Ticker

6/recent/ticker-posts

Tattaunawa Game Da Makomar Nazarin Hausa Da Kungiyar Manazarta Hausa a Zauren amsoshi.com

Dr. Abdurrahman Aliyu

A matsayina na ɗaya daga cikin masu kishin bunƙasa harshen Hausa, ina ganin lokaci ya yi da za mu ƙara mayar da hankali kan taskance ilimi da ayyukan Hausa a duniyar intanet. Kamar yadda Dr. Abu-Ubaida Sani ya sha jaddadawa, akwai buƙatar mu tashi tsaye wajen adana ayyukanmu ta hanyar amfani da fasahohin zamani domin su kasance cikin sauƙin samu ga masu bincike da al'ummar duniya.

A wannan gaɓa, ina kira ga ƙungiyar masana Hausa, (Hausa Scholars Association)  idan tana raye da  ta ƙara zage damtse wajen shirya tarurruka na ilimi akai-akai, samar da mujallu na yanar gizo (online journals), da kuma wasu dandamali na kimiyya da za su taimaka wajen adanawa da yaɗa bincike da rubuce-rubucen Hausa.

Idan kuwa  babu wannan ƙungiya, ina ganin lokaci ya yi da masana da masu ruwa da tsaki su haɗa kai su kafa ta.

Har ila yau, ya kamata mu yi ƙoƙarin kawar da son rai da bambance-bambancen da ke tsakaninmu, domin ci gaban harshe ya fi muhimmanci fiye da bambancin ra'ayi ko alaƙa. Muna ganin yadda ƙungiyoyin malaman Turanci da Faransanci da Kimiyyar Harshe ke gudanar da manyan tarurruka da bita da wallafe-wallafen kimiyya a kowace shekara, waɗanda ke ƙara bunƙasa fannoninsu.

Har ila yau, zai kasance abin alfahari idan masana harshen Hausa suka samar da irin wannan tsari domin bunƙasar harshen Hausa.

Haɗin kai da amfani da fasahar zamani da inganta bincike su ne manyan ginshiƙan da za su tabbatar da cewa harshen Hausa ya ci gaba da bunƙasa tare da samun matsayi mai girma a fagen ilimi na duniya.

Dr. Abu-Ubaida Sani

Lallai wannan batu ne mai muhimmanci. Ƙungiya tana da matuƙar muhimmanci domin hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka - sannan hannu da yawa maganin ƙazamar miya. Yayin da aka zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, a nan ne za a iya magana da babbar muryar da amonta zai kai kunnuwan da suka kamata.

Duk wasu matsaloli da suke gewaye da karatu da nazarin wannan harshe a yanzu tattauna shi kawai ake yi a matsayin ƙorafi mara wani tasiri. Ba shi da tasirin ne koma domin babu murya mai ƙarfi da za ta iya yin magana a saurare ta.

Jama'a ƙarfi ne. Taro ƙima ce. Idan an yi magana da murya ɗaya, dole muryar manazarta Hausa ta girgiza wuraren da ya kamata ta girgiza.

Prof. Abdulrahman Ado

Salamu Alaikum. Zance da Dr. Abdulrahaman ya yi, na juya akalar nazarin Hausa zuwa tubar zamani, gaskiya ne. Halayyar riqau ba tamu ba CE, a wannan zamani. To, amma, ka kuwa san wad'anda ba su koyi Hausar da zummar ciyar da ita gaba ba, suna da yawa? Wasu fa, ba su son shiga zaman. Ba su son komawa zuwa koyo da koyar  da Hausa ta amfani da Na'urorin Sadarwa na Zamani. Ba su gudanar da bincike irin na zamani. Kullum, in an yi  abin da ba su sani ba, sai yi ta fad'a da shi. Ba za su koyar ba, ba za su bari a koyar ba. Dole fa, sai an tashi tsaye, an yak'e su, an kauce masu, an shiga zamani k'arfi da yaji, sannan za iya samun cigaban Hausa. Allah Ya ba matasanmu na Hausa sa'a su cigar da Mazarin Hausa gaba, ya dace da zamani.

Dr. Jibril Yusuf

Tabbas! Dr @Dr. Abdulrahman Aliyu Katsina Gasa ka yi sara a kan gaɓa. Kuma dukkan batutuwa da ka kawo gaskiya ne.

Babbar matsalar da ta sanya nazarin Hausa a gaba take kuma neman ganin bayansa ita ce rashin haɗin kai. Kowa yana ganin shi ne isasshe wane bai isa ba. In da a ce za a kawar ninanci da son rai, ina da tabbacin al'amura za su daidaita.

Hanya ta farko da ya kamata a bi don dawo da ƙimar nazarin Hausa ita ce a farfaɗo da wannan ƙungiyar ta masana Hausa (Hausa Scholars Association) domin sai da haɗin kai ake samun muryar da za a iya magana har a saurara a hukumance.

Idan kuma ba zai yiwu a farfaɗo da wancan ƙungiyar ba, to me zai hana a kafa wata wadda za ta jagoranci dukkan al'amuran da suka shafi harshen a ilmance?

Ya kamata mu sani cewa, dukkan sauran ƙungiyoyi na manazarta wasu harsuna ba fa sun fi mu ido da kwalli ba ne al'amuransu suke tafiya daidai tare da bunƙasa.

Haka kuma, idan muka yi sakaci bakin wuta ya mutu a hannunmu, wallahi tarihi zai rubuta mu da mummunan shaida, kuma magabata da suka yi fafutuka har nazarin Hausa ya kawo yau ba za su yafe mana ba.

Wajibi ne mu rungumi sauye-sauyen zamani a cikin nazarin Hausa. Don ba gargajiya kaɗai ke da amfani a wajen mu ba har da zamani da ci gaban da ya samar. Abin kunya ne gare mu ɗaliban Hausa a samu ba mu iya sarrafa fasahar AI yadda ya kamata ba. Da yawanmu ko amfani da kwamfiyuta ba mu iya ba. Ba mu iya kutsawa cikin intanet mu nemo bayanai na ilimi waɗanda suka yi ƙaranci a daskararrun littattafai. Balle kuma mu mu yi tunanin ɗora ayyukanmu a intanet don duniya ta amfana.

Ya kamata mu farka, mu yi ɗamara don ganin mun kawo sauyi mai ma'ana a cikin wannan muhimmin fage.

Prof. Abdulrahman Ado

Dr. Jibril, na ji dad'in zancenka. Bari ma ta zancen d'aliban Hausa, ka kuwa san akwai malaman Hausa na zamanin nan, wad'anda ba su ma iya sarrafa Na'urorin Sadarwa na Zamani ba, a wajen gudanar da binciken zamani na Hausa ba? Su manyan malamanmu, babu laifi a gare su, don zamaninsu, ya wuce, na ''Analogue'' kuma  sun yi k'ok'ari irin nasu. Amma, a zamanin yanzu na '' Digital,'' a ce, malaman Hausa na Sakandare da Kwalejoji da Jami' o'i, ba su san Ilimin amfani da Na'urorin Sadarwa na Zamani ba? Kai! Da sake! Ki kuma, su hana a yi amfani da su domin koyar da d'aliban Hausa, darurra da su. Yanzu haka, ana can Ikko( Legas) ana ta aikin d'ura bayanai na harsunan Nijeriya a cikin Na'urorin Zamani ba Mutum-Mutumin Giri, amma, babu Hausawa. Babu mai tallafa wa d'alilan da suka ja '' training'' d'in, don  haka duk sun gudo. Bahaushe, mai ban haushi. Allah Ya taimaka mana.

Tattaunawa Game Da Makomar Nazarin Hausa Da Kungiyar Manazarta Hausa a Zauren amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments