Jagora: Mai daraja ɗan Marahwa jikan Andi riƙa ƙwarai
Y/Amshi: Taka lahiya dai uban Bango,
Bida arna,
Mai martaba kak ka ɗau wargi,
Emiyan Gummi Lawal zarumin Sarki
Jagora: Kun gadi hanƙuri
Y/Amshi: Kuma kun gadi taimako,
Mulkin duniya naku na Sarki,
Riƙa da ƙarhin Allah na mai hwada sai madi
Jagora: Sarki ga farin jini
Ga kyauta ga fara'a
Wajjan fasinaliti jikan Ali ba
ayi kamatai ba
Y/Amshi: Kama da ɗan Aisha na nada Daudu yad dawo
Jagora: Yaushe rabo na da ganin daba?
Y/Amshi: Tun lokacin su Sarki Andi,
Na ɗan
Aisha tun tun tun,
A lokacin Mamman ga dawaki...
Jagora: Naga dawaki iri-iri
Y/Amshi: Akwai wani wanda ban saba kallo ba,
Bida arna,
Mai martaba kak ka ɗau wargi,
Emiyan Gummi Lawal Hassan zarumin
Sarki
Jagora: Kowas san Sarki Andi,
Da ganin Sarki Lawal
Igizatili mutun ko bai tambaya ba,
Jagora /Y/amshi: Yasan zuriyash shi ce babu tsentseni,
Bida arna,
Mai martaba kak ka ɗau wargi,
Emiyan Gummi Lawal Hassan zarumin
Sarki
Jagora: Sarkin Tabshi ina godiya gun Wahidun Rahimin Sarki
Y/Amshi: Yanzu hwaɗin Nijeriyag ga,
Kowane taro akai,
Da dud Gummi ta sabka ban
zullumin komi
Jagora: Wajen fasaha
Y/Amshi: Ba akai irin namu Sarki ba,
Jagora: Wajen fahimta
Y/Amshi: Ba akai irin namu Sarki ba,
Jagora:
In an ka shiga ga mulki
Y/Amshi :
Ba akai irin namu Sarki ba,
Jagora :
In an kazo ga ilmi
Y/Amshi :
Ba a kai irin namu Sarki ba,
Jagora :
Haka nan wurin muruwa
Y/Amshi :
Ba a kai irin namu Sarki ba,
Jagora:
Sannan wurin bajinta
Y/Amshi :
Ba akai irin namu Sarki ba,
Da ace kazo lokacin ana yaƙi,
Da kana kama Jangwarzo,
Gobirawa kuyi hattara banda
ganganci,
Ku zo ku kai caffa,
Maigidan naku ne yazzo,
Jagora :
Ɗauko Ɗan guma jini
Y/Amshi :
Ka ɗauko
takobin Waru,
Ƙasag Gobir dum muna son tazan hannu,
Bida arna,
Mai martaba kak ka ɗau wargi,
Emiyan Gummi Lawal Hassan zarumin Sarki.
Ɗiyan waƙa ne ☝️☝️☝️☝️☝️☝️☝️daga cikin wata waƙa da
Sarkin Taushin Gummi, Alh. Sani Ɗan
Aino Gyalange ya rerawa mai martaba Sarkin
Gummi na 15, wato Sarkin Mafaran Gummi Justice Lawal Hassan mai amshi
"Bida arna, mai martaba kak ka ɗau
wargi, emiyan Gummi Lawal Hassan zarumin Sarki".
Sharhin namu na yau zai ƙumshi
abubuwa masu dama gwargwadon hali.
Sarkin Taushi Alh. Sani Ɗan
Aino ɗa ne ga Makaɗa Muhammadu Ɗan
Aino Gyalange wani mashahurin Makaɗin
noma da aka yi a garin Gyalange hedikwatar gundumar Gyalange a masarautar
Gummi, Jihar Zamfara. Ya yi kiɗa
ne da ganga ta ratayawa da ɗansa
Alh. Sani ya gaje/gade shi bayan rasuwarsa sai ya sauya salon sabgar ta hanyar
amfani da Taushi a maimakon ganga kuma ya shiga fagen kiɗan sarakuna da na jama'a.
Ya yi karatun addini da na zamani
domin har takardar shaidar malanta ta ƙasa (NCE) ya samu ya kuma yi aikin
koyarwa a matakin makarantar furamare. Shi ne ma dalilin da yasa ake tsintar
wasu kalmomi na turanci a cikin waƙoƙinsa, misali a wannan waƙa ya
yi amfani da kalmomi biyu na turanci "fasinaliti/personality da
igizatili/exactly.
Ya yi zamani da Sarakunan Gummi
guda 3, Sarkin Mafaran Gummi Alh. Aliyu Isah da Sarkin Mafaran Gummi Alhaji
Aliyu Adamu Abara da kuma Sarki dake
akan karagar mulki a halin yanzu, kenan Sarki na 13 dana 14 da kuma na 15. Ya
rasu kusan watanni 6 da suka wuce yana da kimanin shekaru 61 a duniya. Allah ya
kyauta makwanci, amin.
A cikin waɗannan ɗiyan
waƙa
Sarkin Taushi Sani Ɗan Aino Gyalange ya zayyana wasu daga cikin halayen mai
martaba Sarki Justice Lawal Hassan da kuma irin yadda kasancewarsa Sarki ya
sanya masarautar Gummi ta ƙara samun daraja da ɗaukaka
a idon duniya.
A ciki dai ya fito da salsalar
mai martaba Sarki "Kowas san Sarki Andi, da ganin Sarki Lawal igizatili
mutun ko bai tambaya ba, yasan zuriyash shi ce babu tsentseni".
Wane ne Andi da Sarkin Taushi
Sani Ɗan
Aino Gyalange ya kwatanta da mai martaba Sarki?
Muhammadu Andi shi ne Sarki na 10
a masarautar Gummi yayi sarauta daga shekarar 1910-1933, shi kuma ɗan Sarkin Marafan Gummi na
7 ne, wato Sarki Abdullahi Laje da yayi mulki daga shekarar 1867-1892, shi kuma
ɗan Sarkin Mafaran
Gummi na 5 ne, wato Sarki Ɗan A'isha wanda ya yi
sarauta daga shekarar 1847-1864, shi kuma ɗan
Sarkin Mafaran Gummi na farko ne, wato Sarki Muhammadu Waru wanda ya yi sarauta
daga shekarar 1782 zuwa 1807, shi kuma ɗan
Sarki Ali Bazamfare ne wanda ya samar da masarautar Bukkuyum ta Jihar Zamfara.
Sarki Muhammadu Andi ne ya haifi
Malam Hassan, Malam Hassan ɗan
Muhammadu Andi ɗan
Abdullahi Laje ɗan
Umaru Ɗ/Aisha
ɗan Muhammadu Waru ɗan Ali Bazamfare shi ne
mahaifin mai martaba Sarki Justice Lawal Hassan na yanzu da ya zama Sarki a
shekarar 2013.
Gummi Gumama ta Ali mai kamar yau
sallah, dogon birnin garin mai saje ". Wani Mafarauci ne da ake kira
Muhammadu Bangu sanadiyar samar da wannan suna " Gummi" saboda wata
kibiyarsa da yake yiwa kirari "Guma jini ba amon dahi" ko kuma batun
da yake yi idan ya yi amfani da ita ya kashe wata dabba ta daji ya kance
"na guma mata/na guma mashi kibiya" sannu a hankali sai wannan wuri
da yake zaune ya ɗauki
suna "Gumi ko Gummi".
Sarkin Gummi na farko wato
Muhammadu Waru ɗa ne
ga Ali Bazamfare da ya fito daga cikin Zamfarawan Mafara/Talata Mafara tun suna
zaune a Tumfafiya /Tumfafi a matsayin hedikwatarsu wato kafin su koma
Mafara/Talata Mafara a lokacin mulki Sarki Ɗangarji.
Ali Bazamfare ya nusa kudu maso
yammacin Tumfafiya har zuwa Fakai da
Danko a masarautar Zurun Jihar Kebbi ta yau.
Ya haifi 'ya'ya 3 maza, Kure wanda ya baro a Danko a matsayin Sarki da Ɗanƙofa da
kuma Muhammadu Waru.
Muhammadu Waru ya ɗebi jama'a zuwa wani wuri
da ake kira Kagarar Fulani dake kusa da tungar da Mafarauci Muhammadu Bangu ya
zauna da sannu a hankali ta amsa sunan "Gummi" a shekarar 1782 ya
samar da tsarin mulki irin na sarauta da laƙabin "Sarkin Mafara" domin
tawilin asalin inda mahaifinsa ya fito wato Mafara/Talata Mafara.
Ya yi mulki har zuwa wafatinsa a
shekarar 1807 saboda haka ma ne suka yi mu'amala ta ƙud da ƙud da
masu jihadin jaddada addinin musulunci na Daular Usmaniyya da Mujaddadi Shehu
Usman Danfodiyo Tagammadahullah Birahamatihi ya jagoranta a lokacin.
A cikin waƙar Sarkin Taushi Sani Ɗan
Aino Gyalange ya dawo da wani tarihi domin tunatar da mai martaba Sarki (duk da
zuriyar Dakka ne abun ya faru dasu ba zuriyar Buda Jan Masari inda Ali
Bazamfare mahaifin Muhammadu Waru kakan Sarki bane , amma dai dukan su jinsin Zamfarawa ne) cewa akwai buƙatar
ya ci ƙasar
Gobir /Gobirawa da yaƙi har ma yana nuna masa cewa "Da ace kazo lokacin ana yaƙi, da
kana kama Jangwarzo, Gobirawa kuyi hattara, kuzo ku kai caffa maigidan naku na
yazzo".
Wannan wani abu ne da ya faru a
shiyoyin 1760s zuwa 1770s lokacin da Sarkin Gobir Ibrahim Babari mahaifin
Sarkin Gobir Malam Umaru Bawa Jangwarzo ya mamaye Zamfarawa har ma ya ƙwace
masu hedikwata da ake kira Birnin Zamfara a lokacin mulkin Sarkin Zamfara Maroƙi ɗan Sarki Malo (Kangon
Birnin Zamfara a halin yanzu yana kusa
da garin Isa, Ƙaramar Hukumar Mulkin Isa ta Jihar Sakkwato ta yau).
Lallai Sarkin Taushi Sani Ɗan
Aino Gyalange ya haikato muna lamurra masu yawa da muhimmanci a cikin wannan waƙa.
A wannan hoto mai martaba Sarkin
Mafaran Gummi na 15 ne mai mulkin Masarautar Gummi mai daraja ta ɗaya a Jihar Zamfara,
Nijeriya, Justice Lawal Hassan Gummi.
Allah SWT ya ƙarawa mai martaba Sarki lafiya da nisan
kwana mai albarka, ya jaddadawa dukan magabatanmu rahama ya sa mu wanye lafiya
mu cika da kyau da imani Alfarmar Fiyayyen Halitta Rasulallahi Sallallahu
Alaihim Wasallam, amin ya rabbal alamin.
Daga Taskar:
Hon. Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin
Birnin Magaji) Jihar Zamfara, Nijeriya.
5/08/2026.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.