Amsoshi

Daga


Aliyu Muhammadu Bunza
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu D’anfodiyo Sakkwato
K’ibd’au: mabunza@yahoo.com Waya 08034316508


Takardar da aka gabatar a matsayin babban bak’o mai jawabi a taro na musamman na had’ad’d’iyar K’ungiyar Musulmi MSSN, NACOMYO, FOMWAN, MSO, IMAN, WOMEN IN DA’AWA da MCAN, na Jahar Sakkwato. Ranar Litinin 14th Rabi’ul Awwal 1433 A.H. daidai da 6-2-2012 a babban d’akin taro na FOMWAN, Sakkwato k’ark’ashin Jagorancin Mal. Muhammadu Bello D’anmallam Shugaban Jama’atul Muslimin, Sakkwato.GABATARWA


Gajeren tunanin da ke ga d’an Adam shi ya sa Larabawa ke ce masa Insan wadda aka cirato daga kalmar Nisyan, mai nufin mantuwa. Mutum zai kafa dokar wani abu, da baya ya zo ya sa’ba mata. Wannan dalili ne ya sa Hausawa ke cewa, mai dokar barci ya koma angaje. Matsalolin tsaro sai dad’a ta’bar’barewa suke yi, a koyaushe gara jiya da yau, shekaran jiya ta fi jiya, yau ta fi gobe. Babban abin nufi a nan shi ne , k’ok’arin dangantawa wata al’umma da ke wata nahiya mai rik’e da wani addini alhakin ringingimun da ke wakana a duniyar zamaninsu. Yau, babu, ‘bata gari sai Musulmi. Babu d’an ta’adda sai Musulmi. Babu d’an ra’ayin rik’au sai Musulmi, don haka, a k’asar nan sai Musulmi suka kasance marayu a kundin tsarin mulkin k’asar da suka rinjayi kowane addini da ke cikinta. A kan haka nake son in d’an ce wani abu a kan, wane ne d’an ta’adda?

TA’ADDANCI:


Ta’addanci kalmar Larabci ce mai nufin shisshigi, da wuce gona da iri, da kece wa doka bante ta fuskar tsumbula cikin hane-hanenta a yi kane-kane ba tare da nuna wata damuwa ba. A fassarar k’asashen Turai, ta ke’banta ta’addanci ga Musulmi masu k’wazon neman hak’k’insu da aka haramta musu, ko masu kare kansu da irin makaman da ake kai musu hari, ko masu k’ok’arin tabbatar da dokokin addininsu a mu’amalolinsu. Idan wasu da ba Musulmi ba suka d’auki wannan mataki, akan yi musu suna ‘yan gwagwarmaya ko ‘yan neman ‘yanci ko marasa rinajaye ko abokan hamayya ko ‘yan sari-ka-nok’e. Cikin dabara da yaudara, yau, a kafafen yad’a labarai na cikin k’asa da na waje duk da irin wad’annan fassarori suke amfani na shafa wa Musulmi da Musulunci kashin kaji.
Da za a tambayi wanda aka lak’aba wa suna “d’an ta’adda” mene ne “ta’addanci”? Ba zai sa’ba wa fassarar da addini ko harshe ya tanada ba. Idan aka tambaye shi aikin da yake yi, ko ya san ta’addanci ne? Ba zai yarda ba. Dalili kuwa shi ne, shi, yana k’ok’arin kare kansa ne ga irin farmakin da ake kai masa, ko yana k’ok’arin ramuwar gayya ne ga ta’addancin da aka yi masa da sunan tsaro ko neman zaman lafiya. Don haka, a ganinsa wanda ya kai masa farmaki shi ne “adda” shi da ke kariya shi ne “d’anta” don haka wane ne d’an ta’adda?
Ga dukkanin alamu, ana amfani da kalmar ne a yau domin a d’ebe tausayin wad’ansu mutane da ake son a halaka ga zukatan jama’a. Ana amfani da kalmar ga mutanen da suka k’i mik’a wuya borin Turawa ya hau kansu. Ana lik’a kalmar ga jama’ar da ke ganin kasawar Demokrad’iyya ga kare hak’k’in d’an Adam. Ana danna ta ga wad’anda ke ganin rashin ingancin dokar ta yi takin sak’a da dokokin Allah (SWT). Ana sarkafa ta ga mutanen da suka k’i kafirce wa al’adunsu don na wasu. Ana kururuwa da kalmar ga masu ra’ayin cewa, dokokin Allah ba su tsufa. Ana tabbatar da kalmar ga wanda ya yi ramuwar gayya da hushi. Ana sarrafa kalmar ga wanda ke ganin in an d’ebi na dahuwa yana iya d’ibar na gashi ga ban mak’iyansa. Ana taliyon kalmar ga wad’anda ke ganin cewa, da wulak’anci gara shahada. A wasu lokuta, an fi saka ta ga wad’anda suka k’i yarda a yi musu dodorido da makamai a tarwatsa musu fahinta.
Idan muka sa idon natsuwa sosai muka duba, za mu ga cewa, a duniyarmu ta yau za mu ga akwai:
i. ‘Yan fafitikar neman ‘yancin kai daga duniyar Turawa da mamayarsu irin su Nelson Mandela da ya yi kusan share rabin k’arni a gidan Yari, da mutanen Namibiya, da Zimbabuwe, amma ba a yi masu suna da ta’addaci ba.
ii. Masu fito na fito da gwamnatin da ke ci a k’asarsu. Cikin fafitakarsu sun kashe talakawa da sarakuna da wak’ilan hukuma irinsu Saro Wiwa na k’abilar Igonni, amma ba a kira shi da sunan ba.
iii. Akwai ‘yan gani-kashenin siyasa da suka kai fagen kashe talakawa da masu mulki. A k’asar nan, an sami wad’anda suka kashe Ministan Shari’a bisa ga irin ak’idarsu ta siyasa ba a kira su da sunan ba.
iv. Muna da ‘yan bangar kare gonakin gado da suka fito da sunan Samarin Nija Delta, sun kashe ‘yan gida, sun kashe bak’i, sun talauta k’asa, sun kashe sojoji da ‘yan sanda bila adadin, amma sai tukuici aka yi musu da albashi mai tsoka ga kowane k’ato marashi aikin yi aka kuma bud’e musu ma’aikata tasu ta kansu, wai su ba ‘yan ta’adda ba ne! ‘Yan kare gundumarsu ta gado ne.

