Ticker

6/recent/ticker-posts

Keɓaɓɓun Kalmomin Intanet Da Amfannsu Ga Bunƙasa Tattalin Arzikin Ƙasa

Muƙalar da aka gabatar a taron ƙarawa juna sani kan ‘Matsayin Harshe da Tarihi da
Addini wajen bunƙasa cigaba da haɗin kai da tsaro a Nijeriya’, wanda Tsagayar
Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Usmanu ɗanfodiyo, Sakkwato, ya
shirya daga 1 zuwa 3 ga watan Maris, 2016.

Daga

Jamilu Ibrahim Mukoshy
Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato
Waya: 08038353662
Imel:jmukoshy@gmail.com

ABSTRACT


In this era of internet age, numerous potentials can be drived via entrepreneurial
use of the internet. In the developed countries, particularly countries in Europe,
Asia, the use of internet is the key to success in many sectors relating to day-today
activities, such as areas of education, social communication, security,
economic and health care delivery. The aim of this paper is to discuss some of the
economic advantages of the use of internet with reference to Hausa studies. In the
course of the research, the paper studied amongst other things some of the ways
internet can be used to enhance economic growth. However, while making
analysis, the paper made referece to internet banking (hulɗa da banki kan intanet),
e-commerce (kasuwanci kan intanet), online advertisement (talla kan intanet),
network administration (kula da kafar shiga intanet), web design (tsarawa da gina
shafukan intanet) and web administration (kula da shafukan intanet) as some of
the ways of economic intergration. All the items listed above are in one way or
the other specific boasting economic development. Thus, the paper also related
these areas to Hausa internet based terminological development as another in its
self developing Hausa language. Finally, the paper concludes that the use of
internet is a key to achieving success in studies and economic development. The
paper also proffered suggestions for proper internet use by students and
researchers of Hausa language.

1.0 Gabatarwa


Wannan muƙala tana bayani ne a kan wasu daga cikin hanyoyin da ake iya sarrafa intanet
domin bunƙasa harshen Hausa da inganta jin daɗin rayuwar jama’a, musamman ta hanyar
bunƙasa tattalin arzikin ƙasarmu Nijeriya. Hanyoyin da ake iya amfanin intanet domin bunƙasa
tattalin arziki sun haɗa da hulɗa da banki kan intanet (internet banking) da kasuwanci kan intanet
(e-commerce) da talla kan intanet (online advertisement) da kula da kafar shiga intanet (network
administration) da tsarawa da gina shafukan intanet (web design) da kuma (kula da shafukan
intanet) (web administration) da sauransu.

1.1 Ma’anar Kalmar Intanet


Akwai ma’anoni daban-daban da aka ba kalmar intanet, kuma kowace ma’ana tana da
dagantaka da wata., domin dukkan ma’anonin: (i) Sun aminta da cewa intanet hanyar sadarwa
ce. (ii) Sun yarda cewa intanet haɗaka ce ta hanyoyin sadarwa. Saboda haka, ta la’akari da
waɗannan bayanai, wannan muƙala ta ba nata ra’ayi da cewa:
Intanet kafar sadarwa ce ta na’urorin zamani wadda ta game duk
duniya. Tana ba da damar sadar da bayanai kowaɗanne iri, kuma
zuwa ko’ina a duniya cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

2.1 Gabatar Da Keɓaɓɓun Kalmomin Intanet


A halin da ake ciki, harshen Ingilishi shi ne harshen da ya fi kowane karɓuwa a intanet.
Shi ya sa wasu masana ke da ra’ayin cewa harshen Ingilishi shi ne harshen intanet a wannan
zamani. Ita kuwa intanet wani kandami ce da ke taka muhimmiyar rawa ga lamurran sadarwa na
duniya baki ɗaya. Intanet ita ce hanya mafi inganci da ake amfani da ita domin cimma ƙudurin
globalization (shirin game duniya). Muradin yin hakan kuwa shi ne a samar da tsayayyen harshe
ɗaya wanda kowa zai riƙa amfani da shi a duniya. Idan an lura, harshen da zai iya samun wannan
matsayi shi ne Ingilishi. Crystal (2001) da Rumšiene (2004) da Amfani (2007) duk sun yi ƙarin
bayani a kan wannan batu.
Da yake intanet katafariyar hanyar sadarwa ce, tana da sassa daban-daban a ƙarƙashinta.
Akwai kimanin keɓaɓɓun kalmomin 3000 a harshen Ingilishi waɗanda ake amfani da su a
sha’anin intanet na yau da kullum. Akwai keɓaɓɓun kalmomi da suka ta’allaƙa ga kowane sashe
na intanet na daban. Ga wasu daga cikin sassan na intanet waɗanda aka kawo a ƙamusun SYBEX;
(2000):
i. Fannin samar da sofwaya na sadarwa na kwamfuta (application software, operating
systems and enɓironment).
ii. Sashen samar da haduwaya na sadarwa na kwamfuta (hardware, connectiɓity tools,
products and eƙuiptments, cables, cards, connectors, chips, memory and adaptors).
iii. Kamfanoni masu samar da haduwaya da sofwaya na kwamfuta (leading hardware and
software companies, industry standards, certification scheme).
iɓ. Kafofi da layukan sadarwa na intanet (internet protocols and interfaces).
ɓ. Hanyoyin sadarwa na intanet da intaranet daban-daban (internet and intranet
communication, workstations).
ɓi. Ra’o’i da fannonin sadarwa na intanet (networking theory and concepts).
ɓii. Hanyoyin sadarwa na wayoyin salula (mobile communication).
ɓiii. Tsaro da kula da sadarwa a intanet (security and network administration).
iɗ. Kamfanonin samar da iso ga intanet (internet service proɓiders).
ɗ. Fargamin da zayyanawa da bunƙasa shafukan intanet (web programming, design and
development).
ɗi. Sashen amfani da intanet (internet usage).

