Citation: Sani, A-U. (2026, July 26). Bara da mabarata Hausawa: Duba ga dalilan samuwarta da illolinta. Maƙalar da aka gabatar lokacin bitar labaran Gasar Rubutun Gajerun Labaran Hausa Ta Arc. Ahmad Musa Dangiwa Literary Foundation 2026.
BARA DA MABARATA HAUSAWA: DUBA GA DALILAN SAMUWARTA DA
ILLOLINTA
Daga
Abu-Ubaida SANI,
Ph.D.
Department of
Languages and Cultures,
Federal University
Gusau, Zamfara, Nigeria
Email: abuubaidasani5@gmail.com | official@amsoshi.com
ORCID: https://orcid.org/0000-0001-6447-4334 | WhatsApp: +2348133529736
Maƙalar da aka gabatar lokacin bitar labaran da suka tsallaka mataki na biyu a Gasar Rubutun Gajerun Labaran Hausa Ta Arc. Ahmad Musa Dangiwa Literary Foundation 2026, ranar 26 ga watan Yuli, shekara 2026
1.0 Shimfiɗa
Lamarin bara wani abu ne da ya daɗe yana ci wa
Hausawa tuwo a ƙwarya. Masana da dama sun tafi kan
cewa, Hausawa suna daga cikin al’ummomin da suka fi kowace yawan mabarata a
duniya. Hausawa mabarata sun wuce yankunan ƙasar Hausa kawai. Tuni gararambar yawon baransu ya kewaya
ƙasashen Afirka, har ma da wasu ƙasashen nahiyoyin na daban. Wannan rubutu ya kawo bayani
game da:
a. Wasu daga cikin dalilai ko abubuwan da suke kai ga
samuwar mabarata
b. Wasu dalilan da suka sa aka kasa shawo kan matsalar
bara a tsakanin Hausawa
c. Wasu daga cikin illolin bara a ƙarƙashin rukunoni uku:
i. Illarta ga mabaratan kansu
ii. Illarta ga sauran al’ummar Hausawa
iii. Illarta a matakin duniya
2.0 Matsayin Bara a Musulunci
Duk da sau da dama akan fake a inuwar addinin Musulunci
domin ci gaba da bayar da kariya ga bara, lallai Musulunci ya yi togaciya game
da wannan ɗabi’a. Bai yarda da bara da roƙo ba, sai a ƙarƙashin yanayi na musamman da yake tilasta hakan. Domin
nuna ƙasƙanci da rashin dacewar bara, Manzon
Tsira (SAW) ya ce:
لَأَنْ
يَأْخُذَ أَحَدُكُمْ حَبْلَهُ، فَيَأْتِيَ بِحُزْمَةِ الحَطَبِ عَلَى ظَهْرِهِ،
فَيَبِيعَهَا، فَيَكُفَّ اللَّهُ بِهَا وَجْهَهُ خَيْرٌ لَهُ مِنْ أَنْ يَسْأَلَ
النَّاسَ أَعْطَوْهُ أَوْ مَنَعُوهُ.
La-an ya'khudha ahadukum hablahu, fa-ya'tiya bi-huzmati
al-hatabi 'ala dhahrihi, fa-yabi'aha, fa-yakuffa Allahu biha wajhahu khayrun
lahu min an yas'ala al-nasa a'tawhu aw mana'uhu.
Fassara
"Lalle ne, da wani daga cikinku zai ɗauki igiyarsa, sannan
ya zo da damin itace a bayansa, ya sayar da shi, Allah kuma Ya kare shi da shi
daga wulaƙanci, to wannan ne mafi alheri a gare shi daga yin roƙon mutane, ko da sun ba shi ko sun hana shi."
(A duba: Sahih al-Bukhari)
A taƙaice ke
nan, wanda yake yin itace, ya ɗoro a kansa ko a bayansa, sannan ya sayar domin
samun kuɗi – ya fi mabaraci ƙima da daraja a faɗin Annabin Rahama (SAW). Ya
jaddada cewa ko da mabaracin an ba shi abin da ya roƙa ko ba a ba shi ba.
A wani hadisin mai tsawatarwa, Annabi Muhammad (SAW) ya
ce:
مَنْ
سَأَلَ النَّاسَ أَمْوَالَهُمْ تَكَثُّرًا، فَإِنَّمَا يَسْأَلُ جَمْرًا،
فَلْيَسْتَقِلَّ أَوْ لِيَسْتَكْثِرْ.
Man sa'ala al-nasa amwalahum takaththuran, fa-innama
yas'alu jamran, fal-yastaqill aw li-yastakthir.
Fassara:
" Duk wanda ya roƙi mutane domin ya ƙara yawan dukiyarsa, to yana roƙon garwashi (na wuta), ya rage gare shi ya roƙi mai yawa ko kaɗan."
(A duba Sahih Muslim)
Lallai wannan babbar tsawatarwa ce! Kai tsaye ya nuna
yadda roƙo yake mummunan al’amari
(sai idan mai roƙon ya faɗo cikin rukunin mutanen da aka yarje musu.
A wani hadisin, Manzon Allah (SAW) ya bayyana mutane uku
a matsayin waɗanda su ne kaɗai aka
ba wa damar yin roƙo. Ya ce:
يَا
قَبِيصَةُ، إِنَّ الْمَسْأَلَةَ لا تَحِلُّ إِلاَّ لأَحَدِ ثَلاَثَةٍ: رَجُلٍ
تَحَمَّلَ حَمَالَةً فَحَلَّتْ لَهُ الْمَسْأَلَةُ... وَرَجُلٍ أَصَابَتْهُ
جَائِحَةٌ فَاجْتَاحَتْ مَالَهُ... وَرَجُلٍ أَصَابَتْهُ فَاقَةٌ حَتَّى يَقُومَ
ثَلاَثَةٌ مِنْ ذَوِي الْحِجَا مِنْ قَوْمِهِ... فَمَا سِوَاهُنَّ مِنَ
الْمَسْأَلَةِ يَا قَبِيصَةُ سُحْتٌ يَأْكُلُهَا صَاحِبُهَا سُحْتًا.
Ya Qabisa, inna al-mas'alata la tahillu illa li-ahadi
thalathatin: rajulin tahammala hamalatan fahallat lahu al-mas'ala... wa-rajulin
asabat-hu ja'ihatun fa-ijtahat malahu... wa-rajulin asabat-hu faqatun hatta
yaquma thalathatun min dhawi al-hija min qawmihi... fa-ma siwahunna min
al-mas'alati ya Qabisa suhtun ya'kuluha sahibuha suhta.
Fassara
"Ya Ƙabisa! Lalle roƙo bai halatta ba face ga ɗaya daga cikin mutane uku: Mutumin da ya ɗauki fansar wani
(wanda ake neman fansa a kansa) har roƙo ya halatta a gare shi... da kuma mutumin da wata masifa ta same shi, ta kwashe dukiyarsa... da kuma mutumin da tsananin talauci ya same shi har wasu mutane uku masu hankali daga cikin
al’ummarsa suka shaida hakan... to, duk abin da ya wuce wannan, daga roƙo, ya Ƙabisa, haramun ne ga mai yinsa, wanda ya ci shi to yana cin haramun ne."
(A duba: Sahih Muslim)
Lallai wannan tsawatarwa da ta fito daga bakin fiyayyen
halitta (SAW) ta isa mai jijjigawa. A wani hadisin makamancin wannan, Manzo
(SAW) ya yi gargaɗi da cewa:
مَا
يَزَالُ الرَّجُلُ يَسْأَلُ النَّاسَ حَتَّى يَأْتِيَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ لَيْسَ
فِي وَجْهِهِ مُزْعَةُ لَحْمٍ.
