Ticker

6/recent/ticker-posts

Me Ya Sa Bai Kamata Musulmi Ya Goyi Bayan Iran Ba?

Goyon baya a yaƙi yana babi ne na "wala'i da bara'i". Wato babin jiɓinta; soyayya da taimako da nuna goyon baya ga wanda ya cancanci hakan, wato "Wala'i" kenan, da kuma akasin haka, wato a barranta daga wanda ya cancanci hakan, wannan shi ne "Bara'i".

To shi "Wala'i" ana yinsa ne ga Muminai zallah. Shi ya sa Allah ya ce:

﴿وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَٱلۡمُؤۡمِنَـٰتُ بَعۡضُهُمۡ أَوۡلِیَاۤءُ بَعۡضࣲۚ﴾ [التوبة ٧١]

{Muminai maza da muminai mata sashensu majiɓinta sashe ne (wato masu son juna ne, da taimakon juna)}.

Shi kuma "Bara'i" asali ana yinsa ne ga kafirai, sawa'un kafiran asali, ko munafukai da zindiƙai.

Sai kuma sauran masu saɓon Allah, na fasiƙanci ko bidi'a, su ma ana barranta daga gare su, amma bai kai na kafirai ba.

Da wannan za mu fahimci cewa; kwata-kwata Musulmi ba zai goyi bayan kafirai ba. Don haka a wannan yaƙin da yake gudana a yanzu, bai halasta Musulmi ya goyi bayan Amerka da Izraila ba.

To amma Iran kuma fa, shin za a goyi bayanta, tun da Rafidha suna cewa; su ma Musulmai ne?

To, ita Iran ba za a goyi bayanta ba, saboda dalilai guda biyu:

1- Saboda Rafidha ƴan Shi'a suna da bidi'o'i na kafirci. Wato su ba Muminai ba ne, saboda Aƙidunsu na kafirci, kuma su ba kafiran asali ba ne.

To bisa ƙa'ida; duk wanda ba Mumini ba ne, kuma ba kafiri ɗan asali ba ne, to munafuki ne zindiƙi.

Don haka dukkan ƴan bidi'a masu Aƙidu na kafirci, zindiƙai ne. Zindiƙi kuwa, hukuncinsa hukuncin munafuki ne. Ibnu Taimiyya ya ce:

"أَهْلُ الْبِدَعِ فِيهِمْ الْمُنَافِقُ الزِّنْدِيقُ، فَهَذَا كَافِرٌ، وَيَكْثُرُ مِثْلُ هَذَا فِي الرَّافِضَةِ وَالْجَهْمِيَّة، فَإِنَّ رُؤَسَاءَهُمْ  كَانُوا مُنَافِقِينَ زَنَادِقَةً. وَأَوَّلُ مَنْ ابْتَدَعَ الرَّفْضَ كَانَ مُنَافِقًا. وَكَذَلِكَ التَّجَهُّمُ فَإِنَّ أَصْلَهُ زَنْدَقَةٌ وَنِفَاقٌ. وَلِهَذَا كَانَ الزَّنَادِقَةُ الْمُنَافِقُونَ مِنْ الْقَرَامِطَةِ الْبَاطِنِيَّةِ الْمُتَفَلْسِفَةِ وَأَمْثَالِهِمْ يَمِيلُونَ إلَى الرَّافِضَةِ وَالْجَهْمِيَّة لِقُرْبِهِمْ مِنْهُمْ".

مجموع الفتاوى (٣/ ٣٥٣)

Ma'ana; a cikin ƴan bidi'a akwai zindiƙai munafukai. To waɗannan kafirai ne. Kuma sun fi yawa a cikin Rafidha ƴan Shi'a. Shugabanninsu duka zindiƙai ne munafukai.

To su kuma munafukai ba a yi musu "wala'i" da soyayya, su ya su suke ƙaunar junansu, kamar yadda Muminai suke jiɓintar junansu, kamar yadda Ayar da ta gabata ta nuna haka. Don haka su ma munafukai masoya sashe ne, Allah ya ce:

﴿ٱلۡمُنَـٰفِقُونَ وَٱلۡمُنَـٰفِقَـٰتُ بَعۡضُهُم مِّنۢ بَعۡضࣲۚ یَأۡمُرُونَ بِٱلۡمُنكَرِ وَیَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمَعۡرُوفِ﴾ [التوبة ٦٧]

{Munafukai maza da munafukai mata sashensu daga sashe ne (wato sashensu majiɓinta sashe ne)}.

