Ya kamata Ahlus Sunna masu tattaunawa a kan wannar mas'ala, ta makomar iyayen Annabi (saw), su lura da abubuwa kamar haka:
1- Wannar mas'ala, mas'ala
ce ta tausayawa, ba ta farin ciki da nishaɗi da
jin daɗi da
murna ba. Saboda bayan Allah ya hana Annabi (SAW) iznin nema wa mahaifiyarsa
gafara, Annabi (SAW) kuka ya yi, har sai da ya saka Sahabbansa kuka, saboda
tausaya wa mahaifiyarsa.
«بكى،
وأبكى من حوله»
Saboda haka mu ma ya kamata
mu taya Annabi (SAW) tausaya wa mahaifansa, ba mu ɗauki
mas'alar a matsayin abin nishaɗi da farin ciki, ko gadara
ba.
2- Ita wannar mas'ala,
mas'ala ce ta labarin gaibi. Ahlus Sunna kuwa imani suke yi da duk wani labari
da Allah da Manzonsa suka bayar, ko da ya saɓa da
hankulansu da aɗifarsu, kuma ya saɓa da
yadda ransu yake so.
Kuma su Ahlus Sunna ba sa
kutsawa cikin mas'ala ta gaibi, saboda Allah ne kaɗai
ya san haƙiƙanin gaibi. Kawai Ahlus Sunna sallamawa
suke yi. Wannan ya sa:
3- Ahlus Sunna ba sa Tawili
a mas'alolin labarai na gaibi. Saboda hakan kutsawa ne cikin abin da ba su da
ilimi a kan haƙiƙaninsa.
Wannan ya sa kuskure ne ƙoƙarin
yin Tawilin Hadisan da suka zo a wannar mas'ala, da fassara su da baffan Annabi
(saw), a maimakon mahaifinsa.
4- Abin da ya kai wasu ga ƙoƙarin
yin Tawilin Hadisan shi ne zaton cewa; akwai cin karo (التعارض)
tsakanin Hadisan da wasu Ayoyin Alƙur'ani.
Alhali akwai wani abu mai muhimmanci, wanda da yawan mutane ba sa lura da shi,
shi ne; asali ba a samun cin karo tsakanin labarai guda biyu.
Ma'ana; idan Allah ya ba da
labarin cewa: Ba ya azabtarwa sai bayan ya aiko Manzo, kuma ya ba da labarin
bai aiko Manzo ga Larabawa kafin Annabi (saw) ba,
To ba za a samu cin karo da
labarin da Annabi (saw) ya bayar na cewa; Babansa yana wuta, ya kuma nemi iznin
zai nema wa mahaifiyarsa gafara, amma ba a ba shi izni ba.
To ka ga duka waɗannan
labarai ne da suka zo a Nassoshin Alƙur'ani
da Hadisi. Don haka Nassoshi ne na Labari (نصوص
الخبر), ma'ana; ba Nassoshi ne na umurni da hani (نصوص
الطلب؛ الأمر والنهي) ba.
To sai masu Tawili su ce:
akwai cin karo (التعارض) a tsakanin waɗannan
Nassoshi na waɗannan labaran.
Alhali duka labarai ne guda
biyu; ɗaya
Allah ne ya ba da labarin a cikin Alƙur'ani,
ɗayan
kuma Manzonsa (saw) ne ya ba da labarin a cikin ingantattun Hadisai. To a ƙa'ida; ba a samun cin karo (التعارض)
tsakanin Nassoshin labarai. Don haka ba zai yiwu a ce akwai cin karo (التعارض)
tsakanin waɗannan labarai da Allah da Manzonsa (saw)
suka bayar ba. Don idan an ce akwai cin karo, to dole ɗaya
zai zama ƙarya, ƙarya kuwa ta koru a labarin Allah da na
Manzonsa (saw).
Saboda haka malamai - irin
su Alƙali Abubakar al-Baƙillaniy, al-Khaɗib
al-Bagdadiy, al-Gazzaliy da Ibnu Ƙudama
- sun tabbatar da cewa; ba a samun cin karo (التعارض)
tsakanin Nassoshin labarai, sai dai ana iya samun cin karon ne a tsakanin
Nassoshin umurni da hani, amma ba na labarai ba, kamar dai yadda
"al-Naskhu" (النسخ) yake shiga cikin Nassoshin umurni da
hani, amma ba ya shiga cikin Nassoshin labarai. Al-Khaɗibul
Bagdadiy ya ce:
"وليس
في نص القرآن ولا نص الحديث عن رسول الله صلى الله عليه وسلم تعارض، قال الله
تعالى: {ولو كان من عند غير الله لوجدوا فيه اختلافا كثيرا} [النساء: 82]، وقال
مخبرا عن نبيه صلى الله عليه وسلم: {وما ينطق عن الهوى * إن هو إلا وحي يوحى}
[النجم: 4]، فأخبر أنه لا اختلاف في شيء من القرآن، وأن كلام نبيه وحي من عنده،
فدل ذلك على أن كله متفق، وأن جميعه مضاف بعضه إلى بعض، ومبني بعضه على بعض إما
بعطف، أو استثناء، أو غير ذلك".
الفقيه والمتفقه للخطيب البغدادي
(1/ 535)
Haka Abu Hamid al-Gazzaliy
ya ce:
"معنى
التعارض التناقض، فإن وقع في الخبر أوجب كون واحد منهما كذبا، ولذلك لا يجوز
التعارض في الأخبار من الله تعالى، ورسوله، وإن وقع في الأمر والنهي والأحكام،
فيتناقض، فيرفع الأخير الأول، ويكون نسخا، وهذا متصور".
المستصفى (ص: 279)
5- Wannan ya sa ba ya daga
cikin Manhajin Ahlus Sunna rarraba tsakanin Nassoshin Shari'a zuwa: "ƙaɗ'iy
da zanniy" (القطعي والظني). Su Ahlus Sunna suna karɓan Aƙida da labari daga Annabi (saw) daga
dukkan Hadisin da ya inganta. Sawa'un "Mutawatiri" (المتواتر)
ne, wato "ƙaɗ'iy"
(القطعي), ko "Ahaad" (الآحاد),
wato "zanniy" (الظني). Kuma sawa'un:
(قطعي
الثبوت والدلالة، أو ظني الثبوت والدلالة، أو العكس).
Don haka, a wajen Ahlus
Sunna, matuƙar dai Hadisin ya zo
ta ingantacciyar hanya, hanyar maruwaita amintattu, to suna karɓarsa,
su tabbatar da shi, su sallama masa, su gaskata labarin da ya ƙunsa. Ba sa gwara tsakanin Nassoshin
Shari'a, alhali duka daga wuri ɗaya suka fito.
Saboda haka iƙrarin cewa; Hadisan makomar iyayen
Annabi (saw) sun zo ne ta hanyar zato, kuma dalalarsu ma zato ne (ظني
الثبوت والدلالة), ba "maslaki" ne na Ahlus Sunna
wajen kafa hujja ba, "maslaki" ne na ƴan
bidi'a:
(إنما
ذلك من مسالك المبتدعة في الاستدلال).
6- Sa'annan babu cin karo
tsakanin Nassoshin, saboda Ayoyin da masu Tawilin Hadisan suke kafa hujja da su
gamammu ne (عامة), su kuma Hadisan keɓantattu
ne (خاصة), don haka babu cin karo tsakanin Ayoyi
gamammu, da Hadisai keɓantattu, kamar yadda yake a
ilimin "Usulul Fiƙhi".
7- Wannan ya sa akwai mutane
da dama waɗanda Annabi (saw) ya ba da labarin suna
wuta, kamar Amru bn Luhayyi, wanda ya sunnanta bautar gumaka a cikin Larabawa,
da Abdullahi bn Jud'an...
Kuma hatta cikin Alƙur'ani, Allah ya nuna cewa; zai azabtar
da mushrikai ƴan Jahiliyya, ba don
ya yi musu ni'imar Muslunci ba, inda ya ce:
{وَاعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللَّهِ جَمِيعًا
وَلَا تَفَرَّقُوا وَاذْكُرُوا نِعْمَتَ اللَّهِ عَلَيْكُمْ إِذْ كُنْتُمْ
أَعْدَاءً فَأَلَّفَ بَيْنَ قُلُوبِكُمْ فَأَصْبَحْتُمْ بِنِعْمَتِهِ إِخْوَانًا
وَكُنْتُمْ عَلَى شَفَا حُفْرَةٍ مِنَ النَّارِ فَأَنْقَذَكُمْ مِنْهَا} [آل
عمران: 103]
A Tafsirin Ayar sai Ibnu
Jarir ya ce:
"يقول
تعالى ذكره: وكنتم على طرف جهنم بكفركم الذي كنتم عليه قبل أن ينعم الله عليكم
بالإسلام، فتصيروا بائتلافكم عليه إخوانا، ليس بينكم وبين الوقوع فيها إلا أن
تموتوا على ذلك من كفركم، فتكونوا من الخالدين فيها، فأنقذكم الله منها بالإيمان
الذي هداكم له".
تفسير الطبري ت شاكر (7/ 85)
Ka ga sai Allah ya ce: sun
yi kusan faɗawa cikin wuta, sai Allah ya tsamar da
su. Ka ga sai Allah ya nuna cewa; zai azabtar da su a kan kafircin da suke kai
kafin aiko Annabi (saw), ba don ya yi musu ni'imar Muslunci ba.
Haka Annabi (saw) ya ba da
labarin ana azabtar da wasu mutane cikin Bani Najjar, a cikin ƙabarburansu, alhali sun mutu ne a
zamanin Jahiliyya, kafin zuwan Muslunci:
عن جابر بن عبد الله، يقول: "دخل النبي صلى الله عليه وسلم
يوما نخلا لبني النجار، فسمع أصوات رجال من بني النجار ماتوا في الجاهلية يعذبون
في قبورهم، فخرج النبي صلى الله عليه وسلم فزعا، فأمر أصحابه أن يتعوذوا من عذاب
القبر".
مسند أحمد ط الرسالة (22/ 58) صحيح مسلم
(4/ 2199)
Don haka duka waɗannan
dalilai keɓantattu ne (نصوص
خاصة), suna keɓance gamayyar waɗancan
Nassoshi (عموم النصوص).
Ma'ana; dalilai keɓantattun
suna nuna cewa; ko da ba a aiko musu Manzo wanda ya keɓance
su ba, to lallai da'awa ta iso gare su, hujja ta tsayu a kansu, amma suka yi
shirka, don haka sun cancanci azaba.
8- Kuma abin da zai nuna
maka cewa; akwai waɗanda da'awa ta isa gare su,
hujja ta tsayu a kansu, shi ne maganar Zaid bn Amr bn Nufail, inda yake faɗawa Ƙuraishawa, cewa; babu wanda yake kan
Addinin Annabi Ibrahim (as) sai shi kaɗai:
عن أسماء بنت أبي بكر رضي الله عنهما، قالت: "رأيت زيد بن
عمرو بن نفيل قائما مسندا ظهره إلى الكعبة يقول: «يا معاشر قريش، والله ما منكم
على دين إبراهيم غيري»".
صحيح البخاري (5/ 41)
Haka kuma ya kasance yana
inkari wa Ƙuraishawa a kan abin
da suke yi na shirka, suna yanka dabbobi wa gumaka, yana aibanta su da hakan,
yana tsayar musu da hujja:
عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما، "أن النبي صلى الله عليه
وسلم لقي زيد بن عمرو بن نفيل بأسفل بلدح، قبل أن ينزل على النبي صلى الله عليه
وسلم الوحي، فقدمت إلى النبي صلى الله عليه وسلم سفرة، فأبى أن يأكل منها، ثم قال
زيد: إني لست آكل مما تذبحون على أنصابكم، ولا آكل إلا ما ذكر اسم الله عليه، وأن
زيد بن عمرو كان يعيب على قريش ذبائحهم، ويقول: الشاة خلقها الله، وأنزل لها من
السماء الماء، وأنبت لها من الأرض، ثم تذبحونها على غير اسم الله، إنكارا لذلك
وإعظاما له".
صحيح البخاري (5/ 40)
Saboda haka, abu mai
muhimmanci shi ne isan saƙon
Manzo, idan saƙon ya isa ga mutum,
kuma ya fahimce shi, to shi kenan, hujja ta tsayu a kansa. Allah ya ce:
{وَأُوحِيَ إِلَيَّ هَذَا الْقُرْآنُ
لِأُنْذِرَكُمْ بِهِ وَمَنْ بَلَغَ} [الأنعام: 19]
Don haka duk wanda saƙon Allah ya isa gare shi, ta hanyar
kowane Manzo, to hujja ta tsayu a kansa.
9- Wannan ya sa Malamai suke
kasa "Ahlul Fatra" a dunƙule
zuwa gida uku:
1) Waɗanda
da'awa ta isa gare su, kuma suka yi imani, to waɗannan
ƴan Aljanna ne. Kamar: Ƙiss bn Sa'idah, Warƙatu bn Naufal da Zaid bn Amr bn Nufail.
2) Waɗanda
da'awa ta isa gare su, kuma hujja ta tsayu a kansu, amma sai suka canza, suka
yi shirka, to waɗannan ƴan wuta ne. Kamar Amru bn Luhayyi, da
Abdullahi bn Jud'an da sauransu.
3) Waɗanda
da'awa ba ta isa gare su ba, ko ta isa gare su amma suna cikin gafala, hujja ba
ta tsayu a kansu ba, to waɗannan su ne mafi yawan ƴan Jahiliyya, su ne waɗanda
a kansu Allah ya ce:
{لِتُنْذِرَ قَوْمًا مَا أُنْذِرَ آبَاؤُهُمْ
فَهُمْ غَافِلُونَ} [يس: 6]
To waɗannan
Malamai sun yi saɓani a kansu, magana mafi ƙarfi ita ce: waɗannan
su ne za a yi musu jarabawa a ranar Ƙiyama.
Wannan shi ne zance mafi
inganci game da "Ahlul Fatra".
Saboda haka, duk waɗanda
Annabi (saw) ya ba da labarin cewa; ƴan
wuta ne, to da'awa ta isa gare su, ta fiskar yadda hujja ta tsayu a kansu.
Kamar Amru bn Luhayyi, da Abdullahi bn Jud'an, da iyayensa (saw), da
ire-irensu.
Don haka waɗanda
za a musu jarabawa a Lahira, cikin "Ahlul Fatra", su ne waɗanda
da'awa ba ta isa gare su ba, ko kuma da'awar ta isa gare su, amma kuma hujja ba
ta tsayu a kansu ba, saboda suna cikin gafala. Shi ya sa Ibnul Ƙayyim ya yi bayanin kafircin da yake sa
a azabtar da mutum, da kuma wanda ba ya sakawa, inda ya ce:
"إن
العذاب يستحق بسببين:
أحدهما: الإعراض عن الحجة، وعدم إرادة العلم بها وبموجبها.
الثانى: العناد لها بعد قيامها، وترك إرادة موجبها.
فالأول كفر إعراض.
والثانى كفر عناد.
وأما كفر الجهل مع عدم قيام الحجة، وعدم التمكن من معرفتها، فهذا
الذى نفى الله التعذيب عنه حتى تقوم حجة الرسل".
طريق الهجرتين (ص: 414)
Saboda haka, kafirci na
kau-da-kai bayan bayyanar hujja, da kafirci na tauri kai, su suke sa mutum ya
shiga wuta.
Amma kafirci na jahilci,
wanda mai shi bai ma san me ake ciki ba, to shi ne wanda ba za a azabtar da shi
ba, sai bayan an tsayar masa da hujja, ta hanyar Manzanni.
Kuma ita tsayuwar hujja a
kan mutum, Allah ne ya san wanda da'awa ta isa gare shi, har hujja ta tsayu a
kansa. Ibnul Ƙayyim ya ce:
"والله
يقضى بين عباده يوم القيامة بحكمه وعدله، ولا يعذب إلا من قامت عليه حجته بالرسل،
فهذا مقطوع به فى جملة الخلق. وأما كون زيد بعينه وعمرو بعينه قامت عليه الحجة أم
لا، فذلك مما لا يمكن الدخول بين الله وبين عباده فيه، بل الواجب على العبد أن
يعتقد أن كل من دان بدين غير دين الإسلام فهو كافر، وأن الله سبحانه وتعالى لا
يعذب أحدا إلا بعد قيام الحجة عليه بالرسول. هذا فى الجملة، والتعيين موكول إلى
علم الله عز وجل وحكمه".
طريق الهجرتين وباب السعادتين (ص: 413)
Bayan haka, mutane sun
banbanta wajen tsayuwar hujja a kansu, suna banbanta gwargwadon wuri zuwa, da
zamani zuwa zamani, da mutum zuwa mutum. Ma'ana; za a iya samun ƴan zamani kaza hujja ta tsayu a kansu,
amma ƴan zamanin bayansu ba ta tsayu a kansu
ba.
Ko a zamani ɗaya,
amma ƴan gari kaza hujja ta tsayu a kansu,
amma ƴan wani garin ba ta tsayu a kansu ba.
Haka tsakanin mutane, za a
samu wani hujjar ta tsayu a kansa, amma wani mutumin kuma, ko wasu mutanen,
hujjar ba ta tsayu a kansu ba. Saboda abun ya danganta, ta yadda saƙon Manzon Allah ya isa gare shi. Shi ya
sa Ibnul Ƙayyim ya ce:
"إن
قيام الحجة يختلف باختلاف الأزمنة والأمكنة والأشخاص، فقد تقوم حجة الله على
الكفار فى زمان دون زمان، وفى بقعة وناحية دون أخرى، كما أنها تقوم على شخص دون
آخر".
طريق الهجرتين وباب السعادتين (ص: 413)
Saboda haka lamarin tsayuwar
hujja a kan mutane wani fage ne na ilimin gaibi mai faɗi,
wanda ya wuce ilimin halitta, sai dai Allah mahalicci masanin gaibi, kuma
masanin halin bayinsa.
Idan kuma an ce; lallai duka
"Ahlul Fatra" ne za a yi musu jarabawan, to ai Allah ya san waɗanda
za su ci jarabawan, ya kuma san waɗanda
za su faɗi,
waɗanda
su ne za su shiga wuta. To daga cikinsu ne Allah ya sanar da Annabi (saw) waɗanda
ya ga daman ya sanar da shi, kamar yadda Ibnu Kasir ya ce:
"وإخباره
صلى الله عليه وسلم عن أبويه وجده عبد المطلب بأنهم من أهل النار، لا ينافي الحديث
الوارد عنه من طرق متعددة؛ أن أهل الفترة والأطفال والمجانين والصم يمتحنون في
العرصات يوم القيامة...
فيكون هؤلاء من جملة من لا يجيب، فلا منافاة ولله الحمد والمنة".
البداية والنهاية (٣/ ٤٢٩)
A wani wajen ya ce:
"وامتحانهم
لا يقتضي نجاتهم، ولا ينافي الإخبار عنهم بأنهم من أهل النار؛ لأن الله يطلع رسوله
صلى الله عليه وسلم على ما يشاء من أمر الغيب".
البداية والنهاية (٢/ ٥٥٥)
Shaikh Shanƙiɗiy
ya ce:
"وبهذا
الجمع تتفق الأدلة، فيكون أهل الفترة معذورين، وقوم منهم من أهل النار بعد
الامتحان، وقوم منهم من أهل الجنة بعده أيضا، ويحمل كل واحد من القولين على بعض
منهم علم الله مصيرهم، وأعلم به نبيه صلى الله عليه وسلم، فيزول التعارض".
دفع إيهام الاضطراب عن آيات الكتاب (ص: 141)
To ka ga waɗannan
Malamai biyu, sun tabbatar da cewa; waɗanda
Annabi (saw) ya ba da labarin suna wuta, suna cikin waɗanda
ba za su ci jarabawan da za a musu a ranar Lahira ba. Da ma tun fil-azal Allah
ya sansu, sai ya sanar da Annabinsa (saw) su.
10- Tawilin da wasu suke yi,
suke cewa; ai baffansa ake nufi, ba mahaifinsa ba, to ya kamata su sani; shi
Tawili - a wajen masu shi - ba haka kawai ake yinsa ba, a'a, dole sai da ƙarina.
Saboda haka babu wata ƙarina a cikin Hadisan da za ta sa a yi
Tawilinsu, daga mahaifi zuwa baffa.
11- Sukan ce: ai hatta a
cikin Alƙur'ani lafazin baba "أب",
ya zo da ma'anar baffa da kaka. Alhali sun manta da cewa: duk inda ya zo da
hakan to an samu ƙarina,
ƙarinar ita ce: an anbaci sunan baffan ko
kakan ƙarara a fili, an anbace su da sunayensu.
Don haka a fili an san ba mahaifi kaɗai
ake nufi ba, har da kaka da baffa.
12- Kuma wata ƙa'ida mai muhimmanci da ya kamata su
sani, shi Tawili ana yinsa ne a lafazi "zahiri" (الظاهر),
wato lafazin da yake da ma'anoni fiye da ɗaya,
amma kuma ma'ana guda ɗaya ta fi rinjaye a kan
sauran ma'anonin. To asali irin wannan lafazi, wajibi ne a bar shi a kan
ma'anarsa ta "zahiri", ba za a kawar da ita, a yi tawilin lafazin ba
sai da ƙarina mai ƙarfi.
To idan mun duba lafazin
"baba" (أب), za mu ga cewa; lafazi ne
"zahiri", saboda yana da ma'ana mai rinjaye, ita ce:
"mahaifi". Shi ya sa da zaran wani ya ce maka: "Yau na ga
babanka", to mahaifinka ne zai fara zuwa a tunaninka, sai dai idan ya mutu
ne, ko wata ƙarinar daban, wacce
za ta sa ka yi tunanin baffanka ko wani daban.
Amma da cewa ya yi: na ga
babanka Isiyaku, alhali Isiyakun baffanka ne, ba mahaifinka ba, to babu wata
jayayya, an san "baba" a nan baffanka Isyaku ake nufi, saboda an kira
sunansa ƙarara. To kamar haka ne duka Ayoyin da
suka zo a cikin Alƙur'ani.
Kamar faɗin
Allah:
{أَمْ كُنْتُمْ شُهَدَاءَ إِذْ حَضَرَ
يَعْقُوبَ الْمَوْتُ إِذْ قَالَ لِبَنِيهِ مَا تَعْبُدُونَ مِنْ بَعْدِي قَالُوا
نَعْبُدُ إِلَهَكَ وَإِلَهَ آبَائِكَ إِبْرَاهِيمَ وَإِسْمَاعِيلَ وَإِسْحَاقَ
إِلَهًا وَاحِدًا وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ} [البقرة: 133].
Da faɗinsa:
{وَاتَّبَعْتُ مِلَّةَ آبَائِي إِبْرَاهِيمَ
وَإِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ} [يوسف: 38]
Amma a Hadisin baban Annabi
(saw), babu wata ƙarina
da za ta sa a fahimci baffansa ake nufi, ko kakansa, don haka dole sai dai a
bar Hadisin a zahirinsa.
To idan an ce:
"baba", ma'ana mai rinjaye ta lafazin shi ne "mahaifi". Shi
ya sa da zaran an faɗi lafazin, kai tsaye mahaifi
ake nufi.
13- Sa'annan kuma idan sun
yi Tawilin Hadisin baban Annabi (saw) da baffa, to wane Tawilin suka yi wa
Hadisin mamarsa kuma?!
14- Haka kuma, idan sun yi
Tawilin Hadisin baban Annabi (saw), to wane Tawilin suka yi wa sauran waɗanda
Annabi (saw) ya ce: ƴan
wuta ne, alhali su ma "Ahlul Fatra" ne, kamar baban shi wanda ya
tambayi Annabi (saw) ya ce: ina babana? Sai Annabi (saw) ya ce: "Yana
wuta".... Da sauran waɗanda Annabi (saw) ya ce suna
wuta, irin su Amru bn Luhayyi, Abdullahi bn Jud'an, da sauransu?!
15- Saboda haka, sam babin
labarai da Allah da Manzonsa suka bayar, da sauran lamura na gaibi, na labarin
makomar wasu a Lahira da sauransu, ba a kutsawa cikinsa da hankali ko aɗifa
ko shubuhohi. Kawai sallamawa ake yi, a miƙa
lamarin ga Allah, a ce:
"سمعنا
وصدقنا وآمنا".
Shi ya sa irin waɗannan
Hadisai na labarin makomar iyayen Annabi (saw) da sauransu, duka daidai suke da
Hadisan siffofin Allah, waɗanda Salaf suke cewa:
"أمروها
كما جاءت".
Ma'ana; ku bar su a yadda
suke, a yadda suka zo, kada ku yi shisshigi, ku kutsa cikinsu.
16- Idan an lura, duka waɗannan
bayanai an fiskantar da su ne ga Ahlus Sunna, waɗanda
sun yarda da Hadisan. Don haka ba ana magana ne da ƴan bidi'a, ko sauran masu ƙaryata Hadisan ba.
17- Saboda haka, ya ku Ahlus
Sunna ku sauƙaƙa wa junanku wajen tattauna mas'alar,
mas'ala ce wacce bai kamata a zafafa a kanta ba, idan za a kalle ta a ilmance.
Duk wanda yake ganin zai yi Tawilin Hadisin, to a bar shi, to amma bai halasta
yana amfani da kibiyoyin ƴan
bidi'a yana harba su kan Ahlus Sunna masu tabbatar da Hadisan a zahirinsu ba,
kamar jifansu da cewa; ba sa son Annabi (saw), ko cewa; suna cutar da Annabi
(saw). Gaskiya wannan zalunci ne, da ketare iyaka. Saboda duk wanda ka yi masa
hukunci ba ya son Annabi (saw), to fa kai tsaye ka kafirta shi.
Idan kuma ka ce: yana cutar
da Annabi (saw), to ka jefa shi cikin munafukai, waɗanda
su aka sani da cutar da Annabi (saw), alhali duka waɗannan
ja'iran hukunce - hukunce ne.
18- Kuma ya kai mai Tawilin
Hadisin, kada ka manta cewa; shi mai tabbatar da Hadisin ba daga aljihunsa ya
fitar da abin da yake faɗan ba, a'a, aiki ya yi da
Hadisai ingantattu. Kuma ba a samu inkarin zahirin Hadisan ba sai a ƙarnonin baya, amma a ƙarnonin farkon al'umma, duk waɗanda
suka yi magana a kan Hadisan, ko suka ruwaito su a littatafansu, tabbatar da su
a kan mahaifan Annabi (saw) suke yi, ba sa Tawili.
Don haka, shin zai yiwu a ce
duka manyan Malaman Addini da suka tabbatar da Hadisan a kan mahaifan Annabi
(saw), su ma maƙiya
Annabi (saw) ne, ko masu cutar da shi (saw)?!
19- Sai kuma ku masu
tabbatar da Hadisan a kan mahaifan Annabi (saw), ya kamata ku san wani abu guda
mai muhimmanci; wannar mas'ala, mas'ala ce mai sosa rai. Mas'ala wacce hatta
Annabi (saw) sai da ya yi kuka a kanta, Sahabbansa suka yi kuka, a lokacin da
Allah ya hana shi nema wa mahaifiyarsa gafara. Saboda haka don Allah a dena
tayar da mas'alar idan ba da buƙata
ba. Kuma idan ma buƙata
ta sa an tayar da ita, to don Allah mu zama cikin masu taya Manzon Allah (saw)
tausaya wa mahaifan nasa, don shi har kuka ya yi, ya saka Sahabbansa kuka.
20- Sa'annan kuma sau da
yawa za ka ji masu Tawilin Hadisan suna cewa; bayyana Hadisan makomar iyayen
Annabin (saw) ba shi da wani amfani.
To a gaskiya wannar magana
kuskure ce. Saboda abubuwa kamar haka:
(A) Da a ce ba shi da
amfani, shin Annabin (saw) zai faɗa?!
Kana nufin Annabi (saw) zai
faɗi
abin da ba shi da amfani kenan?!
(B) Kuma ai wajibi ne mu
gaskata dukkan labarin da Annabi (saw) ya bayar, mu yi imani da shi.
(C) Kuma hukunce - hukuncen
Allah kashi uku ne:
(1) Hukunci na Shari'a.
(2) Hukunci na Ƙaddara.
(3) Hukunci na
"Jaza'i", wato hukunci na sakamako.
To mas'alar makoma a Lahira,
tana cikin nau'i na uku ne, wato Hukunci na "Jaza'i". Don haka kamar
yadda wajibi ne ka yi imani, ka gaskata hukuncin Shari'a da na Ƙaddara, to haka wajibi ne ka yi imani,
ka gaskata duk wani hukuncin Allah na jaza'i, da sakamako da zai yi wa bayinsa,
musamman waɗanda Allah ya ba da labari a cikin Alƙur'ani, kamar makomar Fir'auna, ko
Annabi (saw) ya ba da labari, kamar makomar iyayensa, da sauran waɗanda
ya ba da labarin suna wuta, alhali sun mutu kafin aiko Annabi (saw).
21- Kuma ya wajaba masu
Tawilin Hadisan su zama masu adalci, su dena zargin masu tabbatar da zahirin
Hadisan da cewa; suna tayar da fitina, suna yawaita magana a kan mas'alar.
Tsakani da Allah kowa ya san cewa; ƴan
bidi'a ne suke tayar mas'alar, don su rinƙa
tunzura gama-garin mutane, don su ƙyamaci
Ahlus Sunna/ƴan Izala. Har ya kai
ga taruka da maulidi suke shiryawa, na iyayen Annabi (saw). Bai daɗe
ba, kwanan nan na ga sun yi taro a kan iyayen Annabi (saw). To a ƙa'ida; duk lokacin da aka bayyana ɓarna
da bidi'a, to ya wajaba a yi inkarinta, a yi bayanin abin da ya tabbata a Sunna
da Hadisai.
22- Daga ƙarshe, wannar mas'ala ce mai sauƙi idan za a kalle ta da madubi na ilmi,
mai girma ce idan da zallar aɗifa za a kalle ta, kuma za
ta iya janyo fitina.
Ilimi kuwa shi ne gaba da aɗifa.
Don haka wanda ya tabbatar da Hadisan a kan mahaifan Annabi (saw), bisa imani
da Hadisan Annabi (saw) ya yi dadai.
Haka shi ma wanda ya yi
Tawili, saboda ya kasa fahimtar Hadisan a zahirinsu, don ganin Ayoyi da suke
nuna cewa; ba a aiko musu manzo ba, shi ma yana da uzuri.
Amma duk wanda zai yi raddi
ga ɗaya ɓangare,
bisa mummunar manufa, ko a haɗe da jahilci da zalunci, to
ya sani zai haɗu da Allah, kuma zai girbi mummunan
aikin da ya shuka
23- Don haka ina ƙara maimaitawa, su masu tabbatar da
Hadisan a kan mahaifan Annabi (saw), Sunna ita ce; muna taya Annabi (saw)
tausaya musu, saboda shi har kuka ya yi, haka Sahabban da suke tare da shi su
ma sun yi kuka.
Allah ka shiryar da mu hanya
madaidaiciya.
✍️ Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)
25
August, 2026
Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.