Ma yazalu al-rajulu yas'alu al-nasa hatta ya'tiya yawma
al-qiyamati laysa fi wajhihi muz'atu lahm.
Fasasra
"Mutum ba zai gushe yana roƙon mutane ba, har sai ya zo ranar alƙiyama babu nama a
fuskarsa."
(A duba Sahih al-Bukhari da Sahih Muslim)
Waɗannan
hadisai suna nuna cewa, lallai bara abar ƙyama ce, abar a guje mata ne.
3.0 Wasu Dalilan Bara
1. Maraici – Wasu
maraici ne silar faɗawarsu cikin bara. Hakan yana faruwa musamman kasancewar
‘yan’uwan mahaifansu sukan yi watsi da su bayan mutuwar mahaifin. Al’umma ta
zama ramin kura, daga ke sai ‘ya’yanki. Wani lokaci kuma hakan yakan zama tilas
sakamakon tsarin iyali na Hausawa. Uba zai iya haihuwar ‘ya’ya masu yawa ba
tare da wani tanadi ko tsari mai kyau na rayuwa ba. Idan ya rasu, su ma ‘yan
uwa abin ya yi musu yawa da za su iya ɗaukar waɗannan ‘ya’ya har su
riƙe su. Mu kwatanta talaka da ya rasu ya bar ‘ya’ya goma
sha biyar (15), ta yaya ‘yan’uwansa talakawa za su iya ɗaukar lalurarsu
cikin daɗin rai?
2. Talauci –
Zunzurutun baƙin talauci yakan jefa wasu mutane
cikin bara. Rashin madogarar dafawa da toshewar duk wata hanyar samu a rayuwa
takan sa su rungumi bara a matsayin hanya tilo ta dafa tudun na-tsira.
3. Murɗa Fassarar Hukunce-Hukuncen Addini – Akwai waɗanda suke dogaro da koyarwar addini da kwaɗaitarwar da addini
ya yi na taimakon mabuƙata wajen ɓugewa da bara.
4. Aure Da Haihuwa Barkatai – Hausawa da dama sun fi yarda da wani hadisin Bahaushe na
“bakin da Allah ya tsaga, ba ya hana shi abinci.” A bisa haka, za su iya auren
mata barkatai tare da haihuwar ‘ya’ya barkatai ba tare da sun taɓa tsayawa sun yi
nazari ko samar da wani tsari na makomar rayuwarsu da ta mata da ‘ya’yan ba.
Addinin Musulunci, addini ne mai tsari. Bai yarda da rayuwa ballagaza kara-zube
ba.
5. Rabuwar Iyaye – A wasu lokutan, rabuwar iyaye a gidan aure yakan jefa
‘ya’yan cikin wata rayuwa ta rashin tabbas. A ƙarshe dole su faɗa gararambar bara da yawon maula da
roƙo.
6. Almajirci – A shi karankansa, almajirci abu ne mai kyau. Hanya ce ta koyon karatun
addinin Musulunci, musamman abin da ya shafi ƙwarewa a karatun Alƙur’ani mai tsarki.
Sai dai kash! A yanzu almajirci ya yi kusan ɗaukar kinin ma’ana
da “bara.” Dalili kuwa shi ne, sau da dama akan ajiye manufar almajircin, sai a
ɓuge da bara
tsantsa.
Akan samu iyaye da suka tura ‘ya’yansu almajirci don
kawai su rabu da su, su huta da ɗawainiyarsu na ciyarwa da shayarwa da tufatarwa da samar
da muhalli. Ire-iren waɗannan yara akan kai su wurin almajirci ba tare da wani
guzuri ba. A ƙarshe za su ƙare a yawon barace-barace.
7. Son Rai – Akan samu son rai daga ɓangarori daban-daban da suke haifar da bara. Misali, wasu
sun san da hukuncin bara game da haramcinta, kuma ba su da lalurar da za ta
tilasta musu bara, duk da haka, sukan ɓuge da bara saboda son kai da son
rai. A ɓangare ɗaya kuwa, akwai waɗanda ba su da halin ƙara aure, amma suke yin hakan tare da ɗaukar bara a
matsayin mafita ga ‘ya’yan da suke tunkuɗowa duniya.
8. Gado – Bara
takan samu ta hanyar gado a wasu lokuta. Misali, ‘ya’yan wasu masu nakasa da
suka dogara da bara a matsayin hanyar rayuwa, sukan taso ba tare da sanin komai
ba a duniya face yawon bara. Tun daga kan farawa a matsayin ‘yan jagora ko ‘yan
rakiya, sannu a hankali har su ɗore a kan wannan hanya.
9. Safara – An samu rahotanni daban-daban na waɗanda suka tsinci kansu a
matsayin mabarata a dalilin safarar su da aka yi. Safarar za ta iya kasancewa
da saninsu ko kuma cikin yaudarar cewa za a kai su wani wurin da za su gudanar
da aikace-aikace na samun kuɗi.
10. Nakasa – Nakasa wani babban abu ne da wasu Hausawa suke dogaro da shi a matsayin
hujjar ɗaukar ƙoƙon bara. Da zarar mutum ya samu wata tawayar halitta, sai
ya yanke ƙauna ga duk wata ƙofar samu ko hanyar rayuwa face bara.
11. Barin Gida (sakamakon faɗa ko
wani dalili na daban) – Saɓani tsakanin ‘ya’ya
da iyaye da yake sa ‘ya’yan su bar gida yana iya sa ‘ya’yan su ƙare a matsayin mabarata. Wani lokaci kuma guje wa abin
kunya da aka aikata yana iya zama silar barin gidan.
12. Bakin Iyaye – Bakin iyaye mai alaƙa da tsinuwa ko
mugun fata yana iya tambaɗar da ‘ya’yan da aka yi wa bakin har su ƙare a matsayin mabarata.
13. Gudun Hijira – Gudun hijira wani babban lamari ne da yake samar da ƙaruwar tururuwar mabarata a kan tituna a yau. Garuruwan
da suke yankunan Zamfara da Katsina da Sakkwato, musamman waɗanda matsalolin
tsaro suka shafe su, manyan misalai ne na wannan lamari.
14. Camfe-Camfen Hausawa – Hausawa suna da wasu imane-imane da aka gina su a kan
camfe-camfe, waɗanda kuma suke haifar da bara da samuwar mabarata. Misali
daga ciki shi ne ‘yan biyu (tagwaye) da sauran mutane da suka kasance na
musamman a cikin al’umma. Akan tafi kan cewa masu halitta na musamman a cikin
al’umma za su fuskanci wata matsala a rayuwa idan ba su yi bara ba (tare da
cewar Allah ya halicce su a hakan ne domin su yi bara).
A ɗaya ɓangaren kuma, imanin da aka ɗora kan camfin yana
nuna cewa, kyara ko musgunawa ko rashin bayar da sadaka a ire-iren mutanen zai
iya haifar wa mutum matsala a rayuwa. Wannan ya sa idan mace ta haifi ‘yan
biyu, hakan yakan zame mata dalilin yin bara a gida. Za a iya tuna gidajen
Hausawa musamman a da inda masu ‘yan biyu suke zagayawa yawon bara da furucin:
Assalamu alaikum,
Maman ‘yan biyu na gaishe ku.
15. Mutuwar Zuciya Da Son Banza – Akan samu waɗanda zunzurutun mutuwar zuciya da kuma son banza suke sa
su ƙare da bara.
