Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayanau Da Amsa-kama A Cikin Wakokin Muhammadu Gambo Fagada

Takardar da aka gabatar a taron ƙara wa juna ilmi na sashen koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato, a kan waƙoƙin Muhammadu Gambo Fagada (mai waƙar Ƃarayi) ranar Assabar 21 ga watan Maris, 2009.

DAGA

Muhammad Mustapha Umar
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya
Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato
Imel: mustaphahausa@yahoo.com
GSM: +2348065466400

1.0 GABATARWA


Fannin ilmin ƙirar kalma kan samar da azuzuwan kalmomi, don samun sauƙin sarrafa harshe da fahimtar abubuwan da ya ƙunsa. Kalmomi kan rabu gida-gida kwatankwacin irin gagarumin aikin da suke gudanarwa. Haka kuma, kalmomi kan faɗa ne a wani rukuni da ya dace da irin ajinsu.
Duk harshen da ya samu gatan a yi nazarin tsarin nahawunsa, to lalle za a tarar masana sun raba kalmomin harshen gida-gida. Abin lura a nan shi ne masana suna da tsari na musamman da suke bi na ba da sunaye ga azuzuwan kalmomi.
Wannan maƙala za ta yi magana ne a kan tsattsafin azuzuwan bayanau da Amsa-Kama a cikin waƙoƙin Muhammadu Gambo Fagada. Waɗannan sassan magana da ke ƙarƙashin ilmin kimiyyar harshe da nazarin nahawun harsuna kan fito jefi-jefi daga bakin Gambo, mai zimmar adabo da waƙa fanɗararriya wadda masana suka daɗe suna kai ruwa rana a kan rukunin da ya dace da ita.
Domin cimma wannan manufa, mun raba maƙalar gida biyar. Da farko akwai gabatarwa, daga nan kuma sai rukunin kalmomi a sashe na biyu. Sashe na uku ya fito ne da ma’anar Bayanau da Amsa-Kama. A sashe na huɗu kuma muka nazarci yadda waɗannan azuzuwan kalmomi ke bayyana a waƙoƙin Gambo. Akwai kuma jawabin naɗewa.

2.0 RUKUNONIN KALMOMI


Rukunonin kalmomi wani tsari ne na kalmomi a jere a cikin jimla masu bayar da cikakkiyar ma’ana. Wato, kalmomin su ke haɗuwa su bayar da jimla. To su irin waɗannan kalmomi na cikin jimla su ake kira sassan magana, ko sassan jimla, kuma su ne ke haɗuwa su ba da zance mai cikakkiyar ma’ana.
Su kuma waɗannan kalmomi na cikin jimla, suna da nasu tsari na musamman, saboda ana kasa su ne rukuni-rukuni, gwargwadon irin aikin da kowanensu yake yi a cikin jimla.
Haka kuma, akan tattara kalmomi masu nasaba da juna a ba su suna guda. Wannan shi ne ajinsu, kuma shi ne sunansu.
Ibrahim da Abdulƙadir (1986) sun kasa kalmomin Hausa zuwa manyan rukunoni tara kamar haka:- Suna, Wakilin Suna (ko lamiri), Fi’ili (ko aikatau), Sifa, Bayanin fi’ili (ko aikatau), Amsa-kama, Mahaɗi, Harafi da kuma Motsin rai. Shi kuma Amfani (2004) ya bayyana wasu matsaloli uku dangane da rabon kalmomin Hausa. Wato a ganinsa.
• Wasu kalmomin Hausa an ba su sunan kashi wanda bai cancance su ba.
• Wasu kalmomi ba a sa su cikin kowane kashi ba.
• Wasu kalmomin har yanzu ba a yi matsaya ba a kansu.
Masanin ya ƙarfafa a kan cewa ya kamata a yawaita bincike a kan ɓangarorin harshe, saboda la’akari da sabuwar fahimta da ke bayyana da kuma sauyin zamani a harkar yau da kullum.
(Amfani, 1996) Akwai mishkila a Hausa dangane da cewa shin ajin kalmomi na amsa-kam ake da shi ko kuwa ajin bayanau? Idan muka duba ƙamusun Bargery (1934) da na Abraham (1947), za mu dga sam babu wani ajin kalmomi na amsa-kama. Duk kalmomin da yau ake kira amsa-kama, a waɗannan ƙamusun guda biyu, bayanau (Adverbs) ne. To, amma Galadanci (1976) da Newman da Newman (1977) da sauran ayyuka na yau, duk sun bambanta tsakanin amsa-kama da bayanau. Dalilin wannan mishkila bai rasa alaƙa da cewa a ilimin kimiyyar harshe, kalmar ‘amsa-kama’ (idiophone) sabuwar kalma ce da aka ƙirƙiro a tsakiyar ƙarni na ashirin. Don haka, sa’ad da aka rubuta ƙamusun Bargery da na Abraham, babu wannan kalma ta ‘amsa-kama’ Wannan shi ya sa ba su yi amfani da ita ba. Yanzu abin da ya rage shi ne a tabbata akwai ƙwararan hujjoji da za a yi amfani da su wajen tantancewa tsakanin amsa-kama da bayanau. Saboda haka bari mu ji abin masana ke cewa game da ma’anar bayanau da amsa-kama, wanda wannan ne zai tabbatar mana da cewa waxannan azuzuwan kalmomi ne mabambanta, kuma masu cin gashin kansu. Abin lura a nan shi ne ajin bayanau ƙarin bayani yake yi game da aiki. Yayin da amsa-kama ke nuna yadda aka yi wani aiki.