WANE NE D’AN TA’ADDA?


Masana addini sun aminta da tashin duniya kuma nassoshi sun inganta a kan cewa, lallai ranar Jumu’a za a sallame mu da aiki. Bincike ya nuna Jumu’ar ba ta da Assabar, sai dai sanin wace rana ce? An ‘boye muna. Duk da haka, daga cikin manyan-manyan alamominta akwai bayyanar ta’addanci a doron k’asa. Fassarar ta’addanci a littattafan Shari’a yana banga-banga da fassarar Turawan mulkin kama-karya da ‘yan barandansu ‘yan bokon k’arshen zamani. Mutanen da ke walawa da cin gajiyar ganimar duniya, da shan jinin moro, da tursasa wa marasa galihu, da mak’ure mai d’an k’arfi, suna ganin duk abin da ke hana su mik’e k’afafunsu, su baje kolinsu shi ne “ta’addanci”. Ban ga laifinsu ba, domin k’olin tunaninsu daga duniya sai Abuja.
Idan ana biye da zaren tunanina, ta’addanci suna ne k’irk’irarre na wannan k’arni da k’arya ke son ta yi garkuwa da shi ta yak’i gaskiya. Tantance d’an ta’adda a irin fassarar ‘yan bokon zamani yana da wuya saboda yaudarar da aka saka a ciki. Da dai za a tsaya a kalli kalmar da irin yanayinta da za a yi mata fassarar adalci a ce:
“Yin amfani da k’arfi domin a turmuje mai d’an k’arfi, tare da bin kowace dabara ta rashin tausayi da keta hak’k’in bil Adam domin kai ga wata manufa da ake son a tilasta mutane su bi ta. D’an ta’adda shi ne, wanda ya fara takara, ya yi amfani da makamansa domin ya kai ga manufarsa. D’an ta’adda ba ya buk’atar zaman lafiya matuk’ar ba a tsarinsa ba, kuma duk wurin da ya kafa tsarinsa da ta’addanci zai yi amfani ya rusa masu adawa da shi ya kare wad’anda suka bi.”

GANI YA KORI JI:


Na k’irk’iro wannan ma’anar ta’addanci bayan na nazarci fassarorin da ‘yan boko ke d’ora ta’addaci a kai. A ganina, ba a iya gane d’an ta’adda idan ba a bi silalen tarihi ba. A tsarin malaman usulu komai yana kan hukuncinsa matuk’ar ba Shiri’a ta zo ta d’ora masa wani hukunci ba. Don haka, k’asashen duniya duka lafiya lau suke zaune gabanin rigingimun k’asashen yamma ya sunsune su. Tarihi ya tabbatar da cewa, k’asashen Turai suka fara haihuwar ta’addanci suka rene shi, sai da ya zama samari sadauki suka aike shi sauran k’asashen duniya don a san shi, ya san su. Wannan hasashen nawa, ana iya kallonsa da tubarau na tarihin duniya kad’an daga ciki akwai:
i. Yak’e-yak’en da Turawan mulkin mallaka suka kai a k’asashen Larabawa da Asiyawa da Afirka. Yak’e-yak’e ne na mamayar mutane a tilasta su, su bi dokar k’asar da ba tasu ba. Su bi addinin da ba nasu ba. Su yarda da shugabanci da ba nasu ba. Su rungumi al’adun da ba nasu ba. Su rusa tsarin dokokinsu su bi wad’anda aka zo musu da k’arfin soja, so da k’i. Wanda ya mik’a wuya ya zama bawa, wanda ya k’i ba da kai bori ya hau a kashe shi. Wane ta’addanci ya fi wannan a tarihin bil Adam?
ii. Mutanen da aka kashe, da wad’anda aka rataye, da wad’anda aka k’ona, da wad’anda aka sa cikin sahu, aka yi musu kisan takaici a k’asar Libiya zamanin mulkin mallaka wa zai iya k’ididdige su? Haka aka yi wa Bagadaza sama ga Musulmi dubu d’ari biyu (200,000) aka kashe, aka k’ona litattafansu, wasu aka saka teku sai da ruwanta ya gur’bace halittun ciki suka mutu. K’asar Najad da Masar da Sudan duk sun d’and’ani irin wannan k’asak’anci. Idan tarihi na da gurbi a bayanin ta’addanci, a fassarar ma’anar wannan, a ba masu aikin sunan da ya dace da su mu ji. Ai in maye ya manta mai d’a ba ya manta ba.
iii. Mu waiwayi had’ad’d’iyar daular Tanganyika an yi wa mata da yara da jinjirai da tsofaffi kisan kiyashi har sai da suka ari hauka domin su kakka’be wa tabarma kunya k’ura. Turawan mulkin mallaka sun kashe su har sai da suka gaji suka ajiye makamai domin su raga irin da za su taya su noma gonanki kakanninsu da iyayensu da aka kashe. Shahararru daga cikin yak’e-yak’en akwai Maji-maji da Mawo-mawo. Haka aka yi wa daulolin Bantu, aka karkashe k’abilun Zulu aka kashe musu shuwagabanni Mzilikazi da Musheshe da Zwagendaba. Tsananin musibar bala’in kisan kai da k’abilun Zulu ba su ta’ba jin labari ba, balle su gani, shi ya sa suka kira zamanin Turawa Mfacane ma’ana; “zamanin bala’i da waba’i”. Kaico! Wai duk an yi wannan da nufin wayar da kan k’auyawa in ji ‘yan mun waye.
iv. Idan muka waiwayi baya a nan cikin gida, laifin me daular Musulunci ta Sakkwato da Mujaddadi D’anfodiyo ya assasa ta yi? A yak’in Giginya ba a iya k’ididdige shahidai. Aka je Burmi, aka yi kamar ba a yi wani abu a Giginya ba. Aka je Had’eja aka yi kan mai uwa da wabi, fiye da mutum dubu goma sha biyar suka yi shahada. Ba a bar Satirawa baya ba, a 1906 su dubu goma aka k’ona cikin garinsu maza da mata yara da manya. Duk da tsananin wannan ta’asa, wai su ne ‘yan ta’adda. Haka kuma, an k’one garin Raha da Bahindi da Kwantagora wai don a tauna tsakuwa a ba aya tsoro kawai. To! Tsakanin mai abu da marashi da ya zo da makamin yin k’wace, wane ne d’an ta’adda? Idan aka samu accakwama wa ya aikata ta’addanci?