3.1 Wasu Dalilan Da Suka Sa Harkar Bara Ta Ƙi Ƙarewa a
Tsakanin Hausawa
1. Fahimtar baibai ga addini (son a bayar da sadaka da
kyauta)
Misali, Manzon Tsira (SAW) ya ce:
مَا
مِنْ يَوْمٍ يُصْبِحُ الْعِبَادُ فِيهِ إِلَّا مَلَكَانِ يَنْزِلَانِ فَيَقُولُ
أَحَدُهُمَا: اللَّهُمَّ أَعْطِ مُنْفِقًا خَلَفًا، وَيَقُولُ الْآخَرُ:
اللَّهُمَّ أَعْطِ مُمْسِكًا تَلَفًا
Mā min yawmin yuṣbiḥu al-'ibādu fīhi illā malakāni yanzilāni, fa-yaqūlu aḥaduhumā: Allāhumma a'ṭi munfiqan khalfā, wa-yaqūlu al-ākharu: Allāhumma a'ṭi mumsikan talafā.
Fassara
“Babu wata rana da mutane za su tashi face sai mala’iku
biyu sun sauko sannan ɗayansu yana
cewa, “Ya Allah, ka sakawa wanda yake bayarwa (sadaka),’ sannan ɗayan yana cewa
‘Ya Allah, ka tauye wa wanda yake tauye hannu (hana sadaka).’”
(A duba: Sahih
al-Bukhari, 1374 da Sahih Muslim, 1010)
2. Addinantar da bara (almajirci)
3. Raunin imani da ƙaranci ilimi ga
wasu iyaye
4. Raunin al’umma da halin ko-in-kula
5. Ƙarancin ilimin
addini da na boko
6. Son zuciya
7. Rashin hangen nesa ko halin ko-in-kula na shuwagabanni
8. Ɓoyayyun manufofi (ɗorewar talauci da ƙasƙanci...)
9. Rashin mayar da hankalin malaman addini kan lamarin
10. Ɗabi’ar ɗan’adam na son
hutu/banza
11. Naci Ko Maita – Wani lokaci tsabar naci ne da
maitar samun abin duniya ta hanyar ɓagas yake sa mabarata su doge kan wannan hanya. Game da
wannan ne Fasihi Haruna Aliyu Ningi yake cewa:
Kullum a cikin baƙar suttura,
Sanyi, zafi ya turken kara,
Kun kasa bari kamar mai dara,
An so a hana ku ya gagara,
....
(Haruna Aliyu Ningi: Jinjira)
A taƙaice dai, abin ya
kasance musu tamkar maita (addiction) irin na ‘yan caca (dara) waɗanda suke kasa
bari. Dalili kuwa shi ne, wasu sukan samu kuɗi har su tara
kadarori a harkar bara, amma tsantsar maita da addiction yakan hana su daina
yawon bara cikin ƙasƙanci. Game da haka ne ma Haruna Ningi yake cewa:
Ranar da na je garin Ɓaɓura,
Na sha managa a gun Shaɗira,
Ga ‘yar sandarta ta dogara,
Tana ce ta sayo baƙƙara,
Bayan babbar da tsamurmura,
Ga motocinta nan Vectra,
Ta sai fegi guda sha tara,
Ba ta daina bara ba attajira,
(Haruna Aliyu Ningi: Jinjira)
Wannan kuwa ba kambamar zulaƙe ba ce. Akwai mabarata da suke da kuɗi da kadarori, duk
da haka suke kasa barin yawon bara.
4.0 Wasu Illolin Bara
Za a iya kallon illolin bara ta manyan fuskoki guda uku
wato (i) illolin da suka shafi su mabaratan kansu, (ii) illolin da suka shafi
al’ummar da aka samu mabaratan daga cikinta, (iii) illolin da suka shafi sauran
al’ummu baki ɗaya.
4.1 Wasu
Illolin Bara Ga Mabarata
1. Ƙasƙanci – A
kullum mabarata sukan kasance cikin rayuwar ƙasƙanci. Rayuwa ce
wadda babu wanda zai so tsintar kansa a cikinta. Haka kuma, duk mai zuciyar ƙwarai zai so ganin waɗanda suke cikin
irin rayuwar sun fita daga ciki.
2. Cututtuka Masu Alaƙa Da Ƙazanta
– Akan samu mabarata da suke kwana da
kwanaki sanye da tufafi ɗaya. Haka kuma, sukan ɗauki kwanaki ba
tare da wanka ko tsaftace jiki ba. Wannan salon rayuwa ta ƙazanta tana gabatar da su ga yiwuwar kamuwa da cututtuka.
3. Cututtuka Masu Alaƙa Da Zama Ko Tsayuwa Ko Yanayin Duniya (Zafi Ko Sanyi Ko
Iska) - Wahaltacciyar rayuwa da
mabarata suke yi tana iya janyo musu cututtuka daban-daban. Wasu daga cikinsu
suna da alaƙa da yawan zama, ko yawan tsayuwa ko
kasancewa a cikin yanayin duniya da bai dace mutum ya yawaita a cikinsa ba.
Yana iya zama sanyi ko zafi ko iska ko hazo, da makamantansu.
4. Fuskantar Haɗari - Mabarata sukan fuskanci haɗurra daban-daban.
Akan samu waɗanda suke cin karo da haɗurran ababan hawa
saboda yawan kasancewarsu a kan hanya. Wasu kuwa ayyukan ta’addanci ko gungun ɓata-gari da suka
fito (ko wani yanayi da yake buƙatar gudu) yakan
ritsa da su, inda sukan samu raunuka.
5. Fuskantar Tsangwama – Ɗaya daga cikin fitattun ƙalubale da mabarata suke fuskanta shi ne tsangama. Ko da
ma dai, Ubangiji ne kawai ake tambayar sa kullum ba tare da ya gajiya ba. Bugu
da ƙari, wasu da suke ɓata wasu a cikin harkar bara ya sa
mutane da dama suke yi wa mabarata kuɗin goro. Wani lokaci kuwa mabaratan
sukan iske mutane ne a kan tsini (cikin wani ɓacin rai ko damuwar
rayuwa da ta sa ba sa son magana ko takuri). A irin wannan lokaci, wasu mutane
sukan juye fushinsu kai tsaye kan mabaratan ta hanyar kora da kyara da tsaki da
baƙar magana da sauransu.
6. Rashin Gata – Mabarata sukan bayyana a matsayin marasa gata a cikin
al’umma. Tun daga kan tufafinsu, har abinci da suke ci, da kuma uwa-uba yadda
kullum suke kan neman taimako a hannun mutane, duk sukan bayyana su a matsayin
marasa gata.
7. Rashin Gobe – La’akari da bincike da suka gabata game da lamarin bara,
ana iya cewa yawanci mabarata ba su da gobe. Ma’ana a nan ita ce, ba su da wani
babban buri da tsari na rayuwa mai kyau na gina kyakkyawar rayuwa a nan gaba.
Wannan yana da alaƙa da ƙarancin damarmaki da suke da shi da kuma taƙaitaccen tunani a dalilin rashin ilimi da ƙwarewa.
8. Jahilci – Mabarata masu yawa da ‘ya’yansu sukan kasance cikin ƙangin jahilci. Yawanci wannan yakan haɗa jahilci a ɓangaren karatun
addini da na boko. Hakan yana faruwa ne kasancewar iyayen ko dai ba su da kuɗin ɗaukar nauyin
makarantar su, ko kuma son kai da maita da naci (kamar yadda aka bayyana a
sama) ta sa ba za su iya fitar da kuɗi domin kai su makaranta ba. Yara kuwa da suka tsinci
kansu cikin harkar bara, takan ɗauke musu lokaci da daƙushe musu tunani inda suke saka burin samun kuɗi kawai ta wannan
hanya, ba tare da tunanin neman ilimi ba.
9. Rashin ‘Yanci – Za a iya ganin rashin ‘yanci da mabarata suke da shi idan
aka yi la’akari da yadda suke fuskantar cin zarafi a wani lokaci ba tare da sun
samu damar neman wani haƙƙi a
hukumance ba. Musgunawa da koran kare da ake yi musu misali ne na yadda suka yi
fatali da ‘yancinsu.
