𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Salamu alaikum waramatullah malam don Allah ka taimaka min, mlm mijina shi baya saduwa dani haka kawai sai ya saka condum shin idan na hana shi kaina na yi laifi ne? Na gode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikis Salaam Wa Ramatullahi:
Toh Wannan Magana ta ki Akwai Maganganu akai
sosai, shin me ya sa yake son sa Condom idan zai yi Jima'i da ke? Haihuwar ne
baya so ko Kuma menene? sa'annan idan haihuwar ce baya so shin kema ba ki son
Haihuwar ne? idan dukkan ku ba ku son haihuwar ne sai yake sa Condom, toh sai
mu ce babu komai wannan, idan Kuma shi ne baya son haihuwar ke kuma kina so,
toh a nan akwai bayani sosai, zamu yi a gaba. sa'annan idan yana Jima'i da ke
ba ki gamsuwa ne ya sa kike son hana shi domin ba ki gamsuwa? dole ne a samu Amsosin
nan daga gurin ki, Amma kafin nan ga bayanin kamar haka;
1. Abu na Farko Shi ne Matukar Ke Kina gamsuwa da
Mijin ki a Haka, Shima yana Gamsuwa da ke a Hakan wato idan ya Saka Kororon
Roban (condom) dukkanku Kuna samun Gamsuwa. toh Wannan Hurumin Mijin ki ne ya
Sadu da ke ta yadda yake Son Yin Jima'i da ke Wannan Hakkkin Sa ne, Domin inda
Allahu Subhanahu Wata'ala Yana Cewa, Matayen Ku Gonakin ne ku je Musu ta inda
Kuke so, amma banda ta Duburar ta.
Amma idan Shi ne Kaɗai yake Gamsuwa Bukatar sa ta biya, Amma ke ba ki Gamsuwa
ba ki Jin komai idan ya Saka Wannan Kororon Roban (condom), amma idan bai Saka
ba ya Sadu da ke Kin fi Gamsuwa da shi, toh nan Kuma Wajibi ne gare shi ya
Chanja Lalalel, domin Kamar yadda kike Gamsar da shi yake gujewa neman Matan
banza a waje, toh Shi ma yakamata tsaya ya miki Haka, babu Cuta babu Cutarwa a
Ciki.
Amma indai ba Zai rika Gamsar da ke ba, Sannan ya Ƙi Chanja Lalalel, kuma
Hakan yana Cutar da ke ba ki Gamsuwa dalilin haka kada ki faɗa Cikin halaka na zina ko Madigo, toh ki nema Magabatan
ku wato Waliyyan ku sai ki kai Maganar gaban su a Kira sa. Kafin ki fara Ɗaukar Salon rabuwa da
shi Domin kada ya cutar da ke, ki koma Saɓawa Ubangijin ki
ta wajen Aikata abun zai gamsar da ke ko Zina ko Madigo.
Hakazalika, Idan Har hakan da yake yi ba ki
Gamsuwa kuma Kinyi-Kinyi ya gyara ya Ƙi Gyarawa, toh Za a iya Raba Wannan Auren domin Kada Ke ki Faɗa Cikin Saɓawa Ubangijin ki
Wajen yin zina ko Madigo dole ne a raba Auren, Mafi Yawanci a yanzu abun da
wasu Matan Aure suke yi kenan wallahi idan Mijin su baya gamsar su sai su shiga
group na batsa da Namiji ko Mace sun yi musu magana shikenan sai su yarda su ba
da kansu ko Zina ko Madigo sabida haka irin wannan gara an raba Auren ya fi.
2. Na Biyu Shine, Idan Har Ke Kina Son Haihuwa,
Shi Kuma Mijin ki baya Son Haihuwa wata Kila Shiyasa yake Saka Kororon Roban
(condom) don kada ki Samu Ciki ki Haihu, kin ga Ra'ayin ki da nashi ya
Banbanta, toh tunda Ke Kina Son Haihuwa Shi Kuma baya Son Haihuwar Shiyasa ya
Saka Wannan robar domin kada Ki Samu Ciki ki Haihu, toh nan ma Za ki iya Hana
shi Kanki, Sa'annan Ki Nemi Magabatan ku ki Sanar da su Cewa ga Abun da yake
tafiya a Tsakanin ku, idan an kira shi ya dawo ya gyara yana Son Haihuwar ya dena
Saka Wannan Kororon Roban (condom), Shikenan haka ake buƙata, idan Kuma ya ƙi ya dena kuma ke kina Son Haihuwa. Toh kina da Zaɓin ki idan Kin ga Za ki iya Zama da shi a Haka ba ki
Gamsuwa da shi, Sa'annan babu Haihuwa da shi, toh sai ki Ci Gaba da Zama da shi
a Hakan ba tare da yin korafi ba, idan Kuma kina Son Haihuwa, kuma Kina Son ki
Rika Gamsuwa da shi idan yana Jima'i da ke, sai ga shi Shi bayan Son Haihuwar,
kuma ba ya Gamsar da ke, toh Wajibi ne a Raba Wannan Auren domin gudun faɗawa cikin halaka na zina ko na Madigo.
