Ticker

6/recent/ticker-posts

Salon Siffantawa a Cikin Wakokin Addu’a Na Hausa

Article Citation: Hamza A. Ainu (2018). Salon Siffantawa a cikin Waƙoƙin Addu'a na Hausa. DEGEL: The Journal of the Faculty of Arts and Islamic Studies, Vol. 16. ISSN 0794-9316

SALON SIFFANTAWA A CIKIN WAƘOƘIN ADDU’A NA HAUSA

Na

Hamza A. Ainu, PhD

Cibiyar Nazarin Hausa

Usman Ɗanfodiyo University, Sokoto

ainuhamza@gmail.com

Tsakure

Kamar dai sauran takwarorinsu rubutattun waƙoƙin Hausa, su ma rubutattun waƙoƙin addu’a na Hausa ana iya samun kusan kowane irin salon sarrafa harshe na waƙa a cikinsu. Daga cikin fitattun salailai da aka fi samu cikin waƙoƙin Hausa akwai: Salon buɗa waƙa da rufe ta da amfani da salon aron kalmomi da sarrafa nassoshin Alƙur’ani mai girma da na Hadisan Manzon (S.A.W) akwai kuma amfani da sunayen Allah kai tsaye ko fassarar ma’anarsu. Ga kuma salon siffantawa wanda yake ƙunshe da salailai daban-daban kamar na zayyana da kinaya da kamance da jinsarwa da dai sauarnsu. Wannan takarda ƙudirinta ne ta fito da bayani kan yadda salon siffantawa ya yi kaka-gida a cikin rubutattun waƙoƙin addu’a na Hausa.

Gabatarwa

Manazarta kan rubutattun waƙoƙin Hausa sun yi ayyuka sosai ta fuskar taskace su da bincike-bincike kan jigoginsu da salonsu da tsarinsu da samuwarsu. Ayyuka irin na Hiskett (1975) da Ɗalhatu (1977) da Sa’id (1978/2002/ 2016) da Yahya, (1987/1997/2001/2016) da Birniwa (1981/1987) da Tudu (2001) da Dunfawa (2002) da Ainu (2007) da Usman (2008) da Omar, (2010), misali ne kaɗan daga waɗannan masana, kuma gaba ɗayansu sun yi ittifaƙi cewa tasiri rubutattun waƙoƙin Larabci shi ne tushe ga samuwar rubutattun waƙoƙin Hausa.

Ma’anar Salo

Ƙamusun Hausa (2006:385), ya bayyana ma’anar salo da cewa:

 " Ya yi ko sauyi ko lawni ko fice"

Amma a fannin nazarin adabin Hausa zan taƙaita bayani na ra’ayoyin wasu masana adabin Hausa biyu kacal, dangane da ma’anar salo a taƙaice. A binciken da babban malamin nan masanin Hausa Shaihin Malami Abdulƙadir Ɗangambo ya gudanar game da salo (2007:37-42) ya ce:

"Za a iya fassara salo kamar haka:

i. Salo wani abu ne da ya ƙunshi zaɓi a cikin rubutu ko furuci

ii. Salo wani ƙari ne na daraja a cikin rubutu ko furuci, wanda ba lalle ne a same shi cikin kowane rubutu ba.

iii. Salo ya shafi kauce wa wata daidaicciyar ƙa’ida.

iv. Salo harshen wani mutum ne.

 A tasa gudummuwar game da bayyana ma’anar salon Shaihin malami Yahya, (2016:30) ya ce ana iya a ce:

"Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda mawaƙi ya bi domin ya isar da saƙon da yake son ya isar. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon waƙar zai isa ga mai saurare ko karatun waƙa"

 A waɗannan taƙaitattun bayanai na masana adabin Hausa. Za a iya fahimtar cewa lalle salo babban ginshiƙi ne da yake tallabe da waƙa a lokacin da ake tsara ta da aiwatar da ita har ma ga nazarinta da mai sauraron ta. Idan aka keɓe nazarin salon siffantawa, wannan salon yana a matsayin gishiri a cikin ƙulla waƙa. Mai yiwuwa ne wannan ne ya sa Shaihin malami Ɗangambo ya raba salon siffantawa har zuwa kashi biyu.