Waɗannan su ne muhimman sassan da dole sai da su intanet ke tafiya, a nan, muƙalar ta
taƙaita ga sashe na ƙarshe, wato sashen amfani da intanet (intanet usage). Bayan nazari kan
wannan sashe, an kasa shi zuwa gida uku domin hakan shi zai ba da damar tattaro kalmomin da
ke da alaƙa da harkokin tattalin arziki a kan intanet. Ga yadda aka rarraba wannan sashe kamar
haka:

a. Fannin samar da shafukan intanet; ya ƙunshi fargamin da zayyana da bunƙasa intanet da
duk abin da ya danganci haka (Development and Programming Interface).
b. Fannin sadar da bayanan intanet tsakanin kwamfutoci da duk abin da ya danganci haka
(Networking Interface).
c. Fannin mai amfani da intanet (User Interface).
Daga cikin waɗannan sassa, muƙalar ta mayar da ƙarfi ga kashi na uku wato fannin mai
amfani da intanet (User Interface). Wannan ɓangare shi ya fi cancanta a ba muhimmanci domin
samar da keɓaɓɓun kalmomin intanet na Hausa a mataki na farko. Haka kuma, wannan ɓangare
ya fi kusa ga mai amfani da intanet. Ke nan ana iya sarrafa wa mai amfani da intanet shi
gwargwadon iyawa. Shi kansa wannan ɓangare akwai ƙananan fannoni da dama ƙunshe cikinsa
da suka haɗa da (1) Kai-da-kawo a cikin intanet (burauzin/ browsing ko surfing). (2) Hira,
tattaunawa ko musayar ra’ayi (hira ko tattaunawa/ chat). (3) Bincike a intanet (bincike/ search).
(4) Aika saƙonni ko wasiƙu (imel/ email). (5) Yaɗa bayanai a intanet (bulog/ blogging). Bayan
nazari sosai an fitar da keɓaɓɓun kalmomin intanet na Hausa da ke ciki.

