Wani saurayi ne ya je zance wajen budurwarsa. Suna tsakiyar hira sai aka fara ruwa kamar da bakin kwarya. Har zuwa dare ruwa bai dauke ba. Sai baban yarinyar nan ya ce da ita "Na ga alama ruwannan ba mai daukewa ba ne yanzu, don haka ki gyara masa dakin bakin nan sai ya kwana anan. Idan Allah ya kai mu gobe sai ya koma. Budurwar ta mike ta shiga gida don cika umarnin mahaifinta. Bayan ta gama gyara dakin sai ta dawo don yi wa saurayin nata iso amma abin mamaki sai ta tarar ba ya nan. Don haka ta koma ta sanar da babanta halin da ake ciki. Uban ya rinka mamakin inda ya shiga. Ana cikin haka sai ga saurayin ya shigo da gudu. Jikinsa ya jike jagab. Da ganin sa sai uban ya tambaye shi ina yaje haka cikin ruwannan? sai saurayin nan ya amsa da cewa: "Ai gida na koma na dauko bargo saboda ko za a yi sanyi cikin dare!!!

Wai idan kaine uban yarinyar ya za ka yi?

 

Karanta wani:

https://www.amsoshi.com/2017/07/29/tarbiya-cikin-adabin-hausa-tsokaci-daga-karin-magana/