1. Gajeriyar siffantawa

2. Doguwar siffantawa

Wannan ya bayyana irin muhimmancin salon siffantawa wanda Shaihin malami ya sifanta shi da cewa:

"Siffantawa, kamar kamantawa, kwatantawa ce, sai dai ita kwatance ne na kai tsaye, akan ɗauki darajar wani abu ko halayyarsu a ɗora wa wani kai tsaye, wato a ce, "kaza" ko kaza kaza ne. shi ne "kaza" (Ɗangambo 1987:43-44)"

 Shi ma a nasa ƙarin hasken game da siffantawa Shaihin malami A.B. Yahya ya kamanta wannan salo da wata irin 'baza' ce wadda da wuya mawaƙi zai iya shirya waƙa ba tare da amfani da nau’o’inta ba. Ga dai sharhi da Shaihin malami ya yi a taƙaice:

"Dubi abin da Bahaushe ke nufi da 'baza' a cikin kalaminsa. 'Da bazaar wane yake rawa; to kamar haka ne salon siffantawa yake ga mawaƙa. shi ne bazarsu. Duk wata bugewwa, duk wata iyawa ta isar da saƙo a cikin waƙa, duk wata fasaha a cikin waƙa, ta fi kamala idan salon siffantawa ya taka rawa a cikin waƙa (Yahya, 2016:80)".

Waɗannan ra’ayoyin masana wata manuniya ce wanda ta wadatar ga mai nazarin waƙa ya san matsayin salon siffantawa a cikin waƙoƙin Hausa a gaba ɗaya da kuma rubutattunsu a keɓance.

Salon Siffantawa

Salon siffantawa muhimmi ne kuma babba a cikin nazarin waƙa, wanda ya ƙunshi nau’o’in salo daban-daban.

 Da yake na lura waƙoƙin addu’a sun ƙunshi nau’o’in siffantawa daban-daban zan fi ba da ƙarfi ga ma’ana wadda ta ayyana salon da cewa faffaɗan salo ne, saboda in tattara hankali da bayani wuri guda. Nau’o’in salon siffantawa da ake iya samu a cikin waƙoƙin addu’a suna da yawa. Daga ciki akwai zayyana da alamtawa da kinaya da kamance da kuma jinsarwa.

Salon Zayyana

Salon zayyana, a faɗar Yahya (1997, 2001 da 2002) shi ne wanda Ɗangambo (1981), ya kira da sunan doguwar siffantawa. Wannan salon na nufin mawaƙi ya yi amfani da kalmomi don bayyana wani abu, har ya kasance hoton wannan abin da yake bayani ya zo a zuciyar mai sauraro, ya ga kamar ga abin nan yana ganin yadda ya faru. Wannan salo kan zo cikin baiti ko baitoci da dama. Irin wannan salo za mu iya fahimtarsa kai tsaye a cikin waƙoƙin addu’a, saboda irin mamayar da ya yi a cikin waƙoƙin. Misali:

Ga ni yau ban da wurin zama bale kwanci na kai can,

In na ga inwa nis so shigat ta in ga ƙaya ɗai an nan,

In na biɗo mai takasi a iske kura ta ɗai an nan,

Ban da abokin zama gabas ga tasha ni an nan,

Ga ni shawagi ɗai nikai waɗansu sunai min tsawa.

Dubi kuma wadannan baitocin da ke tafe:

Na ji tsoron zangon da nic ciyo da ƙafata ni ɗai,

 Ban da mai min jagora ka sani Allah sai kai ɗai,

Ga shi duk ɗan guzurin da ag garan daji ya ɓassai,

Wani abu wanda ag garan shi ko na saisai,

Ga ni daji nike Rahimi tsare ni ga hyaɗen kaiwa.

Ga shi salkata ba ruwa cikinta ƙishi ya kam min,

Ba gida kusa ba rijiya bale wani mai ɗebo min,

Babu sauran ƙarfi gare ni don gajiya ta kam min,

Babu inwa kusa ba wurin shiga yunwa ta zo min,

Rabbu sauƙaƙe sauran wuyar da ag gaba yo min baiwa.

Ga duwatsu manya ga godabe an ce sai na bi,

Hawansu zan yi ko dole tunda nan hanyan nan tab bi,

Can samansu akwai sarƙaƙi zama na tcinkai gumbi,

Can ƙasan nan kuma gangaren akwai wani babban gulbi,

Wagga hanya sai sannu ban da damar yin gaugawa

(Umaru Sanda/Alƙali Haliru Wurno: Allah Maishin Bawa).

Waɗannan baitoci da suka gabata ko ba faɗi ba, zuciyar maikaratu ko mai sauraron wannan waƙar ta ƙiƙiro masa yanayi da matsanaciyar wahalar da waɗannan mawaƙi yake ciki ta hanyar amfani da salon zayyana.

Haka kuma akwai wata waƙa mai irin wannan salo wadda ke cewa:

Masu kokuwa duka sun shirya,

Ga shi har fagen yi an shaya,

Ga ni ban da karfo ko laya,

Ga shi ko ina son kayaswa.

Wasu sun yi gayya can su ko,

Sun yi taulahi an amsa ko,

Ni fa ga ni nan cirko-cirko,

Agajinka ɗai nika dubowa.

Ga su wane can wai sun kimtsa,

‘Yan farofaganda sun watsa,

Duk cikin ƙasashe sun kutsa,

Wai batunsu ɗai suka gyarawa

(Ummaru Wazirin Gwandu: “Zaɓaɓɓiya).

Waɗannan baitoci da suka gabata suna zayyana muna yadda tura ta kai bango ga yaƙin neman zaɓen kujerar ɗan majalisar dattawa ta Ikko, a shekara ta 1954, wadda wannan mawaƙin ke son a zaɓe shi wakilin Gwandu da Yawuri a cikin jihar Kebbi yanzu. Haka kuma baitocin sun ba da hoton bayanin irin raunin da wannan ɗan takara yake da shi a cikin sauran ‘yan takarar wannan kujera mai muhammanci. Ba ya da wata dabara ko madogara sai Allah (SWT). Don haka ne yake roƙonsa da ya aiko masa da taimakonsa don ya sami nasarar wannan zaɓe.

 Haka kuma, akwai wata waƙa tasa wadda ya tsara don addu’a mai ɗauke da irin wannan salo na zayyana, ga ta:

In nai zamana gida can ya bi ni,

In na hito sai ya taso shi ja ni,

In na ƙiya sai shi dai ɗunguje ni,

In na yi har kwance wai don shi bar ni,

Sai in ga dai ya yi ganwo shi ɗauka.

Ya sa kwaɗan duniya ya haƙe ni,

Ya ko tsare ko’ina ya hwake ni,

Ya zaburo yai farat ya riƙe ni,

Ya ko matsa ya hana min sukuni,

Ƙula-uzu Billahi shaiɗanu minka

 (Ummaru Wazirin Gwandu: “Waƙar Addu’a).

Baitocin da suka gabata suna zayyana muna irin matsalar da mawaƙin ya shiga ta yaƙi da shaiɗan, duk wata hanya da ya bi don ya guje wa makircinsa sai shaiɗan ya ɓullo masa wata hanya ta daban. Wannan ja-in-ja da ya shiga da shaiɗan ya tsoratar da mawaƙin don haka ne ya ga ba wata mafita sai dai ya kai ƙararsa ga Ubangiji Allah.

Salon Alamtawa

A wannan salon na siffantawa ana amfani ne da wani sashi na wani abu domin wannan sashen ya tsaya a matsayin dukan abin. Ko kuma amfani da kalma mai wata ma’ana ta daban ko bayan ma’anarta ta yau da kullum (Yahya 2006 :113). Wannan salo na daga cikin muhimman salailan da suka fi fice a cikin waƙoƙin addu’a. Misali dubi wannan baiti:

Allah iyakokinka inda na ƙetare,

Zunuban da nai Rahamanu kai min gafara,

Ba wanda zai min gafara bayan ka.

 (Alhaji Lawan mai Turare: “Waƙar komawa Ga Allah).

Salon alamtawa a nan shi ne a ɗango na farko wurin da ya siffanta zunuban da ya aikata da ƙetare iyaka. Kamar dai wanda ya ƙetare wata iyaka wadda aka shata masa, wato ya ƙarya doka. Haka kuma a cikin wannan waƙar mawaƙin ya sake yin amfani da salon alamtawa a inda yake cewa:

Neman kadarko wanda zan bi na tsallake,

Don kodayaushe tausayin kaina nake,

Ɓarnar da nai da yawa cikin gonarka.

A ɗango na ƙarshe ne ya yi amfani da salon alamata, a inda ya siffanta laifunka da ya yi da zunubbansa tamkar ɓarna a cikin gona.

Shi ma wannan mawaƙi ya yi amfani da salo irin na alamtawa a cikin wannan baiti da ke tafe:

Yanke ya dai bai don hakanga yas shirya tun farko,

Ya yi ganiyyi Al-mudabbirun yak ko yo kasko,

Babu mai amshewa ga wanda duk yab ba tun farko,

Komi jinkirin rabo zai zaka in dai kai ƙarko,

Ajizi luro da wanda yan nufe ka da yin har barwa.

