Ko shakka babu, duk wanda ya san Ibnu Taimiyya to lallai ya san Malami ne wanda ya cancanci kirarin da ake yi masa da cewa:
"رجل
كل العصور".
Wato shi ɗan
kowane zamani ne, saboda yadda a kowane zamani, kai ka ce: Ibnu Taimiyya a
zamanin ya rayu, har zuwa wannan zamani da muke ciki, kai ka ce a wannan
zamanin yake rayuwa tare da mu. Saboda yadda maganganunsa suka zama fitila, mai
haska hanyoyin warware matsalolin kowane zamani.
To amma duk da haka
maganganun nasa gamammu ne, wato za su zama dalilai ne a kan sababbin matsaloli
da suke faruwa, amma ba maganganu ne ayyanannu a kan ayyanannu ba.
Misali; idan muka ɗauki
yaƙin da Iran take yi a yanzu, ba za mu ce:
ga matsayar Ibnu Taimiyya a kan Iran ba, ko yaƙin
Iran, saboda asali Ibnu Taimiyya bai san Allah zai halicci wata ƙasa mai suna Iran a doron Duniya ba. Sai
dai Ibnu Taimiyya yana da ɗaruruwan maganganu a kan Aƙidar Iran, da mabiya Aƙidar, wato Rafidha ƴan Shi'a, mabiya Aƙidar Rafidhanci.
Saboda haka ba za a ce:
Matsayar Ibnu Taimiyya a kan yaƙin
Iran da Amerka da Izra'ila ba, sai dai a ce: Matsayar Ibnu Taimiyya a kan
Rafidha ƴan Shi'a, da Aƙidar Rafidhanci, Aƙidar Iran.
Bayan haka, akwai wata
matsala da ake samu wajen masu kafa hujja da maganar Ibnu Taimiyya a kan
ra'ayoyinsu da "mawaƙif"
nasu, ita ce; ana samun ƙarancin
fahimtar matsayar Ibnu Taimiyya, saboda kasancewarsa kogi ne maras iyaka, wanda
hakan ya sa maƙiyansa da masoyansa
suna ɗaukar
maganganunsa suna ajiye su ba a muhallinsu ba, saboda rashin sanin dukkan
maganganun nasa, ko rashin fahimtarsu. Wannan ya sa ƴan ta'adda, Khawarijawan zamani, suke ɗaukar
maganarsa, su kafa hujja da ita a kan ta'addancinsu, alhali Ibnu Taimiyya ya fi
kowa yaƙar ta'addanci. Sai maƙiyansa su riƙe su ce; ƴan
ta'adda daga Ibnu Taimiyya suka ɗauki
tunanin ta'addanci, alhali Ibnu Taimiyya ya fi kowa yaƙar tunanin ta'addanci. Shi ya sa masu
husuma da shi a zamaninsa, ba su taɓa
tuhumarsa da ta'addanci ba. An ɗaure shi a kurkuku har sau
bakwai (7), amma duk ciki babu ɗauri ɗaya
da aka yi masa bisa tuhumar ta'addanci.
Saboda haka kafin ka ce
matsayar Ibnu Taimiyya a kan kaza ita ce kaza, akwai jan aiki a gabanka, na
tattara dukkan maganganunsa, da kuma fahimtarsu a dunƙule, fahimta ingantacciya.
To, a wannan yaƙi da ake yi tsakanin Iran da
Amerka/Izraila, mun ga wasu suna kafa hujja da wasu maganganu na Ibnu Taimiyya,
a kan cewa; dole a goyi bayan Iran!
Alhali idan aka kalli
maganganun da kyau, za a ga cewa; maganganun ana ajiye su ba a muhallinsu ba.
Don shi Ibnu Taimiyya yana magana ne a kan matsayin kafiri mai dangantuwa ga
Muslunci, tsakaninsa da kafiri ɗan asali. Ko shakka babu,
zindiƙi munafuki wanda a zahiri ya nuna shi
Musulmi ne, ya yi imani da Annabi (saw) da Addinin Muslunci, ya fi kafirin da
bai taɓa
yarda da Annabi (saw) da Addinin Muslunci ba.
To amma wannan hukunci ne
gamamme, sakakke. Dole sai an lura da maganganun da za su keɓance
su, da waɗanda za su ƙayyade su.
Don haka, idan an samu ɓangarori
guda biyu, masu cutar da Muslunci da Musulmai, ɓangaren
kafirai na asali, da kuma ɓangaren zibdiƙai munafukai, masu Aƙidu na kafirci, to dole hukuncin zai
banbanta da wancan gamammen hukunci, kuma sakakke. Don haka, a wajen
"wala'i" da goyon baya, dole a lura da maganar cutar da Musulmai, da
adawa da su. Duk maƙiyin
musulmai, mai cutar da su, to bai cancanci samun goyon bayansu ba.
Waɗannan
Rafidha ƴan Shi'a, a tsawon Tarihi, sun fi Yahuɗawa
da Nasara cutar da Musulmai, kamar yadda Ibnu Taimiyya ya sha faɗan
haka a wurare da yawa. Daga ciki ya ce game da Rafidha:
"إنهم
إذا كان لهم قوة وعدد في مكان، كانوا عدوا للمسلمين مجتمعين، يعادونهم أعظم من
عداوة التتر بكثير.
ولهذا
يخبر أهل الشرق القادمون من تلك البلاد: أن الرافضة أضر على المسلمين من التتر،
وقد أفسدوا ملك التتر وميلوه إليهم، وهم يختارون دولته وظهوره، فكيف يجوز أن يكون
في عسكر المسلمين من هو أشد عداوة وضررا على المسلمين من التتر؟!".
جامع
المسائل لابن تيمية (٧/ ٢١٠)
Ma'ana; duk girman adawa da
ta'addancin Tatar a kan Musulmai, to Rafidha sun fi tsananin ƙiyayyar Musulmi da cutar da su fiye da
Tatar.
Ya sake cewa:
"إن
جهاد العدو الخارجين عن شريعة الإسلام ليكون الدين كله لله، وحتى تكون كلمة الله
هي العليا من أفضل الأعمال الشرعية.
وسعي
المسلمين في قهر التتار والنصارى والروافض من أعظم الطاعات والعبادات، فإن هؤلاء
محاربون لله ورسوله، خارجون عن شريعة الله وسبيله".
جامع
المسائل لابن تيمية (٧/ ٤٣٦)
Ma'ana; Rafidha ƴan Shi'a suna cikin maƙiya Musulmai waɗanda
ya wajaba a yaƙe su, a murƙushe su.
Yana magana a kan wajabcin
yaƙar Khawarijawa, sai ya ce:
"والرافضة
شر من هؤلاء؛ فإنهم يعاونون اليهود والنصارى، وعاونوهم مع هلاوون لما قدم إلى
بغداد، فأعانوه على قتل بيت النبوة العباسيين وغيرهم من المؤمنين، وأعانوا اليهود
والنصارى بالشام نوبة هلاوون وقازان، وغير ذلك، ولا ريب أن ضررهم على المسلمين
أعظم من ضرر التتر".
جامع
المسائل لابن تيمية (٧/ ٤٣٨)
Ma'ana; Rafidha ƴan Shi'a sun fi Khawarijawa sharri da
cutar da Musulmai. Don haka, idan ya wajaba a yaƙi
Khawarijawa ƴan ta'adda, to
Rafidha su suka fi cancantar a yaƙe
su.
A wani wajen ya ce:
"وَقَدْ
علِمَ أَنَّهُ كَانَ بِسَاحِلِ الشَّامِ جَبَلٌ كَبِيرٌ، فِيهِ أُلُوفٌ مِنَ
الرَّافِضَةِ يَسْفِكُونَ دِمَاءَ النَّاسِ، وَيَأْخُذُونَ أَمْوَالَهُمْ،
وَقَتَلُوا خَلْقًا عَظِيمًا وَأَخَذُوا أَمْوَالَهُمْ، وَلَمَّا انْكَسَرَ
الْمُسْلِمُونَ سَنَةَ غَازَانَ، أَخَذُوا الْخَيْلَ وَالسِّلَاحَ وَالْأَسْرَى
وَبَاعُوهُمْ لِلْكُفَّارِ النَّصَارَى بِقُبْرُصَ، وَأَخَذُوا مَنْ مَرَّ بِهِمْ
مِنَ الْجُنْدِ، وَكَانُوا أَضَرَّ عَلَى
الْمُسْلِمِينَ مِنْ جَمِيعِ الْأَعْدَاءِ، وَحَمَلَ بَعْضُ أُمَرَائِهِمْ
رَايَةَ النَّصَارَى، وَقَالُوا لَهُ: أَيُّمَا خَيْرٌ: الْمُسْلِمُونَ أَوِ
النَّصَارَى؟ فَقَالَ: بَلِ النَّصَارَى. فَقَالُوا لَهُ: مَعَ مَنْ تُحْشَرُ
يَوْمَ الْقِيَامَةِ؟ فَقَالَ: مَعَ النَّصَارَى".
منهاج
السنة (٥/ ١٥٨ - ١٥٩)
Ma'ana; bayan Ibnu Taimiyya
ya ambaci misalai na ta'addancin Rafidha, sai ya tabbatar da cewa; sun fi duk
wani maƙiyin Musulmai cutar da Musulmai. Kuma
suna son kafirai, suna taimakonsu a kan Musulmai.
Don haka idan ya tabbata
cewa; Ibnu Taimiyya yana ɗaukar Rafidha a matsayin maƙiya Musulmai fiye da kowa, kuma mafiya
cutar da su, to shin ya halasta Musulmi ya jiɓince
su?
Alhali Allah ya ce:
﴿یَـٰۤأَیُّهَا
ٱلَّذِینَ ءَامَنُوا۟ لَا تَتَّخِذُوا۟ عَدُوِّی وَعَدُوَّكُمۡ أَوۡلِیَاۤءَ﴾
[الممتحنة ١]
{Ya ku waɗanda
suka yi imani, kada ku riƙi maƙiyina kuma maƙiyinku, a matsayin majiɓinta}.
Ashe kenan, duk wasu maƙiyan Musulmai, ba abin ka goya musu baya
ba ne.
To idan dai Muminai ba za su
riƙi maƙiyansu
majiɓinta
ba, kuma ga Ibnu Taimiyya ya tabbatar Rafidha maƙiya
Musulmai ne, me ya sa za ka goyi bayan Iran, a yaƙinsu
tsakaninsu da kafirai?!
Ni dai ban ga dalili ba. Don
haka ba na goyon bayan Iran, kamar yadda ba na goyon bayan Amerka da Izraila.
Allah ya sa su rusa junansu.
Saboda haka matsayar Ibnu
Taimiyya game da Rafidha, ita ce yana ɗaukarsu
ne a matsayin maƙiya
Musulmai, kuma mafiya sharri, mafiya cutar da Musulmai cikin dukkan maƙiya Musulmai. Don haka tun da Iran
Rafidha ƴan Shi'a ne, maƙiya Musulmai, to ba za a jiɓince
su, har a goyi bayansu a yaƙinsu
da kafirai ba.
Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.