Ticker

6/recent/ticker-posts

Aikin Sabunta Titunan Gusau: Tsakanin Kushe Da Yabo

Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Aladu, Jamiar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).

Federal University Gusau (FUG) Nigeria

Aikin sabunta titunan Gusau: Tsakanin Kushe da Yabo

Na

YUSUF MUHAMMAD
Department: Languages and Cultures
Email: yusuff1227@gmail.com

Tsakure:

Manufar wannan takarda ita ce, nazartan matakan gano abin da ya haifar da banbancin ra'ayoyi a tsakanin al'ummar Gusau game da aikin sabunta titunan Gusau. Wannan Binciken ya ginu ne kan bin ƙwaƙwafi tare da ƙalailaice batutuwan da aka nazarta, kasancewar banci karo da wani aiki da aka yi a kan sabunta tituna ba, hakan ya sa wannan bincike ya kasance a matsayin tushe ko majiiya na farko (primary source) haka kuma, binciken ya gano masu yabawa sunfi masu kushe hujjoji gamsassu ta hanyar cigaban al'umma da bunƙasan tattalin arzikin wannan yanki na Gusau.

Fitillun Kalmomi: sabunta tituna, Gusau, kushe, yabo

1.0 Gabatarwa

Kalmar sabuntawa sananniyar kalma ce da bakuna suka saba furtwa sannan kunnuwa suka saba ji tsakanin al'ummar Hausawa. Idan aka ce sabuntawa yana nufin abun da dama akwai shi ba wai ƙirkiran sabo aka yi ba a'a, tsohon da ake da shi tun asali shi ne aka sabunta tahanyar yi mashi fenti ko kuma canja masa tsari bisa yan da aka sansa can baya. Gusau ita ce babban birnin jahar Zamfara, jahar tana daga cikin daular ƙasar Hausa wanda suka haɗa da daular Kebbi da kuma daular Gobir ƙarƙashin shahararriyar daular ƙasar Hausa wanda ta wanzu a ƙarni na shatara (19). Haka kuma, jahar Zamfara tana ɗaya daga cikin jahohin Najeriya talatin da shidda (36), Jahar tana da ƙananan hukumomi goma sha huɗu (14), wanda Gusau ita ce birni mafi ɗauka a cikin su.

Kasancewar Zamfara jaha ce an yi gwamnatoti waɗanda suka yi mulki tun daga lokacin mulkin soji har zuwa mulkin farar hulla wato demokaraɗiya, kuma an yi gwamnatoti da suka gabata kafin wannan gwamnati maici yanzu. mutane da dama sun tabbatar da cewa tunda aka samu jahar Zamfara a (October1996), ba a yi wata gwamnati da ta ɗauko aiki sabunta titunan Gusau lokaci ɗaya kusan shekara 30 kamar yadda wannan Gwamnati mai ci ta ɗauko yanzu ba. Domin kuwa wannan gwamnati ta ɗauko aikin sabunta titunan garin Gusau lokaci ɗaya kuma gadan_gadan babu kama hannun yaro, sakamakon irin waɗannan aiyuka da ta ɗauko na sabunta tituna ya janyo ra'a yoyi mabanbanta a tsakanin al’ummar garin Gusau.

1.1 Dabarun gudanar da Bincike: Wannan bincike an gina shi ne kan tsarin bayani na ƙwaƙwafi da ƙalailaice batutuwan da aka nazarta. Duk bayanan da aka yi amfani da su, sun kasance a karkashin rukunin bayanai da aka samo daga majiya na farko (primary source) sannan an yi amfani da dabarar kwatanta bayanai da bin didigin ingancin bayanai (musamman daga mazauna wannan wuri) domin tabbatar da inganci da sahihancin bayanan da aka samo. Tussan bayanan da suka kasance majiya na farko (primary information source) da aka yi amfani da su sun haɗa da mazauna yankin da aikin ya shafa da kuma waɗanda ba mazauna wannan yanki ba. Bayanan da aka tattara daga waɗannan tussa, sun taimaka wajan haskaka muhimman batutuwa da aka nazarta daidai da jagorancin hanyar da aka ɗora aikin. Daga karshe kuwa an ƙalailaice tare da ƙwanƙwance bayanan ta hanyar kwatanta (comparison of information) da kuma fitar da sakayayyun bayanai ta la'akari da dalilai.

4.1 Mai ya sa wasu ke kushewa?

Idan aka ce kushewa ana nufin abinda ka nuna ƙiyayya gareshi. wato abinda zuciyarka ba ta ƙaunarsa, inkuma na gani ne idanuwanka ba su ƙaunar ganinsa.

A iya binciken da nayi a kan masu kushe wannan aiki na sabunta titunan Gusau babban birnin jaha wanda gwamnati mai ci take yi, ya nuna ‘yan adawa ne suka fi kushe wannan aikin sakamakon tunda aka ba Zamfara ‘yancin gashin kanta ta zama jahar da take zaune da ƙafafuwanta a shekarar 1996 tun lokacin mulkin soji har zuwa mulkin farar hulla ba a taƃa ganin aiki na ttuna a Gusau irin na wannan lokaciba.

