Ticker

6/recent/ticker-posts

Aminu Ladan Ala: Gilashi

Shimfiɗa: Mai gidan gilasai,
Tubalen gilasai,
Ginshiƙin gilasai,
Mai gidan gilasai.

Amshi: Mai gidan gilashi ba jimirin wargi yake ba,
Mai kaza a ƙugu ba jimirin as-as yake ba yan uwa.Kaliƙi Buwayi ban yi nufin saɓa maka ba,
Rabbi ka sani ni ban yi nufin cutar wani ba,
Ni a yau muradina nas sanar ba da ɓata ba,
Rabbi ka zame mini jagora kar na yi zamba,
Na isar da saƙona da sani ba da kangara ba,
‘Yan uwa.

Hannunka mai sanda na kama ba zamba ne ba,
Arashi nake jama’a ba cin fuska ba ne ba,
Je ka maza gyara in ka tsinci kanka wagga zamba,
Ni kira nake a ji af faɗaka ba nuna gaba,
ƙarƙashin azanci don a ji don a kau da zamba.

Shure-shure ba shi hanin mutuwa ɗan uwa ka duba,
Mai fagafniay bari-bari ba za tai fa’ida ba,
Ma’adi na dangin dangira ba zai yaba ba,
Tuni an gaza da daren kure ba fa’ida ba,
Arziki ake nema da sani ba da ɓata ba.

Tafiyar sahara malam ba da kare ake ba,
Shimili na kaya ba jaki aka ma izo ba,
Kiwo na doki ba wai don a ci fa ake ba,
Dena taka sawun giwa ba san amale ne ba,
ɗaukaka ake nema da sani ba da ja’iba ba.

Sabo da kaza ba hana yanka ta yake ba,
Mai gidan gilashi ba zai so wasan jifa ba,
Haka nan makafo ba zai so wasan jifa ba,
Maagana nake da azanci kai ɗan uwa ka duba,
Nasara ake nema da sani ba da fittina ba.

Aikin fasaha ba wai ɗauki saka ba ne ba,
Baiwar hikima ba kyautar ɗan Adam ne ba,
Aiki a kan ilimi mai rinto ba zai iya ba,
Kai mai ƙwanƙwamai aljannu ba za su ma ba,
Riba ake nema da sani ba da riggima ba.

Rigar izgilanci ba rigar sawa ba ce ba,
Rutura ta iskanci ba kayan ado ba ne ba,
Maza kai shaƙiyi bari tinƙaho dena burga,
Komai kake an yi shi a baya ka je ka duba,
Rahama ake nema da sani ba rashin sani ba.

Ina Firauna da Hamana ɗan uwa ka duba,
Ina Kazaza ƙaruna ko ba kut tuna ba?
Izgili ba kay yi Abujahil Abulahabi ba,
Kusa-kusa fa bambaro shege ka duba,
Lafiya muke nema da sani ba da yin ƙazaf ba.

Zumagiya ta hanya faɗe yaro da babba,
Junwa ba ta jimirin lahaula ka je ka duba,
Wa’azi yana kan kowa ba ware nake ba,
Ai nazari fa da takatsantsan duba-duba,
Buɗi ake nema da sani ba da kokawa ba.

Alla Gafuru Rahimu mai rahama ta duba,
Ya Assataru Azumu mai mulkin a duba,
Ya Muƙutadiru ya Allah na durƙuso a duba,
Na yi nufin saƙo gun bayinka ka sa su duba,
Yarda nake nema da sani na zo a duba.

Adali na sarki bai tsere wa zamani ba,
Shugaba karimi bai kuɓuce wa zamani ba,
Malami waliyi bai tsira a zamani ba,
Mumini ganiyi bai tsere wa ƙasƙanci ba,
Masanin fa kenan balle kwasgi ɗan mahanga uwa uba.

Kowane tsuntsu kukan rinkarsu yake ba,
Saniyar gaba ita ce makwafin ‘yan baya duba,
Hankali ake aiki neman hankali a duba,
Kunya ma’aunin ɗan sunna ba ɗan agwai ba,
Falala ake nema da mutunci babu zamba.

Alan Kanawa mai waƙe na a zo a duba,
ɗan Nasarawa ne na Tudun Muri ku yi duba,
Ke kira da sauti a sauƙaƙe ba cakuɗi ba,
Sautin a yau nazarinsa ake ba ji ka wuce ba,
Dace muke nema da sani ba da tsokana ba.

www.amsoshi.com

Post a Comment

1 Comments

ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.