Ticker

6/recent/ticker-posts

HAUSAR ‘YAN SIYASA A AREWACIN NIJERIYA (BABI NA BIYAR)

Kundin Binciken Neman Digiri Na Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Satumba, 2016

www.amsoshi.com

NA

ASHIRU USMAN GABASAWA


BABI NA BIYAR
KAMMALAWA

5.0 Shimfiɗa


Domin kammala wannan nazari, za a waiwaiyi abubuwan da suka gabata a cikin kowane babi a taƙaice. Sannan akwai sakamakon wannan nazari da aka gudanar domin jaddada mahimmancinsu cikin nazarin harshe. Za a kuma bayar da shawarwari duk a cikin wannan babi na biyar, wanda shi ne babi na ƙarshe.

5.1 Taƙaitawa


Babi na ɗaya ya yi tsokaci ne kan gabatarwa. A babin an bayyana manufar wannan da farfajiyarsa da kuma mahimmancinsa, musamman ga masu nazari da kuma masana da ma mahimmancinsa ga al’ummar Hausawa. Haka kuma mun kawo mtsalolin da muka fuskanta ya yin gudanar da wannan bincike a ƙarshe kuma na kammala wannan babi ne ta hanyar naɗe tabarmarsa.
A babi na biyu kuwa bayan an shimfiɗa tabarmar wannan babin, sai muka shiga yin bitar waɗansu ayyuka na masana da manazarta waɗanda suka danganci wannan nazari, an yi bita kan aro da ƙirƙira da kuma bita kan Hausar rukuni. A ƙarshe kuma an kammala wannan babi da naɗe tabarmarsa.
Babi na uku bayan shimfiɗarsa ya yi bayani kan tsarin gudanar da bincike da adadin bayanan da aka tattara a lokacin da gudanar da aikin da hanyoyin tattara waɗannan bayanan, cikin babin dai an kawo yadda aka tattaro bayanan da kuma bayan samuwar bayanan hanyoyin da akabi wajen sarrafa waɗannan bayanai da muka zaƙulo su. A karshe shima an yi kamar sauran babi an naɗe tabarmarsa.
Babi na huɗu mai laƙabi jadawalin bayanai an rarraba irin kalma ko kalamin da aka samo daga wannan rukuni na yan siyasae arewacin Najeriya kan hanyoyi guda uku ta ɗaya kalmomin da aka faɗaɗa maanarsu da na biyu ƙirƙirarrun kalmo daga na asali na uku kuma kalmomin aro da aka sarrafasu a cikin wannan rukuni, haka aka samarwa kowannensu wani jadawali don sauƙaƙa fahimtar manazarta da ɗaliban ilimi. A ƙarshe aka naɗe tambarmar babin.
Babi na ƙarshe, shi ne na biyar. A cikin wannan babi akwai abubuwa uku: jawabin kammalawa, da shawarwari. Daga ƙarshe kuma manazarta wato litttafai da muƙalu da kundaye da sauran abubuwan da aka yi nazari lokacin da ake gudanar da wannan binciken. A ƙarshe, ba za a manta da waɗanda zanta da su ba, domin samo bayanai daga gare su.

