu na fannu, da
mawaƘan suka adana. Lokaci ya yi kusan Ƙurewa, amma ba a makara ba, don rana
ba ta faďi ba. To! Himma ba ta ga raggo.

https://www.amsoshi.com/2017/08/22/duniyata-kashi-na-farko/

NA'DEWA

Ka da tubar makaďi ta ba ka mamaki komai shahararsa a waƘa, ka binciki
dalilin shigansa cikin kiďa da dalilin tubarsa. A koyaushe makaďan da suka gaji
kiďa, idan suka sami damar sauke faralin Hajji ba su son su Ƙara wasu manyan
kaya, don haka sai tuba. Wasu kuwa shaƘuwarsu da addini da son karatu ke
gaggautar da tubarsu. A wajen wasu, mutuwar uban gida ko saukarsa daga karagar
da yake bisa, na sa su sauke tare da shi. Abin da na ďan gano a wannan bincike shi
ne, kiďa bai sake cin wata kasuwa mai ma’ana ba tun bayan bayyanar hasken
addinin Musulunci a Ƙasar Hausa. Haka kuma, babu mai wata sana’ar da bai son a
gaje shi ko ya mutu a kanta kamar makaďa. MatuƘar Bahaushe bai gaji kiďa ba, ba
ya son a jingina mahaifansa da kiďa, shi da kansa ke tsarkake su kamar yadda
muka ga misalai daki-daki a bakin makaďa.

MANAZARTA


Auta, A. L. 1988. “Gudummuwar WaƘoƘin Makaďan Baka Dangane da Adana
Tarihi”, kundin digirin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza, A. M. 2009. Narambaďa. Wallafar IBRASH, Lagos.
Bunza, A. M. 2011. “Rashin sani ya fi Dare Duhu” muƘala. Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya. Katsina: Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua.
ďakingari, H. M. 2010. “Gudummuwar Mata a Adabin Baka: (Tsokci a kan
WaƘoƘin Baka na Mata a Jihohin Sakkwato da Kabi da
Zamfara)”, kundin digirin PhD, Sakkwato: Jami’ar Usmanu
ďanfodiyo.
Gusau, S. M. 2009. “Waiwaye a kan tarihin rayuwar Muhammadu Gambo na Kulu
Makaďin Ƃarayi”, muƘala, Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya,
Sakkwato: Jami’ar Usmanu ďanfodiyo.
Gusau, S. M. 2005. Makaďa da MawaƘan Hausa. Kano: Benchmark Publishers
Limited.
Gusau, S. M. 2008. WaƘoƘin Baka a Ƙasar Hausa: Yanaye-yanayensu da
Sigoginsu. Kano: Benchmark Publishers Limited.
Ibrahim, M. S. 1982. “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci a kan
Rayuwar Hausawa ta Gargajiya”, kundin digirin MA, Kano:
Jami’ar Bayero.
Tukur, T. 1984. “MawaƘa da Matsayinsu a Al’umma”, cikin Studies in Hausa
Language Literature and Culture, The First International Hausa
Conference. July, 1978. Kano: Jami’ar Bayero.
Umaru, G. 1986. “Mamman Yaro Hore da WaƘoƘinsa”, kundin digirin BA,
Sakkwato: Jami’ar Usmanu ďanfodiyo.
Zurmi, M. A. 1986. “Rayuwar Alhaji Kassu Zurmi da WaƘoƘinsa”, kundin digirin
BA, Sakkwato: Jami’ar Usmanu ďanfodiyo.