Ticker

6/recent/ticker-posts

HAUSAR ‘YAN SIYASA A AREWACIN NIJERIYA (BABI NA HUDU)

Kundin Binciken Neman Digiri Na Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Koyar Da Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato, Satumba, 2016

www.amsoshi.com

NA

ASHIRU USMAN GABASAWA

BABI NA HUƊU

SIGOGIN HAUSAR ‘YAN SIYASA

4.0 Shimfiɗa


Kamar yadda suka rarraba hanyoyin da Hausawa ke bi wajen ƙirƙirar sababbin kalmomin wannan aikin zai bi hanyar domin rarraba irin kalamai ko kalmomin day a samo daga wannan rukuni na yan siyasa domin ƙara sani inda akasa gaba. Hanyoyin da Hausawa ke bi don ƙirƙirar sabuwar kalma sun haɗa da: Faɗaɗa maanar kalmar asali, da ƙirƙira daga kalmomin asali da kuma sarrafa kalmomin aro.
Kamar yadda na ce Hausawa na amfani da hanyoyin nan uku wajen
ƙirƙirar sabuwar kalma ko kalami, to ina so a gane cewa kowacce hanya
Bahaushe ya ɗauka yana amfani da siffantawa ko kamantawa wajen ƙirƙirar wannan sabuwar kalma. A nan aikin mu zai ɗauki kowacce hanya domin kawo abin da ta ƙunsa da masalanta daga kalmomin ko kalaman wannan rukuni na yan siyasa muka samo.

4.1 Faɗaɗa Ma’anar Kalmar Asali


Faɗaɗa ma’anar kalmar asali ana na nufin akwai ita kalmar a harshen da abin da ake nufi da kowa ya sani, amma sai a samar da wani abu daban a danganta shi da wannan kalmar bayan waccan tsohowar ma’anar da kowa ya sani. A ƙarƙashin wannan hanya ta farko za mu ga yadda ake faɗaɗa maanar kalmar asali, misali kalmar zanzaro wato da take nufin ƙwaro wanda kansa ƙato gindinsa ƙato amma tsakiyarsa siriri. To anan sai Turawa suka zo mana da wani irin ado wanda za su cusa riga cikin wando, a ɗaure da bel. Sai aka cewar idan mutum ya yi irin wannan shiga sai ya yi kama da zanzaro. Domin za a ga tsakiyarsa ta zama siririya, amma samanasa da ƙasansa sun yi girma. Cikin wannan jadawalin ne zamu kawo ire-iren kalmomi da kalaman da aka faɗaɗa maanasu a wannan rukuni na yan
siyasa.
Lamba Kalma ko Kalami Ma’ana ta Asali Sabuwar Ma’ana
1. Ɗandatsiya Kalma ce da take nufin datse abu Duk wani na hannun dama ga mai mulki wajen ba shi shawara ko hana ruwa gudu
2. Ɗanazumi Wanda aka haifa cikin watan azumi
(Ramadan) Saboda kwatantawar Buhari wajen tsare haƙƙin talaka ya sa wasu ke yi masa kirari da Ɗanazumi ba ka ci ba ka bari a ci
3. ƙurdawa Jinsin mutane a Yan tawayen yan
 ƙasar Larabawa
(Larabci) siyasa a cikin
jam’iyya ɗaya
4. ‘Yan taka haye Masu samun abu da sauƙi Yan siyasar dab a su mu cikakkiyar gogewa ba a fagen siyasa
5. ‘Yan shan kai A tari gaban abu gaba da gaba da shi Waɗanda a da basa gayon bayan wani ɗan takara sai bayan da suka tabbatar da zai ci zaɓen daga shi sai babban zaɓe (primary election) sai su komo na sa ɓangaren su bar na su
6. Shekarau ya
gaza Shekarau ba zai iya ba / abin ya gagare
shi Wata nau’in fitila mai ƙananan haske da ake amfani da ita idan ba wutar lantarki (NEPA)
7. Ka wuntsila Ka faɗi Kansilan da ya faɗi takarar zaɓe
8. Bincike ake Bincika wani abu Ana amfani da ita wajen bayyana cewa,
Buhari ya fara bincikar yadda akai badaƙalar kashi dukiyar talakawan ƙasa ko rub da ciki kan ta da matsalar cin hanci da rashawa
9. Ɗillin-Ɗillin Daga salon maganar “yadda ɗillin ta kan Irin salon mulkin Gwamna Abdullahi
yi ɗillin haka ma ɗillin yak an yi ɗillin”wato yadda kaza ta kan yi ƙwan nan haka ma ƙwan nay a kan yi kaza umar Gaduje ba zai babanta ba da na tsohon Gwamnan
Kano Enr. Rabiu musa kwankwaso wajen tsemi da tsantsenin dukiyar al’ummar
jahar Kano
10. Hawa
Katanga kan A hau bisa Katanga ko garu Mutum ya fita daga wata jam’iyya ya tsaya yana shawara kafin ya koma goyon bayan wata

4.2 ƙirƙira Daga Kalmomin Asali


A irin wannan ƙirƙira, Bahaushe na harhaɗo kalmomi ne daga cikin kalmomin da yake da su a Hausa ya ta da sabuwar kalma don ba wani baƙon abu. Misali Bahaushe tun tuni yana da kalmar kura ta ɗiban kaya. Turawa suka shigo da mota da ke ɗiban kaya. Irin waɗanda ake zubawa kura a da sai Bahaushe ya ga ya dace yasa mata suna da A kori kura. Wato yanzu ba a buƙatar kura tun daga wannan motar tafi sauƙi da saurin biyan buƙata. Suma ga jerin irin waɗannan misalai na ƙirƙirar daga wannan rukunina yan siyasa.

Lamba Kalma ko Kalami Ma’ana ta Asali Sabuwar Ma’ana
1. Ɗan bakwai rikodin uku
cefane Bakwai a ɗauki Magana uku a yi cefane ‘Yan siyasar radiyo
(sojojin baka) waɗanda suke karɓar naira dubu goma daga yan siyasa suje kafafen yaɗa labarai su biya dubu bakwai don kare iyayen gidansu, dubu ukun su yiwa iyalansu
cefane
2. Abachiya An ƙirƙira daga sunan Abacha Wani suna da ake kiran wani tsagin
PDP a Kano
ɓangaren
Muhammad
Abacha Sani
3. Kwankwasiyya An ƙirƙira daga sunan Rabiu
Musa Kwankwaso Suns da ‘yan jam’iyyar PDP tsagin Gwamna Rabiu Kwankwaso ke wa kansu laƙabi da shi a ƙasa
4. Lema ta yage Kalamin ya samo asali ne daga sunan waƙar da mawaƙa suka yiwa APC Ana nufin an yi nasarar karɓe mulki daga hannun jamiyya mai alamar lema
5. Yawon razana Yawon da zai Yawon angizon
jahili firgita wanda bashi cikakken sani ya
tsorata siyasa lokacin da ɗan takarar zaɓen Gwamnan Kano a ƙarƙashin PDP Rabiu Musa
Kwankwaso yake yawon zagaya
ƙananan hukomomi
44 a zaɓen 2011
6. ‘Yan jagaliya/ ‘yan kalare/ ‘yan sara suka Kalmomin
ƙirƙirarru ne duka Yan bangar siyasa, wato matasa yan shaye-shaye da ake amfani da su domin yaƙin neman zaɓe
7. Ɗan taka kara Mutumin da yake tafiya a kan kara
(karan dawa) Ɗan takarar da yake tsayawa zaɓe da don ya ci zaɓen ba, sai dan ya yi ƙafar ungulu ga wani mai son cin zaɓen
8. Sojojin baka Masu yaƙi da baki ba bindiga ba Masu rajin kare iyayen gidansu a
gidajen rediyo
9. Shagon Bamaina Sunan da shago wani fitatcen ɗambe ne a ƙasar
Hausa ‘Yan hamayya suke kiran wani a garin Bamaina ta jahar
Jigawa
10. Taɓare Asalin Kalmar
daga ɓari ne Jagorancin karya wata jamiyya mai mulki saboda an hana shi takara don a faɗi zaɓen jamiyyar

ta rasa gaba ɗaya
11. Keken |era Layi ne da sojojin baka suka ƙirƙira don amfani da shi a rediyo Hannunka mai sanda ne ga jagorin da suka kauce hanya ta adalci a shugabancinsu
12. Mahaha Yadda ake haukunta abokan
adawa Kalma ko inkiyar da ake yiwa ‘yan jam’iyyar PDP
Kwankwasiyya take
da ita
13. Buhariyya/ ‘Yar Buhari Daga suna shugaban ƙasa
Muhammad
Buhari Salon mulkin shugaban ƙasa Buhari na tsuke aljihun Gwamnati. Da rashin saar da aka yi na hauhawar kayan masurufi
sanadiyar faɗuwa
ɗanyen fetur wanda shafi tattalin arziƙin
ƙasa
14. Baba go slow/ Go slow Baba Laƙabi ne ake kiran shugaba
Buhari ƙosawar rashin ganin canji nan take da yanayin da aka tarar da ƙasa ciki sai haƙuri, domin idan dambu ya yi yawa
baya jin mai
15. Masu-gudu-sugudu Daga kalamar
gudu,guduwa, maguda Sanar da ɓarayin
Gwamnati cewa
Buhari ya ci zaɓe
duk wanda ya yi wata almundahana to ranta cikin na kare kafin janar ya rutsa
shi
16. Buhari ya yiwa ANPP saki uku Tsakanin Buhari da ANPP babu
aure Buhari ya fice daga jam’iyyar ANPP yana ƙoƙarin sauya wata
17. Aji bikon Buhari A dawo da Buhari gidan da ya bari A yi ƙoƙari wajen dawo da Buhari cikin jamiyyar ANPP da
ya bari
18. Mun kusa shan ruwa Mun kusa karya azumin mu Mun kusa dawowa
Kan karagar mulki.
19. Mu haɗu a
Minjibir Wata ƙaramar hukuma a jahar Kano

4.3 Sarrafa Kalmomin Aro
Ana sarrafa kalmomin aro ne bayan an yi musu kwaskwarima domin su dace da tsarin harshen Hausa. An Hausarantar da kalmomin aro, a nan abin da wannan rukuni suke yi shi ne kalmomin aro ko kalami yadda da wuya wani ma ya gane cewa Kalmar aro ce ba ta Hausa ba ce. Akwai kuma wata haɗin gambiza wato a nan za a ɗauki wata kalma daga Ingilishi ko Larabci a haɗa ta da ta Hausa ta da sabuwar kalma ko kalami. Misali kamar Kalmar “illi-ƙaƙal an sarrafa ƙwayar maanar illi daga kalmar illetrate aka ciro, ta ƙaƙal kuwa Hausa ce. A nan ana nufin mace marar ilimin boko, amma duk ɗabi’unta kamar ado da wasu abubuwa irin na ‘yan boko ne. Ga jerin misalai daga wannan rukuni na ‘yan siyasa.
Lamba Kalma ko Kalami Ma’ana ta Asali Sabuwar Ma’ana
1. Daga Liman sai Na’ibi Wajan ba da sallah in ba Liman to sai
Na’ibinsa zai
bayar da sallah Kirarin da magoya bayan mataimakin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke yi masa, wato daga mulkin Gwamna Rabiu Musa
Kwanakwaso sai shi mataimaki ya karɓa bayan ya gama waadinsa na na
tsarin mulki
2. Fasta Hoto daga Turanci (poster) Hoton ɗan takara da ake liƙawa domin neman goyon baya
3. Muƙaddiman jamiya Masu yin hidima a cikin jamiyya Manya-manya masu faɗa a ji na cikin jamiyya
4. Malam
istihara ya yi Malam ya yi sallah tare addu’o’in neman samun
jagoranci Malam ya yi nunen ɗan takara dab a zai kai su ga cin zaɓe ba ko nasara a jamiyyar
ANPP

4.4 Naɗewa

A wannan babi an tattauna abin da ya shafi sigogin Hausar ‘yan siyasa kama daga faɗaɗa ma’ana daga kalmomin asali na Hausa, da salon ƙirƙirar sababbin kalmomi daga kalmomin asali da ake da su a Hausa da kuma dabarar yi wa kalmomin aro kwaskwarima, domin su d ace da yanayin da aka sarrafa su.

Post a Comment

0 Comments