Wad’annan musibu duka ba ‘yan gida suka jawo su ba. Bak’in haure da ke ganin, a ba manya fili ba don Allah ne ba. Wanda ya k’i ba manya fili a ture shi ya fad’i a kashe, wanda ya ba da fili a bautar da shi na har abada. Wai, wad’annan kashe-kashe da babu tarihin da zai iya k’ididdige su an yi su ne da nufin neman wurin zama, da baje kolin sana’a, da kafa mulkin kama karya, da yad’a addinin Yahudu da Nasara, da hana a ga tauraron kowa in ba nasu ba. A ganinka na ma’aboci hankali da wayo, wane suna ya fi dacewa da wad’annan mutane? Wa ya fara ta da zaune tsaye a duniyar bil Adam? Da wace hujja bunsuru zai hana wa akuya shan k’asari?

NASON MIYAR JIYA GA SABON AKUSHI


D’an tsakuren da muka yi muke son mu daddage shi ga abubuwan da ke faruwa a duniyar k’arninmu. Ga al’ada, kazar da aka yanka idan ta tashi cikin d’aukar rai ta fi ban tsoro da firigirtawa da ban mamaki ga wanda ya yanka ta. Idan dai yana buk’atar cin namanta, idan ya kama ta ya danne, zai yi mata dannan takaici. Idan ya ga babu makawa sai ya sake yanka, zai yi mata yankan takaici sai ya raba kai da wuya. Irin haka ne yake faruwa a wannan k’arni namu. A da, Turawan mulkin mallaka sun yi zaton sun gama da kowa. Don haka suka share wa jikokinsu wuri su zo su ci karensu ba babbaka. Da baya suka hango an yanka ta tashi, don haka jikokinsu na yau ke son su yi amfani da dabarun jiya domin su taushe kazar da kakanninsu suka yanke shekaranjiya.
Takaicin Yahudu da Nasara ga Musulmi na gado ne. Zama tare, da karatu tare, da auratayya, da mak’wabtaka, da boko, da demokrad’iyya, da bud’e ofisoshin jekadance, ba zai karkare shi ba. Bunk’asar addinin Musulunci ke ba su tsoro. Yawaitar malamai ke tayar musu da hankali. D’aukakar k’asar da Musulunci ke shugabanci wani abin takaici ne a wajensu ko da kuwa bisa tsarinsu ya d’ora k’asarsa. Yawaitar Musulmi a doron k’asa ya fi gobarar gemu tashin hankali a wajensu. Don haka, duk hasarar da za su yi ta ganin an magance wad’annan abubuwa dole a bi ta, ba tare da ja da baya.
Na tabbata za ku gaskata ni, idan kuka tuna da Musulmi sama da dubu d’ari biyu tare da shugabansu Saddam Hussaini da aka kashe a k’asar Irak’i. Wa zai iya k’ididdige Musulmin da aka kashe a daular Musulunci ta Taliban, a k’asar Afganistan? Dubi yadda aka rugurguza Musulmai da dukiyoyinsa a k’asar Libiya? Aka sake biyo Musulman Egypt da bak’ar yadiya don sun ce, a sa shari’a a tsarinsu na yanzu. Syria na cikin hayak’i, an yi jinga da wasu mataulata su tayar da irin wannan fitinar a Saudi Arabia. Babu wata k’asa da Musulmi za su yunk’uro da farfad’o da addininsu face an yi musu taron dangi na k’arfin soje an tarwatsa k’asarsu, ko sun mik’a wuya ba a bari sai an ga baya ga shugabanninsu da malamansu da matansansu.
Abin ban haushi, hatta a fegen tsaron mutuncin d’an Adam ba a ba mutane sarari ba. Ghana ta k’i yarda da halasta kushili (luwad’i) an jaye tallafin da ake ba ta. Zimbabuwe ta hukunta d’an liwad’i da d’aurin gidan Yari, mai laifin ya d’aukaka k’ara wata k’asa ba tasa ba, Amurka ta tilasta a sake shi, kuma an sake shi tare da biyansa diyya, ba tare da an biya wanda ya yi wa luwad’i diyya ba. Nijeriya ta k’i sa wa dokar halasta luwad’i da mad’igo hannu an ce, ta gyara dokarta ko a d’ebe ta cikin k’asashe amintattu. Hausawa na cewa, sare-saren hauka zubar da yawu. Da jaye tallafi, sai a batse k’asa, daga nan, sai a sa mata takunkumi, daga nan, sai kai mata sojojin tsaro, daga tsaro, sai tsokana, daga nan sai farmaki, don kare ra’ayin mutane ashirin a kashe mutum dubu ashirin. Wane suna ya fi cancanta da wannan salon Yahudu da Nasara na mamayar duniyar k’arni na ashirin da d’aya?

