Takaitaccen Bayani: An rubuta wannan aiki da farko da harshen Ingilishi. Duk da haka, domin Hausawa da masu magana da Hausa, an fassara shi zuwa Hausa. Ko da yake taken Ingilishi na asali shi ne "Revolutionizing Hausa Linguistics: Coined Terms for Core Branches", mun canza shi zuwa "Hausa da Rassanta a Dunƙule: Sabbin Kalmomi na Ilimin Harshe don Manyan Makarantu" domin ya dace da fahimta ta Hausa da kuma jin daɗin mai karatu.
HAUSA DA RASSANTA A DUNƘULE: SABBIN KALMOMI NA ILIMIN HARSHE DON MANYAN MAKARANTU
Na
Dan
Umaru Habibu
Mai
Bincike Mai Zaman Kansa | Nijar, Maraɗi.
Tue,
Apr 7, 2026.
Gabatarwa
Ilimin
Harshe a al’adance ana amfani da kalmomi masu bayani da yawaita ɗafa
macidar (kalmar) "ilimin" ( "the study of"), a kowane sunan
darasi. Misali ilimin ginin jumla (syntax) da ilimin tsarin sautuka
(phonology). Sai dai wasu na ganin cigaba da maimaita kalmar "ilimin"
ga sunan kowane darasi dake ƙarƙashin Ilimin Harshe (subfields), na iya
ruɗa ɗaliban
ilimi. Dalili da girman ma'ana da macidar ke ɗauke
da ita. A ra'ayin su manazarta darusa kamar:
Ilimin Ginin Kalma, "Ilimin Fitowar Sauti" da "ilimin
Tsarin Sauti" da sauran su, tun da ƙarƙashin Ilimin Harshe suke, ba su da
"yancin jingina da macidar "ilimin", don kar a yi zaton wani
ilimi ne mai zaman kansa, wanda bai da alaƙa da
ilimin harshe.
Duk
da haka, waɗannan sunayen darusa suna da tasiri
sosai a fannin koyarwa, musamman a matakan farko na ilimi, inda bayyanawa ko
fayyacewa suke da muhimmanci.
yayin
da Hausa ke ƙara zama hanyar
sadarwa don tattaunawa ta ilimi mai zurfi, buƙata
ta taso ga kalmomi waɗanda ba kawai na bayani ba,
sai dai gajeru a tsare, daidai a fahimta, kuma masu alaƙa da juna. Wannan buƙata na cikin manyan taruka na ilimin harsunan Afirka game
da haɓaka
kalmomin gargajiya waɗanda za su iya tallafawa
ilimin zamani (Yakubu & Lawal, 2017; Heine, 2017).
Masana
irin su Abdalla Uba Adamu sun ba da gudummawa sosai ga zamanantar da kalmomin
ilimin Hausa, musamman a fannin rubutu (Orthography) da fasahar harshe, suna
nuna mahimmancin daidaita harshe da buƙatun
ilimi da fasaha na zamani. Haka nan, gudummawar da masana kamar Ibrahim Aliyu
Malumfashi da Aliyu Mu’azu
suka bayar tana nuna ci gaba da ƙoƙarin faɗaɗa ƙarfin ilimin Hausa a fannoni
daban-daban.
Amfani
Da Ka'ida na Binciken
Wannan
bincike ya ɗauki tsarin dual-register (matakai biyu)
ga kalmomin ilimi, ya kuma bambance tsakanin:
Kalmomin
koyarwa (pedagogical terminology) – masu bayyanawa, da fayyacewa, kuma masu sauƙin fahimta
Kalmomin
fasaha (technical terminology) – gajeru, masu tsari, kuma masu dacewa da
kalmomin na ƙamus.
Wannan
bambance-bambancen ya yi daidai da abubuwan da aka lura a cikin nazarin haɓaka
kalmomi (terminology development), inda kalmomi masu bayani sukan yi amfani da
manufar ilmantarwa, yayin da gajerun macidanni (kalmomi) sukan fito a fannonin
ilimi na musamman.
A
cikin wannan tsarin, kalmomin da aka saba amfani da su kamar "ilimin
harshe" da "ilimin ma'ana" ana fahimtar su a matsayin masu
tasiri a fannin koyarwa, yayin da kalmomin da aka gabatar ke aiki a matsayin
saskiya (synonyms) na fasaha don nazarin ilimi mai zurfi.
Maimakon
maye gurbin kalmomin da aka saba da su, sai binciken ya ba da damar kalmomin
ilimin Harshe su yi aiki a matakai daban-daban na hulɗar
ilimi.
Sabbin
Kalmomin Ilimin Harshe.
1.Harshenci
//Haarshencii/an gabatar da shi a matsayin gajeriyar hanya maimakon ilimin
harshe. An samo shi daga harshe da kari -nci, yana ɗaukar
ma’anar ilimin harshe, har wa yau kalmar na da wata ma’anar dake nufin fagen
(register).
Harshenci
yana ƙunshe da dukkan rassan da ke nazarin
harshe.
2.
Hangirwa //Hangirwaa/ (Semantics – Ilimin Ma’ana). Asalin Kalmar: Daga
"hange" aka samar da ita, wannan kalma ta shimfiɗa
ma’anar yau da kullum zuwa fagen fasaha da ke nazarin ma’ana a cikin harshe.
Haka zalika, kalmar an faɗaɗa ta
tana nufin "ma'ana" a yare na yau da kullum.
Misali:
Hangirwar kalmomi tana da muhimmanci sosai a fahimtar ma’ana.
3.
Hangigiya //Hangiigiyaa / (Pragmatics – Ilimin Amfani da Mahalli). Asalin
Kalmar: An ƙirƙire ta ne ta hanyar "Arbitrariness
Of the Sign" (an kawo cikakken bayani kan wannan ka'ida cikin aikin mu mai
taken Kidayar Hausa Sabon Tsari). Wannan kalma tana ɗaukar
rawar da mahalli (context) ke takawa wajen fayyace ma’anar kalma. Misali:
Masana suna nazarin hangīgiya don fahimtar yadda mahalli ke canza ma’ana.
4.
Nahawu (Grammar – Ilimin Ka’idojin Harshe). Babu buƙatar kawo wata sabuwar macida, saboda
dadewar da tayi ana amfani da ita a cikin ilimin Harshe kuma kalma ce dunƙulalliya.
5.
Zangirwa //Zangirwaa/ (Phonetics – Ilimin Fitowar Sauti). Asalin Kalmar: Daga
zangi (“sauti mai kaifi”), wannan kalma tana nufin nazarin yadda ake fitar da
saututtukan magana. Misali: Zangirwa reshe ne da ke bincike kan yadda ake fitar
da sautuka a harshe.
6.
Zagegewa //Zagegeewaa / (Phonology – Ilimin Tsarin Sauti). Asalin Kalmar: Ta
samu ne daga ka'idar Arbitrariness Of the Sign. Wata sabuwar kalma ce dake ɗaukar
ilimin tsarin sauti a dunƙule. Misali: Zagegewa fanni ne na nazarin tsarin
sauti da yadda ake amfani da su.
7.
Kagarwā //Kagaarwaa / (Syntax – Ilimin Ginin Jumla), Asalin Kalma: Daga kagare
(“tsarawa, jera” a Hausar gobarci), wannan kalma tana nufin ilimin yadda tsara
jumla.
Misali:
Kagarwa tana koyar da yadda ake haɗa
kalmomi don ƙirƙirar jumla.
8.
Katankarniya (Morphology – Ilimin Ginin Kalmomi) Asalin Kalma: Daga katankarni
(morpheme) wannan kalma tana nufin nazarin tsarin ginin kalma da yadda ake ƙirƙirarta.
Misali:
Katankarniya tana nazarin yadda ake haɗa
sassa daban-daban na kalma.
Kammalawa
Wannan
aiki ya yi ƙoƙarin gabatar da sabbin kalmomi na ilimin
harshe cikin Hausa, ta hanyar gina su bisa tsarin da ya dace da fahimtar
harshen da kuma ka’idojin
ilimin zamani. An nuna yadda za a iya rage yawaitar amfani da macidar “ilimin” ba tare da rage ingancin
bayani ba, ta hanyar samar da kalmomi gajeru, tsararru, kuma masu alaƙa da juna.
Wasu
daga sabbin kalmomin da aka gabatar, kamar: Hangīgiya, Zangirwā, Zagegewā,
Katankarniyā, sun nuna cewa Hausa na da ikon ƙirƙirar kalmomi masu ɗaukar
ma’ana mai zurfi, ba tare da dogaro da aro daga wasu harsuna ba.
Taƙaitaccen Bayani kan Arbitrariness of the
Sign.
A
ilimin harshe, akwai wata muhimmiyar ka’ida da ake kira Arbitrariness of the
Sign (wato rashin alaƙar
dole tsakanin kalma da ma’anarta).Ma’anar
wannan ka’ida ita ce:
babu
wata alaƙa ta halitta ko ta dole tsakanin kalma
(sauti ko rubutu) da abin da take nufi. Misali, babu wani dalili na dabi’a da ya sa ake kiran abu “ruwa” a Hausa, ko “water” a Turanci—duk yarjejeniya ce ta al’umma.
Saboda
haka: kalma na iya sauyawa daga
wata zuwa watakuma ana iya ƙirƙirar
sabuwar kalma domin sabuwar ma’ana
wannan ka’ida
ce ta bai wa masana damar ƙirƙirar sabbin kalmomi cikin harshe, muddin
suna da tsari kuma ana iya fahimtarsu a cikin al’umma.
A
cikin wannan aiki, an yi amfani da wannan ka’ida wajen ƙirƙirar
kalmomi kamar Zangirwa da Zagegewā,
inda aka samar da su ba tare da dogaro kai tsaye da tsofaffin kalmomi ba, amma
cikin tsarin da ya dace da Hausa.
Madogara:
Crystal,
D. (2008). A Dictionary of Linguistics and Phonetics (6th ed.). Blackwell.
Heine,
B. (2017). African languages as media of instruction. A cikin Oxford Handbook
of African Languages.
Yakubu, A., & Lawal, A. (2017). Terminology development in African languages. Journal of West African Linguistics, 44(2), 55–73.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.