𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum wai yahalata wata ce ta cemun idan suka gama saduwa da mijinta da dare ba ta yin wanka sai da safe saita wanke inda najasar take sai ta yi alwala ta yi sallah Damarece sai ta yi wanka idan za ta yi sallar azahar wai ana yin hakanan nacemata ba ayi ta ce ana yi nikuma ban yarda ba shine na ce bari nai tambaya.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam:- Inna lillahi Wa inna Ilaihi
Rajee'un, Subhanallah, toh idan haka ta ke Yi ta sani Cewa Ba ta da Sallah. Duk
Sallar da ta ke yi babu shi kuma sai ta sake yin su gaba ɗayan su. Domin ana yin ibadar Allah idan mutum Yana da
Tsarki, ita kuma ba ta da shi sabida ba ta yi Wankan Janaba ba, Haka zalika ba
Taimama ta yi a Lokacin da za ta yi Sallar ba, Kai ji ma dakyau, duk Wadda yayi
ibadar Allah Bai da Tsarki a jikin sa Kuma Yana da sani bawai Mantuwa yayi ba,
Kika Yi shi a cikin Ganganci, toh malamai suka ce mutum ya Kafirta. Allah ya
tsare, ya Shirya.
A cikin Littafin FIQHU Akwai inda ake magana Cewa
Kamar Misalin a Lokacin Sanyin, toh matukar ba ku tanadi Ruwan Dumi wadda idan
Kun Gama Jima'in ku za kuyi Wankan janaba a Lokacin ba, toh suka ce kada ku yi
Jima'in, domin kada ku yi Jima'in Babu Ruwan Dumi da zakuyi wanka sa'annan
lokacin Sallah zai yi, sai ruwan Sanyi ya hana ku yin wankan Janaba kuma ga
lokacin Sallah suka ce kada a yi Jima'in. Toh shin su me matsayin su a yanzu?
Sa'annan idan ma babu Ruwan Dumi na wankan janaba
domin Suna gudun Cutuwa, toh ai ba a ce a yi Alwala a yi Sallah ba haka kawai
ba, Cewa aka yi mutum yayi TAIMAMA a yi Sallar a haka, idan za ki kwanta Bacci
aka ce Yana dakyau ki yi Alwala ki Kwanta da shi, Amma ba a Cewa aka yi Wai
idan za ki yi Sallah ki yi Alwala, kiyi Sallah alhalin kina tare da Janaba a
jikin ki bakiyi Wanka ba, Subhanallah wannan Wasa da ibadar Allah ne.
Sabida Haka ba ta da ibada, domin ita Cewa ta yi Wai
Alwala ta ke Yi Kuma Wai ta yi Sallah a hakan ba tare da ta yi wankan janaba?
Toh ba ta da Sallah duk Sallar ta idan Haka take Yi ba ta da Sallah. Allah ya
shirya.
Sa'annan Kuma ita ba ta tunanin Cewa Ko Allah zai ɗauki Rayuwar ta a Cikin Daren ba tare da ta yi wankan
Janaba ba fa? Wannan wani irin kuskure ne ko Jahilci? Ko Kuma ba ta tunanin
Cewa zata shiga cikin jama'a ko inda yake da Tsarki Alhalin ita ba ta da
Tsarkin, me amfanin ma ku yi Jima'i tun dare Amma Wai ki kwana ba ki yi wanka
ba sai Lokacin Sallar Azahar kafin Nan ki ce Wai Bari ki je ki yi wanka? Duk
Wadda ta ke yin Haka toh Daman ibadah Bai dame ta wannan shiyasa ta ke yin Wasa
da ibadar Allah.
Kuma wallahi Allah ya ce Bone, wato Narkon Azaba🔥ya tabbata ga
masu wasa da ibada! bawai waɗanda suke Yi ba,
A'a ke da kike Yi amma kike Wasa da ibadar Allah, toh Azabar Allah ya tabbata a
kanki a Ranar Alkiyama.
Sabida Haka a ji tsoron Allah Ibadar Allah ba abun
Wasa bane, idan Kun San ba za ku tsaya dakyau ku yi ibadar Allah yadda yakamata
ba, toh me Amfanin Jima'in ku? Ku ji daɗin ku a nan duniya
ku je Lahira ku tarar da Azabar Allah, shin me kuka Yi Kenan? Allah ya tsare ya
raba mu da Son Zuciya.
Sa'annan a yanzu wai sai a samu Mace Matar Aure ce
ko Budurwa sun shiga groups na koyar da styles na Jima'i domin wai ta burge
Mijin ta, amma wallahi da za a bincika Addinin ta ba ta San shi ba, yanzu
wannan matar Ina ta san Addinin ta? Ina Mijin ta ya San Addinin sa? da ace
dukkan su suna da Addini wallahi shi Mijin ba zai taɓa barin ta ta yi irin wannan Kuskuren ba, haka ita Kanta
da Addinin ta ke da shi wallahi da ba za ta yi irin wannan Kuskuren ba.
Amma a yanzu wai Mace damuwar ta shi ne ta koyi
yadda ake yin Jima'i da Namiji tana kallon BF, tana kallon Cartoon, tana
karanta Littatafan novels na Jima'i da sunan ai babu laifi ta yi hakan tunda
ita Matar Aure ce, ga abun da yake wajibi a kanki dole ne ki nema ki Sani shine
Addinin ki amma ba ki nema ba wai kin je kina koyarwan style na Jima'i, ki kawo
min Hadisi ko Ayar da Ya ce Mace Matar Aure ta shiga group domin a Koya mata
style na Jam'i? sabida haka Haramun ne Haramun ne duk Matar da ta ke shiga
group na style na Jima'i da ki shirya amsa tambayar da za ki ba wa Allah a
ranar Alqimaya.
Sa'annan rayuwar Yaran ki suna cikin Hatsari
wallahi ko kina so ko ba ki so Yaran ki wannan rayuwar style ɗin sune za su tashi da shi su zama Yan iska ko Yar Iska a
Anguwar ku ba yadda kika iya domin koyi da Arna da kuka yi.
ke ba ki tsaya kin nema sanin Addinin ki abun da
zai Cece ki a ranar Alqimaya ba kin je kina deban Zunubai, Jinin hailar ki
wannan da zai rikice ba ki San komai a kansa ba, amma kin je kina Shiga group
wai a koya miki yin Jima'i domin kada ki ji Kunya a gurin Namiji, ba za ki ji
Kunya a gurin Namiji ba amma a Lahirar ki za ki ji kunyar da ba za ki dawo ace
ki warware shi ba, Mata a ji tsoron Allah a tashi a nemi ilmin Addini sosai
Sa'annan a Auri Mazajen da suke da ilmin Addini, wallahi idan kin Auri Mijin da
babu Addini kema ba ki da shi toh Lahirar ki akwai matsala sosai wallahi. Allah
ya shirya. Dafatan Kin gane Koh??
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.