5.2 Sakamakon Bincike


A wannan gaɓar ce za a kawo jerin abubuwan da wannan nazari ya gano ko ya fahimta dangane da Hausar yan siyasarmu na arewacin Nijeriya. Ga wasu daga cikinsu:
Daga cikin mahimman masu amfani da Hausar ‘yan siyasa akwai: ‘Yan jam’iyyu daban-daban, da magoya bayansu da sauran jama’a.
Lokutan amfani da Hausar kan fara ne yayin yaƙin neman zaɓe, ta hanyar tarukka, gangami da shirye-shiryen kafafen yaɗa labarai da bayan kafa gwamnati. Haka kuma, samuwar kalmomi irin waɗannan a jamiyya na sa abokan adawa karaya. Kuma yin amfani da wasu kalaman cikin jamaa kan kawo tashin hankalin alumma kamar yadda wasunsu ke kwantar musu da hankali.
Wannan nazari ya gano hanyoyin da Hausawa ‘yan siyasa ke samar da wannan Karin harshensu na rukuni. Hanyoyin sun yi shafuwar aro da ƙirƙira kamar haka: Sarrafa kalmomin Aro, da ƙirƙira sababbin kalmomi da kumafaɗaɗa maanar kalmomin asali
Mawaƙa da kafafen yaɗa labarai sun taimaka wajen samuwa da ƙara yaɗa Hausar yan siyasa ta fuskoki daban-daban.
Hausar da ‘yan siyasa ke sarrafawa wadda ta sha bamban da yadda ake amfani da ita a al’amurran yau da kullum. Sau da yawa sai an nemi tafinta kafin a iya fahimtarta, musamman ga waɗanda ba su cikin wannan rukuni. Ta haka samuwar wannan Hausar ke faɗakar da sauran jama’a halin da rukunin ‘yan siyasar ke ciki.
Abubuwan da ke haifar da Hausar ‘yan siyasa: Adawa, da tsokana, da kuma ƙoƙarin tallata jamiyya ko ɗan takara da mayar da martani.
Hausar ta ƙara bunƙasa harshen Hausa. Dalilin siyasa an samu wadatuwar kalmomin fannu da zantukan waɗanda suka danganci siyasa da mulki.
Hausar ta ƙunshi gamin-gambizar harsuna uku Hausa, da Larabci da kuma Ingilishi.
Jinsin maza a rukunin ya fi na mata samar da kalmomin amma kuma wajen yaɗa su ga al’umma samari da ‘yan mata ne don su suka fi kowa yin amfani da su.
Samuwar kalma ɗaya a wannan rukunin, ta hanyar sukar abokin hamayya ko zolayarsa na haifar da samuwar a ƙalla sababbi da dama, musamman wajen ƙoƙarin mayar da martini a tsakanin yan siyasa.
Hausar na bayyana manufofin ‘yan siyasa da jam’iyyunsu domin yawaitar irin waɗannan kalmomi a bakunan jama’a kan sa a gane magoyaban kowace jam’iyya.
Kalmomin siyasa na zama hannunka mai sanda ko gargaɗi ko nuna adawa kan salon mulkin shugabanni.
Yawan amfani da waɗannan kalmomin a bakin ɗan takara kan sa a gane cewa, ya taɓa riƙe wani muƙami ko kuwa tazarce yake son yi ko kuma wannan shi ne karonsa na farko na yaƙin neman zaɓe. Wata Hausar kan bayyana salon mulkin da yan siyasar ke da ƙudurin yi wa alumma.
Amfani da irin waɗannan kalmomi ga ‘yan siyasa kan zama kamar wani gishirin zance ne a cikin bayaninsu wanda in ba su surkinsu a kai-a kai zancensu zai zama lamin zance.

5.3 Shawarwari


Kamar yadda aka sani, yin tsokaci kan wani abu ko wani lamari yana sa jama’a su farga idan ba a san abin ba a sani. Idan kuma ana sane, sai aka yi waste da shi, sai ya zama wata hanya ta tunatarwa ga al’umma game da mahimmancin wannan abun. Wannan aikin ya nuna wa waɗanda ba su sani ba cewa, wannan rukuni na ‘yan siyasa ya taka rawa matuƙa a cikin harshen Hausa musamman wajen bunƙasa shi da aro da ƙirƙira. Domin duk harshen da ke aron kalmomi daga wani harshe, to wata rana zai ba da mamaki.
Kasancewar harshen Hausa shi ne harshe na biyu daga cikin manyan harsunan da ake amfani da su a nahiyar Najeriya. Don haka, duk harshen da ake buƙasa shi da kalmomin aro da ƙirƙararru to kuwa shima ya kusa ga kai wa fagen manya a duniya.
Haka kuma, tanadi wajen inganta harsunan mutane ba shi da babbanci da inganta rayuwar al’umma gaba ɗaya. Domin harshen Hausa saboda tanadin da aka yi masa ya sa a yau al’ummar Hausawa da ma harshen Hausa suka kasance ja-gaba a nahiyarmu ta Najeriya. Binciken ya nuna cewa, ba al’ummar da ta fi yawan amfani da harshenta a nahiyar Najeriya, irin al’ummar Hausawa.
Muna fatan a samu kafuwar wata hukuma mai kula da irin waɗanan baƙin kalmomi domin watsa su cikin alummar da ba su san irin wainar da ake tuyawa ba a rukunin a ƙoƙarin samun haɓaka harshen Hausa.
A ƙarshe, muna kyautata zaton wannan aikin zai taimaka ga ɗalibai masu shaawar nazarin harshen Hausa. Allah Ya sa aikin ya yi amfani da dukkan alumma baki ɗaya.


5.4 Naɗewa


Kamar yadda bayanan cikin wannan babi suka nuna a sama, babin ya tattauna bayanai a kan waiwayen abubuwan da nazarin ya ƙumsa, da abubuwan da aka gano daga Hausar yan siyasa da kuma shawarwarin
bincike.

MANAZARTA


RUKUNIN LITTAFAI:
Arnett, E.J. 1972. Gazzetters Of Northern Provinces Of Nigeria: Vol. 1.
London: Frankcass.
Bargery, G.P. 1934. A Hausa-English Dictionary And English-Hausa Dictionary Vocabulary. Zaria: Ahmadu Bello University Press Limited.
Fage, U.U. 2002. Ire-iren Karin Harshen Hausa na Rukuni. Kano:
Benchmark Publishers Limited.
Fagge, U. U. 2012. Hausa Language and Linguistics. Zaria: Ahmadu Bello University, Press Limited.