NIJERIYA INA AKA DOSA?


Ga alama ba a yi k’asar da ta fi k’asarmu zaman lafiya ba a fad’in duniyar jiya, mun yi suna ga kwnaciyar hankali, da lumana a nahiyar Afirka, yau abin na son ya sauya zani. A tarihi, al’ummar da ta fara wanzar da zaman lafiya a wannan k’asar ita ce Musulmar al’ummar da aka riska da tsarin dokokinta na shari’a daidaitacciya. Ganin haka, Turawa suka k’ago muna mulkin “Shiga gaba in bi ka” (Indirect rule). A Kudu, aka k’aga musu “Biyo ni a baya” (Direct rule). Dalilinsu a nan shi ne, sun tarar da Musulmi da tsarin da ba za a iya cire shi a kawo wanda ya fi shi ba, don haka dole a sa su gaba a bi su baya da bak’ar yadiya. A Kudu, an tarar da su kara zube, dole aka yi musu jagora. Yak’ar daular Musulunci ta Sakkwato da aka yi da irin raddi mai gauni da suka sha a Sakkwato da Burmi da Had’eja da Kwantagora da Satiru ya sa suke son sai sun mayar da raddi ko da bayan shekara dubu ne. Hanya mafi sauk’i a yau ita ce, a lik’a musu sunan ta’addanci a yak’e su da shi, a kashe musu matasa da malamai sabon mulkin mallaka ya sake bayyana a Arewa. Ba daga waje aka yak’e mu ba daga cikinmu aka yak’e mu.

ZUBI DA TSARIN MUSULMIN NIJERIYA


Musulunci da ya shigo Nijeriya ba da yak’e-yak’e ko tsangwama ya zo ba, balle a ce, mun gaji abinmu. Wayewar Turai ta zo da fad’a, da yak’i, da bauta, da zanga-zanga, don haka, fitina da tashin hankali a ko’ina ka gan shi bak’o ne cikin Musuluncin d’an Nijeriya, ba a ba shi masauki ba balle ya shimfid’a buzun zama.
A tarihance, Mazhabar Malikiyya ta fara ziyararmu, ak’idar Shi’a ta shigo ba ta samu kar’buwa ba ta rushe. Daga nan sai ak’idar Asha’ira ta biyo baya. K’adiryya ta zo, ba ta yawaita k’warai ba, Tijjaniyya ta zo ta kar’bi tuta. Ana cikin wannan fafitikar Shi’a ta sake hudo kai da sabon salon na Mahajuba da Echo of Islam ana cikin wannan yanayi k’ungiyoyi irinsu Izala da Jama’atu suka k’asura. Wad’annan k’ungiyoyin suka haifar da samarin Salafiyya masu ra’ayin ana iya yin tantagaryar addini irin wanda Manzo (SAW) ya yi, ba tare da an yi tak’alidanci da kowace mazhaba ko d’arik’a ko k’ungiya ba. A yau, daga cikin wad’annan kashe-kashen wanda duk aka tsokana, aka hana masa ‘yancin addininsa, aka kashe masa malamai ko iyali ko mabiya, idan ya yi yunk’urin mayar da martani sai a sa masa sabon suna “Boko Haram”. Had’arin da muke ciki shi ne, matuk’ar ana son d’ebe tausayinka a zukatan Musulmin Nijeriya, a yi ma kisan gilla ko a yi ma d’aurin rai-da-rai sai a ce maka d’an “Boko Haram”. Shi ko wanda ba Musulmi ba da ya kai wa Masallatai da Coci hari, wane suna za a ba shi?

