NA


ASHIRU USMAN GABASAWA
ADM.NO:1110106129


KUNDIN BINCIKEN NEMAN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA)
WANDA AKA GABATAR A SASHEN KOYAR DA HARSUNAN
NIJERIYA JAMI’AR USMANU ‘DANFODIYO, SAKKWATO.


SATUMBA, 2016


BABI NA BIYAR
KAMMALAWA5.0 Shimfiďa


Domin kammala wannan nazari, za a waiwaiyi abubuwan da suka gabata a cikin kowane babi a taƘaice. Sannan akwai sakamakon wannan nazari da aka gudanar domin jaddada mahimmancinsu cikin nazarin harshe. Za a kuma bayar da shawarwari duk a cikin wannan babi na biyar, wanda shi ne babi na Ƙarshe.

5.1 TaƘaitawa


Babi na ďaya ya yi tsokaci ne kan gabatarwa. A babin an bayyana manufar wannan da farfajiyarsa da kuma mahimmancinsa, musamman ga masu nazari da kuma masana da ma mahimmancinsa ga al’ummar Hausawa. Haka kuma mun kawo mtsalolin da muka fuskanta ya yin gudanar da wannan bincike a Ƙarshe kuma na kammala wannan babi ne ta hanyar naďe tabarmarsa.
A babi na biyu kuwa bayan an shimfiďa tabarmar wannan babin, sai muka shiga yin bitar waďansu ayyuka na masana da manazarta waďanda suka danganci wannan nazari, an yi bita kan aro da ƘirƘira da kuma bita kan Hausar rukuni. A Ƙarshe kuma an kammala wannan babi da naďe tabarmarsa.
Babi na uku bayan shimfiďarsa ya yi bayani kan tsarin gudanar da bincike da adadin bayanan da aka tattara a lokacin da gudanar da aikin da hanyoyin tattara waďannan bayanan, cikin babin dai an kawo yadda aka tattaro bayanan da kuma bayan samuwar bayanan hanyoyin da akabi wajen sarrafa waďannan bayanai da muka zaƘulo su. A karshe shima an yi kamar sauran babi an naďe tabarmarsa.
Babi na huďu mai laƘabi jadawalin bayanai an rarraba irin kalma ko kalamin da aka samo daga wannan rukuni na ‘yan siyasae arewacin Najeriya kan hanyoyi guda uku ta ďaya kalmomin da aka faďaďa ma’anarsu da na biyu ƘirƘirarrun kalmo daga na asali na uku kuma kalmomin aro da aka sarrafasu a cikin wannan rukuni, haka aka samarwa kowannensu wani jadawali don sauƘaƘa fahimtar manazarta da ďaliban ilimi. A Ƙarshe aka naďe tambarmar babin.
Babi na Ƙarshe, shi ne na biyar. A cikin wannan babi akwai abubuwa uku: jawabin kammalawa, da shawarwari. Daga Ƙarshe kuma manazarta wato litttafai da muƘalu da kundaye da sauran abubuwan da aka yi nazari lokacin da ake gudanar da wannan binciken. A Ƙarshe, ba za a manta da waďanda zanta da su ba, domin samo bayanai daga gare su.

5.2 Sakamakon Bincike


A wannan gaƂar ce za a kawo jerin abubuwan da wannan nazari ya gano ko ya fahimta dangane da Hausar ‘yan siyasarmu na arewacin Nijeriya. Ga wasu daga cikinsu:
Daga cikin mahimman masu amfani da Hausar ‘yan siyasa akwai: ‘Yan jam’iyyu daban-daban, da magoya bayansu da sauran jama’a.
Lokutan amfani da Hausar kan fara ne yayin yaƘin neman zaƂe, ta hanyar tarukka, gangami da shirye-shiryen kafafen yaďa labarai da bayan kafa gwamnati. Haka kuma, samuwar kalmomi irin waďannan a jam’iyya na sa abokan adawa karaya. Kuma yin amfani da wasu kalaman cikin jama’a kan kawo tashin hankalin al’umma kamar yadda wasunsu ke kwantar musu da hankali.
Wannan nazari ya gano hanyoyin da Hausawa ‘yan siyasa ke samar da wannan Karin harshensu na rukuni. Hanyoyin sun yi shafuwar aro da ƘirƘira kamar haka: Sarrafa kalmomin Aro, da ƘirƘira sababbin kalmomi da kumafaďaďa ma’anar kalmomin asali
MawaƘa da kafafen yaďa labarai sun taimaka wajen samuwa da Ƙara yaďa Hausar ‘yan siyasa ta fuskoki daban-daban.
Hausar da ‘yan siyasa ke sarrafawa wadda ta sha bamban da yadda ake amfani da ita a al’amurran yau da kullum. Sau da yawa sai an nemi tafinta kafin a iya fahimtarta, musamman ga waďanda ba su cikin wannan rukuni. Ta haka samuwar wannan Hausar ke faďakar da sauran jama’a halin da rukunin ‘yan siyasar ke ciki.
Abubuwan da ke haifar da Hausar ‘yan siyasa: Adawa, da tsokana, da kuma ƘoƘarin tallata jam’iyya ko ďan takara da mayar da martani.
Hausar ta Ƙara bunƘasa harshen Hausa. Dalilin siyasa an samu wadatuwar kalmomin fannu da zantukan waďanda suka danganci siyasa da mulki.
Hausar ta Ƙunshi gamin-gambizar harsuna uku Hausa, da Larabci da kuma Ingilishi.
Jinsin maza a rukunin ya fi na mata samar da kalmomin amma kuma wajen yaďa su ga al’umma samari da ‘yan mata ne don su suka fi kowa yin amfani da su.
Samuwar kalma ďaya a wannan rukunin, ta hanyar sukar abokin hamayya ko zolayarsa na haifar da samuwar a Ƙalla sababbi da dama, musamman wajen ƘoƘarin mayar da martini a tsakanin ‘yan siyasa.
Hausar na bayyana manufofin ‘yan siyasa da jam’iyyunsu domin yawaitar irin waďannan kalmomi a bakunan jama’a kan sa a gane magoyaban kowace jam’iyya.
Kalmomin siyasa na zama hannunka mai sanda ko gargaďi ko nuna adawa kan salon mulkin shugabanni.
Yawan amfani da waďannan kalmomin a bakin ďan takara kan sa a gane cewa, ya taƂa riƘe wani muƘami ko kuwa tazarce yake son yi ko kuma wannan shi ne karonsa na farko na yaƘin neman zaƂe. Wata Hausar kan bayyana salon mulkin da ‘yan siyasar ke da Ƙudurin yi wa al’umma.
Amfani da irin waďannan kalmomi ga ‘yan siyasa kan zama kamar wani gishirin zance ne a cikin bayaninsu wanda in ba su surkinsu a kai-a kai zancensu zai zama lamin zance.

5.3 Shawarwari


Kamar yadda aka sani, yin tsokaci kan wani abu ko wani lamari yana sa jama’a su farga idan ba a san abin ba a sani. Idan kuma ana sane, sai aka yi waste da shi, sai ya zama wata hanya ta tunatarwa ga al’umma game da mahimmancin wannan abun. Wannan aikin ya nuna wa waďanda ba su sani ba cewa, wannan rukuni na ‘yan siyasa ya taka rawa matuƘa a cikin harshen Hausa musamman wajen bunƘasa shi da aro da ƘirƘira. Domin duk harshen da ke aron kalmomi daga wani harshe, to wata rana zai ba da mamaki.
Kasancewar harshen Hausa shi ne harshe na biyu daga cikin manyan harsunan da ake amfani da su a nahiyar Najeriya. Don haka, duk harshen da ake buƘasa shi da kalmomin aro da ƘirƘararru to kuwa shima ya kusa ga kai wa fagen manya a duniya.
Haka kuma, tanadi wajen inganta harsunan mutane ba shi da babbanci da inganta rayuwar al’umma gaba ďaya. Domin harshen Hausa saboda tanadin da aka yi masa ya sa a yau al’ummar Hausawa da ma harshen Hausa suka kasance ja-gaba a nahiyarmu ta Najeriya. Binciken ya nuna cewa, ba al’ummar da ta fi yawan amfani da harshenta a nahiyar Najeriya, irin al’ummar Hausawa.
Muna fatan a samu kafuwar wata hukuma mai kula da irin waďanan baƘin kalmomi domin watsa su cikin al’ummar da ba su san irin wainar da ake tuyawa ba a rukunin a ƘoƘarin samun haƂaka harshen Hausa.
A Ƙarshe, muna kyautata zaton wannan aikin zai taimaka ga ďalibai masu sha’awar nazarin harshen Hausa. Allah Ya sa aikin ya yi amfani da dukkan al’umma baki ďaya.

 

5.4 Naďewa


Kamar yadda bayanan cikin wannan babi suka nuna a sama, babin ya tattauna bayanai a kan waiwayen abubuwan da nazarin ya Ƙumsa, da abubuwan da aka gano daga Hausar ‘yan siyasa da kuma shawarwarin
bincike.

 

ci gaba da karatu

https://www.amsoshi.com/2017/07/08/hausar-yan-siyasa-arewacin-nijeriya-babi-na-uku/

MANAZARTA


RUKUNIN LITTAFAI:
Arnett, E.J. 1972. Gazzetters Of Northern Provinces Of Nigeria: Vol. 1.
London: Frankcass.
Bargery, G.P. 1934. A Hausa-English Dictionary And English-Hausa Dictionary Vocabulary. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.
Fage, U.U. 2002. Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni. Kano:
Benchmark Publishers Limited.
Fagge, U. U. 2012. Hausa Language and Linguistics. Zaria: Ahmadu Bello University, Press Limited.

Fishman, J. (ed) 1972. Reading In sociology Of Language. Mouton Paris

Gee, P. J. 2014. An Introduction to Discourse Analysis Theory and Method. Fourth Edition. London: Routledge.

Imam, A.G. 2009. Asalin Aro, Ma’anarsa da Ire-Irensa. 070-66182880: Kano.

Kirk-Green, A.H.M. 1966. The Emirates Of Northern Nigeria. London: Oxford University.

Muhammad, D. (ed.) 1990. Hausa Metalangauge’ (Ƙamus na KeƂaƂƂun Kalmomi). Ibadan: University Press.
Sa’id, M. (ed.). 2006. Ƙamusun Hausa Na Jami’ar Bayero. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Skinner, N. 1965. Ƙamus Na Turanci Da Hausa-English, Hausa Illustrated Dictionary (Babban Jagora Ga Turanci). Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Ltd.
Yakasai, S.A. 2012. Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Services
Yule, G. 1985. The Study of Language: An Introduction. Australia:
Cambridge University Press.
.
RUKUNIN MAƘALU
Abba, T. 2013. "Coinage And Neologism in Kano Politics" A Paper Presented at the 1st National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organized by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Held on 14th-16th, January, 2013.
Abbas, N.I. da Umar, M.M. 2016. ‘Harshe da Siyasar Canji A Arewacin
Najeriya’ A Paper Presented at the 1st National Conference on tha Role of Language, History And Religion in the Development, Integration and Security of Nigeria. At Usmanu [anfodiyo University, Sokoto, held on 1st -3rd March, 2016.
Bature, A. 2013. "Sababin Kalmomi a Hausa" A Paper Presented at the 1st
National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organized by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Held on 14th-16th, January, 2013.
Busa, A.M. 2013. "Hausa Loans Words In Gbagyi" A Paper Presented at the 1st National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organized by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Held on 14th-16th, January, 2013.
Dambo, 2013. "ƘirƘirarrun Kalmomin Hausa Ina Makomarsu" A Paper
Presented at the 1st National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organized by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Held on 14th-16th, January, 2013.
[antumbishi, M.A (ba shekara) ‘Neologism In Hausa’ Department of
Nigerian Languages, Usmanu [anfodiyo University Sokoto
Salihi,T.M. 2013. "BaƘin Kalmomi da Gamin Gambiza Daga Turanci Zuwa Hausa" A Paper Presented at the 1st National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organized by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Held on 14th- 16th, January, 2013.
Umar, M.M. 2013. Hausar Masu Ƙwallon Ƙafa a Cikin Garin Sakkwato.
MaƘalar da Aka Gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya.
Jamai’ar Usmanu [anfodiyo, Sakkwato.
Yakasai, M.G. 2013. "Adon Harshe a Fagen Dimokuraďiyya a Kano" A
Paper Presented at the 1st National Conference on Hausa Language,
Literature and Culture, Organized by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Held on 14th-16th, January, 2013.
Yakasai S.A. 2003. ‘Sadarwa Tsakanin Maza da Mata’ Takardar da Aka Gabatar a taron Ƙarawa Juna Ilimi, Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu [anfodiyo Sakkwato, 2 ga Oktoba 2003.
Yakasai, S.A 2005. “Aro da ƘirƘira: Nazarin Samuwar Sababbin Kalmomin Hausa a Jami’a da Kuma Garin Sakkwato”: MaƘalar da Aka Gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu [anfodiyo, Sakkwato.

RUKUNIN KUNDAYE
Aliyu, U. 2007. ‘Kalmomin Aro na Zamani’ Kundin Digiri na [aya. A Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu [anfodiyo Sakkwato, Najeriya.

Asara, G.M. 2013. Hausar Dillalai a Jihar Sakkwato. Kundin Digiri na Biyu. Jami’ar Usmanu [anfodiyo, Sakkwato.
Besse, K.M. 2015. ‘Dangatakar Harshe da Siyasa a Sakkwato’ Kundin Digiri na [aya. A Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu [anfodiyo Sakkwato, Najeriya.

Garba, S.A. 2010. ‘Hausar Gidan Rediyo BBC’ Kundin Digiri na Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu [anfodiyo Sakkwato, Najeriya.

Giro, M.M. 2012. ‘Aron Kalmomi da Tsofaffin Kalmomin Hausa A Littafin Mace Mutum’ Kundin Digiri na [aya. A Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu [anfodiyo Sakkwato, Najeriya.

Sirajo, I. 2001. Hausar Kasuwanci: Yanayin ƘirƘirar Sababbin Kalmomi a Kasuwar Garin Sakkwato. Kundin Digiri na [aya. Jami’ar Usman [anfodiyo, Sakkwato.
Yakasai, S.A. 1999. Language Across Two Borders: A Sociolinguistic Study of Hausa in Ƙonni And Illela Border Towns. PhD Thesis. Bayero University, Kano.
Zailani, A.A. 2012. ‘Hausar Kan Titi’ Kundin Digiri na Biyu. A Sashen Nazari Harsuna Da Al’adun Afrika, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Najeriya.