Fishman, J. (ed) 1972. Reading In sociology Of Language. Mouton Paris

Gee, P. J. 2014. An Introduction to Discourse Analysis Theory and Method. Fourth Edition. London: Routledge.

Imam, A.G. 2009. Asalin Aro, Ma’anarsa da Ire-Irensa. 070-66182880: Kano.

Kirk-Green, A.H.M. 1966. The Emirates Of Northern Nigeria. London: Oxford University.

Muhammad, D. (ed.) 1990. Hausa Metalangauge’ (ƙamus na Keɓaɓɓun Kalmomi). Ibadan: University Press.
Sa’id, M. (ed.). 2006. ƙamusun Hausa Na Jamiar Bayero. Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jamiar Bayero.
Skinner, N. 1965. ƙamus Na Turanci Da Hausa-English, Hausa Illustrated Dictionary (Babban Jagora Ga Turanci). Zaria: Northern Nigerian Publishing Company Ltd.
Yakasai, S.A. 2012. Jagoran Ilmin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Services
Yule, G. 1985. The Study of Language: An Introduction. Australia:
Cambridge University Press.
.
RUKUNIN MAƘALU
Abba, T. 2013. "Coinage And Neologism in Kano Politics" A Paper Presented at the 1st National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organized by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Held on 14th-16th, January, 2013.
Abbas, N.I. da Umar, M.M. 2016. ‘Harshe da Siyasar Canji A Arewacin
Najeriya’ A Paper Presented at the 1st National Conference on tha Role of Language, History And Religion in the Development, Integration and Security of Nigeria. At Usmanu Ɗanfodiyo University, Sokoto, held on 1st -3rd March, 2016.
Bature, A. 2013. "Sababin Kalmomi a Hausa" A Paper Presented at the 1st
National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organized by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Held on 14th-16th, January, 2013.
Busa, A.M. 2013. "Hausa Loans Words In Gbagyi" A Paper Presented at the 1st National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organized by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Held on 14th-16th, January, 2013.
Dambo, 2013. "ƙirƙirarrun Kalmomin Hausa Ina Makomarsu" A Paper
Presented at the 1st National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organized by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Held on 14th-16th, January, 2013.
Ɗantumbishi, M.A (ba shekara) ‘Neologism In Hausa’ Department of
Nigerian Languages, Usmanu Ɗanfodiyo University Sokoto
Salihi,T.M. 2013. "Baƙin Kalmomi da Gamin Gambiza Daga Turanci Zuwa Hausa" A Paper Presented at the 1st National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Organized by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Held on 14th- 16th, January, 2013.
Umar, M.M. 2013. Hausar Masu ƙwallon ƙafa a Cikin Garin Sakkwato.
Maƙalar da Aka Gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya.
Jamai’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Yakasai, M.G. 2013. "Adon Harshe a Fagen Dimokuraɗiyya a Kano" A
Paper Presented at the 1st National Conference on Hausa Language,
Literature and Culture, Organized by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano. Held on 14th-16th, January, 2013.
Yakasai S.A. 2003. ‘Sadarwa Tsakanin Maza da Mata’ Takardar da Aka Gabatar a taron ƙarawa Juna Ilimi, Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jamiar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, 2 ga Oktoba 2003.
Yakasai, S.A 2005. “Aro da ƙirƙira: Nazarin Samuwar Sababbin Kalmomin Hausa a Jamia da Kuma Garin Sakkwato: MaƘalar da Aka Gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jamiar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

RUKUNIN KUNDAYE
Aliyu, U. 2007. ‘Kalmomin Aro na Zamani’ Kundin Digiri na Ɗaya. A Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, Najeriya.

Asara, G.M. 2013. Hausar Dillalai a Jihar Sakkwato. Kundin Digiri na Biyu. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Besse, K.M. 2015. ‘Dangatakar Harshe da Siyasa a Sakkwato’ Kundin Digiri na Ɗaya. A Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, Najeriya.

Garba, S.A. 2010. ‘Hausar Gidan Rediyo BBC’ Kundin Digiri na Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, Najeriya.

Giro, M.M. 2012. ‘Aron Kalmomi da Tsofaffin Kalmomin Hausa A Littafin Mace Mutum’ Kundin Digiri na Ɗaya. A Sashen Nazarin Harsunan Najeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo Sakkwato, Najeriya.

Sirajo, I. 2001. Hausar Kasuwanci: Yanayin ƙirƙirar Sababbin Kalmomi a Kasuwar Garin Sakkwato. Kundin Digiri na Ɗaya. Jamiar Usman Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Yakasai, S.A. 1999. Language Across Two Borders: A Sociolinguistic Study of Hausa in ƙonni And Illela Border Towns. PhD Thesis. Bayero University, Kano.
Zailani, A.A. 2012. ‘Hausar Kan Titi’ Kundin Digiri na Biyu. A Sashen Nazari Harsuna Da Al’adun Afrika, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Najeriya.

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.