SUNA A FAGEN CIN ZARAFI


Idan ana son a gane a ina ta’addanci ya fito? Sai an bi tarihin yadda ake rad’a wa d’aid’aikun k’ungiyoyin Musulmin Nijeriya suna. A tarihi, magoya bayan k’ungiya ko mazhaba ba su ke k’aga mata suna ba. Sunan na fitowa ne daga bakunan ‘yan adawa ko ‘yan jarida ko jahilai. Da wannan suna za a la’be a yi ta kashe Musulmi har sai an k’are mu gaba d’aya bi-da-bi (Allah Ya kiyaye). Dga cikin misalan da zan bayar a nan sun had’a da
a. Magoya bayan karantarwar Muhammad ibn AbdulWahab ‘yan Nak’shabandiyya suka sa musu Wahabiyawa. Ba su ta’ba kiran kansu da sunan ba.
b. ‘Yan Mazhabar Malikiyya da Shafi’iyya da Hambaliyya da Hanafiyya da Zahiriyya, duk ba malaman da suka assasa mazhabar suka sa sunan ba. Malaman fahintocinsu suka fitar cikin gundarin nassi, d’alibansu suka rungumi fahintar aka sa musu suna da fahintar malamansu.
c. Shehu Abdulk’adir Jelani da Shehu Tijjani ba su suka sa wa d’arik’unsu suna ba. Abokan adawa da almajiransu suka sa sunan.
d. Muhammadu Marwa bai san da sunan “Maitatsine” ba ‘yan jarida da abokan hamayya suka sa sunan daga fad’ar da yake yi “Allah Ya tsine wa mak’aryaci”.
e. ‘Yan k’alak’ato ba su suka sa wa kansu sunan ba, daga fad’arsu ne na cewa “In an gabato aya babu sauran k’ala k’ato”. A nan, suna tsoratar da masu kawo nassoshin litattafai su gitta a kan nassin Alk’ur’ani.
f. ‘Yan zando da K’ur’aniyyun duk suna ne da aka lik’a wa masu fahintar ba tare da saninsu ba, kuma galibi ba su yarda da sunan ba.

BOKO HARAM


Wannan ita ce k’ololuwar maganar da ake ciki a duniyarmu ta yau. Marigayi Malam Muhammadu Yusuf (Allah ya gafarta masa) bai kira da’awarsa suna Boko Haram ba, d’alibansa ba su kira ta da wannan suna ba. Ni ina ganin ‘yan boko da boko ya zama wa dole, addini ya zama musu lalura, da su da ‘yan jaridar da ke son a turara hayak’in rashin jituwa tsakaninsu da jama’a ke yi musu wannan suna. Gabanin a ci zarafinsu da wannan suna, ana ce da su “Ahalil Sunnah” kawai. Da baya wasu ‘yan adawa suke kiran su da Yusifiyya. Da suka yi wa ak’idojin boko na Yahudanci da Nasaranci hari gadan-gadan wanda ya tilasta wasu daga cikin masu da’awar barin aiki cikin gwamnati saboda gani babu wata hujja sahihiya da za a iya a tunkari Allah da ita idan an je gabanSa da Demokrad’iyya ko Gwannatin Tarayya suka yi murabus don ganin kansu. Ba a ta’ba samun wurin da suka tilasta wani ya bar aikin gwamnati ba, ko ya bar boko, sai wanda ya gansu da hujjojinsu ya d’auki fahintarsu. Duk da haka, ‘yan boko da ‘yan korensu suka bi su da suna Boko Haram.
A gaskiyar lamari, idan aka ce, al’amari boko gaba d’aya halas ne an ci gyaran Alk’ur’ani da wanda aka aiko da shi. Tun farko a dubi Tsarin Mulki, a dubi Dimukrad’iyya, a dubi fitar mata ‘yansanda, mata kwastan da soja da sauran ma’aikatan tsaro mata. A dubi mata masu aikin jinya da likita. A dubi cin hanci da rashawa. A dubi shugabancin mace da alk’alancinta, da dai sauransu. Me za a ce da su? Halas ko Haram? Me sunan wanda ya ba su suna d’aya daga cikin sunayen da muka fad’a? Idan haka ne kuwa, ya zama tilas Musulmin Nijeriya su gaggauta zama su kalli wannan matsalar da idon adalci domin samun hanyar da za a samu zaman lafiya da juna. Wannan matsalar karatu ce ba ta amfani da k’arfin bindiga ana kashe mutane ba.

IDAN BABU K’IRA ME YA CI GAWAYI?