Ibnul Jauziy ya ce:

"وقالَ مُقاتِلٌ: بَعْضُهم أوْلِياءُ بَعْضٍ، (يَأْمُرُونَ بِالمُنْكَرِ) وهو الكُفْرُ، ﴿وَيَنْهَوْنَ عَنِ المَعْرُوفِ﴾ وهو الإيمانُ".

Don haka Mumini ba zai jiɓinci zindiƙi munafuki ba, ya nuna masa ƙauna, har ya goya masa baya a yaƙi. Don haka ba za a goya wa Iran baya ba, a yaƙin da take yi, saboda gomnatin Iran gomnatin Rafidha ce, su kuma zindiƙai ne masu bidi'o'i na kafirci.

2- Saboda su Rafidha maƙiya Musulmai ne, suna adawa da su, suna cutar da Musulmai. A jiya mun kawo maganganun Ibnu Taimiyya a kan haka. Kuma abin da suka yi wa al'ummar Musulmi, a ƙasashen Larabawa, a wannan zamani babban shaida ne a kan baƙar adawarsu ga Musulmi. Kai, abin da yake faruwa a yanzu haka, yadda Iran take ta kai hare-hare kan ƙasashen yankin Gulf, babbar hujja ce a kan shegen mungun nufinsu a kan Musulmai. Shi ya sa ko kwanan nan Abduljabbar ya tona musu asiri. To haka suke a kowace ƙasa ta Musulmai, ɓarna da neman tayar da fitina, da ɗaukar nauyin aiyukan ta'addanci, da kafa ƙungiyoyin tayar da ƙayar baya, da renonsu, shi ne aikinsu. Ka je ƙasashen Larabawa ka tambayi irin ɓarna da ta'addancin Iran, ka sha labari.

Da ma Allah ya tsoratar da mu game da munafukai, inda ya ce:

﴿هُمُ ٱلۡعَدُوُّ فَٱحۡذَرۡهُمۡۚ قَـٰتَلَهُمُ ٱللَّهُۖ أَنَّىٰ یُؤۡفَكُونَ ۝٤﴾ [المنافقون ٤]

{Su ne maƙiyanku, don haka ku kiyaye su}.

Kuma Allah ya hana Muminai jiɓintar maƙiyansu, inda ya ce:

﴿یَـٰۤأَیُّهَا ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ لَا تَتَّخِذُوا۟ عَدُوِّی وَعَدُوَّكُمۡ أَوۡلِیَاۤءَ﴾ [الممتحنة ١]

{Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku riƙi maƙiyina kuma maƙiyinku a matsayin masoya}.

Saboda haka, ba za a goyi bayan Iran ba, saboda maƙiya Musulmai ne, masu cutar da su.

To amma da a ce: Iran ba ta cutar da Musulmi, kawai dai matsalarta ita ce Aƙidunta na kafirci, to idan aka lura aka ga cewa; goyon bayanta a wannan yaƙi shi ne Maslaha, saboda kusacinsu da Musulmai, sai a goya musu baya, kamar yadda Annabi (saw) da Sahabbansa suka so Rum su yi nasara a kan Farisa, saboda Rumawa sun fi kusa da Musulmai. Sun fi ƙaranci ɓarna a kan Farisawa. Inda Allah ya ce:

﴿غُلِبَتِ الرُّومُ ۝٢ فِي أَدْنَى الْأَرْضِ وَهُم مِّن بَعْدِ غَلَبِهِمْ سَيَغْلِبُونَ ۝٣ فِي بِضْعِ سِنِينَ ۗ لِلَّهِ الْأَمْرُ مِن قَبْلُ وَمِن بَعْدُ ۚ وَيَوْمَئِذٍ يَفْرَحُ الْمُؤْمِنُونَ ۝٤ بِنَصْرِ اللَّهِ ۚ يَنصُرُ مَن يَشَاءُ ۖ وَهُوَ الْعَزِيزُ الرَّحِيمُ ۝٥﴾ [الروم ٢-٥]

Amma Iran, bayan Aƙidun kafircin, sun haɗa da cutar da Musulmai, kamar yadda ya gabata a jiya. Don haka ba su cancanci goyon bayan Muminai ba, saboda maƙiya ne, masu cutarwa.

Akwai wasu mutane da suke ganin dole a goyi bayan Iran, har suke kafa hujja da wasu maganganu na Ibnu Taimiyya a kan haka. To insha Allahu gobe za mu ɗauke su mu warware shubuhohin masu kafa hujja da su, mu nuna wa mutane cewa; ana kafa hujja da su ne ba a muhallinsu ba.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments