WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA
Na
Yakubu Aliyu Gobir
Da
Abu-Ubaida Sani
Waƙa dai ba baƙuwar kalma ba ce. Tuni masana da manazarta suka yi caa a kanta wurin gudanar da bincike da rubuce-rubuce iri-iri a matakan ilimi daban-daban. Wannan ba ya rasa nasaba da yadda waƙa ta kasance komai-da-ruwanka ga rayuwar Bahaushe da ma sauran al’ummu duniya gaba ɗaya. Bahaushe na yin cuɗanya da waƙa a kusan dukkanin al’amuransa na yau da kullum. Wannan ya haɗa da siyasa da bukukuwa da wasanni da ilimantarwa da talla, kai har ma da wasu lamurran da suka shafi addini a wasu lokutan.[1] Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da yadda waƙa ta kasance mai matuƙar shiga jiki tare da kama zuciya da kuma jan hankali.
Sai dai waƙa ba ta kasance nau’i
guda ba kawai. A maimakon haka, akan samu sauye-sauye da kuma sabbin salailai
da sigogin waƙoƙi lokaci zuwa lokaci. Tun Bahaushe yana rera waƙoƙinsa da ka, har aka
kai lokacin da ya fara rubuta su. Wannan ya faru bayan cuɗanyarsa da baƙin al’ummu musamman
Larabawa da Turawa, wanda hakan ya samar masa da ilimin
karatu da rubutu. Da tafiya ta yi tafiya kuma, sai zamani ya zo masa da sabon
salon amfani da kayan kiɗan zamani domin rera
waƙoƙinsa. Irin waɗannan waƙoƙin ne har yau ake
kai-komo kan sunan da ya dace a raɗa musu, musamman yadda suka kasance jemage,
ba ka ga tsuntsu ba ka ga dabba. Wato dai suna ɗauke da siffofin waƙoƙin baka da kuma na
rubutattun waƙoƙi.[2]
Koma dai yaya abin yake, dole ne a yarda zamani ne ya zo da wannan tsari na waƙa.
A ɓangare guda kuma,
samuwar waƙoƙin zamani na sutudiyo da kuma wasu nau’ukan tasirin
zammani a kan waƙoƙin Bahaushe na gargajiya sun daƙusar da su waƙoƙin gargajiyar, wanda
har ta kai ga suna ƙoƙarin ɓacewa gaba ɗaya. Wannan ne ya samar da buƙatar yin wani yunƙuri domin tattara muhimman
bayanai da za su adana waɗannan nau’ukan waƙoƙi wuri guda domin
gujewa salwantarsu. Wato dai ko da an wayi gari babu su a aikace, to kuwa za a
ci gaba da tarar da su a rubuce, HAR MADI.
Wannan littafi ya yi ƙoƙarin
tattara bayanai dangane da waƙoƙin Bahaushe na
gargajiya. An raba littafin zuwa babi-babi har
guda takwas. Babi na farko ya kasance gabatarwa ne ga littafin. A cikin babin
an waiwaici ra’ayoyin masana dangane da asalin waƙa. Baya ga haka, an
kawo amfani ko muhimmancin waƙoƙin na gargajiya. Daga
ciki akwai faɗakarwa da ilimantarwa
da nishaɗantarwa da koyar da
jarumta da
talla da kuma addu’ar alkairi da dai sauransu. Sannan kamar yadda Bahaushe
ke cewa:
“Kowane allazi da nasa amanu…” haka ma waƙoƙin na da naƙasu ko koma baya.
Wannan kuwa ya haɗa da amfani da
maganganun batsa ga wasu daga cikin waƙoƙin.
Babi na biyu ya mayar
da hankali ne kan waƙoƙin wasanni. Wannan wani rukuni ne daga cikin
rukunonin waƙoƙin baka. Akan rera waƙoƙi iri-iri yayin
gudanar da wasanni daban-daban. Waɗannan waƙoƙi na zuwa da jigogi
mabambanta wanda hakan ya danganta da lokaci da wurin wasan,
da kuma masu gudanar da wasan da ma dalilin
gudanar da shi.
A cikin wannan babi na biyu, an kawo misalan wasannin da ke ɗauke da waƙoƙi. Daga ciki har da
wasannin yara maza da na yara mata (wasannin gaɗa) da kuma wasannin tashe.
Babi na uku kuwa, ya
mayar da hankali ne kan waƙoƙin aikace-aikace.
Wannan ya fi shafar mata kai-tsaye. Nau’ukan waƙoƙi ne da mata ke
rerawa yayin gudanar da ayyuka daban-daban. Irin waɗannan waƙoƙi na ɗebe musu kewa tare da
ƙara
musu kuzarin gudanar da aiki. Daga cikin irin ayyukan da akan rera waƙa yayin gudanar da su
akwai: Daɓe da saƙa da kitso da daka da
kaɗi da dai sauransu.
A cikin babi na huɗu, an kawo waƙoƙin gargajiya da suka shafi aure ko raka amarya. Da ma dai, bukukuwan Bahaushe na cuɗanye da waƙoƙi da kirare-kirare,
ciki har da bukin aure. A yayin bukin aure, mata da ‘yanmata
na rera waƙe-waƙe, musamman ma lokacin da suke kan
hanyar raka amarya ɗakinta. Yawanci
jigogin waɗannan waƙoƙi sun fi karkata kan
bankwana ga amarya da tunasar da ita babban aikin da ke gabanta na zaman aure
tare kuma da rarrashinta. Babin ya kawo jeranton misalai na irin waɗannan waƙoƙi.
Babi na biyar kuwa,
ya duƙufa ne wurin kawo misalan waƙoƙin cikin tatsuniya. Tatsuniyoyin Bahaushe sun kasance
wani babban bagire da akan samu misalan waƙoƙinsa na gargajiya. Waƙoƙin na da amfani cikin
waɗannan tatsuniyoyi ta
fuskar fito da jigoginsu da suka haɗa da faɗakarwa da ilimantarwa da jarumta da dai
makamantansu. Sannan waƙoƙin sukan kasance ƙarin gishiri ga waɗannan tatsuniyoyi.
Babin na biyar ya kawo misalan wasu daga cikin waƙoƙin gargajiya na
tatsuniyoyin Bahaushe.
A babi na shida, an
kawo misalan waƙoƙin baka ne da suka shafi roƙon ruwa. Wannan ma dai wani rukuni ne na waƙoƙin bakan Bahaushe. Waƙoƙin sun haɗa da caccayya da
Halilu da Allah mun tuba da dai makamantansu. A gaba
kuwa, wato babi na bakwai, an kawo waƙoƙi ne da suka shafi
bara. Bara dai al’ada ce da ta daɗe a ƙasar Hausa. Mabarata
na amfani da waƙoƙin yayin gudanar da bararsu. Daga cikin irin waɗannan waƙoƙi akwai Saboda Manzon Allah da Mu Roƙi Allah Sarki da makamantansu.
Babi na takwas ya
kasance na ƙarshe a cikin littafin. Yana ɗauke da bayanai
kan siffofin waƙoƙin gargajiya, tamkar dai yadda aka kawo misalan waƙoƙin a babukan da suka
gabata. Siffofin kuwa sun haɗa da rashin tafiya da ƙafiya ko ƙarangiya da
kasancewarsu ba su buƙatar kayan kiɗa da dai makamantansu.
[1]Haƙiƙa
tarihi ba zai manta da yadda Shehu Usmanu Ɗan
Fodiyo tare da jama’arsa suka yi amfani da waƙa wurin faɗakarwa tare da yaɗa addinin Musulunci, musamman a lokacin jahadi.
[2] Akwai masanan da ke ganin ya dace a kira waɗannan waƙoƙi da suna: “Waƙoƙin
Baka na Zamani.” Wasu ko na ganin ya dace ne a kira su da: “Waƙoƙin
Sutudiyo.” Akwai ma masu ganin ya dace ne a ce da su: “Waƙoƙin
Zamani” kaɗai. Har ila yau, akwai masu ganin ya
dace ne a kira su da suna: “Ruwa Biyu.”

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.