Hak’ik’a hatta da masu mulkin k’asa sun aminta da cewa tsaron k’asa ya salwance. Akwai mamaki a ji shugaba da kansa ya yi ik’irarin cewa, akwai ‘yan ta’adda har a cikin gidansa kuma ya ayyana sunan wad’anda yake ce wa ‘yan ta’adda a bayyane. Wannan abin nazari ne sosai domin a gano ina ne salka ke tsatsa? Ana cikin wannan rud’un wani d’an siyasa ke cewa “Kodayake ba dukkanin Musulmi ne ‘yan ta’adda ba, amma dukkanin ‘yan ta’adda Musulmi ne.” Ko kusa ire-iren wad’annan lafuzza ba su dace ga d’an siyasa ba, kowane irin addini yake biya. Ba a shugabanci da rashin k’auna kuma ba a yin sa da rashin amincewa juna.
A tarihin Nijeriya, ba yau aka fara nuna wa Musulmi da Musulunci rashin gatanci ba. Matsalar Malam Muhammadu Marwa da aka yi amfani da k’arfin soja ba a san adadin Musulmin da aka kashe a Kano ba. Aka sake yin irinta Bulunkutu a Maiduguri. Aka k’ara yin ta a ‘Yan’awaki a Kano. Idan an ce wad’annan an tsokane su sun rama ko suna da makamai, to su na Darus Salam na jihar Neja wa suka tsokana? Wane makami aka kama gare su? Da wace hujja hukuma ta tozarta su? An yi wa ‘yan Izala irin wannan cin zarafi da mutunci tun farko-farkon fitowarsu a ko’ina. ‘Yan Tijjaniyya ba su ku’buta ga muzgunawar hukuma ba a Sakkwato da K’aurar Namoda da Gusau da Mungadi da Jega ga su nan dai. Wane makami aka kama gare su?
Babu shakka, wad’annan fitinu da rigingimu akwai masu tayar da su? Dole a wasu wurare a samu rahoton k’arya, irin wanda Amerika ta yi amfani da shi ta rusa Irak’i da Taliban a Afganistan. A wasu lokuta kuwa, a samu wakilan tsaro ke tsokanar tsuliyar dodo don sun ga bakin wuta a hannunsu yake. Ba zan musunta a samu siyasa a ciki ba, domin d’an siyasa na iya shiga kowane rango na biyan buk’atarsa. Haka kuma, akwai laifin Musulmi su kansu na rashin had’in kai, da kuma adawar da ke tsakaninsu sun yi k’awance da hukuma domin a musgunawa abokan sa’banin fahintarsu. K’arancin Ilimi ga masu biya da son shugabanci ga masu wa’azi wani makamin jawo wa Musulmi fitina ne tsakaninsu har hukuma ta shigo ta yi musu kan mai uwa da wabi.

DA LAUJE CIKIN NAD’I


Duk wani kewaye-kewaye da za a yi na a goga wa Musulmi kashin kaji ga rigingimu da ke aukuwa a yau ba zai ci nasara ba domin:
i. An samu hannun wad’anda ba Musulmi ba tsamo-tsamo a cikin k’one-k’onen wurin ibadojin Kirista. To! A nan, me za a ce ga wanda ba Musulmi ba cikin kayan Musulmi ya aikata ta’addanci domin a ce Musulmi ne suka yi?
ii. Ire-iren makaman da ake sarrafawa sun fi k’arfin a ce, wasu ‘yan d’aid’aikun mutane ne ke da hannu. Wanda ke cikin talauci, ina zai sami kud’in sayen makamin da zai saya masa abincin shekara goma?
iii. Rahotannin da kafofin yad’a labarai ke yawaita ambato na makaman da ake kamawa, musamman wad’anda aka sa shari’arsu a Ingila (yanzu) da wad’anda aka kama Ghana da Borno da makamantansu ba a bayyana masu su ba balle a san dabarun da za a d’auka na zaman lafiya.

ME YA KAI MU A WANNAN HALI?