(Ummaru sanda Sarkin Bauran Dange/Alƙali Haliru Wurno: “Allah Ma’ishin Bawa)

Idan aka dubi ɗango na biyu na wnanan baiti za a ga mawallafin ya yi amfani da salon alamtawa, a wurin da ya nuna Ubangiji Allah shi ne wanda ya halicci ganiyyi wato, mai arziki da kasko, wato talaka. Kalmar kasko a nan ita ce alamci da aka yi amfani da ita ga siffanta talaka.

 Haka kuma akwai wata waƙar mai jigo shigen wannan wadda mawaƙin ya yi amfani da salon alamtawa kamar haka.

Ya sarkin da yab ba Alu zaɓen tafiya ƙasar kufa,

Ya sarkin da yabba uban Isa nasara wurin yumfa,

Korena a sa mashi ganye in ga ya tofa,

Abin ga da nib biɗa sashi zo hannuna in ga na dafa,

Ka sa mishi aƙiba ya Ilahi/Arshi bibarkacin salla.

(Garba Gwandu: “Dogara Ga Allah Ya Fi Zuwa Fadanci).

A ɗango na uku ne ya yi amfani da salon alamtawa, a wurin da ya siffanta kansa da koren itace busashe saboda rashin samun ruwa. Haka kuma yana roƙon samun ni’ima da wadata, wadda ya siffanta da ganyen itace lif-lif.

Salon Kinaya

Wannan wani nau’i ne na salon siffantawa wanda Abdulƙadir Ɗangambo (1981), ya kira shi da sunan gajeruwar siffantawa. Yahya (1997/2000/2002), ya kira shi da sunan salon kinaya. Wannan salo a fagen nazarin waƙa na nufin mawaƙi ya kira wani abu da sunan wani abu daban. Yin haka zai sa mai sauraro ya ɗauki ma’anar wannan abin ko siffarsa tamkar wancan abin. Shi ma wannan salon ana samunsa a cikin waƙoƙin addu’a, mislai dubi wannan baitin.

Ga garinmu ban kwana daji,

Ga ka ban biɗar wani budoji,

Tun da na sani kai am munji,

Malja’inka nan nika dagewa.

 (Ummaru Wazirin Gwandu: “Zaɓaɓɓiya).

A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da salon kinaya har sau huɗu. Ya ce Ubangiji Allah shi ne birni kuma shi ne abin dogara. Sannan mawaƙin ya ce Wanda ba Allah ba, shi ne daji, haka kuma shi ne budoji, wato boka. A nan mawaƙin na nufin Allah shi ne ke da kowace irin wadata wadda ɗan adam yake biɗa, haka kuma shi ne madogra. Wanda ba shi ba shi ne daji wanda ba komi a cikinsa sai wahalhalu da rashin tsarewa daga halaka.

Wani misali mai shigen wannan salo shi ne,

Musawwiru gaffarun waƙahharu na kirai,

Jiyamini wahabbun ka ɗamre afolaki,

Mumitun kashe maƙiyi kashin duniya shi zam,

Ana yi shina kallo shi zan baya auraki.

 (Haliru Wurno: “Neman Tsari Daga Maƙiyi).

A cikin waɗannan baitoci guda biyu, mawaƙin ya yi amfani da salon kinaya. A nan ya siffanta maƙiyinsa da nau’in jaki mai suna afolaki da kuma wani nau’in mai suna auraki. Ya nuna cewa siffofin maƙiyansa da ayyukansa duka ɗaya suke da siffofin jakai. Ga wani misali,

Malikul-mulki ka jirkito su duk su tsaya baya na,

Ya Hafizun ka san haƙiƙa kai ɗai ne shinge na.

Gun ƙawiyyun nil laɓe ina mai cin donana,

Kai ne dangali garan kuma kai ne ƙumcina

Babu mai fasa shinginga nau tsaya ka jiya kai wawa.

 (Ummaru Sanda/Alkali Haliru: “Alah Ma’ishin Bawa).

A baitin da ya gabata kalmomin da na ja wa layi a ƙasansu, su ne waɗanda aka yi amfani da su ga salon kinaya.

Salon Kamance

Wannan babban salo na siffantawa ya kasu kashi uku; na daidaito, na fifiko sannan da na kasawa.