3.1 Bitar Hanyoyin Amfanin Intanet Don Bunƙasa Tattalin Arziki


A yau, hanyoyin amfani da intanet suna da yawa. A ƙasashen da suka ci gaba irin na
Nahiyar Turai da Asiya, ana amfani da intanet wajen gudanar da sha’anin kasuwanci (saye da
sayarwa); da neman ilimi (nazari da bincike) da kula da tsaro na ciki da waje da tattaunawa da
hira da musayar ra’ayi da kula da kiyon lafiya da dai harkoki da dama da suka shafi ci gaban
rayuwa na yau da kullum. Don haka har yanzu ana ci gaba da inganta hanyoyin cin gajiyar
fasahar intanet.
Wannan muƙala ta fito da amfanin da ake iya samu ta amfani da intanet domin ya zama
jigon tattaunawa da kuma ba da ƙwarin guiwa domin inganta samar da keɓaɓɓun kalmomin
intanet na Hausa. Kodayake intanet ba ta daɗe da samun wajen zama a Nijeriya ba, duk da haka
ƙiyason ƙididdigar da Internet Live Stats (a shafin www.InternetLiveStats.com) ya gabatar a
shekarar 2014 ya nuna cewa kimanin kashi 37.59% suna iya amfani da intanet a Nijeriya.
Wannan ƙididdiga ta haɗa dukkan al’ummomin da ke ƙasar Nijeriya ciki kuwa har da al’ummar
Hausawa. Kodayake ba a tantance adadin Hausawa masu amfani da intanet ba, duk da haka
dagewa ga samar da wadatattun keɓaɓɓun kalmomin intanet na Hausa zai ba Hausa damar shiga
cikin sha’anin intanet sosai. Yin haka kuma shi zai ƙara kawo gajiyar intanet kusa ga al’ummar
Hausawa.
A taƙaice dai intanet ita ce babbar hanyar sadarwa a duniya baki ɗaya. Matsayinta ya
zarce a kwatanta shi da duk wata hanya ta sadarwa a yau, musamman ta la’akari da yadda
sha’anin intanet yake daɗa samun karɓuwa a duniya. ƙididdigar da shafin Internet Live Stats
(www.InternetLiveStats.com) ya gabatar a shekarar 2014 ya nuna cewa kimanin kashi 40.4% na
al’ummar duniya ke iya amfani da intanet, idan aka kwatanta shi da kashi 18% da ke amfani da
intanet a shekarar 2006, wannan ba ƙaramin cigaba ba ne, kuma yana nuna irin karɓuwar da
intanet take daɗa samu a faɗin duniya. A dalilin haka intanet ta kasance babbar hanyar sadarwa
mafi sauƙi da kuma sauri. Shi ya sa Turawa suka riƙe ta a matsayin makamin ‘shirin game
duniya’ (globalization) ta hanyar amfani da harshen Ingilishi, kamar yadda aka bayyana a baya.
Wannan muƙala ba ta ƙi aminta da wannan bayani ba ne, sai tana hasashen cewa Hausa tana da
gudummuwar da za ita bayarwa domin ta amfana kuma a amfana da ita a kan intanet. Bugu da
ƙari, wannan shi ne dalilin da ya sa intanet ta kutsa cikin kowane sha’ani na rayuwa na yau da
kullum. Ga wasu bayanai da misalai na wasu hanyoyi da ake iya cin gajiyar intanet. Wasu
hanyoyin an daɗe da fara cin amfaninsu, wasu kuwa yanzu aka fara, wasu kuma ci gabanmu bai
kai gare su ba tukuna, amma dai mu je zuwa.

3.2 Kasuwanci A Kan Intanet (internet banking)


Wannan wani muhimmin ɓangare ne da ya samu kulawa sosai a intanet. Intanet ta
kasance wani babban dandali ko cibiyar kasuwanci ta duniya a yau. Wannan ɓangare na cin
gajiyar intanet shi ake kira ‘e-commerce’ a Ingilishi. Ayo da wasu (2011) sun bayyana cewa:
E-commerce is the use of internet for marketing, identification,
payment and delivery of goods and services. Through the ecommerce
technology consumers haɓe the ability to bank, invest,
purchase, distribute, communicate, eplore, and research from
ɓirtually anywhere, anytime where there is internet Access.

Fassara:
Kasuwanci a kan intanet shi ne amfani da kafar sadarwa ta intanet
domin saye ko sayarwa ko tallata haja ko biyan kuɗaɗe kamar na
sufurin kayayyaki duk a kan intanet. Haka kuma masu amfani da
hanyar kasuwanci a kan intanet suna da damar yin hulɗa da banki
da yin dillanci da saka hannun jari da gudanar da bincike kan hajoji
a ko’ina suke a duniya kuma a kowane lokaci matuƙar suna da
damar amfani da intanet.

https://www.amsoshi.com/2017/09/27/jagora-ga-amfani-da-intanet-don-bunkasa-harshen-hausa/

Wannan bayanin ya nuna cewa ana iya cin gajiyar intanet ta hanyar gudanar da
kasuwanci ba tare da an ɗauki lokaci zuwa kasuwa ko kantuna ba. Mai amfani da intanet zai iya
yin zaune a gidansa ya yi cinikin duk abin da yake buƙata, ya biya kuɗi, kuma a kawo masa abin
da ya saya har ƙofar gidansa. ƙasashen nahiyar Turai da dama sun daɗe da fara morewa irin
wannan ci gaban. Kodayake dai wannan ci gaban babban baƙo ne a ƙasar Nijeriya. A halin
yanzu wannan hanyar kasuwancin ta fara samun kulawa a ƙasar nan. Ayo da wasu (2011) sun
tabbatar da cewa a Nijeriya akwai shafuka aƙalla guda huɗu waɗanda suke ba da damar amfani
da wannan kafar ta kasuwanci. Alal misali akwai shafuka kamar: www.234world.com da
www.ɗtaples.net da www.booksng.com da www.oderbay.com. Kodayake wannan bincike ya yi
ƙoƙarin ziyartar waɗannan shafuka, amma abin ya ci tura. Saboda haka wannan bicike ya kawo
wasu shafuka waɗanda ake iya gudanar da hulɗar kasuwanci ta intanet da su. Ga shafukan kamar
haka: www.konga.com da www.jumia.com.ng. Duk da kasancewar irin wannan ci gaban yana
kusa da al’ummar Hausawa, hakan bai sa Hausa ta yi wani abin a-zo-a-gani ba ta wannan
ɓangaren na kasuwanci a kan intanet. Saboda haka wannan bincike yana kira ga manyan ‘yan
kasuwa na ƙasar Hausa, musamman waɗanda suka mallaki manyan kantuna, da su dubi yiwuwar
shiga sha’anin kasuwanci na intanet.
Sha’anin kasuwanci a intanet ba nan kaɗai ya tsaya ba. Ayo da wsu (2011) sun bayyana
cewa, ta amfani da intanet ana iya gudanar da wasu harkokin kasuwanci daban-daban, kamar
biyan kuɗaɗe ta intanet (e-payment) da hulɗa da banki da intanet (e-banking) da kuma yin
rinjista ta intanet (e-registration). Ga ƙarin bayani a kan kowace hanya daga cikinsu:

3.2.1 Biyan Kuɗaɗe Ta Intanet (e-payment)


Kenny, (2003) ya bayyana cewa intanet ta kawo sauƙi ƙwarai ga harkar biyan kuɗi a
wannan zamani. Misali, a halin yanzu ana iya biyan kuɗin haraji na gwamnati; ko biyan kuɗaɗen
amfani kamar na hotel da kuɗin lantarki na PHCN da kuɗin haya; ko biyan kuɗin tikitin jirgin
sama da wasu kamfanoni duk a kan intanet. Bayanan da wannan muƙala ta samu daga shafin
www.firs.goɓ.ng (2013) sun bayyana cewa, mai amfani da intanet zai iya shiga wannan shafin
domin biyan kuɗinsa na haraji. Wannan adireshi na shafi Federal Inland Reɓenue Service (FIRS)
ne wato Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga na cikin ƙasa. Bayanin ya nuna cewa tun daga farko sai
an ziyarci ofishin FIRS an yi rijista da su. Bayan ka yi rijista, za su ba ka lambar da za ka riƙa
yin amfani da ita duk lokacin biyan kuɗin haraji. Wannan lamba ita ake kira Taɗ Identification
Number (TIN) da Ingilshi, mun ari sunanta muka fassara shi da Lambar Tantance Biyan Haraji.
Daga nan sai ka ziyarci shafin nasu mai adireshin da muka kawo a sama domin ci gaba da biyan
kuɗinka na haraji kan intanet.
Mai amfani da intanet zai iya ziyartar shafin hotel ko na wani kamfani da yake haya da su
domin biyan kuɗin hayarsa. Alal misali, mai bincike ya ci karo da wani bayani a shafin
www.tolet.com.ng (2013) kan yadda mai amdani da intanet zai iya biyan kuɗinsa na haya a kan
intanet. Kodayake wannan kamfani yana samar da gidajen haya ne ga mazauna garin Abuja da
Lagos kawai, saboda haka sai mazauna waɗannan garuruwa ne za su iya more wannan damar ta
biyan kuɗin haya a kan intanet. Bayanin ya farad a cewa, tun daga farko sai an yi rijista da
wannan kamfani a shafinsu na intanet. Bayan an yi rijista, ana iya shiga shafinsu domin dudduba
gidajen haya waɗanda ke ƙarƙashin kulawarsu a wannan lokaci. Idan ka samu gidan da ya yi
daidai da ra’ayinka da kuɗinka, sai ka zaɓe shi domin ganin dukkan bayanansa. Idan bayanan
sun yi maka daidai, sai ka wuce shafin da za ka biya kuɗin hayar. Kurbalija (2010) ya yi ƙarin
haske a kan irin wannan hulɗa, ya bayyana cewa irin waɗannan shafuka suna karɓar biyan
kuɗaɗe ta amfani da MasterCard da kuma ɓisaCard, kuma a shafukan nasu za ka shigar da
lambar katinka ta MasterCard ko ɓisaCard da kuma sauran bayananka na banki. Daga nan za su
tuntuɓi bankinka domin tantance bayananka. Idan komai ya yi daidai, za su cire daidai kuɗin da
ya kamata su cire. Daga nan sai a ba ka damar ka gurza shafin a matsayin rasitinka. Duk wannan
je-ka-ka-dawo ba zai wuce cin minti biyar ba in dai akwai kyakkyawan sabis na intanet.
Bugu da ƙari, ana iya biyan kuɗin sufuri na jirgin sama a kan intanet. Harkar sufuri ta
jirgin sama ita ce ta fi kowacce bunƙasa a sha’anin sufuri a nan Nijeriya. Kamfanonin sufurin
jirgin sama kamar Air Nigeria da Airik Air da Dana Air duk sun mallaki shafukan kansu a
intanet. Alal misali, mai tafiya zai iya ziyartar shafin kowane ɗaya daga cikin shafukan
waɗannan kamfanoni domin biyan kuɗin tikitinsa. Alal misali, bayanan da mai bincike ya ci
karo da su a shafin www.arikair.com (2013) sun bayyana cewa ana iya biyan kuɗin tikiti na jirgi
zuwa inda ake so a cikin Nijeriya a kan intanet. Idan aka shiga wannan shafin, a shafin farko ne
mai amfani da intanet zai zaɓi ƙasar da yake. Idan aka zaɓi Nijeriya, sai shafinsu na Nijeriya ya
buɗe. A cikin wannan shafi ne za a zaɓi lokacin da ake buƙatar tafiya da sauran bayanai. Daga
nan za a je shafin da za a biya kuɗin jirgi. A wannan shafin ne za a buƙaci mai amfani da intanet
ya ba da lambar katinsa na MasterCard ko ɓisaCard da kuma lambar sirri. Daga nan za su
tuntuɓi bankinka domin tantance sahihancin bayanan da ka bayar. Idan komai ya yi daidai, za su
cire daidai kuɗinsu. Shi kenan an kammala hadahadar, sai a ba ka dama ka fitar da takardar
tikitinka. Shi kenan an kammala biyan kuɗin jirgi. Ita ma dai wannan hulɗa ba za ta wuce cin
minti biyar ba idan akwai kwakkyawan sabis na intanet.
Abin lura a nan shi ne duk waɗannan hulɗoɗi ko hadahadar kasuwanci ta intanet ba za ta
wuce cin minti biyar ba idan akwai kwakkyawan sabis na intanet. Kenan an taƙaita wa mutane
ɗawainiyar tafiya shaguna ko kantuna ko bankuna ko wasu ofisoshin domin biyan kuɗaɗe na ireiren
waɗannan huldoɗi da muka ambata a sama. A nan, wannan muƙala tana ganin cewa idan
aka samar da wani ɓangare na waɗannan shafuka cikin harshen Hausa zai ƙara bunƙasa cigaban
tattalin arzikin al’ummar Hausawa da kuma haɓaka harshen Hausa. kodayake wannan kaɗai ba
zai yiwu ba sai ɗalibai da manazarta da kuma masana Hausa sun ba da ta su gudummuwa wajen
bunƙasa keɓaɓɓun kalmomin intanet na Hausa. Sannan su kuma ƙwararrun masu gina na’urorin
kwamfuta da intanet (software engineers and web programmers) su iya yin wani abu a harshen
Hausa. Kenan dai, har yanzu Hausa ba ta kai ga wannan matsayi na yin kasuwanci a kan intanet
ba.

