Ticker

6/recent/ticker-posts

Wanka Domin Fitar Maniyyi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wanda ya kalla ko ya shafi jikin matarsa da sha’awa amma bai sadu da ita ba, sai kuma har ya yi maniyi domin hakan, to wai wanka zai yi ko kuwa alwala ta isa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.

A tsarin shari'ar Musulunci, duk lokacin da mutum ya fitar da maniyyi sakamakon motsuwar sha'awa—kamar ta hanyar kallo ko shafa—wankan tsarki (wankan janaba) ya wajaba a kansa, ko da bai sadu da matar tasa ba. Alwala ba za ta maye gurbin wanka ba a wannan yanayin. Idan kuma abin da ya fita ba maniyyi ba ne, sai dai ruwa siriri mai danko da ake kira maziyyi (wanda ke fita a farkon motsuwar sha'awa kafin fitar maniyyi), to wanka bai wajaba ba. Abin da zai yi kawai shi ne ya wanke gabansa da tsabta, sannan ya yi alwala don tsaftace jikinsa da kuma shirya wa sallah.

Malamai dai abin da suka ce shi ne: Janaba tana samuwa ga mutum ne idan ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan ya auku:

1. Fitar maniyyi daga gare shi ta hanyar babbar sha’awar jima’i ko a barci ta hanyar mafarki, ko kuma a farke ta hanyar tunani ko kallo ko shafan jiki ko wasanni.

2. Ɓacewar kan alauran namiji (hashafa) a cikin na-mace kamar a lokacin saduwa ko

wasan banza, ko da kuwa ba su yi maniyyi ba.

3. Fitar maniyyi ta hanyar yin wasa da al’aura ko ta amfani da wani inji ko wata na’ura da turawa suka ƙera musamman domin haka, kamar budurwar roba.

Duk wanda hakan ya same shi kuwa wankan janaba ne ya wajaba a kansa amma ba alwala ba, saboda maganar Ubangiji Tabaaraka Wa Ta’aala cewa:

وَإِن كُنتُمۡ جُنُبࣰا فَٱطَّهَّرُوا۟ۚ

Kuma idan kun kasance masu janaba, to sai ku yi wanka. (Surah Al-Maa’idah: 6)

Sannan kuma Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya bayar da fatawa ga wanda yake yawaita wanka saboda fitar maziyyi cewa:

« لاَ تَفْعَلْ ، إِذَا رَأَيْتَ الْمَذْىَ فَاغْسِلْ ذَكَرَكَ وَتَوَضَّأْ وُضُوءَكَ لِلصَّلاَةِ ، فَإِذَا فَضَخْتَ الْمَاءَ فَاغْتَسِلْ »

Kar ka yi haka. Idan dai ka ga maziyyi to sai ka wanke al’aurarka kuma ka yi alwala irin alwalarka ta sallah. Idan kuma ka fitar da maniyyi mai tunkuɗowa da ƙarfi, to sai ka yi wanka. (Sahih Abi-Daawud: 206).

Allaah ya ƙara mana fahimta.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

WALLAHU A'ALAM.

https://t.me/TambayaDaAnsa

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments