Wannan aiki ya yi bayanin dalla-dalla kamar yadda aka gani a sama inda aka kawo ma’anar kiɗa da nau’o’insa tare da yin bayani dalla-dalla a kan rukunin da wannan aikin ya faɗo a cikinsa, kamar yadda zaruƙ da wasu suka kira su “ganguna” wato kayan kiɗa da ake rufawa da fata, amma su kansu kayan kiɗan wasu daga cikinsu kamar tambari da ganga da kalangu da kanzagi, inda aka ɗauko su ɗaya bayan ɗaya aka yi bayani.
Tambari, Ganga, Kalangu, Duma da Kanzagi (Kuntuku): Yadda Suke Da Yadda Ake Yin Su
Yusuf Hamidu
Nasiru Isah
Usman Aƙilukoko
Yusuf Haruna Arume
Mu’awuya Abdullahi Kamba
Shamsu Umar
Hirabri Shehu
Gabatarwa
Wannan aiki zai yi bayani dalla-dalla akan yadda ake yin waɗannan
kayan kiɗan
wato tambari da ganga da kalangu da duma da kanzagi. Amma kafin nan za a kawo
ma’anar kiɗa da kuma yin bayani mai gamsarwa a kan waɗannan
kayan kiɗan.
Ma’anar Kiɗa
Kamar yadda malam ya bayyana muna a aji cewa “kiɗa
shi ne samar da sauti ta hanyar bugawa ko busawa ko gogawa ko shafawa ko kuma
girgizawa”.
Su kuwa kayan kiɗa kamar yadda Zaruƙ da wasu {2995:57} cewa suka yi “
kayayyakin da ake anfani da su wajen kiɗa suna da yawa kwarai”.
Amma sun rarraba su ne zuwa nau’o’i
huɗu
kowane nau’in kuwa ya ƙunshi rukunin kayayyakin
kiɗa
ne masu dangantaka iri ɗaya. Nau’o’in
su ne:-
1. Tambari
2. Ganga
3. Kalangu
4. Duma
5. Kanzagi {kurkutu}
Haka kuma zaruƙ
da wasu {2005:57}sun ƙara da cewa “
Duk kayan kiɗa mai rufin fata ko ƙirgi sunansa ganga. Duk da haka, wani ana kiɗa
shi da hannu ne, wani da itace, wani da bulala, kamar {tambari}, wani kuwa da
tsuma”.
Saboda haka, ana bambanta sunayen ganguna iri-iri dangane da
siffar su da girman su, da yawan bakunansu da nau’o’in kangansu, ko kirgi, ko
duma wanda aka sassaƙa gangar da shi.
Bayan haka, ana rarrabe ire-iren ganguna dangane da wasu
abubuwa da a kan samu a jikinsu. Misali:- maɗauki, ƙirinya, tsarkiya, nake, zaiga, ceba, ido, awara ƙangu da makamantansu.
Tambari:- kayan kiɗa ne da ake kiɗawa
sarakuna ko ahalin sarki. Haka kuma ana buga shi idan sarki na buƙatar isar da saƙo
zuwa ga al’umma , kamar sanar da su ganin watan azumi ko na sallah.
Tambari take ake yi da shi. Ma’ana kiɗa
ne kawai ba Magana, kiɗan shi ne Magana, domin
shi ke bayyana saƙon da ake son a isar.
Akwai Ire-Iren Tambura Da Dama Kamar Haka
1) Dogon zakka
2) Uwa
3) Miji
4) Kurkutu
Kamar yadda sarkin tamburan yabo ya bayyana muna.
Ana buga tambari da abubuwa kamar haka:-
1) Bulala
2) Igiya
3) Jijiya
4) Hannu
Taken da ake wa tambari shi ne:-
1) Idan ka ji tambari sai sarki!