Tun dawowan mulkin demokaraɗiya a 1999 Zamfara ta soma samun Gwamnatin farar hulla, sakamakon jam’iya guda ce ke ta yin mulki har zuwa 2019. zuwa wannan lokacin babu gwamnati ta farar hullar da tafito da tsarin aikin sabunta tituna irin wanan gwamnati mai ci, wanda ta yi nasaran cin zaƃe a 18/3 2023.

Samun nasarar wannan gwamnati mai ci bai ma ‘yan adawa daɗi ba sakamon haka suka fara kushe wannan aikin sabunta titunan Gusau da kuma wasu wanda ba ‘yan adawa ba,sakamakon hira da na yi da ‘yan adawa da kishiyoyin su kamar haka

i.Ban-bancin jam'iya: wa’yan da ba ‘yan jiiya ba Sun ce suna kushe wannan aiki ne sakamakon ba jam’iyarsu ce take wannan aikiba, idan wannan aiki ya ci gaba da gudana haka tofa in lokacin siyasa ya kewayo ba su da abinda za su faɗa a munbarin kamfen ya gamsar da talakawa har su ƙi zaƃan wannan gwabnati. Wasu kuma ‘yan adawan cewa suke, su ba su son aiki kuɗi suke so domin kuwa tun 1999 duk gwamnati da ake yi kuɗi suke rabawa da muƙanai ba aiki ba Saboda haka sunada yaƙinin in dai wannan gwamnati haka za ta ci gaba to in lokacin zaƃe ya zagayo 2027 za su kada ita.

i. ‘Yan Jamiyar Gwamnati mai ci: Su kuma suna kushe wannan aiki na sabunta titunan Gusau ne Saboda suna sa ran da an ci gwanati za a yi rabon muƙamai a ba su,amma gwamnati ta ƙyale su abokanan hamayya suna musu dariya.

ii. Masu shaguna da abun hawa: Wasu kuma mutanen gari suna kushe wannan aiki ne sakamakon aikin ya biyo ta ƙofar shagunansu an ɗan ɗebi gaban shagunan na su anki biyansu sakamakon gwamnati ta ce ba za ta biya su ba,Saboda wuraren na gwabnati ne.wasu kuma mutanen garin Gusau suna kushe aikin ne tafiskar kafanonin da suke aikin sabunta titunan saboda suna rufe masu hanya mafi sauƙi da suke bi da ababen hawansu sai sun yi zagaye mai nisa tukun su dowa inda suke so.

iii. Wa ‘yanda ba ‘yan Gusau ba: wayanda ba ‘yan Gusau ba amma ‘yan Zamafara ne, kuma suna zaune ne a Gusau, suna kushe wannan aiki ne Saboda ba su son Gusau. suna cewa Saboda ‘yan wannan ramukan da ake tonawa shi ne za a ce ana aiki? sannan aiki a Gusau aka fara dan haka suka tabbatar mun ba su murna da wannan aiki.

4.1.1 Mai ya sa wasu ke yabawa?

Idan aka ce yabawa ko yabo yana nufin abunda ɗan adam ya gani da idanuwansa ko ya ji a jikinsa, sanadiyan haka har ya ji daɗi har cikin zuciyarsa kuma abun ya gamsar da shi sai yabo ya fito daga bakinsa. Yabo ya kasu kash- kashi kamar haka

Yabon Allah.

Yabon Mutun.

Yabon abun hawa. Da dai sauransu.

Wannan ƃangaren zan yi Magana ne akan yabon da mutane suke yi akan aikin sabunta titunan Gusau, wanda mutanen nan sun kasu kamar haka

i. Lokaci ɗaya- Wasu na yabawa ne sanadiyar tunda aka ƙirƙiro jahar Zamfara babu wata gwanabti da ta taƃa aikin sabunta tituna irin wannan lokaci ɗaya. Sakamakon titunan sun mutu suna neman sabuntawa, wasu tun lokacin mulkin soja. Sai da wannan gwamnati ta zo a 18/3/2023 ta ɗauko aikin su, sanadiyar haka ya sa suke murna domin su ma za su shiga tsara irin takwarorinsu Kaduna, da sauran jahohi.

ii. Amfana- Wasu na yabo ne sadiyar kwalta ɗin da aka farfasa suna kwashewa suna cikon gidajansu da shi kuma suna sayarwa su samu abun ƃatarwa. Wasu kuma suna murna ne Saboda sun yi gini sayan ƙasan cikon kangwayen ɗakunansu ya gagaresu sadiyar tsadar man fetur da gas wanda ake sayar da tifa guda 30,000, zuwa 35,000, sakamakon wannan aikin sabunta titunan Gusau dire bobin tifofin aikin titunan suna sayar masu da shi dubu 20,000

iii. Basabonba: Da yawa daga cikin waɗanda suke murna suna zuwa kallo sakamakon abun ya zama musu sabon abu, domin kuwa titunan cikin garin Gusau wasu daga cikinsu sunfi shekara 25 zuwa 30 ba a sabunta su ba in ji wani dattijo. Shi ya sa ma wasu tun ana ginan magudanar ruwa suke shiga ciki suna ɗaukan kansu hotuna suna ɗorawa a yanar gizo.

iv. Ƙayan aikin zamani: -Masu yabawa suna yabawa ne sakamakon sun kasance cikin murna da farin ciki marar musaltuwa game da sabunta titunan garin Gusau ta hanyan sabobbin kayan aiki na zamani wanda ba su taɓa ganin irinsu ba da kuma yanda ake aiki da su, sai aikin sabunta titunan Gusau. Domin kuwa tafiskar gina magudanar ruwa sai sun yi ginan hanyan ruwan mai zurfi sannan su zuba kankare yayi kwana ɗaya zu biyu kafun su ɗauko magudanan ruwan wanda su magudanan ruwan an yi su ne da kankare da siminti gutsure_gutsure ga faɗi ga girma an ajiye su suka bushe mota ke ɗauko su, wata injin ke aza su a jere daki -daki sai a yi amfani da siminti wajan ɗaure su ta hanyan game kansu da juna wajan toshe kusurwan da aka bari sakamakon gutsure gutsure aka yi su dole za a samu ‘yar kofa. Haka kuma yayin da suka gama haɗa magudanan ruwan, wani abun burgewa shi ne su magudanan ruwan sunyo masu murafe wanda su ma murafen gutsure gutsure aka yo su sai suka ɗauko su, su yi ta jera su saman magudanan ruwan ya zama anrufe magudanan ruwan ko da ruwa na wucewa ba ka ganinsu wanda hakan ya sa abun ya zama masu sabon abu na zuwa kallo da murna.

iV. Inganci: An samu masu yaba aikin titunan saboda ingancin su, domin kuwa sai sun fashe tsohon kwaltan kuma su yi gina mai zurfi domin su kwashe ƙasan da suka ce wannan ƙasar ya mutu in anaso tititunan su yi ingaci da daɗewa ana murarsu sai an kwashe wannan ƙasan dan kuwa ya mutu, idan ba kwashe wannan ƙasan aka yi ba to in an yi aikin ba zai ɗau shekaru masu yawa ana amfanar su ba. Bayan sun kwashe ƙasan an zuba sabon ƙasa a daddanne ƙasan da motan daddane ƙasa sai a kawo kankare, a yi ta shimfiɗawa har sau uku suke shimfiɗa wannan kankaren ana watsa masa ruwa mota mai nauyin gaske wadda aikinta kenan daddanne ƙasa da ƙankare kafun su kawo kwalta a bi da shi saman kankaren.

4.2 Sakamakon Bincike: Sakamakon aikin sabunta titunan Gusau ya nuna masu yaba wannan aiki hujjar su ta fi gamsar da wannan bincike ta hanyar tattara bayanai da tantance su ta fiskar ƙwanƙwance gaskiya, domin kuwa hujjar ta su ta shafi cigan al'umma ne da walwalar su baki ɗaya da kuma cigaban tattalin arzikin jar. Sakamakon kishayar bayanan masu kushewa kuwa yana nuni da ce wa suna nuna ƙiyayyar su ne don rashin biyan buƙatun kansu da kansu. Haka kuma aikin yana haifar da cinkoson jama'a ‘yan kallo da ɗakan hotuna ta hanyar ‘yadawa ta yanar gizo (internet).

4.3 Kammalawa: An ji ra'ayoyi mabanbanta game da masu ƙushewa da kuma masu yaba wannan aikin sabunta titunan garin Gusau babbar binnin jahar zamafara wanda masu kushe wannan aikin sun kasu kashi kashi wanda wasu suna kushewa ne sakamakon banbancin jam'yi. wasu kuma ‘yan jam'iyar ne amma suna kushewa ne dan anƙi ba su kuɗi ko mukami domin kuwa sunyi zaɓen ne dan a ba su mukami. Wasu kuma suna kushewa ne don an ɗebi gaban shagonsu ba a biya su ba sakamakon gwamnati ta ce wurinta ne. Yayin da wasu kuma suna kushewa ne lokacin da ake gudanar da aikin an rufe musu hanya mafi sauiƙi sai sun je sun yi za gaye.

Yayin da masu yabawa suna yabawa ne Saboda tunda aka ƙirƙiro jahar Zamfara bas u taƃa ganin akin sabunta titunan Gusau irin hakaba. Wasu na murna Saboda suna amfana da mutattun kwalta suna sayar suna samun na kashewa. Yayin da wasu kuma suna murna ne Saboda suna sayan ƙasa a wuri direbobin kamfani bi as farashi mai sauƙi. Wasu kuma suna murna ne Saboda sabobbin kayan aiki na zamani. Yayin da wasu kuma suna murna ne Saboda wasu titunan sun kai shekara 25 zuwa 30 ba a sabunta suba. Wasu kuma ɗauka suke suna sakawa a yanar gizo.

Post a Comment

0 Comments