3.0 MA’ANAR BAYANAU


Yahaya da wasu (1992) Bayanau kalma ce da ke bayyana aikatau a cikin jimla. Ma’ana, bayanau ke yin ƙarin bayani a kan a bin da aikatau ke ɗauke da shi. A taƙaice, bayanau ƙarin bayani ne da ake samu na yadda aikin ya auku. Junaidu da ‘Yar’adua (2007) Sun bayyana bayanau da cewa, kalma ce ta nahawu wadda ke ƙara bayanin aikin da aka yi. Bayanau wani muhimmin ɓangare ne a cikin jimla wanda ke fitar da ma’anar aikatau. Wato, bayanau wasu kalmomi ne masu ƙara wa aikatau haske, su fito da bayanin yadda aikin ya kasance a cikin jimla.Shi kuma, Bagari (1986) a gudummuwarsa cewa ya yi kalmomin bayanau sun kasu kashi biyu: akwai masu ƙarin bayani ga aikatau, waɗanda suke bayyana lokaci, ko wuri, ko kamanni/yanayin aiki. Irin waɗannan su ne kamar su jiya, gobe, yanzu, ɗazu, waje, ciki, ƙasa da sama. Akwai kuma masu ƙarin bayani ga siffofi ko bayanau ɗan uwansa, kamar su ƙwarai, sosai, garau da shar.
(Wikipedia, the free encyclopeadia) Bayanau kalma ce mai bayyana kowane sashe daga cikin sassan magana, ko wasu kalmomi na aikatau waɗanda ba suna ba. Bayanau kan ƙara bayani a kan aikatau, ko sifa, ko jimloli da wasu kalmomin bayanau. Wato ƙarin haske a kan yadda al’amurra ke faruwa. (Encarta Dictionary, 2009) Bayanau kalma ce da ke bayyana aikatau, da sifa da kuma wani bayanau ko jimla kacokan. (Wehmeier, 2006) Bayanau kalma ce wadda ke ƙara bayani a kan wuri, da lokaci, da yanayi, da sanadi ko nuna matsayin aikatau, da sifa ko wani yanki ko kuma wani bayanau. ( Murthy, 1998) Bayanau kalma ce wadda ke ƙara bayanin ma’anar aikatau, da sifa da wani bayanau. (Nkwocha,2008) Bayanau kalma ce da ke ƙayyade ko kuma bayyana wata kalma. (musamman sifa) a cikin jimla . (Pryse,1984) Bayanau kan ƙara faɗa mana cikakken bayani a kan aikatau, da sifa ko wani lokaci ma yakan ce wani abu game da bayanau. (Aarts, 2001) Bayanau yana aikin fayyace ajin aikatau, da ajin sifa da kuma wasu azuzuwan bayanau.
Da yake an tabbatar da ajin bayanau yana fayyace abin da jimla ta ƙunsa dalla-dalla, musamman ganin babban aikinsa shi ne ƙarin bayani na ƙi-da-ƙari a kan yadda aiki yake gudana a cikin jimla. A taƙaice, wannan ajin kalma kan taimaka wajen yin gwari-gwarin bayanan da suka shafi aikatau, da sifa da kuma wani bayanau a cikin jimla.

4.0 MA’ANAR AMSA-KAMA


( Sa’id, 2006) ya bayyana Amsa-kama a matsayin kalma mai siffanta abin da ake magana akai. Abin nufi a nan shi ne, amsa-kama na aikin fayyace yadda aiki ke aukuwa a cikin magana. Misali:- Audu ya tsaya cik. A nan kalmar cik ita ce amsa-kama, domin tana nuna yadda aka tsayu ko yadda tsayuwar ta kasance. Paul da Roxana Newman (2002) Su ma a ganinsu, amsa-kama kalmomi ne da ke fayyace yanayin sauti, da launi, da bayanin sigar sura da kuma yanayi ko halin da abu yake ciki (Aikatau).
(Zari’a, 1981) Amsa-kama kalmomi ne masu ƙara ƙarfafa abubuwan da suka shafi launi, ko sifa, ko sigar sura, ko wani hali da mutum ko wani abu ke ciki da dai sauran irin waɗannan fannoni. (Cole, 1955) Amsa-kama kamancen sautuka ne, ko launi, ko ƙamshi, ko na yanayin abu, ko abin da ake iya gani, da matsayin abu, ko abin da ake iya aikatawa, ko nuna tsananin kyawon wani abu. Misali zane ko hotuna, ko kuma abubuwa masu wakiltar ido wajen kallo, ko saurare da wasu fannoni masu ba mutum damar fahimta ko lura da abu, da kuma kalmomi masu nuna gogewa da yadda ake aiki da hankali. (Wikipedia, the free encyclopeadia)
Amsa-kama kalmomi ne waɗanda mai magana ke amfani da su domin bayyana abubuwan da ake iya ji ko tantancewa ta hanyar taɓawa, ko waɗanda ake iya gani a kuma fahimta. Misali; ƙamshi, da launi, da girman abu, da sauti, da abin da ake iya amfani da shi ko kuma abin da ke iya motsawa. Misali daga nan zuwa can.
Amsa-kama dai, kalmomi ne waɗanda ke ƙarin bayani a kan aikatau, ko siffanta yadda aikin aikatau yake gudana a cikin jimla. Sai dai kalmomin amsa-kama suna da ɓirɓishin jawo hankali da haifar da motsuwar rai.

5.0 BAYANAU DA AMSA-KAMA A CIKIN WAƘOƘIN GAMBO


A wannan ɓangare, za a kawo jerin baitoci da ɗiyan waƙa daga
Waƙoƙin Muhammadu Gambo. Wannan shi zai nuna yadda kalmomin Bayanau da Amsa-kama ke gagarumin aikin ƙarin bayani a kan aikatau da kuma nuna yadda aiki ya ke aukuwa a cikin hikima.
Da yake sharhi za a yi a kan yadda waɗannan kalmomi ke aikinsu a cikin wasu baitocin waƙar Gambo mijin Kulu. Da farko an fara da misalai masu ɗauke da ajin bayanau, sannan daga baya aka zayyano masu ɗauke da ajin amsa-kama. Kuma za a bayyana kalmomin bayanau da amsa-kama ƙarara, ta hanyar ƙara musu duhu da dabarar jan layi, domin kawai a iya tantance su a ko’ina suke a cikin baitocin da muka kalato.

MISALAN BAITOCI MASU ƊAUKE DA BAYANAU


In Tudu yak karya na nan ga
Ni ko in gilma na nan ga
In nig ga awa dai zai kula ni
In karkata kai in ƙalli rakke
Ba shanyewa za ni yi ba.

In tsoho yaw waiga hakan ga
Ni ko in tarba na nan ga
In nig ga alamun zai kula min
Sai in yi wurin ‘yan koli sada
Ina cinikin banza da yohi
Ko an bar min ban biya nai.

Da yaz zaka ya leƙa ijiyatai
Yar rega na nan ga
Sai yac ce, daga nan haka
Gina ta yi ƙunji
Sai yac ce, a kawo gireda.

Waɗannan kalmomin bayanau sun ƙara haske ne a kan yadda aka gilma ko kuma yanayin ƙoƙarin riskar wani lamari, da yadda Tudu Tsoho ya waiga sa’adda Gambo ke kwararar sa. Haka kuma mawaƙin ya nuna fasalin da ido kan ɗauka lokacin da ake satar kallon wani abu ko kuma kallo na ƙoƙarin ƙwalelece abu.
Ya biyo tsoho sun ci Romo
Mun ka taho daji sukane
Garin- da- garin ko ga ni ga shi
Jakkan tsoho ba su hurji
Shaggu ba kaye su kai ba
Shi ko, tsoho ba ya kora.

Gambo ya tabbatar da yadda suka runtuma cikin daji a guje tare da Tudu Tsoho, lokacin da Muhammadu Inuwa ke laɓaɓar baba.
To in ishe mai kuɗɗi tsugunne
In ga yana naso ga goshi
Ya ɗaura gumi bai yo gudu ba
Kamar da kunama sun da sadu
Nic ce ko in iske mai jikka tamanin
Yai zugum ya sadda kai ƙas
In ga hawaye na zubo mishi
Ba shi da ko sisi ga ran.

To mai ɗunkin tela ya tara kowa tara laihi
Ya dai gunci na liman ya zube ƙasa
Tela ya gunci na malam ya zube ƙasa
Ya ɗebi na…..

Sai nik koma ga kan Tudu
Nic ce tsohon kolo
Kai kad daɗe tudu
Mai hana maiki cin idanu
Gabanka gaba sai ya yi yamma
Yara ba su ganin tashin ƙahwakka
Sai yac cire hulla yak kihe ƙasa
Hulas saƙi ag ga baba duk ko layu sun cika ta
Sai yac ce min ga ɗan gaton uwa.

Sadda nay yi sago
Nis sadda kai ƙasa
Nit tuna Inuwa Ɗanmadwacci.

Su ma waɗannan kalmomi sun bayyana mana bagiren da aka zubar da wani abu, musamman guntayen kyallayen da tela ke zubarwa lokacin da yake aikin ɗinki. Akwai inda aka nuna wurin da aka kife hullar saƙin nan ta baba, wadda ke cike da layu. Mawaƙin ya fayyace yadda ake sunkuyar da kai a riƙa kallon ƙasa saboda zurfin tunani da shiga wani yanayi na ya-ni -‘yasu.

Kyautar mai kuɗɗi ‘yar taƙi ta
In an yi bukin dangi shi nai ma
In an yi bukin salla shi nai ma
Amma a ba ka yau, a ba ka gobe
Kuma jibi a ‘yamma ba a gaza ba
Wallahi ɓarawo ɗai ka yin haka
Ba da guminai na shi kai ba.

Kukan zakaran hwarin ina zamne
Nig ga swahiya ta daɗe ba ta waye ba
Niy yi kiran salla da daddare
Ni dai a de yi ta waye in ga ɓanna
Nid dai matsu baw waye ba ran nan.

Samin hwarin malam Na Gambo
Ka ji masu shiga ɗaki da daddare
Ko kusu ya hi su motci.

Lalle a nan an nuna lokacin da ɓarayi ke cin karensu ba babbaka musamman cikin dare, kuma kalmar da daddare na bayyana lokacin da wani aiki ko al’amari ya auku, lokaci ne na fataken dare, waɗanda sau tari ba a kwana da su ba aka tashi da ta’asar da suka guma wa jama’a.
Sai yac cira tsaye nig ga jikinai na kaɗawa
Haw wani daɗi ya ƙume ni
Na aza dan nan zai wucewa
Su tai su yi gomozo da baba
Yac ce Najeriya duka
Sai nic ce mai Tudu tsoho yat taɓa ni
Sai yay yi kwatakyas yah hwaɗi zamne
Sai nic ce babbab bura uban ga
Sarki ka ji tsoro
Mi ar ranay yaƙin talakka.

Sai yay yi wata kuwa yac cira tsaye
Yay tsalle yah hwaɗi zamne
Yac ce ayyiruru Gambu mijin Kulu
Wai tuba ta tashi yanzu
Mallami da sakin doka ga kainai
Ya baɗa hoda ya yi gazal
Ba ta batun salla akai.

Kalmar tsaye ta fayyace mana abin da ya faru bayan ɓarawon da Gambo ya tunzura ya miƙe tsaye. Sannan kalmar zamne ta sanar da mu yadda mijin Gambo ya faɗi yayin da ya ji tsoron gomozo da Tudu Tsoho.
In don ka tsira ƙiyama ka aje na
Nic ce koma ka yi sata in gaya ma
Gobe ƙiyama in da za ka ba ishe sauƙi za ka yi
Ka cika littafinka dauri
Hab bisa bainai an rubuta
Nic ce wallahi han na maƙwabta an ɗiga mai.

Lalle Gambo ya sarrafa bayanau kamar yadda ya kamata, domin a nan ya nuna mana lokacin da aka aiwatar da wani aiki. Misali shin yanzu-yanzu ne aka yi abu? Ko an kammala aikin, ko an daɗe da yin sa. Waɗannan kalmomi sukan ƙara haske ne matuƙa a kan lokacin aiki da kuma ranar da ake maganar an yi aiki, musamman yadda ya ƙyallaro mana lokacin da Nazaƙi ya tada tuba nan take.
Don ana ta bugu ne tun yana tsaye
Mugu hay yah hwaɗi kwance
Ko kahin holis su amsai
Kaico tarin dutci gaban bawa
Na ga tarin da yay yi hakan ga.

Lokacin da aka tada mijin Gambo Bawa a kasuwa Gummi. Bayanau a nan ya bayyana mana yadda aka yi duka irin na ribiti ko taron dangi wanda jama’a ke yi wa ɓarawon da dubu ta cika. An kuma nuna inda wanda aka daka ya faɗi. Wato ya faɗi ƙasa kuma kwance ga lala.
Sai la’asar ta yi Gambo
Masu jalli dus sun hallara
Sa’adda za ya saye ‘yan cefanan nan
Shi sa’annan yake ɗauko bokitinai
Ya saye Kwanon gumi ɗaya
Ya ƙunsa nama ya nasa ciki
Ya sai tattasai ga attarugu.

Di’on kaji in ka iske shi
Kana aza tsoho ne na gaske
Ya sami gahwakka ya laƙakke
Ga shi da babbat tasbaha shi
Akwai shi da buta ya laƙe haka
Ga ko gwami ya haɗa
Ya saƙi ƙugunai hakan ga
Yana susan ƙugun shi sosai
Kana aza tsoho lahiya yake.

Ba sata mai ban takaici
‘Yansanda ke sata mai ban takaici
Ai in kah hwaɗi da mota kam mace duka
In akwai ka da kuɗɗi sun yi dubbai
In dai dangi ba su na nan
Ba ishe ko sisi akai ba.

Sai yad duƙa yas sabke akwati
Mun hito wuri
Muna tahiya mu lahiya lau.

A nan za a ga yadda ake aikata wani aiki cikin hanzari, ko a hankali ba tare da garaje ba. Wani lokaci ma, kalmomin kan nuna yadda abu ke kasancewa cikin sauri da kuma tsanani ko rashin tashin hankali yayin kai-da-kawon rayuwa. Akwai kuma bayyanar inda aka ke ko inda aka je yayin gudanar da wani al’amari. Wato, cikin gida ake ko a wajen gida ne ake tsaye. Haka kuma, yanayin da ke bayyana na ƙarewar al’amari ko fakuwarsa.

MISALAN BAITOCI MASU ƊAUKE DA AMSA-KAMA


Ina bisa dutci ban cika ba
Sai gangara dutci
Kai
Nan gag ga rahi
Komi adadi nai na tahowa
Nan bakin ɗan marmaron nan
Nan inda ruwa ke hwara yoyo
Nan ni ishe tsoho kwance jicce
Nig ga ƙudahi sun ruhe shi
Sai nik kama haɓatai nit taɓa haka
Nic ce tsoho ai na hwaɗa ma
Ni ah hitinash sheri mijin Kulu
Gambo da iska bai kashewa
Ka ce in zo da dubu had da dubbai
Ga shi guda ɗai ya kashe ka.

Lokacin da yac cirri yuƙa yak kihwa mat
Tai kuwa tah hwaɗi jicce
Nan wani daɗi sai yaƙ ƙume ni
Mun bar su da gawa kwance sharkaf
Mu ga mu da kuɗɗi lahiya lau.

Sai muna rigima shiguhwa na ƙurya
Sadda Alhaji Mamman yac cira ta
Macce na ga gado tai kwance rairan
Tana da ciki ya kai wata tara
Ashe ita ba kwana ta kai ba

Wannan kalma ta jicce ta nuna yadda Tudu Tsoho yake kwance, bayan Muhammadu Inuwa ya kashe shi. Akwai kuma inda kalmar jicce ke ƙara haske a kan abin da ya faru bayan wani ko wani abu ya faɗi. Wato yadda matar da aka kifa wa wuƙa ta kife a ƙasa. Ita kuma kalmar sharkaf tana bayyana sautin da gawar ta yi da ta faɗi. Akwai kuma rairan wadda ta ƙara bayani a kan yadda aka tarar da mace mai ciki kwance a kan gadonta. Wato a rigingine ta tafi ɗari.
Sai yana tahiyatai yanga-yanga
Ba bugu balle mai jihwa ɗan gaton uwa
Sai dai nuni sai a ɓatai
Ana ta hwaɗin shege matcaci
Sai yas shiga jirgi lahiya lau
Dan nan wani daɗi yaƙ ƙume ni
Nic ce mai biya malamanka Arzika
Sun cika aiki lahiya lau.

Kalmar yanga-yanga ta nuna irin yadda ake tafiya cikin alfahari da nuna isa. Kamar yadda wani mijin Gambo ya riƙa tafiya lokacin da ya yi wa masu korar ɓarawo baduhu ko layer zana.
Don na ce Sani in ka ishe maikuɗi kwance sharkat
Kak ka yi mai sata yana kwana, jijjigar shi, tas sai
In shege ya tada kai, tari bakin shege da bindiga
Ce in ba kuɗi ba ran ka
Don shi ka gwadama wurin da duk suke
ba ya musu bai tadda yaya.

Ita ma wannan kalma ta ƙara bayani a kan tsananin zurfin bacci inda za a iske wanda ke kwancen bai san inda yake ba. Irin wannan bacci mai nauyi kan ba masu shiga ɗaki da dare damar washe mutum kaf.
Na kuma san ayar mashaya
Kowaɗ ɗebi marisa yay yi mankas
Sai ai masa bulala tamanin.

Wannan kalma ta bayyana yadda mashaya ke fita cikin hayyacin kansu, musamman idan aka kwankwaɗi giya da yawa. Wato halin da mutun kan tsinci kansa na kiɗimewa.
In nit tuna da ɓarayi
Waɗanda as sake
In ji awa ba a tsare ba
Gambo in ji awa dai ba a kashe ba
Ga su ga banza tarshe birjik
Ƙasa tarshe awa dawa a yashi.

Kalmar birjik a bakin Gambo ta nuna irin tsananin yawan abu, kuma abin kan kasance ana iya ganin sa ko’ina saboda mamayewarsa.
Satar miliyan wa ka yin ta
Wallahi mai riƙa biro ɗai ka yin ta
Nan suka salwanta su ko tahi
Ba ganewa za a yi ba
Ƙyar- ƙyar-ƙyar ya rubuta
Ya sa hannu ya kashe su.

A nan mawaƙin ya ƙarfafa mana yanayin da aka gudanar da rubutu. Wato yadda aka sarrafa abin rubutu wajen rubuta wani abu. Lalle wannan ya nuna irin sauri, da sabon azzaluman ma’aikata masu satar kuɗin jama’a ta amfani da biro.

6.0 KAMMALAWA


Tabbas mun ga yadda azuzuwan bayanau da Amsa-kama ke fitowa daga bakin Gambo mai tunzura ɓarayi ya kuma tumaye. Irin waɗannan kalmomi suna bayyana ne, yayin da Alhaji Gambo ke ƙoƙarin daidaita karin waƙarsa, ta hanyar nuna yadda wani abu ya faru ko ya kasance. Haka kuma, tsarma waɗannan kalmomi na fitowa a lokacin da aka kalli kalmomi ta fuskar daidaitacciyar Hausa da karin harshen Kabanci. A wannan maƙala mun tattauna rukunin kalmomi saboda ganin irin yadda rabon ke da mishkila. Sai ra’ayoyin masana da aka kawo domin ɗebe wa mai karatu ko saurare tababar ma’anar Bayanau da Amsa-kama. Haka kuma, mun yi nazarin wasu baitocin waƙoƙin Gambo waɗanda ke ɗauke da kalmomin bayanau da amsa-kama.
Nazarin harshe kan kasance a kowane fanni na harshe. Hasali ma, saboda kasancewar harshe hanyar magana tsakanin al’umma da kuma kafar bayyana adabi da na al’adun masu magana da wani harshe. Ƙoƙarin zaƙulo nahawun harshe da yadda ake sarrafa shi a cikin adabi, kan taimaka wajen tantance yadda makaɗa ke sarrafa harshe ta hanyar da ta dace ko ma ta hanyar karya ƙa’idar harshe, saboda wasu uzurori na daidaita karin waƙa.


+MANAZARTA


Aarts. B. 2001. English Syntax And Argumentation. London: Palgrave Macmillan.

Abdullahi, W.H 1997. A Comparative Analysis of Hausa And English Adverbs. B.A Hausa Project. Sokoto: Usmanu Ɗanfodiyo University.

Amfani, A.H. 2004. Waiwaye Adon Tafiya: Bitar Rabe-raben Azuzuwan
Kalmomin Hausa: Takardar da aka gabatar a wajen taron ƙara wa juna ilmi. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Abubakar, R. 2008. Alaƙa da Bambance-bambance Tsakanin Amsa-kama da Bayanau a Hausa. Kundin Digiri na Ɗaya. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Bagari, D.M. 1986. Bayanin Hausa: Jagora Ga Mai Koyon Ilmin Bayanin Harshe. Rabat, Morocco: Impremerie Elm’arif Aljadida.

Bargery, G.P. 1951. A Hausa-English Dictionary And English- Hausa. Oxford.

Beck, D. 2005. Ideophones, Adverbs And Predicate Modifiers in Upper Necaxa Totonac: University of Alberta.

Centre For The Study Of Nigerian Languages, 1971. Harsunan Nijeriya 1. Kano: Oluseyi Press Limited.

Carnie, A. 2002. Syntax a Generative Introduction. United State of America: Blackwell Publishers Ltd

en.wikipedia.org/wiki/Adverb.

en.wikipedia.org/wiki/Ideophone.

Ibrahim, Y.Y da Abdulƙadir, Ɗ. 1986. Jagoran Nazarin Hausa. Zariya: Northern Nigerian Publishing Company.

Ibrahim ,Y.Y da Wasu. 1992. Darussan Hausa Littafi na biyu: Don Manyan Makarantun Sakandire. Ibadan: University Press Plc.

Ibrahim ,Y.Y da Wasu. 1992. Darussan Hausa Littafi na uku: Don Manyan
Makarantun Sakandire. Ibadan: University Press Plc.

Isma’il, J. da Tanimu, M.’Y. 2007. Harshe Da Adabin Hausa A Kammale:
Don Manyan Makarantun Sakandire. Kano: Spectrum Books Limited.

Maiyama, U.H. 2008. “Sata a Zamantakewar Hausa: Nazain Waƙoƙin Ɓarayi na Muhammadu Gambo Fagada” Kundin digiri na uku. Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo.

Murthy, J.D. 2007. Contemporary English Grammar. Lagos: Bookmaster.

Newman, P. 1937. The Hausa Language: An Encyclopedic Reference Grammar. New Heaven: Yale University Press.

Newman, P. and Newman, R.M. 1977. A Modern Hausa-English Dictionary. Ibadan: Oxford University Press.

Nkwocha, C.R. 2008. Essential of English Language for Schools And Colleges. Onitsha: Africana First Publishers Plc.

Odiaka, M.O. 1974. Mastering English. Ibadan: Macmillan Nigeria Publishers Ltd.

Pryse, B.E. 1984. English Without Tears. Glasgow: William Collins Sons And co Ltd.

Sa’id, B. 2006. Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya.

Skinner, N. 1977. A Grammar of Hausa for Nigerian Secondary Schools And Colleges. Zaria: Northern Nigerian Publishing Company.

Sani, M.A.Z. 1999. Alfiyyar Mu’azu Sani 2 Ginin Jimlar Hausa a Waƙe. Kano: Gidan Dabino Publishers.

Wehmier, S. 2006. Oxford Advanced Learner’s Dictionary. Newyork: Oxford University Press.

Zaria, A.B. 1981. Nahawun Hausa. Thomas Nelson Nigeria, Lagos

Zarruk, R.M. da Wasu 2005. Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa littafi na biyu: Don ƙanana makarantun sakandire. Ibadan: University Press Plc.

Post a Comment

3 Comments

  1. Auwal muhd kurna kano11 February 2018 at 05:46

    Gaskiya na samu dandalin kara karatu muna godiya

    ReplyDelete
  2. Amsoshi na farin cikin kasancewa tare da kai.

    ReplyDelete

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.