1. ‘Yan Ƙauye hankalinki a Ƙeya
2. Amfanin girma hankali.
3. Ana sa hauka a buge hankali
4. Da hankalinta ta tsame kifi ta nasa dawo.
5. Don duniya ta Ƙare kada hankali ya Ƙare
6. Hankali da kaya ya fi ban-cikiya
7. Hankali hanji ne.
8. Hankali ke gani, ido gululu ne.
9. Hankali ďan uwan mumini
10. Hankalin mai saran kaba ya koma ga rina
11. Idan hankali ya Ƃata, hankali ke nemo shi
12. In maye na da hankali bai fitar da maitarsa a fili
13. Iskar bazara mai sa mutum hankali
14. Ka aiki mai hankali a da horo ba
15. Kashin damo ma hankali ne.
16. Kwantar da hankalinki kamar kin kashe mutum a kasuwa
17. Kwantar da hankalinki kamar tsumma a randa
18. Mai hankali ka ba wa kaza ruwa ga damina

kaza
19. Mai hankali ka gane hurhurar tunkiya
20. Mai hankali ka gane ďingishin kwaďo
21. Mai hankali ka jifar sauro da gatari
22. Mai hankali ya san fushin mai dogon baki
23. Na shiga zunďe, kishi da marar hankali.
24. Nani ya ishi mai hankali
25. Ƙarfi ka tutu, hankali ka fitsari.
26. Ruwa a cokali ya ishi mai hankali wanka
27. Tashin hankali gobarar gemu
28. Tubani, haďiyar masu hankali
29. Ƃata hankalin dare ka yi suna

 

karanta almara:

https://www.amsoshi.com/2017/06/30/almarar-wasa-kwakwalwa-mangoro-da-maigadi/