Kamancen Daidaito

Wannan shi ne kamance na salo; yakan kwatanta abin da ka riga ka sani ko wani abu wanda waƙa ke magana a kai da wani abu daban. To idan ya kawo ma hoton abin ko halinsa ko sifarsa a gabanka sai ya ce, to, yadda ka san wannan abin haka abin da wannan waƙa ke bayani a kai duk ɗaya suke ta wannan fuska. Yanzu ga misalin yadda salon yakan fito a cikin waƙoƙin addu’a. Duba wannan baiti:

Na san ban da mai ba ni sai Jabbaru ina da shi kullum,

Kullum na biɗai shi ka ban, kuma ba ni fashi bale zalum,

Na kuma lura shi ɗai ka bai kuma ba shi hana ba har kullum,

Na kuma farfaɗo hankalina ya koma kamar kullum,

Raina yai fari ƙal kamar nono ban ko ji zahi ba.

 (Ummaru wazirin Gwandu/Alhajin Mazuga: “Ginar Dutsi)

A ɗango na huɗu da na biayr na wannan baiti da ya gabata mawaƙin ya yi amfani da kalmomin mizani; “kamar” da “kamar”, waɗannan su ne suka bayyana cewa wannan salo ne na kamancen daidaito. A nan ya kamanta farin cikinsa da na launi irin na nono daidai suke, haka kuma shi ma hankalinsa da ada yake tashe, a yanzu kam ya kasance a natse kamar ba wata damuwa da ta taɓa samunsu. Har ila yau, a cikin wannan waƙar mawaƙin ya sake yin amfani da salon kamancen daidaito kamar haka:

Komi taliki bai da ƙarya ta ga wanda as sarki,

Mai abu ga shi to, mib bi ƙinƙaho, mai tamkacin jaki.

A nan ma ya kamanta ɗan Adam, wato mutum da jaki kanka suke ga mallakar wani abu ko ma wajen biyan bukata. Kalmar “tamkaci” ita ce mizanin mu.

Haka kuma a wata waƙar ta addu’a an yi amfani da salon kamace irin na daidaito, kamar haka:

Sanin haka ya sa tutut gare ka nike ƙarata,

Tsare ni ga manya ka tsar da ni kumyar tsarata,

Aduwaina Ƙadirun nufarsu da yin sauna ta,

Zama sun mame ni yau da gobe suna kabra ta,

Ka maishe su tibis garan su koma tamkar ɓawa.

(Ummaru Sanda S/Bauran Dange/Alƙali Haliru Wurno: “Allah Ma’ishin Bawa”).

A wannan baiti da ya gabata mawaƙin na yin addu’a zuwa ga Allah da ya ƙarya masa ƙarfin maƙiyansa su koma tamkar yadda ƙarfin ɓawan itace yake. Amfnai da kalmar mizani ta “tamka” ita ce ta nuna wannan salo ne kasance daidaito ne.

Mawaƙin wannan waƙa da ta gabata ya sake amfani da irin wannan salo, a wurin da yake cewa:

Kiyayyan nan wadda taz zaman mini tamkar taru,

Aduwwan nawa masu yo mini tohin Baru,

Kiren ƙarya kodayaushe masu kaɗa min turu,

Tsare ni ga sharrinsu in zamo musu tamkar guru,

Su taka su kare su bar ni ban raki don kowa.

Wannan baiti da ya gabata a ɗango na farko da na huɗu ne, mawaƙin ya yi amfani da kalma mizani mai nuna salon kamance irin na daidaito, a inda ya ce “tamkar”.

 Haka kuma akwai irin wannan misali a cikin wata waƙa ta addu’a mai shigen wannan jigon, a wurin da mawaƙi ke cewa:

Hafizu ka ɗaure la’imi in ya so yi min sharri,

Sharrin duk da yas so shi ƙulla bayyane ko cikin sirri,

Banye ƙulle-ƙullenshi mai san min suwa tamkacin hairi,

Koda ya rubtua a kece hissai ma cikin tsari,

Ka daƙushe ƙoƙarin duk da yay yi na sharri Jalla don salla.

(Garba Gwandu: “Dogara Ga Allah Ya Fi Zuwa Fadanci).

A ɗango na uku na wannan baiti mawaƙin ya yi amfnai da salon daidaito, wurin da yake cewa: “tamkacin” hairi. A nan ya roƙi Ubangiji Allah ya musanya masa da alhairi a duk lokacin da maƙiya suka ƙulla masa sharri. A ƙarshe ga wani misali:

Addau dini su zam kamar ba’a yo su ba,

A rasad da su su zamo kama da gubari.

(Mallam Mahe Ƙaura-Namoda: “Waƙar Addua’a).