3.2.3 Hulɗa da Banki ta Intanet (mobile banking)


Kenny, (2003) ya bayyana cewa intanet ta kawo sabuwar hanyar tu’ammali da kuɗi a
wannan zamani da muke cike. A yau mai amfani da intanet zai iya zamansa a gida, ya kuma biya
buƙatarsa ta mu’amala da kuɗi tsakaninsa da banki ba tare da ya ɓata lokacinsa zuwa bankin ba.
Mai amfani da intanet zai iya biyan kuɗin cinikin da ya yi a kan intanet, kuma a kawo masa hajar
da ya saya har ƙofar gidansa. Haka kuma, zai iya tura kuɗi zuwa asusun wani a kan intanet. Zai
iya biyan kuɗaɗe kamar kuɗin makaranta ko kuɗin hotel a kan intanet. Babbar kasawar wannan
hanya ita ce rashin damar iya riƙe kuɗi tsabarsu a hannu. Domin samun mafita ga wannan
kasawar, sai wasu bankuna suka buɗe cibiyoyin gudanar da hulɗar banki ta intanet (e-banking
centers). Waɗannan tamkar harabar gudanar da hulɗar banki ce, sai dai waɗannan babu
ma’aikata a cikinsu. Da shigarka cikin ɗakin za ka tarar da manyan injuna na ATM biyu ko uku
ko fiye da kuma kyamara (abin ɗaukar hoto) a cikinsu. Amfanin kyamarar shi ne domin kiyaye
tsaro na masu shige da fice a cikin harabar. Na’urar ATM ita ce take ciro maka kuɗi daga
asusunka na banki. Haka kuma za ka iya saka kuɗi cikin asusunka ta wannan ATM. Za ka iya
tura kuɗi zuwa asusun wani ta wannan ATM. Sauran hanyoyin amfani da ATM su ne biyan
kuɗin lantarki na PHCN da sayen katin waya. Bayan wannan kuma, cigaban intanet ya kawo
cewa yanzu mai amfani da intanet zai iya yin hulɗa ta banki ko’ina yake, matuƙar dai yana da
wayar salula ko tabileti (irin ipad da palmtop) wadda ke iya shiga intanet, sannan yana da sabis
na shiga intanet a na’urarsa. Wannan cigaba zai iya inganta tattalin arziki, domin an rega wa
jama’a wahalar kai-da-kawo zuwa banki ko ɗakin ATM. Haka kuma, idan aka ƙara bunƙasa
wannan hanya ta kai ga katse tankiyar da ke tsakaninta da harsunan Nijeriya, ba ƙaramin sauƙi
cigaba za a samu ba. Alal misali, idan aka fassara hanyar hulɗa da intanet ta na’urorin hannu
(mobile banking) zuwa harshen Hausa, ai ka ga da farko dole a tuntuɓi ɗalibai da masana Hausa
domin yin wannan aiki; na biyu Hausa za ta ƙara martaba kuma darajarta ta ɗaukaka a kan
intanet.

