Ticker

6/recent/ticker-posts

Idan Mutum Ya Sadu Da Iyalinsa Sannan Yaso Yasake Komawa Sai ya yi Wanka?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan Mace Ta Sadu Da Mijinta Sai Bayan Sungama Sai ya Sake Neman Yasadu Da Ita, Shin Sai sun yi Wanka Za su Kara Saduwa Kokuwa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

Sunnah ne ga namiji idan yasadu da iyalinsa sannan yai nufin sake saduwa da ita ya yi alwala tsakanin saduwa biyun, amma dazai wanka shi ne yafi.

Daka Abu sa'idul khudri Allah yakara masa yarda ya ce: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Idan ɗayanku yajewa iyalinsa sannan yaso yasake komawa ya yi alwala tsakaninsu ) Muslim (466).

Awata ruwaya ta Ahmad (Alwalar Sallah ) Arna-Uud ya inganta isnadin ruwayar yayinda yake ta'aliƙin musnad Ahmad (3/28).

Shaiek Usaimeen rahimahullah ya ce: halaye ukune mutum kedasu anan.

1. ya yi wanka kafin yakoma wannan shi ne yafi kamala.

2. Inyaga dama ya yi alwala kafin yakoma wannan baikai wanka kamala ba.

3. Yakoma ba tare da ya yi wanka ko alwala ba, shi ne karshen daraja, amma ja'izine.

Abun da ya kamata shi ne kada suyi bacci sai sun yi ɗaya cikin biyu alwala ko wanka.

Majmu'u fatawa (11/167).

Fatawa lajnatul da'imah sukace: Alwala sunnah ce ga maza yayin komawa yin jima'i, an shar'anta alwalar ga mazane kawai domin su aka umarta banda mata.

Fatawa lajnatul da'imah (19/350).

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments