1. Mace mai ciki ke tsoron mutuwa.
2. Furfura manzon mutuwa.

3. Abokin kuka ba a Ƃoye masa mutuwa.
4. Abin da yawa, mutuwa ta shiga kasuwa.
5. Ƙurulla, mutuwa ranar salla
6. Tonon asiri mutuwa gidan kwaraka
7. Tsufa ya zo da gardama
8. Lahira ba ta Ƙin gawa
9. Allah ya hutar da biki, ďan matsiyaci ya mutu ranar suna
10. Sai ai kare ya mutu da haushin kura
11. Tsattsaye sallar gawa
12. Mutuwa ake fasawa, ko hisabi?
13. Ƙurulla, mutuwa ranar salla
14. Ai giwa ta mutu ake ďibar namanta
15. Makashinka na gidanka
16. Kowa ya mutu ya ďebe takaicin kwana
17. Abin da yawa, mutu ta shiga kasuwa

kasuwa
18. Furfura manzon mutuwa
19. Likkafani ba a son ka sai ran mutuwa
20. Mutuwa ba aimiki layar zana
21. Mutuwa ba ki raina ciwo
22. Bita da Ƙulli, bugun kabarin kishiya da mucciya
23. Cakulkuli, Ƙanwar mutuwa
24. Wa albarkar gawa, tai tusa tana ga hannun Allah
25. An kori mutuwa, ciwo sai ya yi yawo
26. Fatalwa mai ta da hankali
27. Tashinku, tashina, inji mai tsaron gawa
28. Gata, ba ya hana mutuwa
29. Wane, mutum inji mutuwa
30. Bidiri, tusa cikin kabari
31. Ba kukana ba, uwar kishiya ta mutu
32. Wai Allah ya isa, an yi wa mai takaba ciki
33. Sai dai a mutu har liman, a rasa mai ba da salla

 

karanta wannan:

https://www.amsoshi.com/2017/06/20/ilimin-nazarin-kakkwafi-na-sauya-wa-jimla-fasali/