10. Rauni Da Yake Bayar Da Damar Sarrafa Su Domin Cimma
Wasu Muradai Marasa Kyau (Fasiƙanci,
Safarar Ƙwaya, Ta’addanci) – Ƙarancin ilimi da
kwaɗayin duniya da rashin madafa da taƙaitaccen tunani (da sauran dalilai masu alaƙa da waɗannan) sukan sa a yi saurin yaudarar wasu mabarata zuwa
aikata wasu ayyukan assha. Waɗannan sun haɗa da fasiƙanci da safarar ƙwayoyi da kuma manya da ƙananan laifuka, ciki har da ta’addanci. Game da haka ne
ma Haruna Aliyu Ningi yake cewa:
Wasu masu barar suna hamɓara,
Don har ƙwaya suke tsakura,
Wasu bayan sha suna saffara,
Wasu in ta ture ta cimma tura,
Kayan wasu ne suke zaftara,
To ka ga ko ba batun lalura.
(Haruna Aliyu Ningi: Jinjira)
11. Raunin Addini – Jahilci ta fuskar ilimin addini da rayuwa marar alƙibla takan sa a samu mabarata da ba su damu da addini ba.
Raunin addini a nan ya shafi wasa da bautar Ubangiji a fanni guda. A fanni ɗaya kuwa ya shafi
zuciya mai rauni da za ta iya munafurci da zalunci da sauran ayyuka na rashin
gaskiya.
12. Rashin More Rayuwa – Duk da Hausawa sukan ce “rashin sanin daɗin daɗi ma daɗi ne,” a bayyane
take mabarata da dama ba sa more rayuwa. Abubuwan da aka ayyana a matsayin
ababan more rayuwa duk sun gagari mabarata. Sun haɗa da ruwa mai
tsafta da wutar lantarki da muhalli da sutura da sauransu.
13. Barikanci Da Haihuwar Bariki – Yawon bara yana iya jefa mabarata barikanci. Misali, an
sha samun ƙananan yara da suka koma wanke-wanke
a gidajen karuwai da sauran wurare na assha. Sannu a hankali zama da maɗaukin kanwa yakan
sa su yi farin kai. Wasu mata kuwa sukan koma “muna bara muna karuwa.”
A ɓangare ɗaya kuwa, akan haifi ‘ya’ya a halin yawon bara. Ire-iren
waɗannan yara sukan taso cikin ƙasƙanci da rashin
makomar rayuwa. Sukan rasa gatan karatu ko duk wata hanyar more rayuwa. A
maimakon haka, za su taso ne kawai a matsayin ‘ya’yan bariki, ko ‘ya’yan
titi/kwalta.
4.2 Wasu
Illolin Bara Ga Al’umma
1. Faɗuwar daraja a idon duniya
2. Akan samu rashin samun wasu damarmaki, ciki har da na
masu yawon buɗe ido da masu saka hannayen jari. Hakan yakan faru ne
sakamakon tsoron ta’addanci da cututtuka da kuma kuɗin goro da ake yi
wa al’ummar a matsayin marar alƙibla.
3. Akan samu barazanar raguwar muradin taimakon mabuƙata. Wannan yana faruwa ne a dalilin maƙaryata da masu son rai da suka yi yawa da har ake kasa
gane na haƙiƙa. An saba tashi a masallatai a yi ƙarya da sunan wani iftila’i ne ya faɗa wa mutum – don
dai kawai ya cimma manufarsa ta bara. Hakan yakan faru a tashoshin mota da
sauran wuraren da al’umma suke taruwa.
4. Akwai yiwuwar fuskantar fushin Ubangiji kasancewar
al’umma tana iya kai gacin gaza taimakon waɗanda addini ya ƙarfafa a taimake su. Babban misali a nan shi ne marayu.
5. Akwai ƙaruwar yiwuwar yaɗuwar ƙanana da manyan laifuka. Akan samu waɗanda daga bara suke
ɓugewa da sata. Wasu
kuwa akan yaudare su ne ko a ja hankalinsu ta hanyar kwaɗaitarwa domin ɗora su bisa wata
muguwar turba.
