Article Citation: Bakura, A. R., & Sani, A.-U. (2025). Jirwayen kishi a wasu waƙoƙin baka na mata. Danyamusa Journal of Current Research in Hausa Studies, 5(1), 90–109. ISSN: 2814-2306.
JIRWAYEN KISHI A WASU WAƘOƘIN BAKA NA MATA
Daga
Adamu Rabi’u BAKURA, Ph.D.
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau
Arbakura62@gmail.com
& adamubakura@fugusau.edu.ng
Da
Abu-Ubaida SANI, Ph.D.
Department of Languages and
Cultures,
Federal University Gusau,
Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com
| official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334
| WhatsApp: +2348133529736
Tsakure
Manufar wannan takarda ita ce fito da hoton ɗabi’ar kishi a wurin matan Hausawa. An yi garkuwa da wasu
waƙoƙin baka na musamman da suke gudanarwa domin ganin wannan hoto na kishi.
Kadadar nazarin ta taƙaita ga laluben kishin da ya bayyana a waƙoƙin da suke
gudanarwa a lokutan wasu al’adu kamar na daɓe da raino da kuma gaɗa. An yi haka
ne domin fayyace yadda kishi yake a rayuwarsu da kuma a
yanayin zamantakewarsu. Takardar ta yi amfani
da hanyoyin tattara bayanai waɗanda suka haɗa da hira da sauraren waƙoƙi daga
bakin wasu daga cikin matan da suke rera su. Haka kuma, an dubi wasu daga cikin
ayyukan da magabata suka gudanar a matakan ilimi daban-daban domin a naƙalci
batun da ake nazari, sannan kuma a cike giɓin da ake da shi a wannan fage. Binciken
ya gano cewa, akwai nason kishi a cikin wannan ɓangaren adabin baka. Bugu da
ƙari, tasirin da kishi yake da shi a wurin mata, shi ne ya sa ya shiga cikin
waƙoƙin da suke gudanarwa na musamman. Daga ƙarshe, takardar ta ba da shawara
ga jami’o’i da hukumomin adana tarihi da al’adu da masana a kan su bayar da
cikakkiyar kulawar da ta kamata don ganin an zurfafa bincike wajen gano
ɓirɓishin kishi a sauran ɓangarorin adabin Hausa.
Fitilun Kalmomi: Waƙa, Waƙoƙi na Musamman, Kishi, Adabin Baka
1.0 Gabatarwa
Ɗabi’ar ɗan’adam ta ƙaunar
shahara a wani fanni na zamantakewa ko kuma na rayuwa, ita ce ta buɗe masa sha’awar
yin kere ta yadda zai zarce kowa a cikin tsaransa da ma waɗanda suka girme shi.
Shi ne dalilin da ya sa wasu mutane sukan yi tsayin daka wajen ganin sun zama
makaɗaita a wasu fannoni na rayuwa. Ga alama, yanayin ɗan’adam na son zaman lafiya ba tare da ya fuskanci cutarwa
daga wani ba, kamar yadda shi ma ba ya ƙaunar musguna wa wani, shi ne ya ba shi
karsashin yin kaffa-kaffa da yanayin da aka tsinci kai. Hasali ma, wasu daga
cikin mutane sukan zaɓi rayuwa cikin kaɗaici, saboda suna tunanin shiga cikin
mutane yakan kawo kishi da juna. Kamar dai wasu al’ummu na Larabawa da
dangoginsu, matan Hausawa suna cikin rukunin jinsin da ba sa maraba da samun
kishiya a zamantakewarsu ta aure da sauran mu’amalolinsu.
Idan
an lura da fasahohin Hausawa na tatsuniya, wata makaranta ce da take nuna irin
yadda mata suke baya-baya da zama da kishiya. Hakan shi ne ya sa Gizo ba shi da
wata mace da ta wuce Ƙoƙi. Ke nan, rashin ƙaunar zama da kishiya da kuma kishi
a wurin mata yana da tushe idan aka bibiyi labarai da waƙoƙin baka na Hausawa. A
bisa haka ne kuma wannan takarda ta dubi jirwayen kishi a cikin wasu waƙoƙin
baka na mata waɗanda suka haɗa da, na daɓe da reno da kuma na gaɗa. Takardar ta karkata akalarta wajen waƙoƙin baka na musamman, domin kallon
ɓirɓishin kishi a cikinsu.
1.1 Bita
Ƙoƙarin takardar na fito da bayanan da ta
ƙuduri aniyar fayyacewa, shi ne ya sa ta bayyana ma’anonin muhimman kalmomin da aka gina taken bincike a
kansu. An yi haka ne, saboda a samu sauƙin fahimtar alƙiblar da takardar ta
dosa. Kalmomin da aka bayyana ma’anonin nasu a wannan muhalli su ne: Waƙa da waƙa
ta musamman da kuma kishi.
1.1.1 Waiwaiyen Ma’anar Waƙa
A
lugga, waƙa tana nufin, “furta abin da ke cikin ƙwaƙwalwa” (Bargery 1993, sh. 1075). A wata ma’anar kuwa, waƙa takan kasance wata murya ko zaƙin murya mai shiga zuciya da faranta rayuwa. Misali, Bahaushe yakan ce:
i.
Ai na zaci waƙa ce.
ii.
Ya matse sauti kamar,
mai waƙa.
iii.
Zaƙin murya sai ka ce zabiya.
Ta
wata fuskar kuwa, waƙa takan kasance wata
magana wadda akan rera da baki, aka tsara bisa wani zubi na musamman, kamar
yadda Garba (1990 sh. 152) ya bayyana.
Idan
aka dubi ma’anar waƙa a mahangar fannin
adabi kuwa, za a tarar cewa, masana adabin baka da dama sun bayyana ma’anarta a wurare mabambanta, gwargwadon fahimtarsu. Daga
cikin masanan, Gusau (1984 sh. 4) inda ya bayyana ma’anar waƙar baka cewa:
Waƙar baka ita ce wani saƙo cikin zance na azanci da ake rerawaBa faɗa kurum ba, ta cikin hikima da
fasaha da zaɓaɓɓun kalmomi, Waɗanda suka dace da saƙon. Kuma tana zuwa gunduwa-gunduwa, Dangane da sautin murya da kiɗa da
amshi da gaɗa da taɓi ko zabi--yanu, mai saka zuciya jin daɗi”
Shi
kuwa Umar (1987, sh. 28) cewa ya yi:
“Waƙa ita ce nau’in sarrafaffen
harshe da ake gabatarwa da sigar gunduwoyin zantukan da ake kira baitoci ko
ɗiyoyi, waɗanda ake ginawa a kan kari ƙayyadadde,
kuma ake rerawa da wani irin sautin murya na musamman.”
Ta
la’akari da waɗannan ma’anoni, wannan
takarda tana iya cewa, waƙa ita ce ta kasance
tsararriyar magana da ke ƙunshe da fasaha da
hikima da ake rera ta, gunduwa-gunduwa, cikin wani amo na musamman.
1.1.2 Waƙoƙi na Musamman
Waƙoƙi na musamman su ne waƙoƙin da tun can
asalatan, su aka fi sani a farfajiyar ƙasar Hausa. Waƙoƙi
ne waɗanda ake aiwatar da su a keɓaɓɓantu lokuta. Gusau (2024 sh. 9) ya bayyana
su a matsayin waƙoƙin da “... ake rerawa a lokutan da ake gudanar da wasu
keɓantattun ayyuka na rayuwa ta zamantakewa da kuma ta zaman aure.” A taƙaice
ke nan, waƙoƙi na musamman ana gudanar da su ne a wasu ayyanannun lokuta. Ire-iren
waɗannan waƙoƙi sun haɗa da:
i.
Waƙoƙin daɓe[1]
ii.
Waƙoƙin daka
iii.
Waƙoƙin gaɗa[2]
iv.
Waƙoƙin niƙa
v.
Waƙoƙin raka amayar
vi.
Waƙoƙin reno[3]
vii.
Waƙoƙin tashe, da
sauransu
1.1.3 Kishi
Bargery
(1993) ya bayyana kishi a matsayin “ganin ƙyashi a tsakanin kishiyoyi.” Ya ci
gaba da kawo rabe-raben kishi da suka haɗa da kishin birni da kishin kai da
kishin sauri da kuma kishin zuci.” Bakura (2014 sh. 8) ya rawaito Tambuwal inda
aka bayyana ma’anar kishi da cewa: “Abu ne da ke cikin zukatan al’umma,
dabbobi, da ƙwari wanda ya ƙunshi jiyewa (ganin ƙyashi) a kan wani abu da suke
tarayyarsa.” Gwargwadon yadda aka fahimci waɗannan ma’anoni, ana iya cewa kishi
wani yanayi ne da zuciya ke shiga na son ganin an samu ɗaukaka sama da sauran
tsara tare da yin hamayya da duk wani mai yunƙurin kamo ta ko tarayya da ita a
farfajiyar ɗaukaka ko jin daɗinta. Kishi na iya kasancewa hanya ta gwagwarmaya
da ke tattare da zargi da tuhuma da saɓani da rashin jituwa da husuma da mugun
nufi, domin ƙoƙarin kare keɓantacciyar ƙauna ga abin so ba tare da yin tarayya
da wani ba.
2.0 Dabarun Gudanar da Bincike
An
taƙaita wannan bincike kan nazartar kishi a cikin waƙoƙin baka na musamman.
Wannan yana nuna cewa, ba a nazarci sauran nau’ukan waƙoƙi ko adabi da suka
kawo hoton kishi ba. A bisa haka, duk matanonin da aka dogara da su domin
ƙalailaice lamarin kishi a wannan mahanga sun fito ne daga waƙoƙin baka na
musamman.
Maganar
Hausawa da suke cewa: “Gani ya kori ji” wata maɓuɓɓuga ce da take nuna
ƙwarewarsu wajen tantance gaskiyar bayanai. Sakamakon cewa, a tunaninsu, ganin
abu yakan hana karɓar jita-jitar da a ƙarshe takan zama hadisin Bamaguje. Bisa
ga haka, wannan takarda ta yi ƙoƙarin tuntuɓar mata tsofaffi da waɗanda suka
kwana biyu, domin jin wasu bayanai daga gare su a matakin farko. Bugu da ƙari,
an yawata wuraren da ake rera waƙoƙin da suka danganci gaɗa da raino, inda aka
naƙalto wani abu daga gare su.
Haka
kuma, takardar ta yi la’akari da cewa,
magabata sun gudanar da ayyuka da dama masu alaƙa da kishi. Haka ya sa aka leƙa
wasu daga cikin ɗakunan karatu, inda aka dubi rubuce-rubucen da aka riska a
matakan ilimi daban-daban. Takardar ta yarda da maganar Hausawa da suke cewa, “matambayi ba ya ɓata” inda ta tuntuɓi wasu masana da suka ratsi al’adun Hausawa. Kasancewar wannan zamani da ake ciki na
amfani da wayar hannu da sauran hanyoyin sadarwa, an yi amfani da su, kuma
hakan ya taimaka wa masu bincike ta fuskar tattaro bayanai.
3.0 Muhallin Kishi a Waƙoƙin Baka na Mata
A
ƙoƙarin wannan takarda na laluɓen gurbin kishi a cikin waƙoƙin baka na mata, an
kasa waƙoƙin baka mata zuwa manyan gidaje guda biyu kamar haka:
i.
Waƙoƙin manyan mata
ii.
Waƙoƙin ‘yan mata
3.1 Kishi a Waƙoƙin Manyan Mata
A
nan waƙoƙin manyan mata na nufin ire-iren waƙoƙin da manyan mata suke rerawa.
Yawanci sukan rera su ne a lokacin aikace-aikace daban-daban. Kamar yadda Sani
(2025 sh. 21) ya kawo, mata sukan yi amfani da ire-iren waƙoƙin nan domin huce
takaici da fito da abubuwan da suke ƙunshe a cikin zukatansu. Misalan ayyukan
sun haɗa da: daɓe da reno da lugude da niƙa da sauran makamantansu.
3.1.1
Kishi a Waƙoƙin Daɓe
Daɓe
wata tsohuwar al’ada ce da Hausawa suka gada kaka da kakanni. Wannan al’adar
ana aiwatar da ita ne a yayin da aka gina sabon ɗaki. Mata sukan taru inda za
su riƙa zuba tsakuwa (birji) da ruwa (yayyafawa ruwan ake), tare da daddakawa
ta hanyar amfani da waɗansu kayan aiki masu kama da taɓarya. Za su yi ta faman
dakawa har ɗakin ya yi sumul-sumul, kamar an sanya siminti.
A
mafi yawan lokuta, tsofaffi da mata masu matsakaicin shekaru aka fi gayyata
wajen daɓe. Hasali ma dangin amarya da abokan arziki ne sukan aiwatar da shi.
Suna gudanar da shi a ƙarƙashin jagorancin wata mace da sukan yi wa laƙabi da suna Lula. Ita Lula, duk wurin da ta
daɓa ba wata mace da za ta sake bi ta kansa, saboda ya daɓu. A yayin da ake
aiwatar da daɓen akan samu ɗaya daga cikin matan ta riƙa bayar da waƙoƙi, sauran mata suna
amsawa. Mai ba da waƙar ita ake kira zabiya.
Waƙoƙin
daɓe suna da nasu sigogi kamar yadda sauran rukunoni na waƙa suke da nasu.
Gusau, (2008, sh. 226) ya fito da wani abu da ya danganci sigogin waƙoƙin daɓe,
inda yake cewa: “Waƙoƙin daɓe
sukan ƙunshi begen wasu mutane da zambo ga abokan hamayya da habaice-habaice ga
kishiyoyi da kalmomin batsa har da na zage-zage da na raha da annashuwa.” Abu
ne mai matuƙar wuya a sami waƙar daɓe tun daga farkonta har zuwa ƙarshe ba tare
da an samu habaici ko zambo a cikinta ba.
Ɓullar
habaici da zambo a cikin waƙoƙin mata, shi ne yake kawo samun ɓirɓishin kishi a
cikinsu. A mafi yawan lokuta, duk lokacin da mace za ta yi habaici ko zambo,
babu inda zai faɗa idan ba a kan kishiyarta ba, ko kuma uwar mijin da suke
takin-saƙa da juna. A duba misali a cikin wannan waƙar da take ƙasa:
Ya
Bisimillahi zan fara,
Na
fara da sunan Allah,
Du
aikin da ba Bisimillah,
Bai
ƙarko bare ƙarshen ƙwarai,
A
kore! A kore! A kore mana uwargida,
Ko
tana da mageduwa.
Ran
kwanan gadon miji tsoron baya,
Ya
ba ni, ya ga arkane!
Ko
da baƙin ciki za ya kashe ta,
Sai ta gan ni a wannan
gida.[4]
Idan
aka dubi ɗiyan waƙar da suke sama, za a
ga ‘yan daɓe sun nemi a saki uwargida. Ba don
komai suka yi hakan ba, sai gudun kar ta haddasa wa amarya wata cuta da suka
kira mageduwa.[5] Wannan ya nuna ƙarara irin tsabar ƙyama da mata suke
nuna wa kishiya wanda ya haifar da ‘yan daɓe suke neman a saki uwargida. Hasali
ma, sukan yi mata arashi da cewa amaryar ta zo da shirin zama daram a wannan
gida. Haka kuma, sun bayyana yanayin da uwargidan za ta fuskanta na damuwa,
saboda tarewar amarya a gidan mijin.
Ga
al’adar waƙoƙin mata na daɓe, sukan zambaci uwar gida da amarya. A lokaci guda
kuma, akan kai wa uwar miji farmaki. Wannan yakan faru ne kasancewar mata da
dama suna ɗaukar uwar mijji a matsayin kishiyarsu, kamar yadda wasu daga cikin
iyayen maza mata suke ɗaukar matan ‘ya’yansu a matsayin kishiyoyinsu. Hakan ya
sa ake samun adawa da juna, har ake jin amon lamarin a cikin waƙoƙin daɓe.
Misali:
Uwar
miji ta zama bunsuru,
Tana
bobowa,
Ta
faɗa cikin tukunyar tsaba,
Tana
ta yin bobowa,
Har shigifa ta tsage.[6]
Idan
an lura, shaɗara ta uku a wannan waƙa ta bayyana yadda masu daɓen suka siffanta
mahaifiyar maigida da bunsuru. Hakan yakan faru ne saboda yadda take shiga
cikin lamuran gudanar da harkokin gida. Shigar tata takan hana matar miji
(surukarta) rawar gaban hantsi, ta yadda shawararta ba za ta zama karɓaɓɓiya ba.[7] Kishin irin wannan
katsalandan shi ya sa suka yi wa uwar miji zambo ta hanyar siffanta ta da
bunsuru, mai kuka, wanda ya janyo ɗaki ya tsage. Haka kuma, waƙar ta bayyana
yadda suke nuna ƙyamarsu ga irin iyayen
miji mata waɗanda suke shigar sugula, wajen bayar da abinci.
A fage guda kuma, masu daɓe sukan taka wata
muhimmiyar rawa wajen ruruta (haɓaka) wutar kishi ta hanyar waƙoƙin da suke
rerawa. Sau da yawa, sukan yi wa uwar gida gugar zana a yayin da suke gudanar
da daɓe, ta hanyar yabon amarya. Duk sukan yi haka ne domin su taya ‘yar’uwarsu
kishi, kamar yadda yake a cikin waƙar da suke cewa:
Na
gan ki kina mur-mur,
Kawo
ruwa mu daɓa.
Ko
uwargida ba ta so ba,
Kowa
ƙasa mu daɓa.
To
uwargida a ɗau haƙuri,
Kawo
ƙasa mu daɓa.
Don
uwargida ba ta so,
Kawo
ƙasa mu daɓa.
Ai
zaman kishiya sharri ne,
Kawo
ƙasa mu daɓa.
Na
ga ana zurum ba magana,
Kawo
ƙasa mu daɓa.
Kai
su oh-oh dai an tsufa,
Kawo
ƙasa mu daɓa.
Wai
ko ana kishi ne?
Kawo
ƙasa mu daɓa.
Lallai
kishi ya ci su oh-oh!!
Kawo
ƙasa mu daɓa.
Wai kishin mi kika yi ne?
Kawo ƙasa mu daɓa.
Ko
kishin uwa kika yi ne?
Kawo
ƙasa mu daɓa.
Tana
kishin gida da uwa ne,
Kawo ƙasa mu daɓa[8].
Tirƙashi!
Da wahala a samu macen da za ta ji waɗannan kalamai kishi bai yunƙuro mata ba.
Domin ko ba komai, jeregen waƙar ya nuna cewa, ‘yan‘uwan amarya suna ganin zama
da uwar gida sharri ne. A bisa haka ne suka yi mata habaici da cewa, ta tsufa.
A ɗabi’ance ko mace ta kai shekara sittin ba ta
son a kira ta tsohuwa. Hasali ma sukan fito fili ƙarara su ce, wai uwar gida
tana jin haushin maigida ya yi amarya, saboda ta tsufa. Babu shakka duka
waɗannan ɗiyan waƙa suna fito da yadda ‘yan’uwan amarya suke taya ta kishi.
3.1.2 Kishi a Waƙoƙin Reno
Ga
al’ada, waƙoƙin reno suna ƙunshe da
zambo da habaici domin amayar da abin da yake cikin zuciyar mai tawai. Waɗannan
waƙoƙi sukan bayyana hoton yanayin da mace take ciki na rashin jituwa a
tsakaninta da sarkuwa ko kishiya ko miji da ‘yan’uwansa. A ƙoƙarinta na neman
kare kanta ko ‘ya’yanta daga tsangwamar mutanen gida, takan gudanar da waƙe-waƙe a lokacin da take
renon ɗanta, saboda ta huce haushinta, ba tare da jin kunya ko tsoro ko kuma
fargaba ba.
Mata
sukan gina waƙoƙin reno ta hanyar amfani da tubalin kishin uwar miji. Wannan yakan faru ne
idan mace ta fahimci uwar mijinta tana yi musu katsalandan a cikin harkokin
gudanar da gida. Wani lokacin kuma uwar kan yi wa ɗanta hannunka-mai-sanda ne
kawai, ta hanyar tsawatar da shi a kan ɗauko salon rayuwar da bai dace da shi
ba. Ire-iren waɗannan dalilai ne suke sa matar ɗa ta ɗauki karan tsana ta ɗora
wa uwar miji, kamar yadda yakan auku ga kishiya. Shi ne kuma dalilin da ya akan
wayi gari a ji tana yi wa sarkuwa habaici ko zambo cikin waƙa, a yayin da take renon abin goyonta. Misali:
E
lale lale,
Aminu
sha nononka,
Ba
na awaki ne ba,
Ba
na jakkai ne ba,
Gobe
gida can za mu,
Tun
da abin dai ƙi ne.
Gidanku
ne dolenka,
Gidanmu
ni dolena,
In
har an yaye ka,
Sai
ta shigo ɗakina,
Ta
ɗauki duk aikina.
In
ka girma ina nan,
Za
ka biya min arfa,
Har
Haji in ya samu,
Kowa
ba ya hanawa,
Allah
don ikonka,
Raya Aminu nawa[9].
A
nan, kishi ne ya yunƙuro ya rufe wa matar
ɗa ido har take ce wa surukarta, idan ta tafi gidansu, to ita surukar ta zo ta
maye gurbinta. Wannan waƙa da makamantanta,
kishi ne yake haifar da su.
A
wasu lokuta kuma, mata sukan gina waƙoƙin reno ne domin su mayar da martani ga kishiya. A ire-iren
waɗannan waƙoƙin za a tarar cewa,
suna ƙunshe ne da habaici ko zambo ga kishiya, tare da nuna
kushewa a kan ‘ya’yanta. Hasali ma mai waƙar tana
ɗaukaka ɗanta ko ‘yarta, yayin da a ɗaya ɓangaren take nuna kasawar kishiya
tare da ƙasƙantar da ‘ya’yanta,
kamar yadda za mu gani a cikin wannan waƙar:
Ke ce ‘yar gadangama,
Sai a ɗora ki gaban
gado,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.
Allah shi ya ba ni ke
ba wani ba,
Dole ne a sa ki gaban
gado
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.
Ga ki kyakkyawa, abin son gani gun kowa,
‘Yar kura sai baƙin jini ga muni,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.[10]
Waɗannan
ɗiyan waƙa da suke sama sun siffanta kishiya da wata dabbar daji,
wato kura wadda a duk tarsashin namun dawa ba mai baƙin jini kamarta. Duk da kasancewarta mai ƙarfi sosai, ta kasance matsoraciya. Ba ta yarda da yin
faɗa da kowa ba, sai ƙananan dabbobi da
marasa lafiya. Ba ta da zuciyar farauto wa kanta abinci, sai ta yi ta
raɓe-raɓen neman mushe. Hasali ma har takan kai ga tona kaburbura. Irin wannan
siffantawa an yi ta ne domin ƙasƙantar da kishiya.
Waƙar ta ci gaba kamar
haka:
An ce ɗan hakin da ka
rena da ma,
Shi ne wanda za ya
tsone idonka,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.
Bilkisu kin riga kin
yi sa’a,
Sai dai kawai a bi ki
a baya,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.
Ga ki nan, ki wataya,
ki yi yawo,
Mahassada na kallo,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.
Su wance da an yi
lamo,
Ana jiran mu ji kunya,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.
Farin wata sha kallo,
Bilkisu ‘yar Ibrahim,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.
Zara kin fito gari
ya waye,
Tauraruwar gabas mai
haske,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.
Sai mu zo mu yi murna,
Ga farin-wata ya
ɓullo,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.[11]
Dubi
yadda kishiya take ɗaukaka ‘yarta ta
hanyar siffanta ta da wata babbar tauraruwa da take duniyar samaniya, mai
tsananin haske da take fitowa kusa da wata (wato Zara). A ɗaya gefen
kuma, ta yi ƙoƙarin ƙasƙantar da kishiya da
‘yarta a inda ta ke cewa:
‘Yar
ballagaza ana shirin a yi ƙwambo,
Ga
shi ba abin sai kuri
Ku
zo, ku zo, ku yi kallo.
Sai
ku zo, ku yi kallo,
Kwalliya
abin banza ce,
Ku
zo, ku zo, ku yi kallo.
Mai
kyau ko ba ƙyale-ƙyale abin kallo ne,
Sai
ko zo, ku yi kallo,
Bilkisu
ta fito tai kyawo,
Ku
zo, ku zo, ku yi kallo.
Ran
aurenki za a sha mamaki,
Domin
ganin abin da na tara,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.
Idan
aka dubi waɗannan ɗiyan waƙar, za a tarar da an
siffanta kishiya da mai aiwatar da lamurranta tamkar marar hankali. Hakan ya
sanya duk wani tsarin da ta yi wa ‘yarta na ado
domin ta burge samari yakan kasance na banza. Ta kuma nuna irin kyakkyawar
sifar da Allah ya yi wa ‘yarta, wanda
hakan ya wanzar mata da farin jini a tsakanin al’umma, ba tare da wasu ƙyale-ƙyalen sutura ba.
A
wata fuskar kuma, kishiyar ta siffanta kanta da kare saboda yadda yake
biye da ubangidansa sau-da-ƙafa tamkar
mahaliccinsa. Abokin maigidansa amininsa ne. Kamar yadda yake adawa da abokin
gabar maigidansa a kowane irin yanayi yake. Hasali ma yana da hikima da hazaƙa, inda yakan koyi duk wani abu da aka koya masa. An yi
irin wannan kwatance ne a cikin waƙar saboda a bayyana yadda mace take tsananin
kare mijinta daga duk wani aibu. Tana cewa:
An
so a kori kare gun ɗunya,
To
ga shi yau kare ya gane,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.
Yayin
da ta dawo kan ‘yarta kuwa, ta nuna duk abin da ta zayyana game da ita ba
cika-baki ba ne. ‘Yarta ta shahara a tsakanin yayunta da suke uba ɗaya har ta
zarta su. Hakan ya sa tilas su bayar da kai bori ya hau, saboda lamari ne daga
Allah. Idan suka yi jayayya da hukuncin Allah kuwa, zai haifar musu da wulaƙanci da tozarta a cikin al’umma. A dubi abin da take cewa:
Ba
ni son yin fahari a kanki ‘yar Ibrahim,
Gudun
nake mu yi sakaci,
A
hau a tattaka mu,
Ku
zo, ku zo, ku yi kallo.
Bilkisu
kin riga kin yi fice,
‘Yan
uba suna kallon ki,
Dole
su bi ki a baya,
In
sun ƙiya, suna yin kunya,
Ku
zo, ku zo, ku yi kallo.
Duk
wanda bai ajiye ba,
Idan
yana son ɗauka,
Ku
tabbata zai yi kunya,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.
A
ɗan waƙar da ke biye ta siffanta kishiyarta da jaki wanda
ya kinkimo abin da ya fi ƙarfinsa. Hasali jaki
yana daga cikin dabbobi marasa basira. Ga abin da take cewa:
Jaki da kayan taiki,
Ko
ina za a nufa?
Ku
zo, ku zo, ku yi kallo.
Kin
riga su kin ce Allah,
Balkisu
kin riga kin zarce,
Ku
zo, ku zo, ku yi kallo.
To
mahassada kun ji mu,
Bilkisu
yau fa sai dai Allah,
Ku
zo, ku zo, ku yi kallo.
Domin
fa kun riga kun yi sake,
Domin
mai ba mu shi ne Allah,
In
mun rasa fa sai mu kira shi,
Ku zo, ku zo, ku yi
kallo.[12]
Idan
aka yi nazarin wannan waƙar za a tarar tana
tattare da habaici da zambo ga kishiya da ‘ya’yanta. Ba wani abu ne ya kawo su
ba face kishi. Sakamkon ƙyama da tsabar kishi,
har kishiya takan ka da baki ta kira kishiyarta da suna “ballagaza.” Kazalika,
an ga yadda amfani da waƙoƙin reno ya jawo mata suke ƙoƙarin ruruta wutar kishin ‘yan-uba ta hanyar nuna kasawar ‘yan‘uwan jaririn
da ake yi wa tawai, kamar yadda ya zo a cikin wannan waƙar.
Kishi
a tsakanin matan mutum ɗaya yakan ɗauki salailai mabambanta ta fuskar yadda
sukan gabatar da shi. Sau da yawa idan kishi ya yunƙuro wa mace, sai ta tsiri tawai tana yi wa kishiya arashi ta hanyar
la’akari da irin jinsin ‘ya’yan da take haifa. Misali idan mai tawai tana
haihuwar ‘ya’ya jinsin maza ne, idan kishiyarta kuma mata take haifa, sai kawai
a ji tana arashi cikin waƙar da take yi a lokcin
da take tawai, a inda za a ji tana cewa:
Ba
ni ciki don Gwamma,
ba
ni ciki don Adama,
Sai
ƙodago abin jefayya,
Mai karab da kalme
gona.[13]
Haka
kuma, wasu matan sukan ce wa kishiya:
Ɗauki mai damuttsan banza,
Da
ba su ɓarkata komai,
Ɗauki ki gwada mana yadda,
Kishiya
ka lalacewa kamar
Hakin
shinkafa.
Kauɗa
ba a son ki sai ran taushe,
Galma ba a son ki sai
ran aiki.[14]
Duk
ire-iren waɗannan waƙe-waƙe ana yin su ne domin a nuna ƙyama ga kishiya. Bugu da ƙari, a fagen tawai ba a bar suruka a baya ba,
domin ita ma takan yi wa jikanta. A yayin da suke yin tawai ne sukan amayar da ƙololon kishinsu da yake cikin zuciyarsu, musamman wanda
ya shafi matar ɗa. Misalin irin waƙoƙin da suke yi su ne:
Da
bagaruwa abin kirki ce,
Da
mun sha ɗiya,
Wanda
bai raga ma miji ba,
Balle matan gida.[15]
A
nan za a fahimci cewa, uwar miji tana ƙoƙarin nuna munanan halayen matar ɗanta, don haka ne ta
kwatanta ta da bagaruwa. Wannan yakan faru ne a sakamakon hamayyar da take
tsakaninsu.
3.2 Muhallin Kishi a Waƙoƙin Baka na ‘Yan
Mata
Wannan
kaso kuma, ya ƙunshi waƙoƙin da ‘yan mata suke
gudanarwa a cikin gaɗa. Ire-iren waɗannan waƙoƙin su ma suna da keɓaɓɓun lokutan da ake gudanar da su.
Ga al’ada, an fi gudanar da waƙoƙin gaɗa a lokutan hasken farin wata da kuma na
bukukuwan aure da na suna.
3. 2.1 Kishi a Waƙoƙin Gaɗa
Duk
da kasancewar ‘yan mata ba su riga sun yi aure ba, kishi yana ɗaya daga cikin
jigogin waƙoƙinsu. Wannan yana faruwa ne saboda damar da suka samu na amayar da
abin da ba za su iya kauce masa ba, wato zama da kishiya. A al’adance da kuma
tsarin addinin Musulunci, an bai wa namiji damar auren mata fiye da ɗaya.
Wannan shi ya haifar da waƙoƙin ‘yan mata suke yi tattare da zagi da zambo da
ƙyama ko ƙi ga kishiya.
Baya
ga haka, idan an dubi yanayin waƙoƙin, za a tarar suna ƙunshe ne da saƙonnin
manya a hannun yara. Hakan ya sa a duk lokacin da suke rera waƙe-waƙensu na
gaɗa, za a zagi kishiya ko a yi mata zambo, a kuma ta’allaƙa duk wani mugun abu
gare ta. Misali, a waƙar Abalilan cewa ake yi:
Yaraye
alo nanaye yaraye alo,
Abalilan
yaraye alo nanaye,
Na
yi gaisuwa ta ƙi ta ƙyale,
Na
yi sallama ta ƙi ta amsa,
Shegiya
uwar ‘yan kishi,
Ba
mijinki zan aura ba,
Sai
na je na auri ubanki,
In
yi kishiya da uwakki,
Dole
na ki ce, abalilan,
Dole na ki ce min
gwaggo (Yahaya, 1997, sh. 81).
A
waƙar Zama-Wa-Zama, an bayyana irin rashin ragowar da
ke akwai tsakanin kishiya da kishiya saboda tsananin kishi. Ga abin da ake
cewa:
Zama-wa-zama
na je ganin gida,
Na
iske baba da inna a zaure,
Suna
ƙidayar goro,
Sun
ba shi goro goma,
Biyar
a wannan hannu,
Wasu
biyar a wannan hannu,
Babban
cikinsu ya faɗi,
Na
durƙusa in ɗauka,
Sai
aka ce abin ba kunya,
Sai
na ce uhum na bar shi,
Amma
zuciya ba ta so ba.
Zama-wa-zama
na je ganin gida,
Wata
kishiya tsinanna,
Ta
ce mu ga ɗanɗan namu,
Ɗanɗan namu har ya girma,
Sai
na zakuɗo na ba ta,
Ta
jujuwa ta yanke,
Sarar
jini ya baltsa.
Zama-wa-zama
sai ta haifi nata ɗanɗan,
Ta
je ganin gida ta dawo,
Sai
na ce mu ga ɗanɗan namu,
Ta
zakuɗo ta ba ni,
Niko
na jujuwa na fyaɗe,
Na
kawo wuƙa na yanke,
Na ce na rama ƙetar kishi.[16]
Ba
kawai an tsaya a ramuwar gayya ne ba; har ma akan bayyana kishiya a matsayin
ɓarauniya. A waƙar A’isha ta Asshibi an nuna cewa kishiya ta yi sata,
kamar yadda za a gani a ƙasa:
A’i
ta Asshibi,
Mai
ɗan jallo,
Ta
yo, ta yo,
Mai
ɗan jallo,
Ta
yo sata,
Mai
ɗan jallo,
Maza
ku tare muna,
Mai
ɗan jallo
Ihu
ihu,
Mai ɗan jallo (Yahaya,
1997, sh. 81).
Ko
bayan zargin kishiya da ake yi da ‘yan ɗauke-ɗauke ba, akan faɗaɗa zargin wani
lokaci saboda kishi. Waƙar Jar Miya tana ɗauke da misali, inda ake cewa:
Bayarwa: Jar miya zan aura,
Amshi: In babu jar
miya me zan yi da koriya?
Bayarwa: Uwar miji ta zagen,
Amshi: Na durƙusa
ina nema mata gafara.
(Sani da Gobir, 2021, sh. 308)
A wannan gaɓa dukkanin ‘yan wasa za su durƙusa
ƙasa, tamkar dai suna nema mata gafarar da gaske. Waƙa kuma za ta ci gaba kamar
haka:
Bayarwa: Uban miji ya zagen,
Amshi: Na durƙusa
ina nema masa gafara.
Bayarwa: Kishiya ta zagen,
Amshi: Na lillisa
ta na juya ta,
Na
kai ta ofishin‘Yansanda,
Sun
lillisa ta sun juya ta,
Shegiya‘yar
banza,
Sun
kai ta lahira sai ga ta a duniya,
Shegiya‘yar banza. (Sani
da Gobir, 2021, sh. 308)
Za
a tarar cewa ba a yi wa kishiya kowace irin nasiha/rangwame, saboda tsananin ƙin da ake yi mata. Hasali ma ba a nuna ana jin kunyar ta,
domin akan fito gaba-gaɗi a yi mata duk wani abu na cin mutunci kamar yadda
muka gani a waƙar da ta gabata.
A
wasu waƙoƙin akan siffanta
kishiya da mummunar sifa ta duk wani abu da bai dace ba. haka kuma, akan nuna
rashin muhimmancin ɗan kishiya, kamar yadda yake a waƙar Ayye Mama Ayye Mama, a inda ake cewa:
Bayarwa: Ayye mama-Ayye mama
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Ayye mama-labo-labo
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Ayye mama ta tafiyarta
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Ba ta da inna, ba ta da
baba
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Ba ta da ɗan ƙanen aikawa
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Sai ɗan kishiya taka aike,
Amshi: Mamale iye
Ko
ɗan kishiya da kwabo-nai
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Sai ya murguɗa mata baki
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Sannan za a aike shi ya je
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Zama da kishiya tilas ne
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Ba don uwar gidana so ba
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Ka san kishiya ‘yar kishi ce
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Mai mugun hali, mai zunɗe
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Mai baki irin na kututta
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Da aure yana raka aure
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Da na bi ki mun tafi tare
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Sai dai kishiya nika tsoro
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Ko tuƙin tuwo in koya
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Ayye mama labo-labo
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Ayye mama ta tafiyarta
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Sai wataran, idan mun sadu
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Da ni da kishiya ai faufau
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Da ni da kishiya ko sannu
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Sai in na gan ta in fyaɗe ta
Amshi: Mamale iye.
Bayarwa: Kuma in na gan ta in share ta
Amshi: Mamale iye.[17]
Ba
nan kaɗai suka tsaya ba, sukan gina waƙe-waƙensu a kan tubalan kishin kai. Sukan faɗakar da kansu
tare da yin kashedi ga irin ‘yan matan nan da suke sakar wa miyagun maza fuska.
Ga misali a ƙasa:
Bayarwa: Mainaƙiye Mainaƙiye,
Amshi: Mainaƙiye.
Bayarwa: Mainaƙiye ta ƙofar
Marke,
Amshi: Mainaƙiye.
Bayarwa: Mainaƙiye shigo ɗaka
ɗari,
Amshi: Mainaƙiye.
Bayarwa: Ban yarda ba ban yarda ba,
Amshi: Mainaƙiye.
Bayarwa: Ban yarda ba da bukkag gona,
Amshi: Mainaƙiye.
Bayarwa: Ban yarda ba a sangarta ni,
Amshi: Mainaƙiye.
Bayarwa: Ban yarda ba a sangarta ni,
Amshi: Mainaƙiye.
Bayarwa: Ban yarda ba a kai ni a baro,
Amshi: Mainaƙiye. (Gobir da Sani, 2021 sh.
18)
4.0 Sakamakon Bincike
Yayin
wannan bincike, an fahimci cewa kishi wani abu ne da ya zama ruwan dare, wanda
ya game kowace halittar Ubangiji, ba wai ya ta’allaƙa ga ɗan’adam ne kawai ba. Ana samun sa a tsakanin aljannu, kamar yadda
yake a cikin mutane. Haka kuma, an samu nason kishi a tsakanin Mala’iku, kamar
yadda nassin Alƙur’ani mai tsarki ya
nuna.
Wani
abin sha’awa kuma shi ne, a ƙasar Hausa duk mutumin
da ba ya nuna kishin iyalinsa akan ɗauke shi bai san ciwon kansa ba. Haka
alamarin yake ga mata. Idan mace ba ta kishin kanta da na mijinta akan ɗauke ta
tamkar ballagaza. Wannan nazari ya gano cewa, kishi wata ɗabi’a ce da manya
suke koyar da yara (musamman mata) a matakai daban-daban. Akan fara koyar da su
tun daga lokacin reno da na gaɗa da kuma a wasu bukukuwa da taruka kamar na
daɓe da sauransu.
Ƙin
ƙarawa kuma, an fahimci cewa nason kishi ya ratsa adabin Hausa. Kai tsaye an
samu misalansa a cikin waƙoƙin baka na musamman. Hoton kishi da yake bayyana a
cikin ire-iren waɗannan waƙoƙi yana nuni ga yadda Hausawa suka ɗauki lamarin
kishi. Haka kuma, a ciki ana iya ganin kwatankwacin mizaninsa a cikin
zuciyarsu.
4.1 Kammalawa
Tabbas
waƙoƙin baka na musamman wani fage ne daga cikin adabin baka na Hausawa mai
nuna hoton rayuwarsu. Yakan yi nuni da hotuna har na abubuwan da ba a gani,
misali kishi. Kamar yadda takardar ta kawo, tsattsafin kishi ya bayyana a cikin
waƙoƙi daban-daban. Wannan yana nuna cewa, waƙoƙin baka na musamman muhimmin
fage ne da za a iya nazartar sa idan ana son fahimtar yanayi da mizanin kishin
Hausawa, musamman mata.
Kamar
yadda aka gani, an gabatar da wannan nazari ne domin fito da yanayin yadda kishi
ya yi naso a cikin adabin Bahaushe (waƙoƙi na musamman). An yi haka ne domin fayyace yadda kishi
yake a rayuwar al’umma. Haka ya sa aka yi garkuwa da adabin baka domin a gano
haƙiƙaninsa. Ta haka ne ake fatar cewa wannan bincike zai taimaka wajen gane
kishi da irin tasirin da ya yi ga rayuwar jama’a. Domin kuwa idan an fahimce
shi za a iya samar da zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin al’umma. Daga
ƙarshe ana bai wa jami’o’i da hukumomin adana tarihi da al’adu da manyan
makarantu da shugabanin al’umma da masana da su bayar da cikakken tallafin da
ya kamata don ganin an zurfafa bincike wajen gano ɓirɓishin kishi a sauran
ɓangarorin adabi. Haka shi zai ba da dama a fahimci yadda yake a sauran
al’ummomi da suke a kowane ɓangare na wannan nahiya tamu. Sakamakon kuwa zai
taimaka wajen haskaka hanyoyin inganta zaman lafiya.
Manazarta
Ahmad, U. B.
(2002). Jiya A Yau: Daɗaɗɗun Waƙoƙin Hausa. Ahamdu Bello
University Press.
Bakura, A.R. (2003). Gurbin Kishi a Adabin Hausa: Tsokaci a Zube na Baka da Waƙa. [Kundin
digiri na biyu da ba a buga ba]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Tsangayar
Fasaha da Nazarin Addinin Musulunci, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Bala, M. da
Wasu (1993). Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai da
Waƙoƙinsa. [Kundin Digiri
na Farko da ba a buga ba]. Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Bargery, G.P.
(1934). A Hausa-English Dictionary and
English-Hausa Vocabulary. Bugu na Biyu. Ahmadu Bello University Press
Limited.
Garba, C.Y.
(1990). Ƙamus na Harshen Hausa. Evans
Brothers.
Gobir, Y.A.
& Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Amal Printing &
Publishing Nigerian LTD. https://www.amsoshi.com/2026/05/wakokin-hausa-na-gargajiya.html
Guau, S.M.
(Bb). Wasanni da Waƙe-Waƙen Yara a Ƙasar Gusau. Kungiyar Hausa, Jami’ar Bayero, Kano.
Gusau, S.M.
(1984). Nazarin Zaɓaɓɓun Waƙoƙin Makaɗan
Baka Na Hausa ittafi na Ɗaya. Sashen Koyar
da Harshen Hausa, Babbar Kwalejin Tarbiyyar Malamai, Jihar Sakkwato.
Kano,
C.N.H.B.U. (1993). Nazari a Kan Harshe da
Adabi da Al’adu na Hausa, Littafi na Uku. Gaskiya Corporation Limited.
Muhammad, S.
da Yahaya, I.Y. (Bb). Darussa a Kan
Adabin Hausa. Institute of Education Ahmadu Bello University.
Sani, A-U.
& Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Amal Printing & Publishing
Nigerian LTD. https://www.amsoshi.com/2026/05/wasanni-kasar-hausa.html
Sani, A-U.
(2025). Raujin hikima: Gurbin waƙoƙin gargajiya a rayuwar Hausawa. Njinga &
Sepé: Revista Internacional de Culturas, Línguas Africanas e Brasileiras. São
Francisco do Conde (BA), UNILAB, Brazil, 5 (Especial I), 11-23. https://revistas.unilab.edu.br/index.php/njingaesape/article/view/2340
Umar, M.B.
(1987). Dangantakar Adabin Baka da
Al’adun Gargajiya. Triumph, Gidan Sa’adu Zungur.
Yahya, A.B.
(1997). Jigon Nazarin Waƙa. Fisbas
Media Services.
[1] An samo
tushen kalmar daɓe ne daga “daɓaa” wadda take cikin jerin kalmomin aikatau.
Takan ɗauki ɗafa-ƙeyan wasalin {-e} ko{-o} da kuma {-u}. A luggace kalmar
“daɓe” wata hanya ce da ake bi ana dukan birji (tsakuwa) da aka zuba a
farfajiyar ɗaki ko wani muhalli domin ya danƙare, ya yi ƙarfi sosai, kamar an
yi siminti (Bargery, 1934, sh. 175).
[2] Waƙoƙin
gaɗa su ne waɗanda yara ‘yan mata suke rerawa a wurin biki ko kuma dandalin
wasanni. Ana haɗa waƙoƙin da tafi da kuma rawa.
[3] Waƙoƙin
reno su ne waƙe-waƙen da ake yi wa jarirai a lokacin da ake yi musu tawai
(wasa/reno). Waƙoƙi ne da ake yi wa jarirai domin a sa su sakewa da motsa jiki
da kuma sa su yin barci (Yahaya 1997, sh. 51).
[4] I.
Maidaji (keɓantacciyar tattaunawa, ranar 26 ga watan 12, shekarar 2002).
[5] Mageduwa
kuwa wani nau’in ciwo ne da yake cinye ‘yan yatsun ƙafa. Cutar tana faruwa ne a
dalilin cizon wani ƙwaro mai jiki da zane-zane da dogon baki.
[6] Y.
Mafara (keɓantacciyar tattaunawa, ranar 24 ga watan Disamba, shekarar 2002)
[7] M.N.
Maru (keɓantacciyar tattaunawa, ranar 12 ga watan Satumba, shekarar 2002).
[8] K.M.
Damage (keɓantacciyar tattaunawa, ranar 6 ga watan 9, shekarar 2002)
[9] I.
Maidaji (keɓantacciyar tattaunawa, ranar 26 ga watan 12, shekarar 2002).
[10] Y.
Mafara (keɓantacciyar tattaunawa, ranar 24 ga watan Disamba, shekarar 2002)
[11] I.
Maidaji (keɓantacciyar tattaunawa, ranar 26 ga watan 12, shekarar 2002).
[12] L. Abdu
(keɓantacciyar tattaunawa, ranar 20 ga watan Disamba, shekarar 2002)
[13] Y.
Mafara (keɓantacciyar tattaunawa, ranar 24 ga watan Disamba, shekarar 2002)
[14] R. Mafara (keɓantacciyar
tattaunawa, ranar 24 ga watan Disamba, shekarar 2002)
[15] Hira da ‘Yar’umma
Mafara, ranar 24/12/2002.
[16] R.
Amadu (keɓantacciyar tattaunawa, ranar 24 ga watan Disamba, shekarar 2002)
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.