Haihuwa na Allah ce idan Allah ya ga dama, sai ya
gama Saka Kororon Roban sa ya Sadu da ke, Sai Ciki ya shige Miki kuma Ki Haihu,
don haka babu Abun da ya gagari Allah. sa'annan ki sani cewa ke Mace ce kina
bukatar taimako nan gaba idan kin karar da Karfin ki gaba ɗayan sa gurin Jima'i babu Yara wallahi za ki dawo kiyi
Allah Wa dai da rayuwar ki, domin Mazajen yanzu ba irin na da bane yanzu sai ki
ji ya sake ki, Karfin ki ya kare ba ki da Yaro ko ɗaya Kuma kin zo Matakin da lallai kina bukatar Yaro a
kusa da ke amma babu, don haka Mata a Rika yin nazari sosai kafin a yi abu
musamman Yan Mata da a yanzu kuke son yin Family planning, ke ko haihuwa 1 ba
kiyi ba wai kin je kin yi Family planning idan Allah ya tashi kama ku sai Allah
ya rike haihuwar ki ko kun dawo kuna son haihuwar wallahi ba za ku samu ba.
Ko kuma ki haifi Yara 2 ku ce a yi Family planning
don a samu Tazarar Yaran ku, toh idan Allah ya tashi kama ku wallahi sai Allah
ya ɗauke Yaran kab duk su Mutu ku dawo yanzu kuna son
haihuwar amma wallahi ba za ki taɓa haihuwa ba ke
da haihuwa sai dai a Lahira idan ana Yi, Hakan ya taɓa faruwa da wata Mijin ta ya ce ta yi Planning ta ce
Wallahi ba za ta yi ba ya buga ya Rawa ta ki, ta yi tambaya aka ba ta shawara
kada ta yi wallahi haka ta qi yin Family planning nan, sauran Ƙishiyoyin suka yi, Kun
San me ya faru?
Wata Rana suka shirya Yaran su za su kai ziyara
zuwa wani garin, sai suka yi Hatsari Yaran kab suka mutu babu wadda ya tsira a
motar, waɗannan matan da suka yi
Family planning suka dawo suna Bukatar Yara ko da 1 ne babu Allah ya rike
haihuwar, ita wadda ta qi yin Family planning ɗin sai haihuwa ta ke Yi ta kira tana godiya ta ce lallai
ta ga illar family planning da Kuma iKon Allah, ta ce da ita ma ta yi Family
planning nan yaya za ta yi? toh kun ga irin abubuwan dole ne fa a matsayin ki
na Mace ki tsaya kiyi nazari akai sosai kafin ki aikata shi, Mazan wannan
Zamanin ba Yan Amana bane su ce kiyi ki dena haihuwar su je su Auro me haihuwa
kina ji kina gani tana haihuwa ke kuma babu.
3. Na uku, idan Kuma wata Kila Kina da Ciwo ne a
tare da ke, ko Kuma Shi yanada Ciwo a tare da shi ba a son a ɗauki ciwon, toh nan ma idan Shi ne mai Ciwon Za ki iya
Hana shi Kanki, Domin kada ya Raɓa miki Cuta,
Sa'annan rabuwa da shi shine ya fi Alkhairi fiye miki akan Zama da shi yana ɗauke da Ciwo, toh sai dai idan Zai tashi ya nemi Magani.
Idan ma kene mai Ciwon, toh Gaskiya rashin Gamsuwar ki a Wajen sa hakan zai iya
sa Ki raba Aure Domin Gujewa Sheɗan na Zina.
Dafatan Kin Fahimta Koh?
WALLAHU A'ALAMU.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku
kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
WALLAHU A'ALAM.
https://t.me/TambayaDaAnsa
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.