Wannan shi ne zuciyar abin da nake son in yi hasashe a d’an bayanina. Yau mun shiga halin da kowa na buk’atar zaman lafiya. Don haka wasu k’asashe na son su samu damar shigowa cikinmu k’asarmu ta shiga wani hali. Babban abin da ya kawo mu a wannan hali shi ne:
i. Kisan gillan da wakilan tsaro ke yi wa shugabannin addini da masu addini a bayyane ba tare da an je kotu ba an tantance maras gaskiya. Ta yaya almajirai da muridai da mabiya da surukai da ‘yan’uwa da Musulmi za su yafe wa wanda ko wad’anda suka yi wa magabatansu kisan gilla na wulak’anci da tozartaswa? Aikin hukuma ne ta lalabo wad’anda suka yi wannan aiki ta barranta kanta da aikin ta kai su kotu a hukunta su, a san ba da yawun hukuma suke kashe mutane ba. Idan hukuma ba ta d’auki matakan hukunta masu laifi ba, kamar tana koya wa wad’anda aka zalunta ta’addanci ne. Kisan gillan da aka yi wa Malam Jafar a Kano da Muhammadu Yusuf a Maiduguri da D’anmaishiyya a Sakkwato (Allah ya gafarta musu), sun isa su zama abin misali a kan haka. Hukuma ta yi shiru kamar an aiki bawa garinsu. Me ake zato ga ‘yan’uwan mamatan?
ii. Rinjayar da aka yi wa wani addini cikin ma’aikatan tsaron k’asa ya sa a koyaushe ake samun ire-iren wad’annan matsaloli. Wakilan tsaro wasu na amfani da su wajen kare addininsu. Don haka, addinin da duk aka fi yawa a cikin wakilan tsaron a koyaushe shi ne mai laifi, shi ake kawo k’ararsa a koyaushe, har sai an sa mai kai an cuta masa da sunan rahoton k’arya. Wannan hak’k’in hukuma ne ta yi adalci a kan tsarin d’aukar ma’aiktanta.
iii. Wakilcin galihu da alfarma da danniya na za’ben shugabannin siyasa na d’aya daga cikin mafarin yin haka. Da za a samu ‘yan siyasa ko da rubabi-rubabi ne wad’anda suka san addininsu da k’asarsu da al’adunsu dole a yi wankin d’a kanoma mashaya a kan kowace matsala da ta shafi ‘yan k’asa. Matuk’ar masarautu da k’ungiyoyin sa kai da jam’iyyun siyasa ke da babbar murya a za’ben shugabannimu, muna da aiki baya, an bar kyau tun ranar haihuwa.
iv. Rinjayar da ak’idoji da dokokin wani addini a k’asar da aka ce ta gamin gambiza ce, shi ke haifar da ta’addanci. Idan k’asar gamin gambiza ce, to tsarinta gaba d’aya ya zama gamin gambiza ba irin kashin dankali ba manya-manya su taushe k’anana. A ce, kowane shugaba ya hau da tsarin addininsa za a yi aiki ko ba a fad’a a rubuce ba, a aikace an tabbatar. Wad’annan abubuwan ke sa masu kishin addnin da ba irin na shugaba ba, su ga gara komi ta banjama banjam! Da za a d’ora Nijeriya da tsarinta a kan sikelin addinin Musulunci ko Kiristanci ko makaho ya laluba ya san an k’wari wani addini. K’in gyara wannan shi ke sa wad’anda ake shugabanta su kasa hak’urin walak’anci, su da k’asarsu a mayar da su bayi. Dole wannan ya haifar da sa’bani a k’asa hukuma ta fassara shi da sunan “ta’addanci.”
v. Burin wasu marasa kishin k’asa da addini da sanin ya kamata na a raba k’asar nan, su ci moriyar arzikin ‘bangarensu. Wasu na ganin kamar da arzikin da ke yankinsu ne aka gina Nijeriya. Bayan an fifita su ga rabon arziki wanda yake kure ne. Aka bud’e musu ma’aikatun tarayya na kansu cikin kuskure. Aka yanka musu albashin zauna-gari-banza mai tsoka ga matasansu marasa ilimi da aikin yi. Watak’ila ganin irin tsoronsu da ake ji, da reno na musamman da suke samu daga cikin gajiyar arzikin tarayya, wanda babu wani yanki na k’asar nan da ya ta’ba samun irin wannan gata, shi ya sa suke burin a dai raba k’asa, a yanka musu tasu k’asa, su gargad’i bak’in haure daga yankunansu. Da yake ba addinin Musulunci suke yi ba, ba ‘yan ta’adda ba ne, samarin neman ‘yanci ne.
vi. Burin da wasu mak’iya Nijeriya ke yi na ta sake shiga yak’in basasa domin su samu shigowa ciki su tarwatsa jama’arta da tattalin arzikinta ya kyautu a Harare shi. Tuni sun barbaza a kafafen yad’a labarai na duniya cewa, a shekarar 2015 Nijeriya za ta barkace ta warwatse ta rarraba. Yanzu kuma sun gurgusa shi zuwa shekarar 2030 bayan an gama da mu duka. Da suka ga hasashensu ya k’arato, abubuwan da suke son su wakana, ba su wakana ba. Wad’anda ake zaton su fito su yi aikin, wasu sun mutu, wasu sun kasa, wasu ba a yi da su, wasu an gane su, wasu sun ji tsoro sun tuba, daga nan sai bakin zaren hasashen lisafinsu ya ‘bata suka fito da sabon salon na yak’i da ta’addanci a jiohohin Arewa da mak’iyansu suke.
vii. Cin hanci da rashawa da handama da babakere da shugabanni ke yi ya taka rawar gani na fitinun da ke wakana a yau. Yau arzikin k’asa duka na masu mulki ne, wanda ba ya da mulki sai dai ya mutu. An mayar da matasa ‘yan ta’adda, an ba su makamai da tsaro domin su aikata abubuwan da k’ungiyoyin siyasarsu ke so. An mayar da malamai marok’a. Sarakai sun zamo fadawa. An mayar da maza mata, mata sun koma maza. An cusa yunwa cikin talakawa, an ba masu arziki tsaro. An mayar da managarta lalatattu, lalatattu an mayar da su bayi. Wad’annan abubuwa duka cin hanci da rashawa ya haifar da su. Don haka, yau an kai mutane bango ko ba su bin kowane irin addini za su yi fito-na-fito da hukuma da ‘yan barandarta ko da za su yi hasarar rayukansu. Idan aka k’i duban tashin hankali da ke aukuwa a Nijeriya ta wannan fuska an cuci ‘yan Nijeriya. Yaya za a ilmantar da matasa su rasa aikin yi, a hana su shiga wani hali? Ta yaya za a bar matasa babu ilimi babu abinci a hana su k’unar Bak’in Wake ga kai ka muradinsu? Yaya za a tura talaka a bango, ba arziki, ba lafiya, babu abinci, babu matsagunni, babu tsaro, babu kulawa, babu kare hak’k’i, ba a sa ranar gyara ba, ya fito da gora don ya gyara a ce masa Boko Haram? Idan aka bi wannan fassarar wane ne ba d’an Boko Haram ba a Nijeriya?
viii. Ina daga cikin masu ra’ayin cewa, babu Boko Haram. Wani samfarin yak’i da Musulunci ne aka k’irk’iro bayan da aka k’irk’iro ciyon k’anjamau na rage yawan jama’a a duniya musamman na Musulmi da suka k’i yarda da k’ayyaje iyali na ba gaira ba saba. An k’irk’iro Boko Haram ne, domin a tabbatar da an kawar da duk wani mai kishin addini da buk’atar ci gabansa. Martanin da ake zargin ‘yan Boko Haram suna kai an fara gano ba ma Musulmi ne ke kai shi ba. Wad’anda ke magana da yawun Boko Haram an gano ‘yan jeka-na-yi-ka ne da ake son a la’be gare su a kashe Musulmi. Zargin da ake yi musu na haranta Boko an gano mafi yawansu ‘yan boko ne, wasu ‘ya’yansu na boko ga su nan dai. Ala tilas Musulmi su yi zama na musamman a kowace jiha cikin k’asar nan a fuskanci wannan al’amari tun ba a k’are mu cikin guguwar siyasa ba. Ba za mu yarda wani ya lik’a muna sunan da ba namu ba don ya kashe mu ya raya jama’arsa.