4.3 Wasu Illolin Bara a
Matakin Duniya
1. Samun ƙaruwar yaɗuwar
cutuka
2. Ci gaba da samun
bambancin rukunin al’umma mai faɗi
(social class)
3. Yiwuwar faɗaɗar
ta’addanci (su mutane ne da za a iya yaudara da kuɗi
cikin sauƙi)
4. Yiwuwar faɗaɗar
safarar miyagun ƙwayoyi
5. Yiwuwar faɗaɗar
safarar mutane
5.0 Naɗewa
Lamarin
bara a tsakanin Hausawa ya zama kurar gardi. Abu ne da yake buƙatar a mayar da hankali a kansa matuƙa domin ganin yadda za a shawo kansa.
Yana buƙar haɗa ƙarfi da ƙarfe
daga ɓangarorin
al’umma da shuwagabanni da ƙungiyoyi
da malaman addini. Wane ƙoƙari kake/kike/kuke yi domin ganin an taƙaita bara a tsakanin Hausawa?
Manazarta
Abubakar, Y. A. (1972). The
political and administrative implications of the rehabilitation of beggars.
University Press.
Bunguɗu, H. U. (2015). Nazarin waƙoƙin bara na ƙarni na ashirin da ɗaya a Zamfara [Doctoral dissertation,
Usmanu Danfodiyo University]. Department of Nigerian Languages, Usmanu
Danfodiyo University.
Bunguɗu, U. H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a kasar Hausa. Ahmadu Bello University Press
Limited.
Francis, O. O. (1972a). The
rehabilitation of beggars in Nigeria: National Council of Social Work in
Nigeria. University Press.
Francis, O. O. (1972b). Sociological
aspects of the rehabilitation of beggars. University Press.
Karofi, D. S. (1980). Mabarata:
Tasirinsu da gudummuwarsu a kan adabin Hausa [Bachelor's
thesis, Ahmadu Bello University]. Department of Nigerian and African Languages,
Ahmadu Bello University.
Lere, S. A. (2022). Almajirci: Ya kare zai kashe
ragon layya? Amsoshi. https://www.amsoshi.com/2022/11/almajirci-ya-kare-zai-kashe-ragon-layya.html
Mahmudu, A. (1978). Muhimmancin maroƙan baka a ƙasar Hausa.
In Studies in Hausa language,
literature and culture: The First International Conference 7th–10th July, 1978. Bayero University.
Maimuna, L., et al. (2000). Problem
of begging in Islam [B.Ed project, Ahmadu Bello University].
Department of Islamic Studies, Ahmadu Bello University.
Malumfashi, A. I. (1997). Matsalar barace-barace a
Nijeriya. Dandalin Hikima 2, Makon Hausa. Zakara Press and
Publishers.
Muhammad, S. S. (2021, February 7). Tasirin Arc.
Muhammadu Namadi Sambo a tsarin karatun tsangaya a jihar Kaduna. Amsoshi.
https://www.amsoshi.com/2021/02/tasirin-arc-muhammadu-namadi-sambo.html
Mujaheed, A. (2017). Adabin bara: Nazarin waƙoƙin Salisu Sa'in Makafin Zazzau [Master's thesis, Ahmadu Bello University]. Department of
African Languages and Cultures, Ahmadu Bello University.
Odumosu, O. I. (1971). Legal
aspects of rehabilitation of beggars. University Press.
Sarkin Gulbi, A. (2007). Nazari
a kan al'adar bara a ƙasar Sakkwato [Master's thesis, Usmanu
Danfodiyo University]. Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo
University.
Ummar, M. H. (2002). Nazari a kan waƙoƙin bara na yau da illolinsu [Bachelor's thesis, Ahmadu Bello University]. Department of Nigerian and African Languages, Ahmadu Bello University.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.