Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Kallon Korean Films Tare Da Yawan Istigfari

TAMBAYA

Aslm malam ya aiki Ubangiji ya karawa malam lpy,malam akwai lokacin da na ji wani ya tambayi malam Yelwa akan yana aikata zunubi yana istigfari mene hukuncin haka shi ne ya ce mishi yana akan tsinuwar Ubangiji ne. Ni kuma, tambaya ta a nan ita ce: ina yawan kallon Korean film ne, ba wai wanda bai kamata ba; a'a, normal films ne wanda ina iya kalla da ni da yaran gidanmu ko mamata. To, idan ina kalla, ina yin istigfari, dan Allah, me ne hukuncin hakan?

AMSA:‼️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.

Yar'uwa Abinda aka sani shi ne, idan mutum yana aikata wani zunubi sannan yana yawan istigfari, hukuncin hakan ya danganta da halin zuciyarsa. Idan yana istigfari da gaske yana nadamar zunubin, yana fatan Allah Ya gafarta masa kuma yana ƙoƙarin dainawa ko da yana sake faɗawa saboda raunin ɗan Adam, wannan yana cikin masu fatan samun rahamar Allah, ba'a cewa yana ƙarƙashin tsinuwar Allah kai tsaye ba. Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:

 قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِن رَّحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعً

 Kace Ya bayina waɗanda suka yi wa kansu ɓarna Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah Yana gafarta zunubai gaba ɗaya. (Suratul Zumar ayata 53).

Haka kuma Annabi ya ce:

«كُلُّ ابْنِ آدَمَ خَطَّاءٌ، وَخَيْرُ الْخَطَّائِينَ التَّوَّابُونَ»

Ma'ana:

"Dukan 'ya'yan Adamu masu yawan kuskure ne, kuma mafi alherin masu kuskure su ne masu yawan tuba." Amma idan mutum ya mayar da zunubi abin wasa, yana aikata shi da ganganci ba tare da nadama ko niyyar dainawa ba, sannan yana ɗaukar istigfari kalma ce kawai, wannan hali ne mai haɗari kuma ya kamata yaji tsoron Allah.

Game da kallon Korean films kuwa, idan fina-finan na halal ne, basu ƙunshj tsiraici, alfasha, saƙonnin da suka saɓa wa Musulunci, ko abinda zai tayar da sha'awa ba, kuma basa hana ki cika wajibai na addini, to asali babu laifi a kallonsu. Saboda haka, idan kina kallonsu sannan kina yawan istigfari, babu laifi a cikin hakan. Amma idan suna ƙunshe da abubuwan da Allah Ya haramta, to wajibi ne ki nisance su, ki cigaba da yin tuba da istigfari, domin Allah Yana karɓar tubar bayinsa masu komawa gare Shi da gaskiya, kuma Manzon Allah ya ce:

«التَّائِبُ مِنَ الذَّنْبِ كَمَنْ لَا ذَنْبَ لَهُ»

 ma'ana: "Mai tuba daga zunubi kamar wanda bai taɓa yin zunubi bane." Sboda haka, ki cigaba da yawan istigfari da ƙoƙarin nisantar duk abinda kika san zai saɓa wa Allah, tare da kyautata zato ga Ubangijinki da kuma ƙarfafa kanki a kan biyayya. Allah ta'ala yasa mudace,

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam   

Post a Comment

0 Comments