SAKAMAKON BINCIKE:


A fahintata hukuma da kafafen yad’a labarai na cikin gida da na waje ba su taimaka wa ‘yan Nijeriya wajen samar musu zaman lafiya da lumana ba. A ‘bangaren ma’akatan hukuma wasu k’abilarsu suke yi wa aiki. Wasu addininsu suke yi wa aiki. Wasu yankinsu suke yi wa aiki. Wasu k’ungiyoyinsu suke yi wa aiki. Wasu son ransu suke yi wa aiki. Wasu aljihunsu suke yi wa aiki. Wasu siyasarsu suke yi wa aiki. Wad’annan su suka taru suka yi ma’aikatan tsaro da farar hula da masu gudanar da mulkin k’asarmu. Ta yaya za a samu zaman lafiya da had’in kai alhali kowa da fuskar da ya kalla irin zaman ‘yan marina? Yaya za a yi wanda ke da k’iyayya da wani addini a tura shi da makami ya kwantar da tarzomar ma’abota addinin da yake k’iyayya, bai yi wa addininsa aiki ba? Yaya za a tura d’an PDP sulhun auren d’an CPC a ci nasara? A kan wannan tunani nake cewa
i. Idan dai da’awar hukuma da ‘yan jarida na danganta musibun da ke aukuwa a Nijeriya ta yau ga Musulmi wai Boko Haram! To, ai a Kudu can boko ya yanke cibi me ya sa ba a samu hare-harensu a can ba?
ii. Idan dai tabbas ne manufar Boko Haram a daina boko, yaya aka yi ba su kai hari a makarantun boko da ake haihuwar ‘yan boko ba?
iii. Kai! Hankalin tuwo ya isa ya yi hukunci manufa ita ce, ana son tarwatsa mu, a rage muna k’arfi, a rage muna yawa gabanin a zauna teburin raba k’asa da wasu ke da’awar a yi. Idan haka ne kuwa, ya kamata mu kama kanmu tun dare bai yi ba.
iv. Masu hangen nesa na ganin, da halastar da Luwad’i da Mad’igo aka fara taya wa mahukuntar k’asarmu. Da suka k’i tayawa aka k’ago Boko Haram.
v. ‘Yancin mata na k’arya da haranta auren mace k’asa ga shekara 18 da tilasta wa mata boko da tilasta shugabancin mace da tabbatar da gado ga shege kad’an ne daga cikin abubuwa da aka so a yi amfani da su a murk’ushe mu. Da abin ya ci tura aka ba mu suna na dabam.

MAFITA


Ga zatona ko ban fad’a ba muna iya kirdadon mafita da kanmu. Ina ganin K’ungiyar Izala ta fara yada muna fitila. Idan muka yi koyi da tsarinta za mu gane ina ta’addanci yake. Mu taru mu duka kamar yadda Mazhabobinmu ba su hana mu salla wuri d’aya ba, ba su hana mu son juna ba da yi wa juna d’a’a da fatar alheri. Da yardar Allah k’ungiyoyinmu da d’arik’ok’inmu ba za su hana mu zama abu d’aya ba mu tunkari abin da ke tunkararmu. Duniya ba a ta’ba samun wurin da ma’abota addini suka samu fahinta iri d’aya ba, amma kuma su zama abu d’aya a muryoyinsu da manufofinsu. Maganin wannan kawai gaggauta taro na dukkanin wanda abin ya shafa a yi zama na musamman na ganin an kai k’arshen kowace irin fitina da sunan addini a Nijeriya. Ku tuna, a Kaduna ga zanga-zangar tsadar man fetur Musulmi da Kirista aka had’e kai wuri d’aya, Kirista ke gadin Musulmi idan lokacin salla ya yi, sai sun k’are salla a ci gaba. To! Da aka yi haka ai ba a ji rahoton ‘yan Boko Haram ko jami’an tsaro sun kashe kowa ba. Wasu jahohi da ba a yi haka ba, yaya aka yi? Ban ga laifin shugaba ba idan ya ce cikin jami’an tsaro da wakilan hukuma Boko Haram suke, mun ko ga alama a Kaduna. Madalla da wannan haske. A hasashen shugabanmu Bobo Haram gamin gimbizar Musulmi ne da Kiristan Nijeriya su ne ma’aikatan k’asa. To! In haka ne don me a jihohin Musulmi kawai ake kai hari da jami’an tsaro ana kashe Musulmai?

NAD’EWA


Shugabannin addinin da Sarakuna su daina su’bul da baka idan aka aikata wani ta’addanci aka jingina ga jama’arsu. Tabbas! Abubuwan da ke aukuwa a Nijeriya a yau na ta’addanci ba Musulmi ke aikata su ba. Yayatawar da ‘yan jarida ke yi na alhakin wasu ayyukkan ta’addanci ga wasu mutane bai isa a yi aiki da shi a kama kashe mutane ana tsare su ba, domin babu dasisar da mak’iya ba su yi wa Musulunci. Tursasa Musulmi da ake sa wakilan tsaro da ba Musulmi ba na yi wani k’aramin ta’addanci ne mai sa k’iliu ta tono balau!