2) Tambari a ji ka sama’u
Kayan Da Ake Haɗa Tambari
1) Itace na ƙirya
2) Fatar shanu
3) Tsirkiya/ciroki
4) Maɗauki
5) ɗamarar ƙarfe {zobe}
Yadda Ake Yin Tambari
a. Ana sassaƙa tambari da itacen ƙirya a yi masa ciki mai faɗi
a yi masa baki ɗaya kamar na akushi.
b. Sai a ɗauko fatar shanu wadda
aka jiƙa ta cikin ruwa amma ba a jeme ba a rufa ta a
bakin icen.
c. Sai a sa tsirkiya {ciroki} ko tsawo ko ko wani abu
makamancinsu a ɗaure bakin.
d. Sannan a dunƙule
fatar bakin wanda za a yi kagun, sai a daure shi da tsirkiya.
e. Ana amfani da ƙahon
barewa a matsayin allura.
f. Sai a ɗaura ɗamarar
ƙarfe {zobe} a gindin icen.
g. Sai a ɗauko tsirkiya a ɗaura
ga zoben sai a haɗa da kango a tsuke.
h. Sai a shanya ya bushe.
i. Idan ya bushe sai a sa reza ko waninta a karkare.
j. Sai a shafa man shanu ko man kaɗe.
k. Sai a gasa shi da wuta. Shi kenan an gama tambari sai
bugawa.
Ganga:- tana cikin manya-manyan kayan kiɗan
da hausawa ke amfani da su tun iyaye da kakanni, ma’ana lokaci mai tsawo. Ganga
ita ce kamar uwa a rukunin kayan kiɗa mai rufin fata.
Kasancewar ta matsayin uwa a wannan rukuni shi ya sa masana
irin su zaruƙ da wasu (2005) suka ce “duk
kayan kiɗa
mai rufin fata ko ƙirgi sunansa ganga”.
Gusau (2016) ya kira waɗannan kayan kiɗa
kamar mandiri da ganga da bangari da bishi da kanzagi da gangi da suna ganga.
Idan ko haka ne to babu shakka itace uwa a wannan rukuni.
Ganga ta kasu kashi-kashi kamar haka:-
1. Gangar fada
2. Gangar noma
3. Gangar algaita
4. Gangar girke
Kayan haɗa ganga:-
1. Itacen aduwa ko ƙirya
ko ɗinya
ko marke
2. Fata tumaki ko awaki jemmama
3. Tsirkiya {ciroki}
4. Nake
5. Zaren zaida
6. Maɗauki
Yadda ake yin ganga:-
i. Da farko za a fafare/ rarake cikin itace mai kauri a yi
masa baki biyu sama da ƙasa.
ii. sannan a ɗauko jemmamar fatar
tumaki ko awaki a rufe bakunan biyu ɗaya bayan ɗaya.
Ana sa fatar cikin kwatarnin jima, mai ɗauke da dagwalon jima,
dagwalo kuma na nufin kayan haɗi da ake jima kamar ruwa
da bagaruwa da toka da katsi. Bayan an jeme sai a wanke fatar a kaita ga turmin
jima, sai a sa wuƙa mai suna kartaji a
karkare ta.
iii. Sannan a ɗauko fatar arufa a bakin
iccen ganga.
iv. Sai a sa zare ko tsawo a daure bakin guda biyu.
v. Sannan a sa ƙyalle
saman icen,
vi. Sai a sa zare ko tsirkiya ko waninsu tsakanin bakunan
biyu ana ɗinke su. Ana amfani da ƙusa ko wani abu makamancinta amatsayin allura.
Su kuwa wasu yadda suke yin ganga kamar yadda sarkin gangar
masarautar yabo wanda ake yiwa laƙabi
da Lando, cewa ya yi ita gangar sarauta suna yin ta ne da fatar gawurtaccen
bunsuru ko rago, sai a sa ta cikin ruwa kamar kwana biyu, sai a sa mata gishiri
a sanya ta, ta ɗauki kamar kwana biyar ko
shida sai a fara haɗa ta karar yadda aka yi
bayani a sama. Sai a sa reza akarkare, sai a shafa man gyaɗa,
sai a shanya ta ga rana. Ana yi mata maratayi da kyallen igiyar fata.
Ana kada ganga da abubuwa kamar haka:-
1. Kurya
2. ɗanmakallo
3. Gula
4. Itacen kiɗa
Sautin ganga iri biyu ne.
1. Sautin sama
2. Na sautin ƙasa.
1.Ana samar da sautin sama ne idan an ɗauke
hannu saman ganga.
2. Ana samar da sautin ƙasa
ne idan an aza hannu saman ganga.
Ana amfani da ganga a wajen kiɗan sarauta da na noma da
na farauta da kokuwa. Awurin kiɗan za a yi ɗamara
da irin kyallen da ke jikin gangar, a yi hulla da rawani da farin ƙyalle, waɗannan tufafin sune
matsayin uni form na makaɗan ganga na masarautar
yabo.
