Ticker

6/recent/ticker-posts

Almajirci: Ya Kare Zai Kashe Ragon Layya?

Shehu Sani Lere

Nigerian Language And Linguistics Kaduna State University
08062798146

Kalmar 'Almajiri' balarabiyar kalma ce da aka kankareta daga kalmar 'ALMUHAJIRUN', wato masu yin hijira don Allah. A jikinta aka kankari Kalmar 'Alhaji', wato, Wanda ya tafi aikin Hajj domin Allah.

Kamar yadda Harshen Hausa ya zama Hankaka " mai da Dan wani na ka", haka ya hausantar da Kalmar larabcin zuwa 'Almajiri' don samun saukin furtawa.

Tarihin Hausawa bayan zuwan addinin Islama, ba zai kammalu ba, sai an kawo maganar almajirci domin kuwa ta zama wani bangare na Adabin Malam Bahaushe.

Tarihin samuwarsa a kasar Hausa, ba zai gaza shekaru 700 ba bisa kaddarawa. Kaga kenan shi ya fi asali da rigaye akan takwararsa ilimin Boko da bai wuce shekaru 150 ba kacal.

Tarihin gwarazan wannan kasa, na dauke da tasirin waccan nau'in karantarwa ta tsangaya, an kuma ga irin yadda kwalliya ta biya kudin sabulu a cikin rayuwarsu ta fuskar nagarta idan aka kwatanta su sa wadanda suka yi boko zalla.

SHIN  ALMAJIRCI NA NAN YADDA YAKE A BAYA KO YA GURBATA?

ALMAJIRCI A DA:

Cuɗanyar Bahaushe da Larabawa a Karnoni Masu yawa a baya, ta samarda 'yan sauye-sauye da dama a gudanar rayuwarsa. Karbar addinin Islama ga Bahaushe ita ta sanya shi bukatar Neman ilimin sa. Karancin Malamai a kusa, ita ta tilasta masa barin Gari zuwa wani don yin karatun Al'kur'ani da littattafai da nufin dawowa da cigaba da karantar da shi ga wasu.

Hadisai da suke nuni da daraja da kuma dinbin lada Ga Wanda ya fita ya bar garinsu da nufin Neman ilimi su ke karfafa gwiwwar duk wani mai sha'awar yin hakan.

A wancan lokaci, mutum kan riki guzuri don zuwa garin da zai yi karatu, idan ya je, karatun ne aikinsa kawai, baya shagaltuwa da Neman Kudi ko wata Sana'a, don haka, ya kan yi barar abinci ne kawai don ya ci ya samu kuzarin yin karatu.

Galibi tsangayar malamai kan kasance a dan nesa da gari don gujewa hayaniyar da zata dauke wa almajirai hankali. Saboda haka, Baka ganin Almajiri a cikin gari sai in wata bukatuwa ta shigo da shi. Kullum yana makaranta yana karatu, da hantsi kuma ya tafi daji don yin itacen makaranta. Ta wannan kyakkyawan tsari, an kyankyashe malamai da Alarammomi da Gangaran Masu yawan da babu misali. Kuma galibunsu kan taso da tarbiyyan hakuri da kadan, juriyar yunwa  da kuma ' ZUHUDU' ( gudun duniya).

Tarihi ya taskace mana labaran wasu daga cikin su da kololuwar darajar walittaka da suka kai, saboda ilimi da suke da shi da tsoron Allah. Sau da yawa, a wurinsu ake samun mafita a yayin  da kasa ta Fada yanayi maras dadi ( kamar wadda muke ciki a yanzu) wajen yin addu'ar samun sauki, akan kuma dace idan sun yi.

Hakika tsari ne mai tsafta a waccan lokaci da ya samu kulawa daga salon tsarin mulkin sarakunan musulunci, ana gudanar da shi bisa turbar da aka dora shi wadda ya dace da Addini,al'ada,yanayin al'umma da muhallinsu.

Tsari ne da ya burge hatta Turawan mulkin mallaka duk da kasancewarsa kishiyar abin da suka zo da shi, suke yi masa kuma kallon hadari ga  ɗorewar na su matukar yaci gaba a bisa kyakkyawar tsarin  da suka same shi.

 ALMAJIRCI A YAU DA TASIRIN TURAWAN YAMMA:

Ingantuwar tsarin koyo da koyarwa ( na tsangaya) a waccan lokaci, na da nasaba ne da tsarin mulki na Sarakunan Addini da galibansu malamai ne da suka kurba daga irin tsarin makarantar, a yawan lokuta ma su ne malaman da ake daukar karatun daga wajensu. Su ne Sarakuna, su ne Malamai kuma su ne Alkalai da kan zartar da hukunci shi yasa ake kiransu da MASU WUƘAR YANKA.

Zuwan Bature da karbe ragamar jagoranci daga Sarakuna Malamai, shi ne farkon tubalin rugujewar tsarin Karatun almajirci. Malamai suka mai da hanyar ta neman girma da tara dukiya ta hanyar bautar da almajiran. Daliban suka saki sha'awar karatun, suka shagaltu da neman tara dukiya ( suka zabi tsanantar Neman lakani a maimakon karatu don zama malaman tsubbu ko duba) da jin dadin duniya, tsarin ya rasa mai taimakonsa dole ya zama mai zaman Kansa.

Tsawon lokaci da aka diba da tsarin ya zama garke babu makiyayi, shi ya ba ma'abotansa damar juya shi gwargwadon bukata. Suka rika shiga kauyuka su na yekuwar magidanta su taimaka su basu 'ya'ya su tafi dasu don su karantar da su. Sai hakan yayi tasiri ga Hausawan da suke da al'adar auren mata fiye da daya, da kuma yawan haihuwa barkatai bisa imani da ce wa, " Bakin da Allah ya tsaga, baya hana shi abinci". Don haka, kwasan 'ya'ya a tafi da su wasu wurare Masu nisa da nufin karatu ta karbu, ko da dai dan  bai samu karatu ba, ya samo Kudi.

Talauci da rashin sanin kimar zumunci shi ma na taka muhimmiyar rawa a wannan sashi, domin a wasu lokutan 'ya'ya marayu da 'yan uwa suka kasa rikewa aka fi turawa almajirancin domin duniya ta ci da su. Ba karatun ne aka fi ba muhimmanci ba, a a, a dai tafi da su don rage wahalhalun dawainiya.

Wasu manazarta na zargin tsarin almajirci na yanzu, ya kara Samar da kangararru da Masu aikata laifuka, ba don komai ba, sai don rasa kyakkywar tsarin da ya samu a baya.

MENENE MAFITA?

Idan muka duba dadewar zamani da tsarin almajiranci yayi a Kasar Hausa, muka kuma duba irin gudummawar da fannin ya bayar, har ya zama tarihin Bahaushe ba zai cika ba sai da shi, to kuwa ba zai yiwu a hana shi kwata-kwata ba.

Hakkin gwamnati ne kare al'umma da taskace tarihin ta da kyawawan al'adunta, yin hakan shi ne kimar Kasa da al'ummar da ke cikin kasar shi yake nuna dadewar al'ummar da irin hikimominta da azancinta da kyawawan al'adunta. Kashe shi, kashe al'umma ne da tarihinta kurmus!.

Karatun Boko  da ake kokarin ganin wanzuwarsa, bakon al'amari ne da aka dankarawa al'ummar Hausawa bisa tilas ba don suna so ba, shi yasa ma suke yi masa kirari da " BOKOKO A WUTA". Tsari ne da har yanzu bai cika shekaru dari da hamsin ba (150), alhali karatun tsangaya ya kai kimanin shekaru dari shida zuwa bakwai (6-7), to idan kuwa za ayi adalci, " KARE BA ZAI KASHE RAGON LAYYA BA".

Abin da ya kamata a yi shi ne, inganta tsarin, da dawo masa da martabar da ya rasa a sanadiyyar rashin tsari. Gwamnati ta Samarda duk abubuwan bukata da suka kamata don dorewarsa cikin kyawun tsari. Ana iya dorawa daga inda tsohon shugaban kasa Ebele Jonathan yayi na kokarin giggina makarantun tsangayoyi Masu yawan gaske a fadin wannan kasa. A kuma samarda isassun malamai da kayan koyo da koyarwa na Alkur'ani da kuma ba boko don samun nagartacciyar al'ummar da zata zama shugaba a nan gaba.

Kinyin haka, na nuna rashin damuwar gwamnati ne a kan natsalolin da ya shafi al'ummarta, wato bata damu ba, ko al'ummar ta zama nagartacciya ko ta zama ta banza.

 Kuma daukar wani mataki mai gauni a kan wannan, ba zai taba biyan bukata ba, don haka, a bi hanyar da zata bulle ba mai tukewa ba. Idan kunne yaji, gangan jiki ya tsira, Allah ya fisshemu aikin da-na-sani.

Almajiranci

Post a Comment

0 Comments