Ticker

6/recent/ticker-posts

Mafita Daga Kuncin Rayuwa

A wannar kasa da muke rayuwa a cikinta, a wannan lokaci da muke ciki, musamman a wannan hali na kuncin rayuwa da muke ciki, mutane suna cikin rudu da damuwa, kowa yana neman mafita, da yanayi da zai samu saukin kuncin tsadar rayuwa.

Kowa cikin mutane yana ta fadi-tashi na neman jin dadin rayuwa; a ce ya fi karfin abincinsa shi da iyalansa, ya fi karfin kiwon lafiyarsa da ta iyalansa, ya fi karfin dawainiyar ilimi da karatunsa da na iyalansa, ya mallaki gida da abin hawa na alfarma, dukkan wata bukata a rayuwa yana iya biyanta, bayan ya samu iyali irin kalar da ya fi so, har yana samun daman tafiye-tafiye na shakatawa.

Mafi yawan mutane sun dauka wannan kadai shi ne sa'ada da jin dadin rayuwa. Shi ya sa kowa ya gigice ya bazama wajen neman tara dukiya, yana ganin a nan sa'ada da jin dadin rayuwa take. Wasu kuma neman mulki da shugabanci ido rufe, wasu kuma neman shahara da neman suna da girma da daukaka a wajen mutane, da sauran hanyoyi da mutane suke zaton a nan za su samu sa'ada da jin dadin rayuwa.

To idan muka lura da kyau za mu ga masu wannan sun takaita jin dadin rayuwa ne a kan gangar jiki kadai, shi ya sa duka tunaninsu ya kare a kan hanyoyin jin dadin rayuwa na zahiri.

Alhali mutum nawa suka samu kudi, ko shahara ko mulki, ko mata, amma kullum a cikin bakin ciki da damuwa suke?

Mutum nawa ne suka samu irin wadannan abubuwa, amma suna kashe kawunansu, saboda damuwa?

Mutum nawa suke da wadannan abubuwa, amma sun afka cikin shaye-shaye da ta'amuli da miyagun kwayoyi, don neman kwanciyar hankali?

Mutane nawa suna da kayan jin dadin rayuwa na zahiri amma kuma sun afka aikata miyagun laifuka na ta'addanci da zubar da jini?

Ashe kenan hakikanin jin dadin rayuwa, da samun sa'ada da kwanciyar hankali da samun rayuwa mai dadi tana bayan wadannan abubuwa gaba daya.

Duk wanda yake son rayuwa ta hakika to ya amsa ma Allah da Manzonsa ga kiran da suka yi masa. Allah ya ce:

{استجيبوا لله وللرسول إذا دعاكم لما يحييكم} [الأنفال: ٢٤].

Duk wanda yake son rayuwa mai dadi to ya yi imani da Allah ya yi kyakkyawan aiki. Allah ya ce:

{من عمل صالحا من ذكر أو أنثى وهو مؤمن فلنحيينه حياة طيبة} [النحل: ٩٧].

Duk wanda yake son nitsuwa a zuciyarsa to ya rike zikiri da ambaton Allah. Allah ya ce:

{ألا بذكر الله تطمئن القلوب} [الرعد: ٢٨].

Rashin zikiri da ambaton Allah shi yake janyo kuncin rayuwa. Allah ya ce:

{ومن أعرض عن ذكري فإن له معيشة ضنكا} [طه: ١٢٤].

Hakikanin rayuwa, da rayuwa mai dadi tana cikin rayuwar ruhi, wacce ake raya ta da imani da jin tsoron Allah. Lallai duk wanda ya riki wannar hanya ba zai taba shiga cikin kuncin rayuwa ba, ko da ba shi da sisin kwabo a rayuwarsa. Kuma wannar hanya ita ce hanya ta hakika ta samun arziki da fita daga mawuyacin halin rayuwa, na talauci da fatara da yunwa da tsadar rayuwa. Allah ya ce:

{ولو أن أهل القرى آمنوا واتقوا لفتحنا عليهم بركات من السماء والأرض} [الأعراف: ٩٦]

Saboda haka bin hanyoyi na Shari'a, sannan sai aiki da sabuba na halal na samun arziki su suke samar da kwanciyar hankali da sa'ada da jin dadin rayuwa.

Dr. Aliyu Muh'd Sani (H)

10 August, 2023

Daga zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

zauren Dr. Aliyu Muhammad Sani

Post a Comment

0 Comments