Kalangu:- wani kayan kiɗa ne da hausawa ke amfani
da shi a wurare kamar wurin bukukuwa da dandali.
kalangu ƙarami ne baida girma,
yana da baki biyu, ana rataya shi ga wuya ko kafaɗa.
Kayan haɗin kalangu:-
1. Itace
2. Fata
3. ƙirinya
4. Tsirkiya
5. ƙango
Yadda ake yin kalangu:-
v ana sassaƙa kalangu ne da itace na
aduwa ko ƙirnya ko na kimba.
v Daga nan sai a rarake cikinsa,
v sannan a sassaƙe
icen ta yadda zai bada asalin da ake nema ta ƙirar
jikinsa.
v Sannan a rufe bakin kalangun na ɗaya
da na biyu da fatar akuya ba tare da an jeme ba.
v Sassan a ɗaure bakin guda biyu da
tsirkiya ko wani zare.
v Sannan a dunƙule fatar bakunan biyu waɗanda
za a yi ƙangun sai a ɗaure su da tsirkiya.
v Sannan a ɗaura masa maratayi.
v Ana kaɗa kalangu da urya wadda
aka yi da iccen ƙirya, haka kuma
Anaamfani da hannu.
Kanzagi (kurkutu) a na yin sa ne da fata a dunke fatar a
bakunan nasa biyu waɗanda za a yi wa ƙangu,kuma sai a ɗaure su da tsarkiya, ana
kiɗa
shi da tsumma na gula biyu da aka naɗawa, sai a ɗinke
da allura. Yana da maɗauki da ƙirinya da tsarkiya da zaiga da ƙangu. Sannan ana rataya shi a wuya, kuma akwai
wasu kaɗe-kaɗe
da ake yi da kanzagi kamar kiɗan gambara ko kamanci. A
irin wannan kiɗa a kan yi amfani da hannuwa ne.
Kanzagi mahaɗin kiɗa
ne na kalangu ko duma.
Duma:- wani masaki ne wanda yake yin girma sosai. Ana fafe
babban duma ne a saman sa, sannan a rufa bakin da fata wadda a ka jeme. Ana
shafe ta da man gyada ko man shanu. A kan kuma ɗaura igiyar tsarkiyar
wadda aka gitta ta a saman fatan domin ta dinga bada damar sassauya amo.
Ana girka ta a saman wani gamwo na kaba a ƙasa. Ana kiɗa ta da gula wani bi ana
kiɗa
shi da hannu. Yawanci makaɗan noma ne ko na dandali
wato na samari da 'yan mata ko kiɗan gardawa masu sayar da
magungunan gargajiya ne ke amfani da ita.
Ire-iren Duma:-
Duman girke
Duman rataye
Duman tsaye
Amale subbu yana amfani da duma wajen kiɗinsa.
Kammalawa
Wannan aiki ya yi bayanin dalla-dalla kamar yadda aka gani a
sama inda aka kawo ma’anar kiɗa da nau’o’insa tare da
yin bayani dalla-dalla a kan rukunin da wannan aikin ya faɗo
a cikinsa, kamar yadda zaruƙ da wasu suka kira su “ganguna”
wato kayan kiɗa da ake rufawa da fata, amma su kansu kayan kiɗan
wasu daga cikinsu kamar tambari da ganga da kalangu da kanzagi, inda aka ɗauko
su ɗaya
bayan ɗaya
aka yi bayani.
Manazarta
Damfawa A.A, (2015/2016). daasin aji, ALH 404 hausa musical
instrument.
Gusau, (2016) ƙamusunkayan
kiɗan
hausa:Maɗaba’ar
century research and publishing limited kano Nigeria.
IdrisY. (2016/2017). darasin aji ALH 404 hausa musical
instrument.
Zaruƙ da wasu, (2005). sabuwar
hanya nazarin hausa: maɗaba’ar
uniƂersity press plc Ibadan.
Hirarraki
Hira da Sarkin Tamburan Yabo, Muhammad Sarkin Tamburra,
20/6/2017.
Hira da Sarkin Gangunan Yabo, Ummaru Muhammad, 20/6/2017
3 Comments
[…] karanta […]
ReplyDeleteIna nuna godiya dafarin ciki kan wannan dandali.
ReplyDeleteMu ma mun gode.
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.