 Duka dai waɗannan misalai da suka gabata, kalmomin mizani ne suka yi muna jagora ga fito da wannan salo na kamancen daidaito. Kalmomin kuwa sune “kamar”, da “tamkacin”, “tamkar”, “kama”, da “awa” da sauransu.

Kamancen Fifiko

Wannan kuwa salo ne da mawaƙi ke amfnai da shi a inda yake nuni da cewa wani abu na farko da ya kawo maka misalinsa ya fi wani abu wanda ka riga ka sani. A cikin waƙoƙin addu’a mawaƙa kan yi amfani da wannan salo a cikin waƙoƙinsu. Misali:

Shirin tafiya aljanna ‘yan uwa,

Ya fi hawan daba wajen ƙawa,

Dawaki an shirya su sai hawa,

Ba tsoho ciki babu tsohuwa,

Sun zan samari masu kyan ƙawa.

 (Muhammadu Umar Kwaren-Gamba: “Waƙar Roƙon Ruwa).

A cikin wannan baiti a ɗango na biyu ne mawaƙin ya yi amfani da salon kamancen fifiko ta amfani da kalmar mizani ta “fi”. Shi dai a nan yana bayani cewa shirin da za a yi na tafiya a shiga aljanna bayan an ƙare hisabi, a ranar lahira ya fi ƙawatarwa a bisa ga yadda ake shirin hawan daba a nan duniya.

 Haka ma mawaƙin ya ci gaba da yin amfani da irin wannan salon a cikin waƙarsa kamar haka:


Sai a kira mu a ƙara ce muna,

Yan mata na ciki an aje muna,

Nonna tsaitsaye sun fi tuluna,

Da shinfiɗɗu lantsan abin muna,

Ba’a ‘yan matan ba su ƙwaruwa.

Ga kuma wani wurin da yake cewa:

Babu abin da ka tada hankali,

Ciki muke kullum mai ta shagali,

Ga hasken shina ta ƙyaƙyali,

Hasken ya fi gaban na cocali,

Irin hasken har bai misaltuwa.

A cikin waɗannan baitoci guda biyu da suka gabata mawaƙin ya sake amfani da wannan salo na fifiko a ɗangon da ya kamanta nonnan ‘yan matan aljanna da cewa sun fi tululunan da muka riga muka sani waɗanda muke zuba ruwa a nan duniya. Na biyun kuma mawallafin ya bayyana hasken waɗancan ‘yan mata na aljanna da cewa ya fi na fitilar hannu ta cocilan. Kalmar “fi” da mawaƙin ya yi amfani da ita ita ce jagora da gane cewa wannan salo ne irin na “fifiko”.

 A wata waƙar mai kama da wannan ta addu’a mawallafinta ya yi amfani da irin wanann salo kamar haka:

Ya fi bom ya fi bindiga sharri,

Mai bugu shi yi iza shi yi shuri,

Shago farta gare shi da mari,

Har da rura garai da kirari,

Jalla tun ba mu taka ba kiyaye min shi.

(Ummaru wazirin Gwandu: “Waƙar Addu’ar Yunwar Shago”).

A wannan baiti da ya gabata tun a cikin ɗango na farko mawaƙin ya kawo muna salon fifiko ta amfnai da “fi” har sau biyu. Ya kamanta bugun wani ɗan dambe wai shi shago da cewa ya fi na tashin bom da ma na ita kanta bindiga ɓarna. A nan yana kwatanta ɓarnar waɗannan makamai ba ta kai ga ta wannan yunwa ɓarna ba, ga rayukan ɗan Adam. Haka kuma baitin ya kamanta bugun da shago yake yi ga abokan karawarsa, shi kuwa ya fi wannan yunwa ɓarna.

Kamancen Kasawa

Kamar dai wada taken sunan wannan salo ya nuna cewa na kasawa ne, a nan mawaƙi kan kwatanta abubuwa biyu, sai ya ce ɗaya bai kai ga ɗayan ba. Misali a wata waƙa wadda muka yi amfnai da ita ɗazu ga yadda mawaƙin ya yi amfani da salon kasawa:


Ya Allah ka ƙaro daɗin tsirarka ga Ahma komi duk,

Duk roƙon da yay yo gare ka karimi rirriɓa mai duk,

Don shi kaf fi so kay yi kab ba shi hairinka duk duk duk,

Allahumma sallim salaman bisa fiyayye duk,

Ahma wanda annabawanka ba su kai kama tai ba.

(Ummaru Wazirin Gwandu/Alhajin Mazuga: “Ginar Dutsi).

A baitin da ya gabata a ɗango na ƙarshe ne mawaƙin ya yi amfnai da salon kamancen kasawa. A nan ya bayyana cewa dukan Annabawa darajojinsu ba su kai na Annabi Muhammadu (SAW) ba. Kalmomin “ba su kai” su ne mizanin kamancen kasawa a wannan baiti.

Salon Jinsarwa

Salon jinsarwa a ra’ayin Yahya (2001) ko mutumtarwa (A. Ɗangambo 1981), shi kuwa wata dabara ce ta amfani da harshe a inda ake ɗora wa wani jinsi halayya ko daraja ko aikin wani jinsi daban da ba na shi ba. Saboda haka ne masana sun kasa wannan salo kashi uku: Mutumtarwa da dabbantarwa da abuntarwa.

Mutuntarwa

Wata halayya ko daraja ta mutum da aka ɗora wa abin da ba mutum ba, ita ce ake kira salon jinsarwa na Mutumtarwa. Ana samun wannan salo da yawa a cikin waƙoƙin Hausa da na addu’a, misali:

Jiya gaskiya yau ɗamre takkwana kurkuku,

Ana bata kashi anka sa mat awartaki.

 (Alƙali Haliru Wurno: Waƙar Neman Tsari Daga Maƙiyi).

A wannan baiti mawaƙin ya yi amfani da salon jinsarwa na Mutumtarwa da ya ce an ɗaure gaskiya har ma an saka ta a kurkuku. A zahirin gaskiya mutum ne ake kai kurkuku a ɗaure shi. A nan ya bai wa gaskiya daraja irin ta mutane da yake ya ce ita ma an daure ta a kurkuku. Haka ma wannan misali yake a wannan baitin:

Kowacce shina yi ku bar shi shi yo mun gane ƙarshenta,

Kunya za shi yi ba shi yin komi ai tun da ƙarya ta,

Mai jagora duk don ayo fitina shi an na tammnarta,

Ci nai za ta yi har ta nemo ƙari ba shi ƙwassheta,

Ya jama’ar Musulmi mu bar sharri shi yaf fi don salla.

 (Garba Gwandu: “Dogara Ga Allah Ya Fi Zuwa Fadanci).

A ɗango na uku zuwa na huɗu nan ne mawallafin wannan waƙa ya yi amfani da salon Mutumtarwa a inda ya ce duk wanda ya yi jagorancin ta da fitina shi ne za ta ci. A nan ya baiwa fitina darajar cin abinci wanda za ta ci har ta nema ƙari saboda ba ta ƙoshi ba. Ga al’ada mutum ne ko dabba ke cin abinci har ma ya nemo ƙari idan bai ƙoshi ba, amma ga shi mawaƙin ya ce fitina ita ma tana cin abinci.

Dabbantarwa

Mawaƙi kan ɗauki hali ko yanayi ko daraja ko ɗabi’oi ko aikin da dabba ce kaɗai aka sani da shi sai ya ɗora wannan abu a kan wani mutum. Misali dubi abin da wannan mawaƙi ke cewa:

Ruwa na sunka so su dume min kai ban ga ganga ba,

Har na fara cewa Habu na Habu ban kama kowa ba,

Na yo yad dabara da duk nika yi ban gane komi ba,

Don na fafaka ban ji duk wani reshe za shi hissan ba.

(Garba Gwandu: “Dogara Ga Allah Ya Fi Zuwa Fadanci).

A ɗango na (4) huɗu na wannan baiti a sama mawaƙin ya dabbantar da kansa inda ya ce ya faffaka. A zahiri tsuntsu ne aka san yana da diffike har ya yi amfani da su ya tashi sama ya faffaka. Amma sai ga shi ya baiwa kansa daraja da halayyar tsuntsaye. Wani misali kuma shi ne:

In yau Allah yaz zubo ruwa,

Sai ka ga dum mun tada kunnuwa

Maza har mata masu haihuwa

Bale dabba dum masu shan ruwa,

Sai murna Allahu yai ruwa.

(Malam Muhammadu Umar Kwaran-Gwamba: Waƙar Roƙon Ruwa).

A ɗango na biyu na wannan baiti da ya gabata mawaƙi ya dabbantar da ‘yan adam (mutane) wurin da ya nuna cewa sun tada kunnuwa. Wannan ɗabi’a ce ta dabbobi da suke tayar da kunnuwa a lokacin da suka ga abinci tafe. A ƙarshe ga kuma wannan misali:

Shago farta gare shi da mari,

Har da rura garai da kirari.

 (Alhaji Ummaru Wazirin Gwandu: “Yunwar Shago).

Abuntarwa

Wannan salo na nufin liƙa wa mutum hali ko ɗabi’a ko daraja ko kuma saka mutum cikin yanayi na wani abu wanda ba dabba ba (misali dutse ko ruwa ko mota). Misalin wannan a waƙoƙin addu’a shi ne:

Alƙahharu komi ka samu na ka san shi sarkina,

Kay yi nufin da kat tabbata shi garan in falke in kwana,

In kuma na ji tsoronka daidai na kai al Ilahina,

Amma na ji tsoro ƙwarai na hirgita don mahwalkina

Na katce ƙwarai walla na tsinke, rai bai yi daɗi ba.

(Alhaji Ummaru Nasarawa Wazirin Gwandu/Alhajin Mazuga: “Ginar Dutsi).

Dango na karshe mawaƙin ya liƙa wa kansa ɗabi’a irin ta igiya ko tsawo wanda shi ne ke katcewa ko tsinke wa idan har ya ji tsauri. Sai ga shi mawallafin ya saka wa kansa wannan ɗabi’a don haka a nan ya yi amfani da wannan salon na abuntarwa.

Kammalawa

Wannan takarda ta tattauna ne a kan wasu fitattun salailai da ake iya samu cikin waƙoƙin addu’a na Hausa, musamman ma salon siffantawa wanda ya ƙunshi salailai da dama kamar salon zayyana da alamtawa da kinaya da salon kamance da kashe-kashensa tare da misalan waƙoƙi da suke tabbatar da kasancewar salon siffantawa salo ne da yake da bazaarsa ne mawaƙa ke taka rawa.

 A nan za a taƙaita ga tattaunawa kan salon siffantawa a cikin rubutattu waƙoƙin addu’a na Hausa, ba wai don waɗannan da aka kawo misalinsu ba su kaɗai ba ne. Akwai ire-iren salailai da yawa da ba a taɓo ba. Don haka wannan bincike wata matashiya ce ga masu nazari a kan rubutattun waƙoƙin Hausa gaba ɗaya da kuma na addu’a a keɓance.

Manazarta

Ainu, H.A. (2007), " Rubutattun Waƙoƙin Addu’a Na Hausa, Nazarin Jigoginsu Da Salailansu, Kundin Digirin Ph,D. Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.

CNHN (1977), Waƙa A Bakin Mai Ita I Zaria NNPC

CNHN (1977), Waƙa A Bakin Mai Ita II Zaria NNPC

C.N.H. (2007), Wa’azu Gonar Malam, Diwanin Waƙoƙin Ummaru Nasarawa UDUS Press, Sakkwato

Ɗangambo, A. (1980), “Hausa Wa’azi Verse From C.A. 1800-C.A. 1970 A Critical Study of Form, Language and style:, kundin digiri Ph,D. London S.O.A.S.

Ɗangambo, A. (1981), "Daurayar Gadon Feɗe Waƙa", Kano, Jami’ar Bayero

Ɗangambo, A. (1984), "Rabe-raben Adabin Hausa Da Muhimmancinsa Ga Rayuwar Hausawa, Kano Triumph.

Ɗangambo, A. (2007), "Daurayar Gadon Feɗe Waƙa (Sabon Salo)", Amana Publishers Limited New Kano Road, B.O. Box 1265, Zaria, Kaduna State, Nigeria.

Gusau, S.M. (1995), Dubarun Nazarin Adabin Hausa, Kaduna FISBAS Media Services.

Ibrahim, M.A (1984), Aƙali Halliru Wurno Da Waƙoƙinsa”, kundin digirin B.A. Sokoto, Jami’ar Sakkwato.

Yahaya, I.Y. (1988), Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce – Rubucen Cikin Hausa Zaria: NNPC.

Yahya, A.B. (1997), Jigon Nazarin Waƙa, Kaduna FISBAS Media Services.

Yahya, A.B. (2001), "Dangantakar Waƙa Da Tarbiyyar ‘Ya’yan Hausawa", cikin Harsunan Nijeriya, Na xix, CNHN, Jami’ar Bayero, Kano.

Yahya, A. B. (2016) Salo Asirin Waƙa (sabon bugu), Sokoto: Guaranty Printers.

 Degel Journal

The official website of the DEGEL Jounal is https://www.degeljournal.com

Post a Comment

0 Comments