3.3 Samar Da Ayyukan Yi


Manyika, da Roɗburgh, (2011) suna da ra’ayin cewa intanet a yau ta kasance wata babbar
kasuwa mai samar da ayyukan yi ga jama’a. Aikin yi shi ne wani abu da mutum zai yi domin a
biya shi ladar aikinsa. A yau, akwai nau’o’in ayyuka daban-daban da ake aiwatarwa ko dai a kan
intanet ko kuma waɗanda suka danganci intanet domin samun abin hannu. Morton (2006) ya
bayyana cewa daga cikin ayyukan da ake aiwatarwa a kan intanet akwai talla kan intanet (online
advertisement) da kula da kafar shiga intanet (network administration) da tsarawa da gina
shafukan intanet (web design) da kuma kula da intanet da hanyar sadarwa ta intanet (network
and web administration). Duk waɗannan sababbin ayyukan yi ne da intanet ta kawo. Haka kuma,
Aliego da Aliogor (2010) sun bayyana cewa akwai harkokin tallace-tallace da intanet ta kawo
(online advertisement). Alal misali, ana tallata gurabun neman aiki na ma’aikatu da kamfunna a
kan intanet, ana kuma tallata kowace irin haja a kan intanet. Yanzu haka akwai shafuka dabandaban
da suka shahara a kan samar da bayanai na gurabun ayyukan yi a ko’ina a duniya. Misalan
waɗannan shafuka su ne: www.jobberman.com (a ƙasar Nijeriya) da www.careerbuilder.com (a
ƙasar Amurka) da www.naukri.com (a ƙasar Indiya). Bayan wannan, akwai wani samfurin talla a
kan intanet (online advertisement) wanda yake *****
A lura cewa waɗannan hanyoyi na bunƙasa tattalin arziki da intanet ta kawo, an yi musu
bugun ɗiyan kaɗanya ne, saboda dukkansu a halin yanzu ba wanda ake aiwatarwa ƙarƙashin
ƙwarewa da harshen Hausa. Wato ɗaliban Hausa sai sun falka daga bacci sun rungumi karatun
wasu abubuwa game da kwamfuta da yawaita amfani da kwamfuta da sa kai cikin al’amurran
intanet sannan za su iya cin moriyar waɗannan hanyoyi na bunƙasa tattalin arziki. Ya kamata
ɗalibai su sani cewa, dukkan waɗannan hanyoyi na samar da ayyukan yi masu tsoka ga ɗimbin
mutune waɗanda galibinsu ba Hausawa ba ne, ba ɗaliban Hausa ba ne, sannan ba Hausa suke yi
wa aiki ba; saboda haka ayyukan da suke yi ba zai taimaka ga bunƙasa tattalin arzikin Hausawa
ba, ballantana a yi maganar haɓaka Hausa ko yayata ta.

4.1 ƙalailace Bincike


A yau, amfani da intanet ya zarce duba imel (email) ko fezbuk (Facebook) ko was’af
(WhatsApp) Tuwita (Tweeter) da link’in (LinkedIn) da instagaram (Instagram) da sauran
shafukan sadarwa na walwala a kan intanet. Hanyoyi da aka tattauna kansu a cikin wannan
muƙala na bunƙasa tattalin arziki da suka haɗa da hulɗa da banki kan intanet (internet banking)
da kasuwanci kan intanet (e-commerce) da talla kan intanet (online advertisement) da kula da
kafar shiga intanet (network administration) da tsarawa da gina shafukan intanet (web design) da
kuma kula da shafukan intanet (web administration) duk hanyoyi ne na cin gajiyar intanet kuma
masu amfani. Ana iya amfani da kowace daga cikin waɗannan hanyoyi kai tsaye ta amfani da
kwamfuta ko kuma wayar salula ko na’urar hannu (tabileti). Babban abin sha’awa game da
intanet shi ne ɗauke wa mai amfani da ita wahalar tattaki zuwa biyan wasu daga cikin buƙatunsa
waɗanda ake iya aiwatarwa ta amfani da intanet. Alal misali, intanet ta ɗauke wa mai amfani da
ita yawon zuwa wasu shaguna da kantuna; intanet ta ɗauke wa mai amfani da ita wahalar yawon
neman jaridu da mujallu; intanet ta sauƙaƙa wa mai amfani da ita ɗawainiyar zuwa biyan kuɗin
jirgi ko na lantarki ko na haya; intanet ta taimaka wajen samar wa wasu jama’a ayyukan yi;
intanet ta rage wa mai amfani da ita ɗawainiyar yawon neman aiki, ga su nan dai. Waɗannan duk
suna daga cikin cigaban da intanet ta kawo ta fuskar bunƙasa tattalin arziki; duk da yake dai ba a
fara damawa da Hausa a kan wasu ɓangarori na cin gajiyar intanet, fatar wannan muƙala ita ce
zaburar da ɗaliban Hausa da Hausawa domin su tashi tsaye su samar wa Hausa ‘yanci ta samu
mallakar wasu muhimman ɓangarori na intanet. Wannan zai samu ne kaɗai idan an waiwaya an
bunƙasa samuwar keɓaɓɓun kalmomin intanet da sha’anin kwamfuta da na ginin sofwayasofwaya
cikin harshen Hausa.

https://www.amsoshi.com/2017/08/22/duniyata-kashi-na-farko/

5.1 Shawarwari


Ta la’akari da bayanan da aka gabatar da abubuwan da suka biyo baya, wannan muƙalar
tana ganin cewa samun wadatattun keɓaɓɓun kalmomin intanet na Hausa zai taimaka wajen ƙara
kawo gajiya ta intanet kusa ga al’ummar Hausawa. A kan haka, wannan muƙalar take ba da
shawarwari kamar haka:

1. Tsamo keɓaɓɓun kalmomi da taskace su wani jan aiki ne da yake buƙatar ƙwarewa tare da
samun tallafi. Da farko dai dole malamai da hukumomin jami’a sun shiga ciki. Saboda haka
sai hukumomi da ‘yan kasuwa da masu hannu da shuni sun ba da gudummuwa ƙwaƙƙwara
wajen ci gaba da bunƙasa taskace keɓaɓɓun kalmomi a sha’anin intanet.

2. Ya kamata attajirai da ‘yan kasuwarmu su yi nazari kan irin ɗimbin ribar da ke cikin saka jari
a sha’anin sadarwar kwamfuta. Dalili kuwa shi ne, ƙididdigar 2013 ta Forbes a shafin
www.forbes.com ta lisafo Mr. Bill Gates a matsayin ɗaya daga cikin manyan masu kuɗi na
duniya. Haka kuma a jerin masu kuɗi ‘yan ƙasa da shekaru 40 waɗanda suka yi fice a
duniya, akwai mutane goma waɗanda dukkaninsu suna tafiyar da harkokinsu ko dai a kan
sha’anin kwamfuta ko intanet ko kuma sadarwa ta zamani ne. Wannan yana nuna irin ribar
da ke cikin ɓangaren kasuwanci na kwamfuta ko sha’anin intanet. Saboda haka ake ba da
shawara ga ‘yan kasuwa da su dubi yuwuwar saka jari a wannan ɓangare.

3. Ya kamata Hausa Language Board (Hukumar Kula da Harshen Hausa) ta ƙara tashi tsaye
domin tabbatar da daidaito a ƙoƙarin samar da keɓaɓɓun kalmomi a Hausa.

4. Masana da manazarta da ɗalibai masu nazarin Hausa a kowane mataki su taimaka a bunƙasa
ire-iren wannan bincike. A ƙara ƙoƙari domin tsamo wasu ɗaruruwan keɓaɓɓun kalmomin
intanet na Hausa waɗanda wannan bincike bai kawo ba. Yin haka zai ƙara ɗaga matsayin
harshen Hausa a sha’anin intanet da kwamfuta.

5. Ya kamata Hausawa su shiga cikin sha’anin nazarin fannin kwamfuta, su yi ruwa, su yi tsaki
a dukkan ɓangarorinta.


6.0 Kammalawa


A wannan ƙarni da muke ciki (ƙarni na ashirin da ɗaya), intanet ta riga ta shiga gaban
kowace hanyar sadarwa ta wannan zamani. A kan haka, wannan muƙala ta kammala da cewa
Hausa tana da haske a sha’anin intanet. Sai dai akwai ƙalubale ga ɗalibai da manazarta wannan
harshe, matuƙar suna son harshen ya ci gaba da haskakawa a duniya, dole ɗalibai da manazarta
Hausa su dage wajen koyon amfani da kwamfuta da kuma intanet. Sannan su tashi tsaye a dama
da su a ɓangaren amfani da intanet. Daga ƙarshe, muƙalar tana kira ga ɗalibai da manazarta
Hausa da su ƙara ƙoƙari wajen amfani da intanet wajen taskace sahihan bayanai domin bunƙasa
bincike da nazarin harshen Hausa.

7.0 Manazarta


Aliego, J. E. da Aliogor, O. (2010). Total Free Browsing and Simple Ways to Make Money
Online. Enugu: De Joe Publication and Communication Limited.
Almajir, T. S. 2008. Hausa da Sadarwar Intanet. Harsunan Nijeriya, Vol. ɗɗI. CSNL - BUK,
Kano, Nigeria.
Amfani, A. H. 2007. “Globalization and Documentation of Nigerian Languages.” Paper
presented at the 21st Conference of Linguistics Association of Nigeria (LAN), University
of Uyo, Akwa Ibom State, Nigeria.
Ayo, C. K., Adewoye. J. O. and Oni, A. A. 2011. “Business – to – Consumer E-Commerce in
Nigeria: Prospects and Challenges.” cikin African Journal of Business Management. Vol.
5 (13). Pp. 5109 – 5117. A shafin http://www.academicjournals.org/AJBM DOI:10.5897
AJBM10.822
Becker, S., et al 2010. Opportunity for All: How the American Public Benefits from Internet
Access at U.S. Libraries. Washington, DC: Institute of Museum and Library Services. A
shafin http://www.tascha.washington.edu/usimpact.
Crystal, D. 2001. Language and the Internet. Cambridge: Cambridge University Press.
Illingworth, ɓ. (ed.) 1996. Oxford Dictionary of Computing. New York: Oxford University
Press.
Kenny, C. 2003. “The Internet and Economic Growth in Less-developed Countries: A Case of
Managing Eɗpectations?” a cikin Oxford Development Studies, Vol. 31, No. 1. Oxford:
International Development Centre. ISSN 1360-0818 print/ISSN 1469-9966
online/03/010099-15. DOI: 10.1080/136008103200004721.
Manyika, J. da Roɗburgh, C. 2011. The Great Transformer: The Impact of the Internet on
Economic Growth and Prosperity. London and San Francisco: McKinsey Global
Institute.
Morton, F. S. 2006. “Consumer Benefit from Use of the Internet.” cikin Adam, B. J., Josh, L.
and Scott, S. (editoci). Innoɓation Policy and the Economy, Volume 6. available at:
http://www.nber.org/books/jaff06-1; http://www.nber.org/chapters/c0205
Muhammad, ɗ. 2004. “Hausa a Duniyar Yau: Tasirin Game Duniya Kan Harshen Hausa”. Cikin
Yalwa, L.
D. da wasu editoci (2011). Studies in Hausa Language Literature and Culture
– Proceedings of the Sixth Hausa International Conference – Center for the Study of
Nigerian Languages, Bayero University, Kano, 15th
– 17th December 2004. Zaria:
Ahmadu Bello University Press Limited.
Mwangi, J. 2014. “Open for Business? the Economic Impact of Internet Openness” daga shafin
http://www.dalberg.com ranar 1 ga watan Maris 2016.
Rumšiene. G. 2004. “Development of Internet English: Alternative Leɗis, Syntax and
Morphology.” cikin KALBU STUDIJOS No. 6. ISSN 1648-2824.
SYBEX;. 2000. Dictionary of Networking. Sybex; – Alameda, CA. a shafin
http://www.sybex;.com.
Tsangarwa, A. M. 2006. Kwamfuta a Sauƙaƙe. Kano: Dandalin Fagge.
Ureigho, R. J., Oroke, G. U. da Ekruyota, G. O. 2006. “The Impact of Internet Usage: A case
study of Delta State (Nigeria) Tertiary Institutions” cikin Scientific Research and Essay
Vol. 1 (2), Pp. 054 – 056. a shafin http://www.academicjournals.org/SRE.
Williams, C. da Strusani, D. 2014. value of Connectiɓity: Economic and Social Benefits of
Expanding Internet Access. Deloitte, London: The Creative Studio.
Manazarta ta shafukan intanet
http://www.wikipedia.org
www.jobberman.com
www.careerbuilder.com
da www.naukri.com
www.arikair.com
www.tolet.com.ng
www.firs.goɓ.ng
www.konga.com
www.jumia.com.ng
www.InternetLiveStats.com

Post a Comment

1 Comments

  1. […] KeƂaƂƂun Kalmomin Intanet Da Amfannsu Ga Bunk’asa Tattalin Arzikin K’asa […]

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.