1. Mace mai ciki ke tsoron mutuwa.

2. Furfura manzon mutuwa.

3. Abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa.

4. Abin da yawa, mutuwa ta shiga kasuwa.

5. ƙurulla, mutuwa ranar salla

6. Tonon asiri mutuwa gidan kwaraka

7. Tsufa ya zo da gardama

8. Lahira ba ta ƙin gawa

9. Allah ya hutar da biki, ɗan matsiyaci ya mutu ranar suna

10. Sai ai kare ya mutu da haushin kura

11. Tsattsaye sallar gawa

12. Mutuwa ake fasawa, ko hisabi?

13. ƙurulla, mutuwa ranar salla

14. Ai giwa ta mutu ake ɗibar namanta

15. Makashinka na gidanka

16. Kowa ya mutu ya ɗebe takaicin kwana

17. Abin da yawa, mutu ta shiga kasuwa

18. Furfura manzon mutuwa

19. Likkafani ba a son ka sai ran mutuwa

20. Mutuwa ba aimiki layar zana

21. Mutuwa ba ki raina ciwo

22. Bita da ƙulli, bugun kabarin kishiya da mucciya

23. Cakulkuli, ƙanwar mutuwa

24. Wa albarkar gawa, tai tusa tana ga hannun Allah

25. An kori mutuwa, ciwo sai ya yi yawo

26. Fatalwa mai ta da hankali

27. Tashinku, tashina, inji mai tsaron gawa

28. Gata, ba ya hana mutuwa

29. Wane, mutum inji mutuwa

30. Bidiri, tusa cikin kabari

31. Ba kukana ba, uwar kishiya ta mutu

32. Wai Allah ya isa, an yi wa mai takaba ciki

33. Sai dai a mutu har liman, a rasa mai ba da salla
www.amsoshi.com